NOVELSUncategorized

KUNGIYAR ASIRI 1-2

????????????????????????
????????????????????????
☠ƘUNGIYAR ASIRI☠ 
????????????????????????
????????????????????????

       NA

          L££MAT


  Sadaukarwa gare ku????????
MUHAMMAD KAREEM KD(DADDY)

REAL HASEENA NABULISI BAKO(DR OGANNIYA)

{ƙirƙirarren labari}

????1-2
         Wata mace ce  wacce ba zata haura shekaru talatin da biyar ba a duniya  cikin kitchen tana ta yanke yanken da alama girki zata ɗaura tana sauri sai faɗin take,”Mami dear miko mun cabbage cikin fridge..,shiru babu amsa”

“Mami!!!”ta furta da ƙarfi 
 “me kike tunani haka tun dazu ina magana bakya jina”? 

Murmushi yar yarinyar da ba zata wuce shekaru goma ba tayi tare da sauke ajiyar zuciya!
  “mum kin san me”? amsa mata tayi da
 “A’a sai kin faɗa!”

“Kawai nayi wani tunani ne akan wukar dake hanun ki kamar na amshe na soƙa maki a ƙahon zuciya sai in jawo shi har cikin ki da ƙarfi sai kawai jini ya fara fita kina bani hakuri ina ƙara chaka maki shi sai naji bakya numfashi sanan in kwashe kayan cikin ki in zauna inaci a matsayin abinci,jinin kuwa ya zamo ruwan sha na”!!
Tana kai nan,ta fashe da wani irin dariya mai ban mamaki….

Hannu biyu zainab ta ɗaura a kai tare da kurma ihu har sai da Muhammad mijinta dake parlour ya shigo a guje yana faɗin”lafiya dai sweet?”

 Mami ta nuna mashi tana hawaye tare da girgiza kai….

Cike da tsoro ya rungume yar shi yana tambayar ta
  “menene ya same ki mami na”?

Dariya ta ƙara yi sanan ta maimaita mashi abinda ta gama faɗa kuma tana kwatanta yadda zata yi amfani da wukar a cikin mum d’in ta…

 “Subhanallah,kada ki sake irin wanan hasashe bashi da amfani kwata kwata kin ji mamata”? haka ya fadi cikin tsantar mamaki..
 Kuka ta fashe da shi tana fadin 
  “Gaskiya ba zan yarda ba ni daddy kullum idan inason yin abinda zuciyata ke so sai ka rinƙa hana ni”!katse ta yayi ta hanyar cewa

“Shiiiiii!,kada ki sake faɗin haka domin zuciyar ki a kullum babu abinda take dasa maki sai mugun nufi wanda ba daidai bane,yanzu canza kaya mu fita ki sha ice cream ko”?da murnar ta ta ce

“Yeeeeeeeeeeeh,shi yasa nake sonka Daddy saboda kafi mum sona kuma idan na shiga
ƘUNGIYAR ASIRI ba zan sha jinin ka ba,ke kuma”ta nuna mum ɗin ta”,Sai na farka cikin ki da wuka na cinye naman ki ɗanye”!!tana kai wa nan ta ruga zuwa d’akin ta….

Kuka mai ciwo zainab ta fashe dashi sosai, gaskiya lamarin yarinyar nan yana bata  tsoro sosai kullum abu sai gaba yake yi?
 “Kana ji fa bata da magana sai zama yar ƘUNGIYAR ASIRI”!?abin da Zainab ta fada kenan cikin karayar zuciya.. 

Rungume ta yayi sosai yana shafa bayanta cikin tsigar rarashi yake fadin..,
  “Ki yi shiru haka nan zainab quruciya ke damin Mami kuma babu abinda zai faru dake  da iznin Allah kin ji”?

Alamar shigowar ta suka ji…tana sanye cikin doguwar riga yar kanti wace ta wuce  gwiwa kaɗan, sai head band sumanta a nade tsakiya wanda hakan ya ƙara mata kyau ainun.

 Shiru ya biyo baya,suna ƙare mata kallo cikin so da kauna.

