NAFEESAT 1-END

NAFEESAT Page 41 to 50 (The End)

Wajen awanni biyu da shigar da Kaka, kafin su Abbu su fito, sai dai basu ba ma kowa damar ganin sa ba, sabida a time ɗin sun yi masa alluran barci; yana cikin barci, domin ba sa son ayi hayaniya da zai ja har ya farka daga wannan barcin.     Gaba ɗaya iyalan gidan sun kasa kataɓus a ranan, ko jirgawa sun kasa yi a baƙin ƙofar, sai da su Big Dady suka yi musu magana ne, akan “su tafi gida,” sannan ne su Hajiya suka koma gida, yayinda su Ɗahira kuma suka koma bakin aikin su, but jefi-jefi suna kewayo wa ko Kaka ya farka.

     Har dare be farka ba, haka ilayan Doctor Al’ameen suka kwana a cikin wani hali a wannan ranan, sai washe gari aka samu ya farka, sai dai sosai suka shiga farin ciki a ranan, sabida Kaka ya samu sauƙi tamkar ba shi ba, babu wanda yayi tunanin zai tashi da lafiya haka, sai ga shi har magana yana iya yi, kuma yana iya yin sallan sa, domin tunda ya tashi ya buƙaci a kai sa yayi alwala, sai da ya gabatar da sallolin da ake bin sa, sannan ya samu yaci abinci daƙyar, aka ba shi magani ya sake komawa barci, sakamakon alluran da aka sake mishi, sabida ana son ya sake samun hutu sosai.

      A ranan haka mutane sukai ta zuwa duba sa, gaskiya Kaka na mutane ne, ba ga talakawan ba; ba ga attajiran ba, manyan mutane kama daga ko wani gari duk ana ta zuwa gaishe shi, har mutanen Maiduguri dangin su duk sun zo wasu daga ciki duba sa, su Hajiya Ikram, Hajiya Laila tun a ranan suka shigo Kaduna.

     Kwanan sa biyar a asibitin yana samun kulawa daga ƴaƴan sa da jikokin sa, ya samu sauƙi sosai, sai dai sun hana a mayar dashi gida dole sai ya ƙara samun sauƙi

Shi da kansa ya matsa musu dole suka sallame sa ya koma gida, a ranan sun ga mutanen anguwa, suna ta ɓulɓulowa gaishe da Kaka, da waɗanda suka je asibiti, da waɗanda ma basu je ba duk sun biyo sa gida.

     Bayan kwana uku da sallamo sa ne, wanda ta kama ranan Lahadi, ya saka aka tattaro masa iyalan gidan

Bayan kowa ya hallara ya soma musu jawabi akan abinda ya sa ya tara su, ba komi bane illa maganar aure

“Fodio da takwara na da ku zan so ma, har yanzu shiru ban ji kun kawo min maganar wacce kuke so ba?” Yayi maganar idanun sa a kan su

Shiru suka yi ko wannen su, don basu yi zaton akan hakan ya tara su ba. Sai da Abba yayi musu magana kafin Baffa ya buɗi baki yace, “Kaka Ni dai har yanzu bamu gama daidaitawa da wacce nake so ba, but I will bring it to you in a short time,  Calm down baza ka mutu ba insha Allahu sai ka ga auren mu”.

Sosai maganar Baffa ya ba wa waɗansu dariya, sabida yanda yayi maganar cikin barkwanci

Abba kuma daƙuwa yayi masa yace, “ka ga naka Baba na, ba maganar wasa ne ya tara mu anan ba kaji ko?”

Duƙar da kai Baffa yayi yana sosa ƙeya yana murmushi

Haka zalika ma Kaka murmushin yayi yace, “to takwara na Allah ya kawo ta lafiya, sai dai a wannan gaɓar lokaci zan ba ku, sabida ina so nan da wata ɗaya kacal ayi auren ku mu huta, ba wai ku kaɗai ba, ina nufin har ƴan matan, gaba ɗayan ku zaku fid do da miji ayi muku aure”.

Sosai maganar Kaka ya razana Ɗahira dake kusa dashi, dasauri ta ɗago kai ta zuba masa manyan idanuwan ta, kamar an tsikare ta kuma tace, “Kaka, do you mean us?” 

Kallon ta yayi yana murmushi yace, “Yes, my wife, I hope all of you will be married in just one month, domin tabbas na san ba zan jima ba a duniyar nan, wannan ciwon ya ɗaga min hankali, shiyasa na yanke shawaran gaba ɗayan ku; ku fitar da mazajen aure sai a haɗa dana yayyin ku, zuwa nan da sati ɗaya na ba ku ko wacce sai ta turo wanda zata aura, kun ji ko?”

