NAWA BANGAREN

NAWA BANGAREN COMPLETE

NAWA BANGAREN COMPLETE HAUSA NOVEL

Kai tsaye Wuro barka ta dira inda tayi wani babban lulluɓi a unguwarsu Bobbo.


Washe gari da safe su Mamma suka duƙufa zuwa gidan Malam Rabi’u . Wani ɗan ƙaramin gida ne a ido amma cikinshi babba ne sosai, mutane sai shige da fice suke yi a gidan kowa da matsalarshi , kasancewar Malam sanannen malami ne , daga garuruwa daban-daban ake zuwa neman magani , kuma alhamdulillahi ana dacewa . Yana zaune kan kujerarshi su Bobbo suka shigo . Wuri suka samu suka zauna kan Wata ƙatuwar tabarma , “Me kike yi tare da su ” ya tambaya , Mamma ta kalli Asama , Asama ta kalli Mamma , malam Rabi’u ya ce “da ta bayanku nake “, juyawa suka yi har su Baffa , banda Bobbo da yake jin wani matsanancin ciwon kai .

“Ina take ?” Mamma ta tambaya , “Gata nan tsaye bayan Sadauki ” Malam Rabi’u ya faɗa yana nuna saiti da inda Bobbo yake , sannan ya ce “Malama ki faɗa min me kika biyo su yi nan ” , Nahad ta ce “So nake a cike min ɓangarena ” ,Malam Rabi’u Ya ce “To zauna ayi magana “, Zama Tayi gefen Bobbo wanda shi yana ganinta kuma yana jinta kusa da shi .

Malam Rabi’u ya ce “A zahirin gaskiya Zan faɗa muku ɗanku ba halitta ba ne kamar ku ” , Baffa ya ce “Ban Fahimta ba . Me kake nufi “, Mamma kuwa tuni ta fara zarar ido , Malam Rabi’u ya ce “Ni ka san mutum ne da Allah ya ƙaddara da tarin Rauhanai haka yasa nake ganin abubuwa “, Mamma ta ce “Malam ni dai bana son sai an faɗa ,ɗana mutum ne kamar kowa ” , Baffa ya ce “ Ki mana shiru wallahi ,na lura duk lokacin da aka zo wurin nema ma Bobbo magani sai kin hana ” , Malam Rabi’u ya jinjina kai ya ce “Dole ta hana , yanzu dai ba wannan ba zan yi bincike ku bani minti biyar ” , idonshi ya rufe ya kira Aljani ya ce “Ka tabbatar min da maganar da nake ji , ka zagaya cikin ƴan daƙiƙu ka dawo min ina jira ” , wannan alhajin ya tashi . Bayan ɗaƙiƙa 30 ya dawo , bayanan daya samo ya zayyanawa Malam Rabi’u , sannan ya ɓace .

Malam Rabi’u ya ɗago ya kalli Su Baffa yana faɗin “Mahaifiyar Sadauki…………

Anan zan dakata sai mun baɗu a next chapter dan jin yadda zata kasance a wannan littafin mai suna NAWA ƁANGAREN.

LOVE U ALL .

NASMERH LIMAN
09121873529
[8/6, 3:08 PM] QUEEN-NASMAH ❤️✍️: NAWA ƁANGAREN

HAƘƘIN MALLAKA : QUEEN-NASMAH

????MOONLIGHT WRITER’S ASSOCIATION????
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

”’We are the moonlight writers we shine all over the world.”’
بِسم الله الرحمن الرحيم

????????    ????????    ????????
*Wohoho ! Garin daɗi na nesa ungulu ta leƙa masai . Wani Kaya Sai amale shin kun san k'ayatattun magungunan Mata na maman Haidar ko kuwa an bar ku baya *
*To ƴar uwa Kayan maman Haidar basu da matsala domin traditional medicine ne Kuma Ana had'asu da ingantattun kuma nagartattun itatuwa masu aminci da karfi da Basu da wata illa sai ma taimaka miki da zasu yi. Malam bahaushe dai ya ce In kana da kyau ka ƙara da kwalliya* ????????*Akwai wani ingantacce hadin. Manyan Mata da mamàn haidar takeyi bakowa takewa wnnn hadinba sai me matsaloli. Allah ya yaye sabida karfinsa Wanda yasan yanada kudin yi saiyay magana*
*Sannan Akwai wasu mayatattun kayan haɗi masu Matuƙar ƙarin Ni'ima da mamàn haidar take yi.

