NAFEESAT 1-END

NAFEESAT Page 41 to 50 (The End)

Gyaɗa kansa yayi yana bin Doctor Said da kallo

A haka dai har Doc. Sa’id ya gama abinda zai mata, sannan ya zauna ana hira da shi

Sosai a nan Kaka ya sake fahimtar akwai wani abu a tsakanin su, inda lokaci ɗaya ya ji farin ciki a ransa, shiyasa ya sake jan Doc. Sa’id a jikin sa, ko ba komi nan da lokaci kaɗan zai ga auren Jikar tasa, ko kaɗan ba ya son ƴan uwan ta su yi aure su bar ta, sosai hatsarin nan ya sake ɗaga masa hankali.

     Ana haka su Aunty Amarya suka zo

Ɗahira taji daɗin ganin su sosai, nan ta sake sakin jiki ana ta hira gaba ɗaya, ga shi sosai take farin cikin yanda ake ba ta kula wa, musamman su Big Dady, da zaran mintuna ƙalilan ya wuce za su taho duba ta.

     Sai yamma duk suka tafi har Kaka.

     Kwanan ta biyar a asibitin tana samun kulawa, kafin aka sallame ta, ta koma gida tana ci gaba da jinya. A haka har ta samu sauƙi sosai, inda ta nemi ta koma bakin aikin ta, amma sai Abbu ya hana ta tunda har yanzu ɗingishi take yi.

    Sai da aka shafe kusan sati Uku kafin ta warware, sannan ta koma bakin aikin ta, zuwa yanzu sosai Ɗahira da Doc. Sa’id suke mutunci, koda aka sallame ta a Hospital be taɓa zuwa gidan su ba, amma kuma suna waya sosai, hakan yasa suka saba, har ita Ɗahira tana tunanin son ta yake yi, sabida yanda yake ba ta kula wa ainun, shiyasa ma ta sake sakin jiki sosai da shi, sai dai har yanzu kalman da take so taji a bakin sa ya ƙi ya sanar mata, ko kaɗan ba ta ƙaunar a sake zaman meeting ba tare da tana da tsayayye ba, sai dai babu yanda zata yi tunda be ce yana son ta ba har yanzu, sai ma daga baya ta gane yana da mata har da ƴaƴa biyu, amma hakan be ɗaga mata hankali ba, a ganin ta idan yana son ta zata iya auren sa, tunda duk wani ɗabi’u na kirki shi yake nuna mata, sai dai lokaci na ta ja babu wannan kalman a bakin Doc. Sa’id, ga shi har yanzu saura sati biyu auren ƴan gidan.

        Kamar yanda suka saba meeting ranan Lahadi, haka wannan Lahadin aka tara su, Ɗahira aka soma tambaya, amma tace musu “bata da wanda take so” maganar ya girgiza su

Kaka yace, “kina nufin wannan Doctorn har yanzu be yi miki ba?”

Kallon Kaka tayi tace, “Kaka ai ba soyayya muke yi da shi ba, it’s just Friendship”.

“Uwata dama ai ta hakan ne soyayya take ƙulluwa, ke dai kawai ki sanar mana idan da akwai wani abu a tsakanin ku, kar ki zauna ki ce zaki ja mishi aji kinji ko?”

Gyaɗa kanta tayi kafin kuma tace, “amma Abba wlh be taɓa cewa yana so na ba, kuma ma yana da iyalan sa”.

Shiru suka yi duk kan su, kafin kuma Kaka ya sake Tambayan Usman da cewa, “to kai kuma Fodio aina taka take?”

“Nima Kaka har yanzu ban samu wacce nake so ba”.

“Kana nufin har yanzu maganar da muka yi maka baka ɗauke ta da muhimmanci ba?” Big Dady ya faɗa yana kallon sa

Shiru Usman yayi kansa a ƙasa

Nan Dady ya dinga faɗa kamar zai ari baki, kuma ya ce “dole sai yayi aure da ƴan uwan sa, idan be samo matan ba shi yana da hanyar da zai samo masa”

Kaka ne ya tsayar da shi da faɗin, “ƙyale shi Noor, duk hakan be ta so ba, yanzu dai aci gaba da hidiman biki kar a fasa, su kuma Allah ya kawo musu na gari, lokacin su ne be yi ba babu yanda zamu yi da su”.

Daga haka ba’a sake yin wata maganar ba, aka sallami kowa.

