NOVELSUncategorized

KWAI CIKIN KAYA 11

ƘWAI cikin ƘAYA!!????


                    Bilyn Abdull ce????????

              BOOK ONE
                    Shafi na goma sha ɗaya
______________
………….Mama Atika tsohuwa mai ran ƙarfe dake zaune a falonta tana jan cazbaha ta ɗago tana kallon Shahudah data shigo a guje kamar an korota, ga jikinta harya fara jiƙewa da yayyafin da har yanzu akeyi, sai da ta ƙarema guntun wandon jikin Shahudah da bai gama zuwa koda rabin cinyartaba kallo da riga mara hannu, wadda inda zata ɗaga hannu sai anga cibiyarta.

       Janye idanunta tayi daga barin kallonta sannan ta girgiza kanta.
        Ƙarasowa Shahudah tayi ta zauna a jikinta tana kumbura fuska ga hawaye na kwarara.
      Mama Atika ta shafa addu’a tare da maida hankalinta ga Shahudah.
      “Kekuwa Sabirah miya jamiki fitowa a haka cikin wannan ruwan? Ko ɗankwali ma babu fa a kanki, baza dai kibar wannan shigar ta bayyana jikinki ba ko?”.
         “Ni ki daina cemin Sabirah, idan bazakice Shahudah ba basai kin kira sunanaba, Wlhy hajiya nagaji da abinda Jawaad kemin a gidansa, ni gaskiya ku kirasa kuyi masa faɗa”.
        Mama Atika tace, “Hummm, yauma tsiyar kuka sakeyi kenan? Waishi wannan yaron wane irine? Ni abindama ke ƙaramin takaici dashi kokin kawo ƙarar tasa an kirasa sai yace shi baki masa komaiba, narasa irin wannan rikitaccen zama naku”.
        Kuma fashewa da kukan shagwaɓa Shahudah tayi, sai kuma lafewa jikin tsohuwar takeyi.
        “K yanzu yasan kin fitone?”.
      Mama Atika ta tambayi Shahudah.
       “Ni ban sani masaba,  dan fitowata kawai nayi bayan yamin wulaƙancin”.
       “Hummm, to shikenan, yanzu tashi ki koma, da safen zansa iyayenku su nemeku”.
     “Ni dai anan zan kwana, dan inason ya gane kuransa yau”..  
      Murmushi irin na girma mama Atika tayi tana gyara zama, “Shikenan, tashi kije ki sauya waɗanan shiɗanun kayan ki kwanta muga idan zai biyoki, idan bai zoba ai iyayenki zasuzo gaisheni da Asuba zan sakasu kiransa ayi zama yau, dan bazan yarda da irin wannan halin na wulaƙanciba, sai dai yasan mai yuwuwa”.
     Jin hakan da Shahudah tayi saiya sake kai kanta sama, ta shige bedroom din ƴar tsohuwar da aka narkama dukiya ta kwanta abunta.

        Tun mama Atika na zuba idon ganin ko Jawaad zai shigo a daren harta fidda, dan har tagama cin abinci da duk abinda ta saba yi kafin ta kwanta, har lokacin kuma babu Jawaad babu labarin.
  
        Da safema koda suka tashi bai zoban, harta gaƙaraci mitarta akan Shahudah da bata tashi tai sallaba tai shiru, sai kuma ta koma kan Jawaad.
      Da mitar Jawaad ɗin a bakinta su baba Usman suka shigo suka sameta, bayan sun gaisheta take sanarmusu komai.
     A take suka aika a kira musu Jawaad, amma sai akai rashin sa’a aka iske ya wuce aiki abinsa.
      Takaicin hakan ya hanasu motsi har saida suka fara jiyo kakarin aman Shahudah daga bedroom ɗin Mama Atika.
      Itace ta shiga ta isketa duƙe tanata amai cikin banɗaki, mamaki ya kamata, amma saita ajiye mamakin ta taimaketa harta gama sannan ta bata ruwa ta wanke bakinta suka fito.
      Sannu taketa jera mata da tambayarta komi taci haka daga tashinta?.
       A galabaice Shahudah ke faɗin, “Ni banci komaiba Hajiya, dan rabona da cin wani abu tunma jiya da yamma, bansan miyasaba kwana ukunnan kullum da amai nake farkawa da safe, narasa mike damuna”.
     Tsiramata ido mama Atika tayi ba tare da ta iya cewa komaiba, tsawon wasu sakanni tana a kanta tana nazarinta, sai kuma ta fice daga ɗakin a hanzarce tare da wani irin ɗoki akan fuskarta.
            Shahudah kam kanta ta maida ta kwantar barci ya kuma kwasheta.

