NAFEESAT 1-END

NAFEESAT Page 41 to 50 (The End)

       _A.A.A. Masoyin ki._✍️

      Lumshe idanuwan ta tayi, hawayen dake tsiyaya akan kuncin ta tun soma karanta text ɗin; suka ci gaba da kwaranya, wani irin ƙunci ne ya tokare mata maƙogwaro, wanda daƙyar take iya haɗiye yawu

Dauriya dai me dauriya sai da ta gwada yin shi, amma ta gaza, dole ta zube kan gadon ta hau rusa kuka, kuka take yi sosai zuciyarta na mata zafi tamkar zai faso ƙirjin ta

Taya ma zata iya jure wannan halin da take ciki, meyasa zai mata haka? Meyasa zai tafi ya bar ta a lokacin da take buƙatar sa cikin rayuwan ta? Ya tafi ba tare da ta gansa ba, ya tafi ba tare da tasan sunan sa ba, dama ashe ba son ta yake yi ba? Meyasa to ya koya mata ƙaunar sa?…

      Fadila ce ta shigo ɗakin, ganin Ɗahira a wannan halin, sai tayi saurin ƙarisowa wajen ta hankalin ta a tashe, ta hau tambayan ta “lafiya?”

Cikin kuka Ɗahira ta bata amsa,

“He is gone ..! Wlh I really love him, ban taɓa son wani ba sai shi, meyasa zai tafi ya bar Ni?..” ta kasa ƙarisa wa illa kukan da taci gaba da yi, hawaye na ambaliya a kyakykyawar fuskar ta

Sosai Fadila ta tausaya mata, riƙo ta tayi tana faɗin, “ki nutsu Ɗahira, tell me what happened, shin wane ne shi wanda ya tafi ya bar ki?”

Ɗago idanun ta da suka kaɗa suka yi jazur tayi ta aza akan Fadila, cikin raunin murya take faɗin, “wanda muka yi alƙawarin aure dashi, ya ce min Mahaifiyar sa ta haramta masa aure na, me zai saka yayi min haka? Me zai sa in ba aure na zai yi ba ya zo ya koya min son sa? Meyasa tun farko ya zo wuri na?” Taƙarishe maganar cikin kuka

Da mamaki take kallon ta, sabida ta san babu wanda ke zuwa wajen ta, tunda take bata taɓa ganin Ɗahira ta kawo baƙonta gidan nan ba, “shin aina shi kuma wannan suke haɗuwa?” Tayi ma kanta tambayar, sai dai babu me bata amsa, dole ta kawar da zantukan daga ranta ta soma rarrashin ta. Ta daɗe tana rarrashin ta, amma Ɗahira ta kasa yin shiru, dole ta haƙura ta bar ta, ta miƙe tabar ɗakin.

       Kuka sosai Ɗahira tayi, kukan da ke fitowa daga zuciyar ta. Tunda take bata taɓa yin soyayya ba, koda da rana ɗaya bata taɓa son wani ba, amma kuma ta rigada ta kamu da ƙaunar wannan bawan Allan da bata san ko shi waye ba, bata san sunan sa ba, ko kaɗan baza ta iya juran rasa shi ba, soyayyan gaskiya take mishi, taya lokaci ɗaya zai tafi ya bar ta a lokacin da take matuƙar buƙatar sa? Wannan amsoshin su suke yawo a zuciyar ta, wanda ya ƙara haddasa mata cinkushewar baƙin ciki a ranta

Allah ya gani ita baƙuwa ce a soyyayya, ko kaɗan baza ta iya juran wannan yanayin ba.

      Har Fadila ta sake dawowa ɗakin Ɗahira na kwance tana kuka

“Wai don Allah Ɗahira baza ki dena wannan kukan da kike yi ba? Taya kuka zai miki maganin matsalan ki? Ke fa ba ƙaramar yarinya ba ce”. Cewar Fadilan tana kallon ta daga bakin gadon ta da ta tsaya

Ɗahira bata ce komi ba, illa miƙe wa da tayi ta shiga Toilet, alwala tayi ta fito ta soma gabatar da sallan isha’i da aka daɗe da yi, har ta idar tana zaune a wajen ta kasa tashi, sai ma haɗa kanta da gwiwowin ta da tayi; tayi shiru tana tsiyayar da hawaye

Fadila dake kwance tana faman latsa waya, ta kalle ta tace, “I forgot I didn’t tell you, Aunty Amarya is calling you”.

Shiru Ɗahira tayi mata

Ita kuma bata sake bi ta kanta ba, taci gaba da charting ɗin ta ita da K.B, tana yi tana sakin murmushi.

      Sai da kusan mintuna goma suka shuɗe sannan Ɗahira ta tashi ta fice, babu kowa a Parlour, kai tsaye ta wuce ɗakin Maman ta. Sai da tayi sallama aka ba ta iznin shiga sannan ta shige

Aunty Amarya na zaune akan sallaya, shi kuma Abbu na gefen gado zaune yana waya, da alamun wayan me muhimmanci ne shiyasa gaba ɗaya attention ɗin sa ya ba wa wanda suke wayan ne

Durƙusa wa gaban Aunty Amarya tayi, cikin dashashshiyar muryan ta na wanda tasha kuka tace mata “ga ta”.