 *1 Gumbar kankana da aya* 
3 *Gumbar Madara da kwakwa*
4 *Kaza me ƙwai *
5 *Zabo me zuma*
6 *Kaza me allurai, sahihiyar hanyar zaki mallake mijinki ƴar uwata ba boka ba malami*
7 *Kwallin idonka inadona*
8 *Tauwadar mata*
9 *ketar larabawa magani me kankarowa mace kima da daraja*
10 *Maganin sanyi me fatattakarsa duk kuwa nacinsa Koda bakya haihuwa indai matsalar sanyice gwada wnnn*
11 *Maganin nono. Sahihi* 
12 *Maganin hips and bobbs* 
13 *hodar. Ni I'ma koramar mata*
14 *nakasan Mara babban sirri*
15 *kafi jijjibi*
16 *daga Sha Sai wanka kasaitacce magani*
17 *Dan kwankwalati namata da mazajensu Kevin Mata* 
18 *matsin kinfi budurwa dubu ko haihuwa nawa kikai Babu magana*
19: akwai magani maza , da kuma maganin Feeling both gender Mata da maza .
*Maman haidar Bata tsaya anan ba*
*Tana Saida hijabai da yadikansu akan farashin sari yadika dila dila, hijaban Ƴan gayu sannan*
*ta kawo muku hadaddan sabulun gyaran jiki da hadin dilka Me sa shek'i da laushin fata, ga kuma mayukkan kitso Wanda laraba ke amfani dashi inkin gwada sai kin dawo ku dai ku neme Maman Haidar a wannan number domin neman ƙarin bayani*????????  08146017245

----------------------
_You’re a blessing to me and everyone that comes across you. Thank you so much for coming into my life and being my light. I appreciate the love and colors you bring into my world. You may not understand how much it means to me._*HABEEB-ALBI*

€pisode 23..................

 Malam Rabi'u ya ɗago ya kalli su Baffa yana faɗin “Mahaifiyar Sadauki na ɗauke da cikin Bobbo wata ɗaya cif , a wannan daren Aljani Mazbandala ya saka ƙwanshi a cikinta ", Baffa ya ce “Tabbas Mamman Sadauki ta wahala matuƙa cikin Sadauki , a lokacin tagwaye ta haifa ɗaya ya zo ba rai ɗaya kuma ya tsaya shi ne Sadauki ", Malam Rabi'u ya ce “Wanda ya mutu shi ne ɗanku , ya mutu ne saboda jaririn ɗanku bazai iya rayuwa tare da Sadauki ba " , hawaye na bin kuncin Mamma ta miƙe tsaye , Malam Rabi'u ya kalle ta cikin tausayawa ya ce “Zauna na fahimce ki , Mahaifiyar Sadauki ta riga ta san sirrin tun Sadauki na shekara bakwai duniya , dalilin da yasa ta ƙirƙiri tafiya zuwa Zuru ganin wani malami , malamin ne ya sanar da ita halin da Bobbo yake ciki , anan ne aka rage mishi ƙarfinshi na halittarshi , wannan dalilin yasa Mamman Sadauki bata so a san gaskiya ", Arɗo ya ce “Amma Mamma bai kamata kiyi shiru ba  , ina amfanin baɗi ba rai ", cikin kuka da faɗa Mamma ta ce “To ko ka ƙi ko ka so Bobbo ɗan uwanka ne , daga Cikina ya fito kuma ni na shayar da shi ,kuma ina sonshi", Arɗo ya ce “Ai bazan guje shi ba ko da ba komai Bobbo bai taɓa ƙin girmama ni ba " , Baffa ya ce “Yanzu malam ya za a yi ", Malam Rabi'u zai yi magana Mamma tayi karaf karɓi zance da cewa “Ba wani abun da za a yi , in duk duniya zata taru babu mai Rabani da Sadauki " jinjina kai Malam Rabi'u yayi tare da faɗin “Tabbas babu wanda zai raba ki da Sadauki sai Allah , a taƙaice ma asalin mahaifin Sadauki ya mutu a Farmakin da Sarki Zawatunduma ya kaima garin Mubanuwa " ,  Bobbo sai jin su yake yi amma shi abunda suke yi bai dame shi ba .