       Albishir ɗin da tsohuwa takaima ƴaƴan nata ne ya sakasu miƙewa zumbur a wani irin razane.
      Kowa na ambaton mama da gaske?.
      Dariyar jin daɗi tayi tana zama, “Ƴaƴannan mizaisa na muku ƙarya nikuwa, sam bakwa bina bashin rantsuwa akan wannan maganar haka take. Amma danku tabbatar a kira likita ya gwadata yanzunnan”.
          Duk da sun yarda da batun mahaifiyar tasu haka suka nemo Doctor domin sake tabbatarwa a aikace.
        Jikin Shahudah rijib da zazzaɓi zuwa yanzun, haka dole Mama Atika ta tasheta, tambayoyi likitan yaymata tare da bata tsinken gwaji saboda ba’a buƙatar jan lokaci.
    Gwajin farko ya tabbatar akwai ciki, tuni falon ya ruɗe da wani irin murna, kowa fuskarsa a washe saɓanin ta Shahudah dake a rikice.
     Ciki kuma? A wannan shekarun natane zatayi ciki? Kai da sakal wai anbama mai kaza kai, sam babu tsarin ɗaukar ciki a gareta a nan kusa, yaushema sukai auren da har tagama morarsa da za’ai batun ciki a jikinta, so ake ta ragwagwgwaɓe da wurima kenan tamkar wata matar Afirika, ina wannan shirmen bamai yuwuwa bane, dolene Jawaad yazo asan abinyi, dan bazata haifi wannan cikinba koda za’a tada yaƙin duniya na ukune.


      ????????hummm ashe akwai kallo, dan inba’a tada yakin duniya na uku ba to lallai Shahudah za’a tada na ƙarshe akanki????????, yanda naga cikin yazama burin mutane da yawa aiko yagalgalaki zasuyi harma da Fans  din ƙwai cikin ƙaya????????.