Gaba ɗaya amsa mishi suka yi, ban da Ɗahira da tunanin ta ma ya bar duniyar

Sai kuma Usman da tun sanda Kaka ya soma zancen, ya ɗaure fuskar sa tamau, ko ɗago kai ya ƙi yayi, bare kuma yasa baki.

    Daga haka Kaka ya sallami kowa taron ya tashi

Ai kamar jira Ɗahira take yi tuni ta bar parlour’n, sabida ruɗewa har so tayi ta bangaji Usman da yazo ficewa shima, Allah ya tsare hakan be faru ba ta dawo hayyacin ta

Wani banzan kallo ya watsa mata yayi hanyar Part ɗin su hannayen sa biyu cikin aljihu.

      Ɗahira bata bi ta kansa ba, tunda ba ta shi take yi ba, yanzu hankalin ta duk a tashe yake, burin ta kawai ta ƙebe tayi tunani, “shin ita wa take dashi ne da zata kawo a matsayin miji? Wannan tunanin shi ne yayi matuƙar wargaza mata duk wani walwalan ta da nutsuwar ta.

       Tana shiga Part ɗin su, ta shige ɗakin su ta yaɗa zango a kan gadon ta, buga tagumi kawai tayi ta hau tunanin mafita, bata ankara ba sai ga hawaye

“Innallillahi wa’inna ilaihi raji’un! What is going to happen to me? By the time I get married no one has ever said he loves me, so who will I choose as my husband?” Tayi maganar a cikin zuciya tana me share hawayen da bayan hannun ta

Sai kuma ta saka hannu ta ɗauki wayan ta ta hau lalubo Numban Masoyin ta na ɓoye, wanda tayi serving Numban sa da My LOVE. Shiru tayi tana tunanin me zata yi, sai kuma ta soma kiran Numban, sai dai a kashe yake, wani yawu me ɗaci ta haɗiye cike da baƙin cikin da taji ya tokare mata maƙoshi, bata taɓa jin haushi irin na yau ba a duk sanda tayi yunƙurin kiran sa, amma wayan a kashe. wannan maganar me muhimmanci ne shiyasa ba ta so suyi sa a text message, tafi son ta Kira sa suna jin muryan juna, sannan ta faɗa masa abinda take so ta sanar masa. 

    Sai dai babu yanda ta iya haka ta tura masa text message kamar haka:

_”Now everything is over between us. If you really want me, then I need you to explain yourself to me at this time. I don’t want you to talk to me again unless you do what I need you to do.”_

       

Abinda ta rubuta kenan ta tura masa, sai ta kwanta tana lumshe idanun ta, tare da zaman jiran reply ɗin sa.

       Bata fi mintuna goma da tura saƙon ba, sai ga reply ɗin sa ya shigo

Da sauri ta tashi zaune ta janyo wayan tana duba wa, sosai tayi farin ciki da amsar da ya bata, murmushi kawai take saki tana karanta wa

_”I am also waiting for this day to be beautiful, insha Allahu zuwa gobe zan bayyana miki kaina, just choose me when I come to you.”_

Take tayi mishi sending ɗin time ɗin da zai zo, ƙarfe 03:00pm. Tana tura masa ta kwanta tana zuba murmushi, tunanin kawai yanda haɗuwar na su zai kaya take yi, take ta lumshe idanuwan ta tana sake dulmiya a kogin tunanin masoyin nata.

         ⚫⚫⚫⚫⚫

       Baffa dake tsaye kan benen Part ɗin su, yana tura mata text ɗin ya saki murmushi me fid da haƙora, ya sani dole ne wannan ranan zata zo, amma yanzu ya rigada ya gama shirya mata, ya shirya yanda zai fito fili ya bayyana ƙaunar sa ga masoyiyar sa, domin samun mallakan ta a matsayin matar sa, wanda ya daɗe yana tsimayen zuwan ranan

Wani kyakykyawar murmushi ya sake saki cike da farin ciki a ransa, shafa suman kansa yayi kafin ya soma taka wa ya wuce Part ɗin su, shiga yayi da sallama a bakin sa

Hajja Fatu dake zaune tana jiran dama shigowar sa ne, shiyasa ta zauna a parlour’n zaman jiran sa. Amsa mishi sallaman tayi tana murmusawa tace, “yauwa Baffa na, taho ka bani labarin surukar ta wa”.

Dariya ya saki yana isowa wajen ya zauna tare da faɗin, “kai Hajja wai dama jira na kike yi?”

“Iyi wlh, ai tunda kafaɗa na kasa zaune na kasa tsaye ina so inji wacce me sa’ar ce ta same ka?”

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button