Nahad dake tsaye ta ce “Malam shi ne Nawa ɓangaren ka bar mu tare da shi ", Malam Rabi'u ya ce “Ki fito a siffar da bazai wahala ba  " , Baffa ya ce “Ya kamata a kare aikin da aka mishi saboda ya samu yayi rayuwa irin wadda Allah ya mishi ba mai kauce ƙaddararshi " , Mamma dai yanzu hankalinta ya kwanta dan dama duk fargabanta bai wuce a ce yau an raba ta da Sadauki ba , ko kuma za a raba ta da shi ba .

Nan Malam Rabi'u da Arɗo suka shiga da Sadauki bisa umurnin malamin . Baffa ya bi bayansu aka Bar mamma da Asama zaune .
Nahad kuma na tsaye.

_________________________

Ɓangaren Hajiya Maryam kuwa ta tashi tun safe tana mai mugun jin kunyar Alhaji Sulaiman , haka yasa ta yi wanka ta shirya tsaf cikin wata ƙyatattar riga wadda ta zauna a jikinta , kitchen ta shiga ta ɗora mishi abinci da ya fi so fiye da kowane abinci wato Shinkafa da wanke da miyar kifi da salat ,  wanda ta yanka ziri-ziri ƙanana-ƙanana tare da Albasa da tumatur .  Ta haɗa mishi zoɓe wanda ya ji haɗin kayan ƙamshi da yaji , ya kuma ji cucumber Dan ƙamshinta Sai tashi yake yi , sannan ya zuba a basket da plate da cup ,  ta kai mishi har ɓangarenshi .

Yana zaune yana taɓa duba wasu takardu Hajiya Maryam ta shigo da sallama a bakinta riƙe da basket a hannunta . Amsa mata yayi yana tattare takardun ya aje gefe ɗaya , Cikin jin kunya ta  aje kwandon abinci , ta ɗago ta ce “ga wannan na san zaka so shi " , murmushi yayi ya ce “Na gode Amaryata Allah ya miki albarka ", wani nannauyan numfashi ta sauke tare da kallonshi ba tare da ta ankare ba kawai sai ki tayi hawaye na kai kawo a kuncinta , da sauri Alhaji Sulaiman ya tashi ya durƙusa gabanta tare da sa hannun ya share hawayen dake bin kuncinta yana girgiza kai alamar kar tayi kuka , cikin rawar muryar dake nuna mutum na ƙoƙarin shanye hawaye ta ce “Haƙiƙa mijina na tafka Babban kuskure , kuma ina Dana sanin aikata hakan , dan Allah mijina kayi haƙ......... " , hannunshi ya ɗora kan bakinta ya ce “Shhhhhhh , kar ki ce komai . Mafi alkhairin mutum shi ne wanda yayi kuskure kuma ya fahimci kuskurenshi , ki gode ma Allah da yake sonki da rahamarsa har ya ganar dake gaskiya cikin dubunnin mutane , badan kin fi so ba , amma dai ya zaɓe cikin masu rabo daga rahamarsa , ki ɗauka hakan darasi ne gare ki da kuma ƴan baya " ,  hawaye suka ƙara gangaro mata .ta ce “Haƙiƙa da ni Maryam ban aure ka ba ban san wane mijin zan aura mai adalci kamar ka ba ,  kai ɗin nan mutum ne mai Matuƙar arziki , idan na ce maka arziki ba wai iya duniya nake gane maka ba , ina hango maka lahirarka " , ƴar dariya yayi yana miƙewa tsaye tare da ɗaga ta tsaye itama .suka zauna gefen gado . jawo ta yayi sosai ya manna a ƙirjinshi ya ce “Hajiyata mutum baya ganin gobenshi . Ke ɗin nan ba za ki iya gane ɗan aljanna da ɗan wuta ba sai an je can , mutum zai kasance yana aikin lada iya rayuwarshi amma rana ɗaya ya tafka babban kuskuren da zai jefa shi wuta , haka ma mutum zai kasance yana ɓatanci tsawon rayuwarshi , amma Maryam in Allah na sonka da rahamarshi sai ya sa kayi aikin alkhairi ɗaya wanda zai maye maka gurbin kura-kuranka , ke dai kawai kiyi fatan Allah yasa mu cika da imani " , Rufe ido tayi cikin soyayya ta ce “ba ja in ja na gamsu da duka bayananka mijina " sai kuma tayi saurin tashi daga ƙirjinshi tana faɗin “Baka ci abinci ba fa ", “Zan ci matata , ki zuba min tare zamu ci " ya faɗa  , zuba mishi abincin tayi suka ci tare cikin raha da annashuwa .


