KISSA KO MAKIRCI Page 41 to 50 (The End)

Salma ta shiga dakin da sallama, salamatu ta amsa tare da fadin sannu aunty yanzu nake son inzo wajanki inji koh kina son wani abu, salma tayi dariya tare da fadin ina mama? Tace tana bayi, nan salma ta zauna suna ta fira da takwaranta, har mmn ta fito daka bayi, salma tace sannu mm nan tayi murmushi tare da fadin yauwa ya jikin naki? Salma tace da sauki, nan taci gaba da magana gobe da safe zaki shirya zaku asibiti Dr ya duba ki, mmn ta kalli salma da mamaki ya akai tasan bata da lafiya, ko dai taji warin da takeyi ne, salma ta katseta da fadin salma ta fadamin komai, insha Allah zaki warke kuma za’a dace da yardan Allah, mmn tace ngd Allah ya saka da alkairi, da ana samun irinku masu taimako da talaka yaji dadi, Allah ya kara arxiki salma ta amsa da ameen, salamatu tace aunty Allah ya saka miki da gidan aljanna, ina son mmn ita daya ta rage min, ita nake gani inji dadi, ciwon yana damunta sosai, bani da wani Jin dadi, kullum ina kwana da fargaba, Amma a yau zanyi bacci cikin Jin dadi, salma idonta ya ciko da kwalla tace takwara ta insha Allah komai zai wuce babu abunda zai sameta kici gaba da addu’a, sun dan taba fira sannan ta tashi ta nufi gefensu,
Fauxiya gaba daya, ta shiga damuwa komai tayi baya yi, gashi tana ta kashe kudi, harta gidajan da take dashi ta saida, dan dai kawai taga ta sami Mahmud, sannan abun dake cikin salma yaxo bada rai ba, indai taje wajan boka ko nawa yace zata bashi dan dai taga ta sami biyan bukata, Amma kullum kaman ana kara sama Mahmud tsanarta, ga hjy binta itama yanzu ta dawo wajan salma, komai tasa ayi a kanta shima yaki aiki, Amma duk da haka Fauxiya bata saduda ba, ita da mahaifiyarta.
Washe gari da safe, kaman yanda Mahmud yace za’a kai su asibiti, hakan ko akayi, salma tace ya bari suje tare yace a’a baya son tana fita kar wani abu ya sami baby dinshi haka ta hakura, driver ya kaisu Mahmud yace ya tsaya ya musu komai, hakan ko akayi, sunje Dr ya dubata, yaga dayan wajan da aka yanke, sai kuma dayan daya kama, yace dole sai an miki aiki ta wajan gefen breast dinta akwai wani bkin abu daya fito, shima yace za’a yanke shi, tace Dr Idan aka cire zan warke kuwa? Yace insha Allah, nan tace toh ta yarda, yace taxo jibi a mata aikin nan suka tashi suka fita, ita dai salamatu gaba daya hankalinta bai kwanta da wannan aikin ba, sun dawo sunma salma bayani, ta fadama Mahmud ya bama driver kudi yace ya biya komai da komai, kafin jibi din,matar gaba daya ta shiga cikin damuwa, tun da suka dawo babu abunda take sai tagumi da hawaye, salamatu itama ta shiga damuwa, tana ta rarrashi amma sai tace ina ganin kaman bazan tashi ba, yarinyar ta tashi da sauri tana kuka tayi gefen su salma, a nan ta ganta ita da Mahmud a falo, salma ganin yanda ta shigo cikin tashin hankali tana kuka, yasa tace salma lafiya kuwa? Maiya faru? Tace mama,… Ta kasa magana nan salma tace maiya sameta? Mahmud yace muje mu gani, suka fita sukai dakin suka ganta tana ta kuka , salma ta matsa kusa da ita tace mm maiya faru wani abu aka miki? Tayi dan murmushi tace babu ko daya ina ganin kaman wannan ciwon nawa bazan tashi ba, ina tausaya ma yarinyar nan ban san wani hali zata shiga ba, bata da kowa sai ni, salma tace mama ki daina fadin haka cuta fah ba mutuwa bane, tayi murmushi tace hakane ta kama hannun salma tace dan Allah kimin alkawari koda na mutu ban tashi ba ki rike min yarinyar nan,har zuwa sanda za tayi aure, salma ta waiga ta kalli Mahmud ya daga mata kai alaman eh, tace nayi miki alkawari zan riketa amana, balle ma insha Allah zaki tashi, tace ngd Allah ya saka miki da alkairi, salma wani kwalla ya zubo mata ta amsa da ameen, salamatu babu abunda take sai kuka, salma ta rarrasheta tare da fada mata cuta ba mutuwa bane, tayi hakuri,