★★★★★★★★

            Ya isa ƙofar kurkukun (Jail) da abokansa uku kuma aminansa suka tsinci kansu a ciki dalilin ƙaddara, dan kuwa shekarunsu na biyu kenan a wajen bisa sharri da akai musu dan a durƙusar da Jawaad ɗin, yayi iya bakin ƙokarinsa a lokacin ganin sun kuɓuta amma sai hakan ya gagara, dankuwa ƙulline mai cike da ruɗani a ka ƙulla dan kawai a dakusheshi tunda ansan abokansa suna cikin manyan abinda ke ƙara masa ƙwazo da ƙarfin gwiwa, duk yanda yaso gano wanda ya aikata masa hakan kuma bai samu nasaraba, shiyyasa ya tattara komai ya maida hannun ALLAH, sai gashi a yanzu cikin sauƙi ALLAH ya kuɓtar dasu.
       Shigarsa wajen ta saka ma’aikatan gidan yarin bashi girma na musamman, dan sunsan wanene shi da matsayinsa, tunda dama jail ɗin bana kowa da kowa bane, jami’an tsaro masu laifi kawai ake sakawa a ciki.
      Bayan shigarsa Office ɗin shugaban wajen na wasu mintuna aka kammala komai, yana nan zaune aka fito dasu.
        Idanu suka tsurama juna da ga shi harsu, tuni idonsa ya kaɗa yay jazur tamkar an hura barkono, jijiyoyin kansa sunyi wani irin fitowa ruɗu-ruɗu, ya miƙe ahankali yana tunkararsu tamkar yanda shima suke nufoshi cikin wani irin yanayi na kewa da farinciki, dan shekaru biyun da suka ɗauka a rufe sam an hana Jay ganinsu.
         Rungume juna sukai su huɗu, dukda yanda jikinsu yake baiji ƙyamarsuba, kowanne hawaye masu raɗaɗi suna kwarara a idanunsa.
       Su dai ma’aikatan wajen kallonsu kawai sukeyi.
       Kusan mintuna uku suna a haka, kafin su ɗago kowanne yana ƙokarin sharema ɗan uwansa hawayensa, sai kuma suka sake rungume juna suna dariya saikace wasu zararru.
      Nanma kusan sakwan arba’in suka ɗauka kafin suyi haramar fitowa ba tare da ko bakin ɗayansu ya saɓa ba wajen furtama juna magana.
        Gimba dake jikin mota tsaye ya hangosu suna fitowa daga cikin Jail ɗin a yanayin da yasansu a baya, jarumai kuma aminai, sannan ƴan uwan juna masu ɗaukar kansu JINI ƊAYA.
      Cike da wani irin ɗoki yake washe musu baki har kunne, lallai yau farin cikin boss ɗinsa sun dawo, yanzu sauyi zai sake zuwa a hukumarsu, hannunsa ya dunƙule waje ɗaya yana cigaba da washe bakinsa, yama kasa magana saboda tsabar farinciki.
        Suka dafashi a kusan tare suna dariya suma.
      Da ƙyar ya iya furta, “ALLAH mun gode maka, yau ga basawan boss sun dawo gareshi, tarkon da makiya suka kafa ya buɗe”.
      Jawaad da fuskarsa babu walwala ya girgiza kai kawai ba tare da yace komaiba ya buɗe mota yana musu nuni dasu shiga.
       Basu ɓata lokaciba suka bar wajen zuwa gidan Jay ɗin dake Empty babu kowa ciki, gidan yayi ƙyau sosai, gashi anguwar da yake babu yawan hayaniya.
          Suna shiga gidan dukkan farin cikinsu da suka danne da kewar juna sai ya bayyana, dan sake rungume juna sukai a tare kowa na faɗo yanda yay kewar ɗan uwansa.
      Tsawon lokaci suka ɗauka a haka har Gimba ya dawo da ledojin abinci ba tare da sunsan zaiyi wannan ɗawainiyarba.
      Godiya sukai masa duk da kuwa yana ƙasansu, ya nuna musu hakan ba komai bane tare dajin daɗinsa na murna da sukai, ya jajanta musu da addu’ar ALLAH ya kiyaye gaba.
          Wanka suka shiga su duka a mabanbanta banɗakin dake cikin gidan, sun ɗauki tsawon lokaci, dan Jawaad ma harya fice zuwa wani kiran gaggawa daya samu daga office ya barsu akan kafin ya dawo su tabbatar sunci sunsha sun huta…….


________
BILKEESU
________


     ………Har dare babu labarin bilkisu a cikin anguwar, ga kuma ƴan sanda ta ko’ina an bazasu nemanta, sai kuma yaran Jazuuga dasuma ke aikinsu domin taya ƴan sandan.