-------------------------

Bayan awa uku Malam Rabi'u da su Bobbo suka fito daga ɗakin . Nahad ta nufi Bobbo da gudu wanda yanzu ya kasance kowa yana ganinta ta rungume shi , lumshe ido yayi yana ji wani mugun sonta har zuciyarshi . “Mu je muyi shirin aure " Nahad ta faɗa . Bobbo ya kalli su Mamma ya ce “muna gayyatarku ku kaɗai zuwa aurenmu jibi da misali 2:30 na dare " , Mamma da Su Baffa suka tsaya turus suna kallon Bobbo ko ya manta su mutane dare lokacin barcinsu ne . Nahad ta ce “Kar ku damu daren jibi zai kasance kamar safiya gare ku " . Malam Rabi'u ya kalli agogonshi ya ce “Yanzu lokacin dana ɗibar muku yayi zaku iya ci gaba da labarin waje mutane na jira na " , sosai su Baffa suka gode mishi , Nahad ta mishi kyautar sarƙar Murja ni da lu'ulu'u .


_________________________

Waje suka fito inda Bobbo ya riƙe hannun Nahad ya ɗaga sama ɓat suka ɓace sai gidansu Nahad . Hajiya Maryam da His excellency Alhaji Sulaiman suna tsaye gaban mota , yayin da sojoji suke tsaye kamar yadda suka saba jerawa duk sun ƙame , kawai kawai suka ji wata gigitacciyar ƙara , nan take duka sojojin suka saita bindinga , iska ya taso ko ina kaɗawa yake yi , “Ummana !" Suka jiyo sautin muryar Nahad , da sauri suka juya yayinda sojojin suka juyar da bindingarsu ga Nahad tare da saita harsashensu . His excellency ya musu umurni cikin tsawa akan su aje bindiga , jikinsu na rawa suka sauke bindigoginsu .


Nahad da idonta suka yi ja ta tunkaro iyayenta tana riƙe da Bobbo , Kallon Alhaji Sulaiman tayi ta ce “ Abbana Na gode , Na gode da zama da ni da kayi duk da na kasance bana ji , duk da na kasance ina janyo maka hasara , Amma duk da haka ka baka gaji dani ba , kayi haƙuri . Ni zan koma Nahiyarmu , asalin inda na fito " , kanta ya dafa ya ce “ke kamar ƴa ce a gare ni ba sai kin min godiya ba ,Allah ya miki albarka ", “Ameen " Hajiya Maryam da Bobbo suka amsa , yayinda Nahad ta ci gaba da magana “Abba da Umma ni ɗin nan da kaina ina gayyatarku zuwa wajen aurena da Nawa Ɓangaren , ɓangaren nan da nake yawan baki labari Umma , yau dai burina ya cika , zamu yi aure da shi jibi da misalin ƙarfe biyu da rabi na dare , 


“Daddare fa kika ce ? " Hajiya Maryam ta faɗa cikin sigar tambaya . Nahad ta gaɗa kai tare da kallon Bobbo, gaɗa mata kai yayi yana murmushi , Alhaji Sulaiman ya ce “Allah ya kai mu , ni bari na wuce , zan yi meeting da ƴan majalisu " , Hajiya Maryam ta ce “Allah ya tsare hanya " , da ameen ya amsa , sannan ɗaya daga cikin sojajin ya buɗe mishi mota ya shige , motoci guda biyar kamar kullum suka fita .