Kaman yanda Dr yace su koma, haka suka shirya suka tafi, wannan karan harda salma, an kaita dakin theater, nan Dr uku suka shiga, salamatu gaba daya jikinta yayi snyi tana tuna abunda ta fad’a mata jiya, da daddare ko bayan raina inaso ki zauna da wannan baiwar Allah bisa amana ki dauketa tamkar ciki daya kuka fito, sannan ki rike maraicin ki dan Allah kar ki manta ko ke wacece, salma ce ta katse ta tare da dafa ta, tace kiyi hakuri insha Allah zata tashi, Dr sunyi wajan 3hr kafin suka fito ko wanne a sanyaye, salamatu tana ganinsu ta tashi da sauri tana tambaya ya jikin mmnta? Duka suka mata shuru, har salma ta karaso tace Dr ya jikin nata da fatan anyi a sa’a, daya daka cikin Dr din yace hajiya sai dai kuyi hakuri Allah ya mata rasuwa, salamatu ta saki ihu tare da fadiwa kasa sumamma, nan aka dauketa akai emergency da ita, aka bata taimakon gaggawa cikin ikon Allah ta farfado, salma na kusa da ita tace aunty dagaske mmna ta rasu bazan sake ganinta ba, nan salma ta rike mata hannu tana fadin kiyi hakuri duk mai rai mamaci ne, muma lokaci muke jira, yanzu kibar wannan kukan addu’a take bukata, tace aunty ban taba zata mmna zata rasu yanzu ba, mai yasa ni mutuwa bata daukeni ba, salma ta toshe mata baki tare da fadin kar kiyi sabo, salamatu Allah baya barin wani dan wani yaji dadi, ki mata addu’a Allah ya gafarta mata, a dai2 nan Mahmud ya shigo, gaba daya yarinyar ta bashi tausayi, ya mata gaisuwa tare da mata nasiha daka karshe yace bari su tafi dan a mata sutura, nan salamatu ta sauko tace su wuce tare, taga mahaifiyarta na karshe, hakan ko akayi Dr yace zata iya tafiya, gidan hjy binta suka nufa ga mutane sun taru, an mata sutura aka kaita gidanta na gaskiya duk wanda yaga salamatu saiya tausaya mata, musamman salma da aka bama amanarta itace yanzu uwa a gareta, saida akai uku suka koma gidansu, Fauxiya ko lekowa ba tayi ba, bayan sun koma aka gyarama salamatu wani daki a gefen su salma, kullum zaka ganta tayi shuru tana tunani salma intaga haka taita mata nasiha,
Cikin salma ya kai wata7 Mahmud kullum inya fita yaga kayan yara saiya siya na mata dana maza, salma inya kawo kayan tayi ta dariya, Fauxiya gaba daya ta fita hayyacinta domin yanzu komai nata ya kare malamanta duk sun cinye kudin, amma duk da haka bata saduda ba, tana ganin za tayi nasara dan ta rasa wannan inta kara mallake Mahmud zata sami wanda ya fishi,. Yayin da salamatu take zama tare da Salma,wata rana suna fira salma take ce mata wai salamatu kina da saurayi kuwa, tayi dan murmushi tace a’a aunty bani da kowa, ni bama na sha’awan saurayi domin maza basu da kirki, amma ke kinyi dace, inda zan sami irin namiji mai halin mijinki dana more, salma tayi shuru tana kallonta, har salamatu ta lura da shurun yayi yawa, sai taji wani iri akan maganan data mata, tace aunty kiyi hakuri inna bata miki rai, salma tayi dariya tace zaki auri mijina……? Cikin zabura salamatu ta dago tana kallonta…….
Maryam Obam????
????????????KISSA KO MAKIRCI????????????