     Inda daga ranan gadan-gadan aka ci gaba da hidimomin biki, ko wanne fanni suna nasu, tunda kowa a cikin su zai aurar, illa Aunty Amarya ce kaɗai da babu ita, amma kuma komi da ita ake yi ana Fadila, duk ita take shirin komi, sai ƴan uwan Umman dake nasu, duk da suna yaɓa mata maganganu amma ko bi ta kansa ba ta yi, abinda yafi ɗaga mata hankali yanda gidan duk ya cika da mutane, babu hiran da suke yi sai na Ɗahira, wai “har yanzu bata da mashinshini, tayi kwantai, maza ma tsoron zuwa wajen ta suke yi, bare su furta mata suna son ta.” Kowa ba ya lura ba ita kaɗai bace a gidan da baza ayi auren ta ba, har da Usman, shi da yake ma babban su amma yaƙi auren, amma ita kaɗai ake gani

Sanda Ɗahira ta soma jin ƙananun maganganun nan bata wani damu ba, sai dai yanda ƴan uwa suke taran ta da maganar, har wasu suna mata Shaƙiyanci suna yaɓa mata magana, sai abin ya soma damun ta, amma babu yanda zata yi haka take barin abun a ranta, duk da ita bata cika iya ɓoye damuwa a ranta ba, ko ya ya ne idan har tana da damuwa sai ka gane..

        Gida fa ya sake cika maƙil inda har an soma events, duk da ba kowa bane ke wajen, wasu sun tafi can Katsina, Hajiya Laila ma can ta tafi, sai su Firdausi da sauran ƴaƴan ta masu aure da suka zo nan, Aunty Zainab ma da ita da Aunty Amarya, ana gobe suka wuce can a bisa umarnin Kaka, tunda ba za’a bar Hajiya Ikram ita kaɗai tana biki babu ƴan uwa ba, kowa ya zo nan ya shantake, wasu ma zuwa gobe ranan bikin za su wuce idan za’a kai Fadila can, sai su kwana biyu wasu kuma su yi kwana ɗaya.

       Tun ana kwana biyu Sa’adatu ta koma Legos, sai ranan bikin za a kawo ta.

⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫

         Dafa ta Fadila tayi, hakan yasa tayi firgigit tana kallon ta

“What are you thinking sister, I’m talking to you are you quiet?”

Murmushin yaƙe Ɗahira tayi, sai ta gyaɗa kanta tana son mayar da hawayen dake cikin idanun ta tace, “nothing”.

Cike da tausayin ta Fadila tace, “don Allah ki dena saka damuwa a kan maganganun su Inna, ko ma su waye ne zasu yi miki gori don Allah ki dena saka damuwa kinji, ke baki ga yanda kika faɗa bane? Ana bikin mu amma gaba ɗaya kin tsame kanki a cikin mu”.

Shiru Ɗahira tayi, don bata san me zata ce mata ba

Sai itama Fadilan tayi shiru, sai dai bata tashi a wajen ba. Tsawon lokaci suna a haka kafin Fadilan ta kalle ta tace, “Sister, there is something I want to tell you, akwai maganar da naji wajen Hajja da Shakira, shiyasa naga dacewan in faɗa miki”.

_What do you think Fadila will tell her? ????_

_mu je zuwa yanzu aka soma._

[6/8, 8:45 AM] Oummu Ɗahirah: ????????????????????????????????????????

              *FAMILY DOCTOR’S*

                         ????

????????????????????????????????????????

????????????????????????????

   *NAFEESAT RETURN*

????????????????????????????

*MALLAKAR:*

                 _NAFISAT ISMA’IL LAWAL_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT* ????????‍

*بسم الله الرحمن الرحيم*

*PERFECT WRITER’S ASSOCIATION*????

“`( WE AIN’T PERFECT BUT WE’RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS ????)“`

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

               *P.W.A✍️*

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattapad: UmmuDahirah*????

        

*SADAUKARWA*

_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA’S FAMILY*_

        *EPISODE 29 & 30*

         Idanu Ɗahira ta zuba mata tana jiran taji me zata faɗa

Fadila tace, “na lura a gidan nan Hajja ba ta ƙaunar ki, kuma ba ita kaɗai ba har ta da Shakira, domin tasha sanar dani abu game dake domin ta haɗa mu faɗa, ban taɓa biye mata ba, sabida narigada nasan abinda ke cikin ranta. A kwanaki biyu da suka wuce na ji su suna zancen ki, maganar rashin samun tsayayye ne da baki dashi, suna faɗin hakan yayi musu daɗi, har suna cewa Allah yasa ma ki dauwama a haka baza ki taɓa aure ba, sannan Hajja take cewa koda ma kin samu, ita tayi alƙawari baza ta taɓa barin ki ki zauna da mijin ki lafiya ba, duk yanda za’a yi sai tayi don raba ki da Mijin, sai ta mayar dake ƙaramar bazawara idan kin yi aure, idan kuma baki yi ba, zata bi duk hanyan da taga zata iya wajen hana ki aure”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button