 Murmushi suka sakar wa juna  da dad d’in ta yace.. 
 “My angel kinyi kyau sosai!”.
 “Thank you daddy na”abin da ta ce kenan daga haka ya riƙe hanunta yana faɗin 
 “Honey sai mun dawo ko”?

Hannu kawai ta daga masu zuciyarta a dagule har taji tashin motar shi alamar sun fice daga gidan ba tare da wata ƙwaƙwarar motsi ba!

Kashe gas cooker tayi tare da yin zaman dirshan a kitchen ɗin tana cigaba da kuka tare da waiwayen rayuwar su na baya.


*******
        Zainab shanono shine asalin sunan ta,iyayenta yan Kazaure ne suna da rufin asiri irin nasu wanda hakan ya basu daman kula da tarbiyyar ta da sauran yan uwanta har ta samu ingantaccen ilimi zuwa matakin karatun jami’a!

 Kwatsam Allah ya haɗa ta da Muhammad a wurin bautar ƙasa a garin Abuja  inda soyayya mai ƙarfi ta ƙullu a tsakanin su.

Ba’a ɗauki lokaci mai tsayi ba iyaye suka shigo kan gaba akayi shagulgula mara misaltuwa!,Tun daga lokacin zainab ta samu karɓuwa wurin ahalin mijinta,gefe ɗaya kuma rayuwar aure mai cike da dimbin kyautatawa juna da kulawa suke gudanarwa a gidan su.

Matsala ta farko da suka fara fuskanta shine rashin haihuwa!

Wanda mahaifiyar Muhammad ta fara nuna damuwarta ƙarara.., basu ɗauki abun da wani muhimmanci ba domin sun riga sun tsara yadda zasu gudanar da rayuwar su!

 Kwanaki na tafiya,shekaru na ja, ma’auratan suka  fara shiga damuwa, duba da yadda dangin miji suka sata a gaba da habaici iri iri…

Wasa wasa har suka shekara biyar da aure babu labarin haihuwa,wanan dalili yasa mahaifiyar Muhammad ta shata mashi layi akan koya saki zainab ya auro wacce zata haifa mata jika,ko ta tsine mashi!

Faɗin irin tashin hankali da suka shiga ba’a magana!

A dalilin haka wata yar uwar Muhammad Dr faiza,wacce babban likitar mata ce tana aiki karkashin wani qungiya na turawa(UNICEF) a nan Abuja,shawara ta basu mai zai hana su same ta a Abuja akwai shawarwari da zata basu ko Allah zai saka su dace .

Ba tare da bata lokaci ba suka shirya zuwa offishin ta ….,,ta haɗa su da wani kwararran likita Bature  domin ayi masu gwaji na  musamman.
  Tun daga kan maniyi,jini zuwa fitsarin su babu wanda ba’a diba ba domin yin gwaji..

Lokacin da sakamako ya fito aka gano matsalar daga wurin  zainab ne saboda  ta taɓa amfani da wani hanya na tsarin iyali mai suna Tubal ligation(wata hanya ce da ake daure ko hana ko katse hanyar wucewar kwayayen halittar mahaifar mace da haduwa da maniyin da namiji da nufin hana daukar ciki),shine dalilin da yasa maniyyin mijinta baya wuce wa cikin mahaifa idan sun yi kwanciyar aure!.

A lokacin ne suka tuna dalilin da yasa suka yi tsarin iyali a farkon auren su domin zainab dake burin zuwa makarantar lauya domin cikar burin ta na zama cikakkiyar lauya.

Faɗa sosai Dr faiza tayi masu a matsayinta na babban likita kuma yar uwa a gare shi!.

Shawara biyu ta basu wanda sune kawai mafita a gare su;
  Na farko shine; IVF(wata hanya ce ake amfani da fertilized egg wanda ke aje  cikin lab a sakawa mace cikin uterus/mahaifa,iyaka ta raini cikin ta haihu).. 