NA
MARYAM ALHASSAN DAN’IYA
(Mrs nura kuriga)
90to95
Girgiza mata kai ta fara yi, alaman a’a, salma tace takwara dagaske nake miki, ba wasa ba, sai a sannan salamatu ta sami daman magana tace aunty dan Allah kar ki karamin wannan maganan abune da bazai yiwu ba, bazan iya auran mijinki ba, ko a mafarki balle a zahiri, salma tace kina nufin bakya son shi?? Tace bawai bana son shiba, kodan taimakon da kuka min dole in soshi , balle ma akwai soyayya na musulunci, salma tace toh miye a aibun aurenshi bayan kince kina son namiji mai irin halinshi, salamatu tace haka ne, samun namiji irin shi sai an tona, amma bazan iya auranshi ba dan aunty kinyi katangar karfe a tsakani ko hauka nakeyi bazan taba auran mijin da kika aura ba, salma tace kenan ni bani da ikon in miki zabi? Shuru tayi tana hawaye tace aunty kina dashi, kece uwata kece ubana, kina da iko dani amma….. Ta dakatar da ita tare da fadin tunda ina da iko bana son in kuma ji kince bakya so, ta daga mata kai alaman toh, ta sannan ta tashi dasauri tabar wajan, salma ta bita da ido tare da tausaya mata, tace salamatu wannan shine gatan da zan miki amana abune mai wuya, na amsa amanarki, ban san mijin da zaki kawo ba, inma nace zan xaba miki ban San ya halinshi yake ba, Amma nawa mijin nasan koshi waye, nasan halinshi, nasan bazai cutar dake ba, auran Mahmud shi zaisa in sami kwanciyan hankali muna tare, jin an taba ta tayi firgit ta waiga taga Mahmud ne, ya hura mata ido tare da fadin tunanin mai kikeyi haka? Murmushi tayi tare da fadin yaushe ka shigo? Yace tun dazu nayi wajan 5mnt akanki Amma baki sani ba, kina ta tunani, lafiya kuwa? Tayi Murmushi tare da fadin lafiya dear muje kayi dinner, kai tsaye danning suka nufa, ta tashi zata zuba mai abinci yace ta zauna zai sa dakanshi, dariya tayi tare da zama ya zuba a plate ya dawo kusa da ita, yana bata shima yana ci, har suka koshi, fauziya ce ta shigo cikin fushi sukai ido hudu da Mahmud ga salma a jikinshi tana ta faman yi mishi shagwaba, haushin nata ya kuma karuwa taje ta janyo salma ta tureta salma ta saki kara, Allah yaso akan kujera ta fadi, nan Mahmud ya tashi ya wanke ta damari tare da fadin ke mahaukaciyar inace, tace ta gidanku wannan tso…… Kafin ta karasa ya kuma kwasheta da mari, yace kije na sakeki saki uku, mara tarbiya, ta cakume shi tana fadin wlh baka isa ba, yau ko ni ko kai saina kashe ka sannan in kashe wancan yar iskan da abunda yake cikinta, hjy binta data shigo da kaya niki2 na baby ta kawo ma salma, tazo taji ana rigima ana za’a kashe mata d’a da jika nan ta kira police, suka shigo gidan tace ku kama min ita, fauziya da mamaki tace wlh baki isa ba, ai zan fito sai na kashe ku wlh, nan police suka tasa keyarta sukai gaba da ita, salma gaba daya ta shiga cikin tashin hankali hjy binta ta matsa kusa da ita, tana fadin sannu y’ata bata dai taba kiba ko? Kafin salma tayi magana nan Mahmud ya fara bata labarin farkon abunda ya faru, hjy binta tayi Shuru tare da fadin kayi hakuri duk ni naja maka, na tsani matarka haka kawai ba tare da tamin komai ba,, inata matsa maka kayi aure, gashi na baka yar’uwarka tana kirarin zata kashe mu, hjy binta harda hawaye, tace ma salma dan Allah ki yafe min duk abunda na miki, salma tace mm baki min komai ba, kefa mahaifiyata ce,, komai kika min kin isa ne, ban taba rikeki a raina ba, hjy binta cikin kuka tace ngd Allah ya miki albarka ya saukeki lafiya, salma ta amsa da ameen, Mahmud yau yana cikin farin ciki ya rabu da fauziya zai zauna daka shi sai matarshi, suna ta fira, hjy binta tace ina yar amananki? salma tace tana daki, hjy binta tace Allah sarki, bari inzo in wuce dare yayi, ga kaya can dazu na amso su, nace bari in kawo shine naji wannan bala’in, kayan baby ne masu tsadan gaske, ta tashi, suka rakata har mota sannan suka dawo,yanxu gida ya dawo na salma sunsha love ranan ita da Mahmud duk da ta nuna Mai bai kamata ya saki fauziya har saki uku ba,