“Ya naga kamar kin yi kuka? What’s wrong with you?” Aunty Amarya asked her this question keeping an eyes on her

Sake sunkuyar da kanta ƙasa tayi, in a weak voice and said, “nothing”.

Shiru Aunty Amarya tayi na ɗan wani lokaci, sai kuma tace, “je ki kici abinci, kar ki kwanta da yunwa kin ji ko?”

Gyaɗa mata kai tayi tana miƙe wa ta fice

Aunty Amarya tabi ta da kallo cike da tausayin ɗiyar ta ta, tabbas ta san akwai ɗinbim damuwa a tattare da ita, kuma ta gane kuka tayi, amma kuma ba ta son ta dame ta da tambaya a wannan lokacin ne har sai ta samu sauƙin damuwar nata..

“Har kin sallami Maman nawa ne?”

Maganar Abbu ya katse mata tunanin ta, sai ta juyo tana kallon sa, ta ce, “eh, na ga ai kana waya ne, kuma bata ci abinci ba shi ne nace ta je taci. Ko in Kira ta ne?”.

“No. Let her eat her food.”

Koma wa Aunty Amarya tayi ta zauna, don har ta rigada ta yunƙura zata tashi.

               ⚫⚫⚫

        Ɗahira na fita bata ci abincin ba ta koma ɗaki, domin baza ta iya saka komi a bakin ta ba, ko da taci kuwa, baza ta ji daɗin sa ba.

    Tana shiga ta haye kan gadon ta ta kwanta, sai dai ta daɗe kafin ta samu barci ya ɗauke ta, gaba ɗaya tunani ya hana ta sukuni, sai daƙyar ta samu tayi barci.

     Washe gari da zazzaɓi ta tashi, dole ta sake komawa ta kwanta bayan ta yi sallan asuba, har gari ya waye bata farka daga barcin da ya ɗauke ta ba.

     Kowa ya hallara wajen Breakfast amma ban da ita

Aunty Amarya tambayan Fadila tayi “where is she?”

Sai ta faɗa mata, “she was sleeping, she didn’t wake up”.

Har ta ce “taje ta taso ta sabida kar tayi lattin zuwa wajen aiki”

Amma Abbu ya ce, “su bar ta”.

Har suka gama Breakfast ɗin, shi da Fadil suka fice, Umma ta shige ɗakin ta, yayinda Fadila kuma ta koma cikin Parlour ta zauna abun ta tana aikin latsa waya

Aunty Amarya har ta koma ɗaki, sai kuma ta kasa jure wa, don tasan Ɗahira sarai, tunda ta kwanta ba lafiya ba, bare yanda take son Aikin ta, haka kawai yau ranan aiki ba zata ƙi fitowa ba in babu Dalili

Ɗakin ta wuce kanta tsaye don ta duba ta. Tana shiga ta hange ta saman gado ta rufe kanta da blanket, da sauri ta ƙarisa wajen gadon ta saka hannu ta yaye saman kanta, fuskar ta take kallo tana kiran sunan ta

A hankali Ɗahira ta buɗe idanuwan ta da suka yi ja, ta aza su kan Maman ta

“Baki da lafiya ne, me ke damun ki?” Ta jero mata tambayar a yanayin damuwa

Cikin matuƙar sanyin murya da ciwo yake cin ta tace, “zazzaɓi ne ya rufe Ni Mama”.

Cike da tausaya wa take mata sannu, kana tace mata, “ta tashi tayi wanka, inyaso sai ta sha magani bayan taci abinci”.

Babu yanda ta iya haka ta miƙe, da taimakon Aunty Amarya har ta ƙarisa Toilet

Ita kuma Aunty Amarya ta fice haɗo mata Breakfast don ta kawo mata har nan cikin ɗakin. Bayan ta haɗo mata ta kawo mata ta zauna zaman jiran ta.

     Kamar shuɗewar mintuna sha biyar Ɗahira ta fito a Toilet, ɗaure take da towel me tsawo iya ƙasan gwiwan ta, sai ta saka wani da ya rufe mata kanta zuwa kafaɗun ta

Tana fitowa Aunty Amarya tace, “yi maza ki shirya ki zo ki karya ki sha magani, kina likita amma kina wasa da shan magani, wataƙil ma tun jiya da kika yi kukan naki zazzaɓin ya kama ki amma kin zauna baki sha magani ba”.

Kallon ta Ɗahira tayi da sauri, sai kuma ta kawar da kanta cike da sanyin jiki ta kariso gaban Sip ɗin kayan su, buɗe wa tayi ta ciro doguwar rigan atamfa. Sai da tagama shirya wa kafin ta iso gaban aunty Amarya dake bakin gadon ta, a ƙasa ta zauna ta tanƙwashe ƙafa ta soma shan tea ɗin da ta haɗa mata, tana yi tana haɗa wa da bread kamar yanda Aunty Amarya ta umarce ta, sai dai tana cin ɗaya biyu taji kamar zata yi amai, ta kalli Aunty Amarya ta marairaice fuska kamar zata yi kuka tace, “zan yi amai bazan iya ci ba”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button