NAFEESAT 1-END

NAFEESAT Page 41 to 50 (The End)

              ⚫⚫⚫

       Direct ɗakin Maman ta tawuce, ta shiga ta kulle kan ta ta hau rusa kuka babu ji babu gani, kukan da ke taɓa mata zuciya, yake ƙara mata raɗaɗin da ke cinkushe a zuciyar ta. Sosai tayi kukan wanda har ya haifar mata da ciwon kai me tsanani

Ita da kanta ta rarrashi kanta tayi shiru, sai dai duk yanda taso ta danne abun da take ji a ranta, ta kuma jure baƙin cikin dake zuciyar ta, ta kasa, gaba ɗaya rauni ne a zuciyar ta, waye zai rarrashe ta? Waye zai kwantar mata da hankali har taji sanyi a ranta? Ya faɗa mata tayi haƙuri haka ƙaddaran ta take?

Lumshe idanuwan ta tayi, hawayen dake maƙale a cikin idanun ta suka zubo saman kuncin ta, ta saka hannu ta share tana me miƙe wa zaune, kanta ta riƙe tana jan majina

“Allah Sarki Mamana, da ace kina nan ke ce zaki share min hawaye na. Meyasa ne Ni kuwa bani da Sa’a a rayuwa ta? Menene aibu na? Shin me na tare wa Hajja da ta tsane Ni har haka? Ya Allah.. ka saka min juriya domin in tsallake wannan jarabawar taka”.

Miƙe wa tayi ta wuce Toilet ta ɗauro alwala ta fito, sallan magriba da isha’i ta gabatar, sannan tayi shafa’i da wutri, ta jima tana kwararo addu’a tana hawaye kafin ta shafa ta miƙe

Ta san Abbun ta ba anan zai kwana ba, sabida jama’a masu biki, kuma dama Aunty Amarya ce ke dashi, shiyasa ta kwanta a ɗakin tunda tasan ba ma zai zo Part ɗin ba.

     Daƙyar a ranan barci ɓarawo ya ɗauki Ɗahira.

⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫

              Ranan Saturday 25 March 2021. Aka shaida ɗaurin auren *AL’AMEEN ABUBAKAR AL’AMEEN* tare da Amaryan sa *SA’ADATU ABDULLAHI*

*SHAKIRA ABUBAKAR AL’AMEEN* da Angon ta *SAHABI MAHMUD*

Sai *YUSRA NOOR AL’AMEEN* tare da Angon ta *SULAIMAN HABIB*

*FADILA AL’AMEEN AL’AMEEN* da Angon ta *KHABEER ALH. MUNIR.*

        Ɗaurin auren da ya tara dubban jama’a ta ko ina, sai dai mu ce Masha Allah.

        Zuwa huɗu ko wacce aka kai ta ɗakin ta bisa umarnin su Big Dady, Fadila aka wuce da ita Katsina da sauran jama’a. Yusra kuma da Shakira duk a nan Kaduna za su zauna, gidan Yusra ma ya fi kusa da gidan su, kuma duk ka su biyun za su ci gaba da aiki a Hospital ɗin su, sabida sai da aka yi yarjejeniya da mazajen nasu kuma sun amince.

      Inda Baffa zai zauna kusa da gida ne, gini ne da aka yi musu shi da Usman a gefen gidan su, ga Gate ɗin gidan su ga nasu, sai dai kuma ta ciki a kwai ƙofan da aka yi wanda zai riƙa kai su cikin gidan su, ba sai sun yi wahalan fito wa ta Gate ba, wannan duk tsarin Kaka ne, shi ya siya filin kusa da gida, sabida yafi so iyalan sa su zauna waje ɗaya, har filin Fadil da yake ƙarami akwai shi an ajiye masa, idan ya tashi aure sai ya zauna a nan ɗin

Part ɗin Baffa dana Usman suna kallon juna ne, komi iri ɗaya aka yi musu, ɗakuna uku ko wanne da Toilet a ciki, sai babban Parlour da kichen a ciki da kuma wani Toilet, sannan idan ka fito waje ko wanne yana da faranda a ƙofan ɗakin, komi dai masha Allah, domin ba kaɗan ba an kashe kuɗi a ginin nan, su Big Dady duk suka yi musu komi babu ko ƙwandalan su, kayan ciki kuma suka bar musu su yi da kan su

To Part ɗin Baffa dai ya tsaru sosai, domin zance kuɗi yayi kuka a nan, iyayen Sa’adatu sun kashe mata kuɗi sosai, don ganin sun fito da ɗiyar su, itama zuwa dare aka kawo ta, can babban gidan aka fara kai ta, sai da aka kai ta wajen Kaka yasa mata albarka, sannan su Big Dady suka haɗa su da Baffa suka yi musu nasiha sosai. Daga nan kuma suka wuce wajen Hajja, inda itama tayi wa Baffa faɗa da nasiha sosai, akan “ya riƙe ta da amana, kar taji kar ta gani wajen ya muzguna mata, domin ita ɗin ƴar uwan sa ce, idan kuma aka ce ta kawo ƙarar sa, to wlh sai ta ɓata masa rai”.