         Ina cikin mankarar har dare, tun ina kuka da hawaye da murya harna koma na zuciya kawai nake iyawa, hankalina bai gama tashiba sai da na farajin motsin mutane masu shigowa sallar magriba, kuma nutsuwa nayi a wajen duk da ƙarfina ya ƙare, hannuna dafe da bakina gudun kar wani mai ƙarfin ji ya iya jiyo fitar numfashina.
         ALLAH ya aramin wannan lokacin har akai sallar magriba aka kammala.
     Sosai ƙarfina ya gama ƙarewa, na gaji da tsaiwar, burina kawai na zauna nahutama raina, ƙafafuna sunyi nauyi tamkar ba’a jikina sukeba, gashi wasu suna a massallacin basu gama ficewa ba, sun zauna har sai anyi sallar isha’i.
      Haka na cigaba da dauriya a wannan yanayi mai wahalar musaltawa har lokacin sallar isha’i yayi ya wuce, mutane sun fara barin massallacin, inda akabar tsirarun da suka koma fita ɗai-ɗai.
       Wani da ya fita na ƙarshe shida abokinsa naji suna faɗin ƙarfe goma da rabi na dare, bana a hayyacina zuwa lokacin sosai, amma bayan fitarsu da wasu mintuna saina leƙo kaina cikin massalacin, babu kowa sai mutum ɗaya dake barci, da gyar na tattaro ɗan sauran ƙarfina na janye mankarar na fito, tafiya nake tamkar bugaggiyar da tayi mankas da kayan maye, ni kaina bansan a ina nake jefa ƙafaba, tafiya kawai nake tamkar bahagon raƙumi.
       Ƙwaƙwalwar kaina sam bata aiki da zuciyata, ni kaina na fara manta wacece ni?.
         Ƴan sanda biyu dana hango gabana suna tunkaroni yasani firgicewa, nai saurin komawa baya na maƙale jikin bangon wani gida, ta gabana sukazo zasu wuce suna magana wadda na fahimci akainace. 
       Ɗaya a cikinsu ke faɗin, “Oga kana ganin Alhajin nan zai bamu maƙudan kuɗinnan kuwa daya faɗa inhar aikinnan ya kammala yanda akeso?”.
            “Hhhh bayarwa kuwa zaiyi ɗan sambo, bakaga yanda yake a firgiceba, bashi da burin daya wuce akama yarinyar, sannan ɗansa ya kuɓta, shiyyasa nima nace muyi ƙaimi, dan inada tabbacin tana cikin anguwarnan bata fitaba, sai dai idan wani munafikinne ya bata mafaka a gidansa”.
          “Shegun ba, ai zamu kamatane, idan kuma har kuɗinan suka tabbata lallai lokacin ƙara aurena yayi kenan, dan wlhy zama da kubra kawai nafi ƙarfinsa”.
         “Hhhhhhh!! Wato ɗan sambo shiyyasa nake sonka wlhy, kai abokin neman arziƙine, idan kana abu sainaji daɗi saboda lallai kana kan tsarina, saikace uwa ɗayace ta haifemu”.
     Dariya suka kwashe da ita tamkar wasu mahaukata su duka biyun, da wannan mahaukaciyar dariyar suka wuceni batare da ɗayansu ya hankalta dani ba.
     Numfashi na sauke cikin gajiyawa, sai da na tabbatar sun ɓacema ganina sannan nacigaba da tafiya ina zirar da hawaye, wace irin ƙasa muke da ita hakane? Masu bada tsaro da kariya sune suka koma masu ɓata tsaro da zalunci?.
        Ta yaya har muke tunanin samun shugabanni adalai bayan muma talakawan azzaluman junane?.
      Nacigaba da tafiya ba tare da namasan ina nakeba, abinda na sani kawai shine nayi nesa da anguwarmu kam tabbas, sannan ina buƙatar zama na huta, sai dai tsoro da fargabar kar azo a kamani sun hanani damar samun wajen yada zango.
        