Nahad ta ce “Umma zan je in nemo Naheela a yau ɗin nan " , Hajiya Maryam ta kalli Bobbo ta ce “Ka kula min da Nahad " . Nahad ta ce “Kar ki damu zan iya wannan " , Hannun Bobbo ta riƙe tare da rufe idonta Shima yadda ta rufe ido haka yayi , suka ɓace a tare ...........To masu karatu yau gashi dai na muku da yawa . 


Anan zan dasa aya sai gobe


LOVE U ALL .


NASMERH LIMAN
09121873529
[8/7, 1:11 PM] QUEEN-NASMAH ❤️✍️: *NAWA ƁANGAREN*

HAƘƘIN MALLAKA : QUEEN-NASMAH 


*????MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION????*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.'''* 
بِسم الله الرحمن الرحيم

???????? ???????? ????????
*Wohoho ! Garin daɗi na nesa ungulu ta leƙa masai . Wani Kaya Sai amale shin kun san k’ayatattun magungunan Mata na maman Haidar ko kuwa an bar ku baya *
To ƴar uwa Kayan maman Haidar basu da matsala domin traditional medicine ne Kuma Ana had’asu da ingantattun kuma nagartattun itatuwa masu aminci da karfi da Basu da wata illa sai ma taimaka miki da zasu yi. Malam bahaushe dai ya ce In kana da kyau ka ƙara da kwalliya ????????Akwai wani ingantacce hadin. Manyan Mata da mamàn haidar takeyi bakowa takewa wnnn hadinba sai me matsaloli. Allah ya yaye sabida karfinsa Wanda yasan yanada kudin yi saiyay magana
*Sannan Akwai wasu mayatattun kayan haɗi masu Matuƙar ƙarin Ni’ima da mamàn haidar take yi.

1 Gumbar kankana da aya
3 Gumbar Madara da kwakwa
4 *Kaza me ƙwai *
5 Zabo me zuma
6 Kaza me allurai, sahihiyar hanyar zaki mallake mijinki ƴar uwata ba boka ba malami
7 Kwallin idonka inadona
8 Tauwadar mata
9 ketar larabawa magani me kankarowa mace kima da daraja
10 Maganin sanyi me fatattakarsa duk kuwa nacinsa Koda bakya haihuwa indai matsalar sanyice gwada wnnn
11 Maganin nono. Sahihi
12 Maganin hips and bobbs
13 hodar. Ni I’ma koramar mata
14 nakasan Mara babban sirri
15 kafi jijjibi
16 daga Sha Sai wanka kasaitacce magani
17 Dan kwankwalati namata da mazajensu Kevin Mata
18 matsin kinfi budurwa dubu ko haihuwa nawa kikai Babu magana
19: akwai magani maza , da kuma maganin Feeling both gender Mata da maza .
Maman haidar Bata tsaya anan ba
Tana Saida hijabai da yadikansu akan farashin sari yadika dila dila, hijaban Ƴan gayu sannan
ta kawo muku hadaddan sabulun gyaran jiki da hadin dilka Me sa shek’i da laushin fata, ga kuma mayukkan kitso Wanda laraba ke amfani dashi inkin gwada sai kin dawo ku dai ku neme Maman Haidar a wannan number domin neman ƙarin bayani???????? 08146017245


My hearts stereo it beat for u so listen close. Hear my thoughts in every note . Make me ur radio. Turn me off when u feel slow . HABEEB-ALBI

€pisode 24……………..

Nahad da Bobbo Sun bazama neman Naheela amma duk zagayen duniyar nan sun yi shi amma sun gagara gano ta , wanda a ɓangaren Naheela ya kasance jikinta ya bata ƴar uwarta na nemanta . Naheela ta riga ta san daga gare ta ne shiyasa Nahad bata samu ganinta ba , kowa ya san irin ƙarfin sihirin Naheela . Hannunta ta miƙe duka hannayen suka wani ƙamƙame , sai kuma ta miƙe yatsanta ɗaya wanda ya fara fitar da wani hayaƙi , idonta kuma na fitar da wani haske , wannan hayaƙin dake fita ya dawo takobi . Duk abun da Naheela ke yi Naheel yana kallonta .