Shi dai be ce komi ba, har ta ƙarashe faɗan ta ta sallame su, suka nufo gidan su.

Sai mu ce Allah ya ba da zaman lafiya Amare.

⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫

            Ɗahira dai taci bikin nan ne ba a daɗin rai ba, domin kuwa fama take yi da matsanancin zazzaɓi me zafi, kowa be san halin da take ciki ba, ko Kaka da take zuwan mishi hira, ƙin zuwa tayi bare ya san me ke faruwa da ita, shima be neme ta ba tunda ya san sha’anin biki ne

Fadila ita ke matsa mata tasha magani, domin sosai take bata tausayi, ita duk a ganin ta tana damuwa ne saboda rashin auren ta, bata san cewa Ɗahira ta kasa jure rabuwan da suka yi ne da Baffa ba, har yanzu abun na cin mata rai, shiyasa dole ciwo ya kamata.

           A haka Aunty Amarya ta dawo ta tarar da ita babu lafiya, hankalin ta yayi matuƙar tashi, duba da yanda ta dawo ta ganta gaba ɗaya ta rame a ɗan kwana biyu kacal da ba ta nan, babu wanda ya duba lafiyan ta, har kuka sai da Aunty Amarya tayi, nan ta kira Abbun su take sanar mishi

Shima hankalin sa ya tashi sosai, tare da ɓacin rai da ya nuna a kan Umma, tunda ai ita ce take zaune da su, amma ta kasa kula da ita, ga shi gida ya hargitse da ƴan biki, shi kansa ba kwana a Part ɗin yake yi ba, kuma ko da yana son ganin yaran sa, yawan jama’a bazai bar sa ganin su ba, shi duk a tunanin sa da ita ake bikin

Dole aka ɗaura mata drip, sabida sosai take jin jiki, duk hankalin su Kaka ya tashi matuƙa, irin su Hajja Fatu kuwa murna fal ciki, domin duk a ganin su baƙin cikin rashin auren ta ne ya saka mata damuwa

Su ma su Kaka abinda suke tunani kenan, shiyasa tayi matuƙar ba su tausayi, a ranan Kaka ya zauna da ƴaƴan sa meeting, inda suka yanke shawaran kawai za su haɗa auren Ɗahira da Usman, tunda dai baza su zuba musu idanu suna kallon su sun ƙi aure ba, sai dai babu wanda ya tayar da zancen, sun bari sai nan da kwana biyu, lokacin an gama huta wa da bikin nan da suka yi.

      Itama Ɗahiran sosai take samun lafiya, tunda ana kula da ita sosai

Baffa dai sau biyu yana zuwa gaishe ta, yanda Ɗahiran ta nuna masa ne, yasa shi jin daɗi, domin ko kaɗan bata sauya masa daga yanda suke da ba, gaba ɗaya ta nuna masa tamkar wani abu be faru tsakanin su ba, duk da a zuciyarta tana jin ƙaunar sa. Hakan sai ya mishi daɗi sosai, shima sai ya saki jikin sa yana jan ta da hiran da suka saba

A ranan na ukun ne da zai zo, suka taho da Sa’adatu don ta duba ta, amma daƙyar ta taho, don sai da suka yi faɗa da Baffa ɗin, da cewa tayi, “ba ta zuwa” amma da ya nuna mata ɓacin ran sa, dole ta biyo sa

Suna zuwa tayi mata ya jiki ta miƙe zata tafi, sai ta ga Baffa ma gyara zaman sa yake yi be da ninyan tafiya, ta kalle sa tace, “a’a ya haka kuma? Kai da za mu tafi kuma kake shirin zama?”

Kallon ta yayi, sai ya harare ta, sabida akwai Aunty Amarya a wajen, dayake suna zaune a Parlour ne har Ɗahiran. Kawar da kansa yayi ya soma jan Ɗahira da hira

Sai ta ja dogon tsaki tana faɗin, “Da kai fa nake yi ka zauna ina magana?”

A fusace Baffa ya kalle ta yace, “Ni sa’an wasan ki ne wai Sa’adatu? Ni ne zaki tasa a gaba sai ka ce ɗan ki?”

Murguɗa baki tayi ta hau jijjiga jiki, sai dai bata iya cewa komi ba sabida ganin yanda ya taso mata a fusace

Aunty Amarya ce tace dashi, “ya isa haka Miji na, tashi ka tafi tunda baka san me take buƙata ba, ka je kaji ka dawo anjima”.

“But wlh Aunty Amarya this girl…”

“ya isa tashi ka je kaji?” Ta katse sa da faɗan haka cikin lallami

Miƙe wa yayi yana kallon Ɗahira da ta kawar da kanta yace, “Sweet sister I’m leaving, I will be back soon, we have something to talk about, Allah ya ƙara lafiya kinji?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button