KISSA KO MAKIRCI 1-END

KISSA KO MAKIRCI Page 41 to 50 (The End)

Washe gari da safe, suna breakfast, salma ta kalli Mahmud tace ya kamata kaje kasa a saki fauziya, ya bata fuska tare da fadin dan Allah salma kar ki karamin maganan fauziya a nan, tace shikenan bazan kara ba, kayi hakuri plz, yayi Murmushi yace matar da take ikirarin kashe ki, shine har kike tausaya mata, dole sai an hukunta ta, salma dai Shuru Tayi, amma inda za’a nata da an barta da hlinta an saketa, zata hadu da dai2 ita, Indai duniya ce wanda bai zoba ma tana jiranshi balle wanda yake cikinta, Mahmud ya katseta da fadin yau kina da zuwa hspt ki tashi muje, tace toh ta kira salamatu suka fita, bayan ya kaisu asibitin yace bari yaje ya dawo Kafin su gama, tace toh, kai tsaye gidansu yayi nan yaga hjy zaliha tana ta bama hjy binta hakuri akan a saki fauziya, hjy binta tayi banza da ita, ganin Mahmud yasa ta fara fadin dan Allah dana kayi hakuri kasa a saketa, hjy binta tace ai babu ruwanshi a wannan maganan, bai isa yayi komai ba sai yanda nace, hjy zaliha cikin fushi tace shikenan in baki sa an saketa ta dadi ba, zaki sa a saketa ta wuya, ta fita fuuuuu, hjy binta tace ina jiranki, Mahmud ya gaidata ta amsa sannan ya zauna, yace mm ni a nawa ganin da ansa an saketa ko dan xumuncin dake tsakani, hjy binta tace hakane amma ba yanzu ba sai naga abunda zaliha za tayi, yace kar ki biye mata bacin rai yasa ta fadi haka, nan Mahmud ya shawo kanta ta yarda, sannan ta dauki waya ta kira police ta bada umarnin a saketa,Mahmud yace bari ya koma hspt yabar salma acan, tace ita daya dan mai zaka barta, yace ita da wannan yarinyar ne, tace oho toh maza ka koma hala sun gama, ya tashi ya fita. 

Fauziya gidansu tayi, hjy zaliha tana falo a zaune, taganta tace fauziya ya akai kika fito, tace haka kawai suka ce inzo in wuce Kuma gidan iyayena zani, kar ince zani gidan Mahmud, hjy zaliha tace bari zanyi maganin su wlh, duk da ya sakeki sai na wulakanta hjy binta ita da danta wlh, fauziya tace ko ke baki haka ba ni sai nayi, matsala ta daya shine banda kudi a hannu ina ganin gidan nan zamu sa a kasuwa, hjy zaliha tace toh ina zamu zauna? Tace haya zamu kama a hankali na siya mana wani amma yanzu ina bukatar kudi, hjy zaliha tace ai kiyi duk abunda ya dace, akwai wani boka a maiduguri dana sami labarinshi ance wlh inya maka aiki Kafin ya karye sai anyi dagaske, fauziya tace toh sai muje can yanzu ki kira dillali ki fada mai gidan nan a kasuwa yake, hjy zaliha tace an gama, 

Mahmud suna daki shida salma, ta kalleshi tace dear, ya amsa da na’am, tayi Shuru na wani lokaci, yace ya naji kinyi Shuru inaji, tace inaso kamin wani Abu guda daya, yace salma koma guda dari ne zan miki Indai kina so, tayi Murmushi tare da fadin kayi alkawari yace yes nayi, tace toh dama ina so ne ka auri salamatu, tashi yayi tare da fadin what????……….. 

Maryam obam????

????????????KISSA KO MAKIRCI????????????

                 NA

MARYAM ALHASSAN DAN’IYA

(Mrs nura kuriga)