Kallon takobin Naheela tayi ta ce “Kiyi musu jagora zuwa gare ni ” , sai ta ɗauki takobin ta saita bangon wurin ka cilla ta , buɗewa bangon yayi wannan takobin ta shige sannan ya rufe .

Ɓangaren su Nahad kuwa suna nan zaune Nazarin wata hanya , tunda su ba kamar sauran Aljanu ba ne ,rabinsu mutum rabi aljan. Kwatsam sai ga wata farar takobi mai Matuƙar sheƙi ta zo , a jikinta an rubuta «TAKOBIN SARAUNIYA NAHEELA» da manyan haruffa . Miƙe Nahad tayi tana faɗin “Duk yadda aka yi wannan takobin zata taimaka , mu bi bayanta ” , Bobbo ya ce “Naheela ce ta aiko da ita da kanta ” .
Hannun Bobbo Nahad ta riƙe , sannan ta riƙe takobin da hannu ɗaya ɓat suka ɓace sai wurin Naheela.

Naheela zaune gefen Naheel da yanzu ya fara sabawa da ita su Nahad suka shigo . Miƙewa tayi ta rungume Nahad cikin kuka ta ce “Barka da zuwa Masoyiyar ƴar uwata ” , kuka Nahad ta fashe da shi , Naheela ta jaye ta daga jikinta tana kallonta cikin Matuƙar soyayya ta ce “Ki daina kuka ƴar uwata mun haɗu daga ƙarshe ” , gaɗa kai Nahad tayi tana murmushi ta ce “Eh bayan shekaru masu yawa gashi mun haɗu ” , Naheela numfasa ta ce “muna da sauran rayuwa a tare ƴar uwata ” , gaɗa kai Nahad tayi .

Naheela ta maida dubanta ga Bobbo sannan ta kalli Nahad ta ce “Miyasa nake ji a jikina aurenku gobe ne ke da Ibrahim Sadauki “, Sam Nahad bata yi mamaki ba kasancewar ko ita tana jin irin haka a jikinta , Nahad ta ce “Eh gobe ne da yardar Allah ” , kallon Naheel Tayi ta tunkare shi ta ce “Naheel zan lunka ƙarfin ikona gare ka domin na tabbatar an yi aurenmu tare da su Nahad ” , “Naheela !” Naheel yayi maganar ba tare da ya san ya furta ba , Naheela ta ce “Bazan saurare ka ba Naheel ka kalli idona kawai ” tayi maganar da ƙarfi wanda yasa ko ina amsawa , juyar da fuskarshi yayi yana faɗin “bazan kalle ki ba ” , zara-zaran faruttanta ta miƙe ta juyo da fuskarshi Yadda zai fuskance ta tana faɗin “Na ce ka kalle ni baka ji ” , “Ni na ce bana so na kalle ki baki ji ba ” ya faɗa shi ma a fusace.

Nahad ta sako Wata wata mai ƙarfi daga idonta zuwa tsakiyar bayan Naheela , wannan wutar ta janyo hankalin Naheel ya ƙura Mata ido yana kallon cikin idonta dan ya ga yanayinta , bai san tarko ba ne , kawai wani ɗan ƙaramin dutsi ya fito daga idon Naheela da ƙarfin gaske ya shige idon Naheel . Ji yayi kamar an zuba mishi wasu ruwa masu Matuƙar sanyi duk ilahirin jikinshi , sai kuma ya ji zuciyarshi ta wanke tas kamar ba ita ba ,da sauri ya miƙe tsaye a gigice ya jawo Naheela cikinshi yana faɗin “Ina sonki Naheela !” hawaye suka gangoro mata a kunci ta ɗaga hannunta sama tana murmushi ta ce “Alhamdulillahi !”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Leave a Reply

Back to top button