Hanya ta biyu;shine artificial insemination (wanda za’a dibi sperm din mijin ki a haɗa da na wata mace sai a haɗa wuri ɗaya shima ayi placing cikin uterus din ki.

Akwai mata kala kala wanda suke bada maniyyin su a biya su, already an riga an masu Physical examination,an gwada jinin su tare da sperm analysis domin kariya daga cuta.

Tsoro ya kama zainab tana ganin kamar yiwa Allah shishigi ne a haɗa maniyyin mijin ta da na wata macen da ba muharraman shi ba a saka mata a mahaifa ta raina kuma ta haifa,kenan menene matsayin abinda zata haifa,ɗan halak ko shege?

Ganin hankalin ta ya tashi yasa Muhammad ya karfafa mata gwiwa a ganin shi wanan shine kawai mafita a gare su,idan kuma ta aminta a raba auren su shike nan su koma gida!

Babu shiri ta nuna amincewar ta ba don taso ba sai don kare martabar auren ta.

Cikin kankanin lokaci aka samo wacce zata bada maniyyin ta bayan an dibi nashi,an diba nata an auna yayi daidai aka saka wa zainab cikin uterus nata tare da basu shawarwari masu inganci.

Kuɗi Naira miliyan ɗaya ya biya na wanan aiki yana mai cike da farin ciki suka dawo gida..

Gare ku ma’aurata masu neman haihuwa ko ta halin yaya,wallahi wanan abun da turawa suka kirkira bai halarta ba a addinin musulunci,sanan kuma ire iren wanan shishigi da ake yiwa Ubangiji ke sa a haifi ɗan da zai zama fanɗararre a rasa gano inda ya kwaso mugun hali,bayan iyaye na matuƙar ƙoƙarin ganin sun bashi ingantacciyar tarbiyya!,wace aka haɗa maniyyin ta dana mijin ki har aka samar da ɗan basu san asali,nasaba,halaye da kuma dabi’unta ba.haihuwa,aure,mutuwa da arziki duka lokaci ne idan Allah bai baka ba,bawai ya manta dakai bane maybe rashin shi,shine mafi alheri a gare ka domin da wata haihuwar gwara babu wallahi


Tun daga lokacin da aka yi wanan aiki zainab bata sake samun cikakkiyar lafiya ba,azabar yau daban,na gobe daban!

Ga dai buri ya cika an samu ciki,yan uwa kowa na farin ciki amma ita kaɗai tasan azabar da take sha har ciki ya isa haihuwa da kyar ta haihu lafiya aka samu Baby girl mai kama da ubanta wacce taci sunan mahaifiyar shi(Aminatu).

Wani irin so da kauna suke yiwa Aminatu wanda baya misaltuwa, tun tana jaririya abubuwan al’ajabi ke faruwa akanta wanda ake firgita zainab har ta kai munzalin shiga makaranta aka saka ta nursery 1,lokacin  tana da shekaru uku  a duniya.

Abubuwa take aikata kamar wata babbar mace,tun daga kan mallamai har ɗalibai ta fitine su kamar wata iblis kullum cikin kiran iyayen ta a makaranta!

Daga ta fasa wa yaro kai,ta yanki wata da razor,ta caka wa wata pencil a hanci da sauran su..  
  Kusan ko wane term sai an canza mata makaranta wanda da kyar ta  kamalla primary school!

Wani babban abin mamaki har iyayen ta bata bari ba domin kusan kullum sai ta saka zainab kuka,idan bata haɗa iyayenta faɗa ba hankalin ta baya kwanciya,abubuwa nata gaba dai har zuwa wanan lokaci data cika shekaru goma a duniya zata shiga jss1 kenan idan an koma hutun karshen zango.

********

   Cikin kuka ta ɗaga hannayen ta sama tana mai kaskantar da kanta.. 
  “Ya Ubangij,gare ka na dogara kuma a gare ka nake neman taimako,nasan Ni mai laifi ne,kuma baiwar ka mai rauni,ka dube mu da idanun rahama ka shirya mana zuri’a,Allah ka kare mu da wannan yarinya tamu,Allah ka shirya ta ka kawo mana karshen wannan tashin hankali…..