          Nayi tafiya mai nisan gaske, wadda sam banida nutsuwar ƙididdigeta koda da ƙiyasine, tun ina gamuwa da mutane da kallon motoci a titi har garin ya fara ɗaukar shiru, bakaji koda ƙarar mashin, ƙafa tafara ɗaukewa, hakama motoci, lokacin da garin ya gama ɗaukar shiru babu abinda kakeji sai haushin karnuka.
     Da ƙyar na iya kawo kaina wani wajen da nakeji sautin kiɗa na tashi, duk yanda naso samun dauriyar matsawa daga nan na kasa, cikin rashin kuzari da ƙarewar ƙarfi na zube jikin wata bishiyar mangwaro dake a gaban gidan, mashina ne birjik a wajen duk an faka, sai jefi-jefi na mutane dake fitowa daga wajen mace da namiji ko mata zalla.
      Tun ina kallonsu har na gazama hakan, idanuna da sukai nauyi jingim saboda kukan da nasha na lumshe a hankali, badai barci nakeba, bakuma ina tare da duniyar mutane bane sam.
        Tsawon lokaci ina a wajennan ba tare dana fargaba, sama-sama naji ana tadani, na buɗe idanu da ƙyar ina saukesu akan ƴanmata biyu da bazasu gaza sa’annina ba, sai namiji dake gefe yana faɗin, “Ƙila tasha abinda kanta ya gaza ɗaukane ko?”.
      Ɗaya a cikin ƴanmatan da ke ƙokarin taimakamin na tashi tace, “Anya ma wannan kuwa bamma santa ananba sam, dan inaga baƙuwace”.
        Kaɗan ɗayar ta ɗan haskani da fitilar wayarta rakani kashi, ta kautar da hasken daga fuskata tana cewa, “A gaskiya baƙuwace, dan nima bamma taɓa ganintaba a gidan wasannan”.
        “Da wannan surutun da kuka tsaya da kamata kukai mukaje da ita gida, dan tabbas tana bukatar taimako” namijinne yay magana cikin nuna kulawa.
        Basuce komaiba sai taimakamin da sukayi na miƙe tsaye sosai, ni dai ban iya cemusu uffanba, suka kamani a kafaɗinsu  mukabi wani lingu.
          Banwani damu da inda suka kawoninba, duk dama gidan tsitt yake alamar duk anyi barci, namijinne yasa key ya buɗe ɗakin suka shiga dani ciki.
      Sun kwantar dani a katifar ɗakin wadda halin danake ciki baisa na fahimci komai akantaba.
        “Ƴar daɓas kunna risho a dafa mata ruwa tasamu tai wanka, dan a halin da take ciki na fahimci bazata iya jin daɗin barciba”.
       Da to wadda aka kira ƴar-daɓas ta amsa, cikin mintuna kalilan aka haɗamin ruwan wanka mai matsakaicin dumi, yanzuma da taimakonsu na shiga banɗakin dake a cikin ɗakin.
         Ban cutar da kainaba na daure nayi wankan, naji daɗin hakan sosai, bayan nagama na ɗauki doguwar rigar da aka ajiyemin na saka sanann nayo alwala na fito, dan yin wankan yasa naɗan fara dawowa a hayyacina.
       Zaune na iskesu sunacin nama, na ɗan kallesu na duƙar dakai ina faɗin, “Dan ALLAH ku taimakeni da abin salla da hijjab”.
     Ganinai sun kalli juna a wani irin yanayi na shakku, ni saima na fara tunanin koba musulmai bane…….
      Ɗayar ta katsemin tunani da faɗin, “ƴar uwa samun abin salla a ɗakinnan lallai babban abune, ke ama gidannan gaba ɗaya zance, amma dai ga ɗankwali idan zaki iya maneji dashi, hijjab ma inaga za’a iya samun wanda nazo dashi a farkon zuwa gidanan, tunda kuma na ajiyeshi ban sake waiwayeba”.
      Ban fahimci zancen nasuba, bankuma tambaya ba, inadai tsaye aka bani hijjab da ɗankwalin, shinfiɗawa nai na tada salla, sai da nayi sallar la’asar da banyiba da magrib sannan nai isha’i, harma da shafa’i da wutiri, hannuna na ɗaga sama ina addu’a hawaye masu zafi na kwarara saman kumatuna, nakai tsawon lokaci ina kaima ALLAH kukana, kafin na miƙe.
         “Wai, wannan salla taki akwai tsawo, zokici abinci muɗan kwanta, dan gari gab yake da wayewa”.
         Yunwa nakeji, hakan yasa banyi musuba nai zaman cin naman da sukaci suka ragemin, sai fura mai sanyi wadda naji daɗinta sosai.
     Ina kammalawa suka nunamin wajen kwanciya.