                  95to100

Lokaci daya yayi murmushi tare da fadin, wannan wani irin wasa ne salma? Kar ki mata we are not in April fah, balle kice kina fooling dina ne, itama murmushin tayi tare da fadin dear am serious, ba wasa nake ba, ina so ka aur……… Daga mata hannu yayi alaman tayi shuru ya tamke fuska, yace salma daka yau bana son ki karamin wannan maganan indai baso kike kiga fushi naba, tashi tayi tazo kusa dashi tana hawaye tare da rike mai hannu, ganin tana hawaye yasa yaji wani iri, tace dear kayi hakuri ban fadi haka dan in bata maka raiba, ban kuma fadi hakan ba sai da nayi tunani sosai akai, kuma kar ka manta kamin alkawari komai na fada zakamin, yace look salma bawai inaso ayi ta wannan maganan ba, ki bari zan duba mata miji wanda zai aureta kinji, tace Idan ka duba mata miji, shin mai kalan halinka ne? Koh kuma zai iya riketa kaman yanda kai zaka iya,? Yace shuru yayi yana kallonta, Lokaci daya yace salma bari kiji koda ba iri na bane karki manta akwai wanda suka fini, kiyi hakuri kibar wannan maganan plz, shuru tayi tare da matsawa daka kusa dashi ta juya baya tana kuka mai kara kadan, tace wannan ne Karo na farko dana taba nuna ina son abu kaki min, gaba daya jikinshi yayi sanyi, taci gaba da cewa wanda ko a mafarki bazan taba yarda zaka ki abun dani nake so ba, matsowa yayi kusa da ita tare da janyota jikinshi yace salma mai yasa kike son in aureta? Tace Mahmud yarinyar nan amana aka bani ita, kuma ta isa aure, bata da saurayi tace tana son namiji mai hali mai kyau, ni kuma nasan nawa mijin yana da hali mai kyau, sai yasa naga ya dace kai ka aureta, ance imanin dayanku baya cika har sai yaso ma dan’uwanshi abunda yaso ma kansa,Mahmud kai nake so kuma nake ganin nayi dacen miji, dan mai zaisa inki so ka aureta tunda nasan halinka, tace dan Allah ka yarda hakan zai sani farin ciki, yayi shuru har na wajan minti hudu, babu abunda yake kara a dakin sai sautin kukan salma, yayinda yake ji har cikin zuciyarshi, yace shikenan tun da haka kika ce na amince, amma ki sani bazan aureta ba har sai an nemo dangin ta, cikin murmushi tace kar ka damu wannan mai sauki ne, tace ngd Mahmud Allah ya barmu tare ya baka ikon yi mana adalci,.

Fauziya sun saida gidansu, a ranan da aka biya kudin sukai maiduguri wajan sabon boka, Fauziya ji take kaman mota baya sauri, dan ta kosa ta ganta a gabanshi dan tana ganin Idan taje duk wani matsalanta ya tafi kenan, gudu suke zubawa, karan harbi sukaji an fasa musu taya nan motar ta fadi ta fara kundun bala ta tsaya ta cikin daji, har ta tsaya, yan fashin suka karasa motar tana kife da yake suna da yawa sun kai su goma sha biyar, suka fara kokarin daga motar, cikin ikon Allah suka daga ta, yayinda duk yan motan sunji jiki wasu kuma sun mutu, ciki harda Fauziya wanda ta rasu hjy zaliha kuma kafanta daya ya karye ga harshenta ya datse, driver dinma ya rasu da wanda suke gaba, bai fi mutum uku suka rayu ba, nan yan fashin suka dibe duka kayan motar, suka wuce, hjy zaliha ganin fauxiya bata motsi ta tabbatar ta rasu, gashi ita babu daman magana babu baki harshe ya datse da karfe ga karaya a kafa kuka take kaman zararra tana takaici, namiji daya sai mata biyu suka rayu suma duk sunji jiki sai hjy zaliha, nan namijin ya fita dakyar yana tsayar da mota amma kowa yki tsayawa sai wani mai motar albasa ya tsaya, nan ya mishi bayani abun daya faru yana ta salati yace ina sauran? Yace suna ciki, nan yace bari ya karasa gaba kadan akwai gari sai a sanar da sarki, hakan Koh akayi aka kira sarki da mutan gari, da yan sanda aka kwashe wa inda suka mutu, aka kira tashar motar aka sanar domin su kira yan uwansu ita dai fauxiya anan aka birne ta, yayin da wasu yan uwansu sun zo an tafi dagawarsu, hjy zaliha kuma an daure mata kafa, hmm rayuwa kenan hausawa na cewa in zaka gina ramin mugunta gina shi gajere wata kila kai zaka fad’a,hjy zaliha tana gidan mai gari, babu abunda take sai kuka tare da nadama tana fadin na cuceki fauxiya na bata ki dabin malamai kin mutu akan turban, matan maigari in suka ga tana kukan suyi ta tausaya mata, 

Hjy binta da Mahmud yayi maganan auren taki yarda tace sam bata amince ba, akan me zai kara aure yama rasa wacce zai aura sai wannan yarinyar da ba’a san kowa nata ba, gwara ka zauna da salma ita daya yafi maka, yace mama salma ce ta matsa min akan in aureta, nan hjy binta tace bana son wasa, ya fad’a mata komai nan tayi shuru tare da fadin lallai salma wannan abun da take shirin yi ban taba gani ba, gaskiya tana da xuciya mai kyau, amma baka san dangin yarinyar ba, yace eh salma tasa anyi bincike akwai wani yayan babanta yace babu komai shiya amince, yanzu turawa kawai za’ayi da komai a daura, tace toh Allah ya tabbatar da alkairi ya amsa da ameen, 

Previous page 1 2 3 4Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button