NAFEESAT 1-END

NAFEESAT Page 41 to 50 (The End)

Gyaɗa masa kai tayi, a wannan karon tana kallon sa tayi masa murmushi tace, “to Yaya na, na gode”.

Fuuuu Sa’adatu ta wuce ta bar parlour’n

Shima bin bayan ta yayi bayan ya sake yin ma Aunty Amarya sallama

Aunty Amarya ci gaba tayi da ɓare lemon dake hannun ta, a ranta sosai take mamakin abinda yasa Sa’adatu take kishi da Ɗahira, domin tuni ta gane abinda ke zuciyar ta, sai dai kuma bata san cewa da Baffa Ɗahiran tayi soyayya ba

Ɗahira kuwa gyara wa tayi ta kwanta kan two sittern da take kai, tana lumshe idanu tare da faɗa wa duniyar tunani, ita ko kaɗan abubuwan da Sa’adatu take yi ba ya damun ta, amma duk idan ta tuna da yanzu ita ce a makwafin Sa’adatu ɗakin Baffa, abun na mata zafi sosai a zuciya, har ta zubar da hawaye.

                ⚫⚫⚫⚫

           Kai tsaye gidan su suka nufa, Sa’adatu tariga shi isa, inda ta zauna a kan ɗaya daga cikin kujerun parlour’n ta tana faman karkaɗa ƙafa, sosai ta cika tayi maƙil tsaban kishi, ita ko kaɗan yanzu ba ta ƙaunar Baffa ya raɓi Ɗahira, gani take yi hakan zai saka mutanen gida su san me ke faruwa tsakanin su, kuma ta san ako yaushe za’a iya kawo mata ita a matsayin kishiya, tunda ita ɗin ƴar uwan sa ce, baza su yi la’akari da daɗewan auren ba ko rashin sa. 

        Shigowar Baffa ne ya dawo da ita daga guntun tunanin da ta afka

Kallon ta yayi kamar yanda take kallon sa yace, “ke wai Sa’adatu wani irin baƙin kishi ne kike son ki shigo min da shi gida na? Wato rashin hankalin naki ya kai har ki shiga tsakani na da ƙanwa ta? A kan me zaki riƙa min haka? Ke fa baki isa ki hana Ni abinda nayi ninya ba, kuma idan Allah yace Ɗahira mata ta ce, wlh daga ke har wacce take ɗaure miki gindin baku isa ku hana ba”.

Sai kawai yaga ta fashe masa da kuka, cikin kukan take cewa, “wlh tallahi kamar a kunnen Hajja, wato kana nufin Ni da ita ba mu isa mu hana ka kula wancan yarinyan ba ko? Kenan Hajja bata da mutunci a wajen ka? Da kake cewa kar na shiga tsakanin ka da Ƙanwar ka; ai ba Ni ce na raba ku ba, wlh na gaji da abinda kake min, tunda ba ka gani na da mutunci ƙarar ka zan kai”. Tana ƙare zancen nata ta tashi fuuuu ta fice tana ci gaba da kukan ta

Direct cikin gidan ta nufa, inda ta wuce Part ɗin Hajja don Kai ƙaran sa.

         Ta bar sa nan tsaye da sakakken baki, sosai ransa ya ɓaci da abinda ta faɗa, “kenan shi be da ikon da zai mata faɗa, sai ta ɗibi ƙafafu ta kai shi ƙara wajen Mahaifiyar sa? Anya zai iya wannan auren kuwa?”

Share this

[ad_2]

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button