           Sai a yanzune dana samu nutsuwa komai ke iya dawomin dalla-dalla, wasu hawaye ke sauka saman fuskata a gurguje, koyaya Firdausi take? Inna da baba da sauran ahalin gidanmu, na ɗago hannuna ina kallo zuciyata na wata irin suka, ni Bilkisu yau nice matsayin wadda tai kisan kai, wai ni na kashe mutum?….
     Kuka mai ƙarfi ya ƙwacemin, nanfa na shiga rairashi babu mai lallashi, dan masu masaukin nawa bansan ya akai daga kwanciyarsu barcinsu yay nauyi irin hakaba, na daɗe ina kuka har aka kira sallar asubahi a kan kunnena.
         Tashi nai cikin layi da nauyin jiki nayo alwala, nazo ina ƙokarin tashinsu amma sam babu wadda tai motsin kirki balle na saka ran zasu tashi, haka na haƙura saboda jin zan rasa sallah.
       Koda na idarma na sake gwada tashinsu amma basu tashinba, nanma haka na haƙura, sai dai zuciyata na mamakin irin wannan nauyin barci haka?, nima ban fargaba barcin ya kwasheni a wajen.


★★★★★★

                A daren ranar yaran jazuga suka dawo gidan da taimakon ƴan sandan nan, duk wani makami da sukasan sun ajiye gidan harda wanda Bilkisu ta gani da yawa a kwali randa ta kasa masa shara duk suka fitar dasu, kayan shaye-shayensu da duk abinda za’a iya kalubalantarsu dashi saida suka fitar dashi.
      Hakama innar Firdausi sun fito da ita, asibiti suka kaita inda baba yake cikin wani yanayi da baki bai iya musaltawa.
         Innar Firdausi ta fashe da sabon kuka saboda ganin halin ruɗani da mijinta ke a ciki, gefe yaran Jazuga sukaja baba da inna, suka shinfiɗa musu dokoki tare da gargaɗi mai tsoratarwa.
        A tsorace baba da inna suka amince kodan son tsira da ransu.
      Alhaji Lado yace, “Zamu baku ƴarku mu canjata da gawa, munaso kuyi nesa da garinanma gaba ɗaya, koda sau ɗaya naga masu kama daku na rantse saikun mutu dukanku, bayan na gama gallaza muku azaba mara musaltuwa, sannan koda wasa kuka taimaki yarinyar data kashemin ɗa wlhy kuma saikun mutu, dan daga yanzu dukkan motsinku zai cigaba da gudana ne a kan idona”.
       Cikin kuka baba da inna suka amsa.
         A munafurce aka fiddo firdausi da taimakon likita da shima aka toshe bakinsa da kuɗi, tare da yaran Jazuga da ƴansandan nan.
       A wata mota aka sakasu harda Firdausi da har yanzuma bata farfadoba, sai dai raunikan jikinta duk sun sami kulawa.
        A wannan tsohon daren aka nufi asalin ƙauyen su baban Firdausi dasu, sunaji suna gani, suna kuka da ɗunbin tausayin Bilkisu da tunanin tana cikin wane haline? Wane kuma hali zata iya shiga daga nan zuwa safiyar gobe………….✍????
https://www.youtube.com/channel/UCl9IGLUXrqUtta-Tjmhoo7Q


MANHA HAUSA NOVEL’S

      Maza garzaya domin bada gudunmawarka kaima, dan ALLAH a danna mana subscribing, tare da bibiyar shirye-shiryanmu masu ƙayatarwa a koda yaushe, harma da tsaftatattun littatafan hausa masu ƙayatarwa da zasu dinga zuwa muku a Audio, yanzu haka ƘARAYAR ARZEEƘI ya fara sauka, garzaya kar ayi babu ku????????????????????.ALLAH ka gafartama iyayenmu

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button