****
Bayan fitar su daga gidan sun hau titi sosai Mami ta kalli daddyn ta ta ce,. 
  “Kasan me daddy na”?hankalin shi na kan hanya ya ce. 
“A’a sai kin faɗa mamata”.. cigaba da magana tayi
  “Dama motar nan ta kama da wuta kawai na fita da gudu,ta kone da kai yadda ba za’a iya kashe wa ba har sai ka mutu a ciki”!!..da sauri ya taka burki yana maimata
  “innalillahi wa’inna ilaihi raji’un”cikin zuciyar shi yana faɗin wanan wace irin masifa ce!
 “Daddy me yasa ka tsaya”?ta mai tambayar tana son sanin dalilin sa na tsayawar
A zafafe ya ƙure ta da idanu cike da ɓacin rai domin ji yake kamar ya faffala mata mari!

Jin horn yayi yawa ta ko ina yasa ya juya hancin motar zuwa hanyar gida …

A zuciye ta kalle shi ta ce.. 
  “Saboda na fadi abinda ke zuciya ta shine zaka koma gida daddy”?
 Banza yayi da ita kamar ma bata wurin ya cigaba da tuƙi a tsiyace…, ƙoƙarin buɗe murfin kofa take yi zata fita ya fincikota da ƙarfi tare da danna lock ta gefen shi!
  Naɗin suman kanta ya riƙe da ƙarfi da hannu ɗaya cikin ɓacin rai ya fara magana;

“Ke wace irin shaidaniyar yarinya ce? baki da magana sai mugun furuci? menene laifin mu a gare ki da a koda yaushe baki da buri daya wuce kiga bayan mu?na san maganin ki,wallahi makarantar kwana zan kai ki kowa ma ta huta da iskancin ki”!!.

Tunda ya fara faɗa runtse idanun ta tayi tare da cije lips nata azaba na shigar ta amma taurin zuciyar ta ya hana ta bada hakuri bare ta nuna alamar tayi nadamar furuncin ta.

Sai daya gaji don kanshi ya sake ta,nan take tayi kwafa dai-dai sun iso gida har mai gadi ya buɗe masu gate.
  Zuciyarta na tafasa burinta kawai ta sauke wanan ɓacin rai a kan mum ɗin ta!..
  Har ya buɗe kofa ya fice zuwa cikin gida bata lura ba,sai daga baya ta sake yin kwafa sanan ta fito zuwa ciki….

Zainab na mashi sannu da zuwa amma ko kallon ta bai yi ba domin duka laifin a kanta yake daurawa,a ganin shi itace bata kula da tarbiyyar mami yadda ya kamata ba shi yasa aka samu taɓara a ɗabi’un ta.


Tana tsaye inda ya barta taji shigowar mami a guje wace ta wuce d’akin ta ba tare da ta kula da maganar da zainab ke mata ba….

  Wani tashin hankalin zainab ta shiga domin ta rasa wurin wanda zata fara zuwa,gashi ta haɗa masu abinci mai kyau su kawai take jira.

Cikin su tasan halin kowa; Muhammad idan yayi fushi yafi buƙatar keɓewa shi ɗaya na wani lokaci.

Ita mami kuwa taurin kai ne da ita sosai,tasan koda taje ba zata taɓa kallonta ba bare har ta amsa ta!
  Tun tana faɗa da duka har ya gaji ta zuba wa sarautar Allah idanu kullum cikin addu’a take Allah ya shirya mata zuri’a..!!!

Wani irin ihu ta jiyo daga cikin gidan…,saboda tsabar rude wa ta rasa ina zata nufa!

Daidai kofar dakin mami ta tsaya turus hango jini na biyo Ƙasan kofa wanda ko tantama babu jinin mutum ne!!!Banyi alƙawarin typing kullum ba,haka zaliki banyi alƙawarin typing da yawa ba saboda halin yau da kullum


HALIMATUS SADIYA MUHAMMAD????????

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button