NAWA BANGAREN

NAWA BANGAREN COMPLETE

NAWA BANGAREN COMPLETE HAUSA NOVEL

”’We are the moonlight writers we shine all over the world.”’
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~
???????? ???????? ????????
*Wohoho ! Garin daɗi na nesa ungulu ta leƙa masai . Wani Kaya Sai amale shin kun san k’ayatattun magungunan Mata na maman Haidar ko kuwa an bar ku baya *
To ƴar uwa Kayan maman Haidar basu da matsala domin traditional medicine ne Kuma Ana had’asu da ingantattun kuma nagartattun itatuwa masu aminci da karfi da Basu da wata illa sai ma taimaka miki da zasu yi. Malam bahaushe dai ya ce In kana da kyau ka ƙara da kwalliya ????????Akwai wani ingantacce hadin. Manyan Mata da mamàn haidar takeyi bakowa takewa wnnn hadinba sai me matsaloli. Allah ya yaye sabida karfinsa Wanda yasan yanada kudin yi saiyay magana
*Sannan Akwai wasu mayatattun kayan haɗi masu Matuƙar ƙarin Ni’ima da mamàn haidar take yi.

1 Gumbar kankana da aya
3 Gumbar Madara da kwakwa
4 *Kaza me ƙwai *
5 Zabo me zuma
6 Kaza me allurai, sahihiyar hanyar zaki mallake mijinki ƴar uwata ba boka ba malami
7 Kwallin idonka inadona
8 Tauwadar mata
9 ketar larabawa magani me kankarowa mace kima da daraja
10 Maganin sanyi me fatattakarsa duk kuwa nacinsa Koda bakya haihuwa indai matsalar sanyice gwada wnnn
11 Maganin nono. Sahihi
12 Maganin hips and bobbs
13 hodar. Ni I’ma koramar mata
14 nakasan Mara babban sirri
15 kafi jijjibi
16 daga Sha Sai wanka kasaitacce magani
17 Dan kwankwalati namata da mazajensu Kevin Mata
18 matsin kinfi budurwa dubu ko haihuwa nawa kikai Babu magana
19: akwai magani maza , da kuma maganin Feeling both gender Mata da maza .
Maman haidar Bata tsaya anan ba
Tana Saida hijabai da yadikansu akan farashin sari yadika dila dila, hijaban Ƴan gayu sannan
ta kawo muku hadaddan sabulun gyaran jiki da hadin dilka Me sa shek’i da laushin fata, ga kuma mayukkan kitso Wanda laraba ke amfani dashi inkin gwada sai kin dawo ku dai ku neme Maman Haidar a wannan number domin neman ƙarin bayani???????? 08146017245


You are the reason why I wake up with eyes full of dreams. You are the reason why I go to sleep knowing everything is alright in my life. But most of all, you are the reason why I feel happy all the time. HABEEB-ALBI

€pisode 25(LAST EPISODE)……………..

Ihun aka tsagaita da yi , Naheela ta fara magana cikin kuka , “A yau ina godiya gare ka Abbana ƙaunarka gare ni ce ta nuna min hanya wadda ta zama babban haske gare ni , ban san iya yadda zan misalta muku farincikin da nake ciki ba amma Ina farinciki , duk a ranar yau na haɗu da Mahaifiyata kuma Na samu cikar farincikina , a NAWA ƁANGAREN sai dai in ce Alhamdulillahi dan komai daidai ne ”  Kallon Naheel tayi ta ce “Ina fatan zaka bani sauran farincikin da nake buri ” gaɗa kai yayi ya janyo ta tare da Rungume ta ya ce “Tun daga lokacin da macijin aure ya naɗe mu Naheela na ɗauki alƙawarin kasancewa da ke tare da baki duk wani farinciki da kika cancanta , na gode miki sosai da bani sabuwar Rayuwa mafi inganci ,kin ciƙa ɓangarena da duk wata daraja da ya cancanta ke ce ɓangarena ina Matuƙar alfahari da hakan “,  nan ma ihu aka ci gaba da yi , Nahad ma magana ta fara yi cikin rawar murya “Duk da ban samu kasancewa da kai ba Abban ina so sani so nake Maka mara misaltuwa , ina miƙa godiyata zuwa ga mutumin da ya zame min uba lokacin da bani da kai , ban san da wane baki zan gode mishi ba amma dai ina mishi kamar ɗa da mahaifi , A yau da zan fara sabuwar rayuwa a duniyarmu ina so in gode miki Ummana da yaya Ahmad kun jure duk wata halayya tawa saboda haka Allah ne kaɗai zai biya ku ” . Hajiya Maryam da Ahmad sai kuka suke yi . Sarki Zawatunduma da sauran mutanen Nahiyar macizai suka wuce , Naheela ta umurci Aljani Faskandara da ya maida su Mamma da su Hajiya Maryam gidansu .  Nan aka ci gaba  da Raye-Raye ana wasar wuta , sai da ƙarfe huɗu na dare kowane ango ya ɗauki matarshi .
Naheel ne ya rufe ido ya buɗe har sau uku sai ga wata haɗaɗɗiyar fada mai Matuƙar ɗaukar hankali . Kallon Naheela yayi ya ce “Nan ne gidan da sarauniyata ta cancanta ” , murmurshi tayi ta ce “Godiya nake yi maimartaba “. Hannunta ya riƙa suka shige cikin gidan .

Ɓangaren Nahad kuwa cikin teku suka shige wani ɗan ƙaramin dutse Bobbo ya kafe da ido , a hankali dutsen ya fara girma har yayi tsayi ya  fito wajen teku , hasken wata ya haska shi nan take ya dawo gida . Wani haɗaɗɗen gida na ban mamaki , shigewa suka yi ciki .


Tun da Aljani Faskaranda ya aje su Mamma gida zazzaɓi ya rufe ta , sai kakkarwa take yi , Asama jajirtacciyar mace mai mutunci duk da gajiyar da take ji haka ta zage damtse ta ɗora ruwan zafi sai da suka tafasa sannan ta zuba ma Mamma a kofi ta zuba madara da sugar ta kawo mata , sai da mamma ta sha da yawa sannan ta kai Mamma wanka ta fito ta shirya , ta kwantar da ita kan cinyarta tana gasa mata jikinta har barci mai mugun nauyi ya fizge ta .

Baffa kuma ya kwana ɗakin Bobbo ganin Asama a ɗakin Mamma .

Arɗo ya ja ɗanshi Abdul da Amadu suka kwanta tare .
Mamma bata farka ba sai da haske ya fito lokacin Asama har ta gama abinci tana zaune tana jiran mamma ta tashi , buɗe Mamma tayi ta sauke kan Asama “Allah ya miki albarka Asama , Allah ya saka miki da alkhairi kina da mutuƙar kirki da tarbiya , yadda kika kyautata min Allah yasa matan su Abdul su kyautata miki “, murmushi Asama tayi ta ce “Ameen ya rabbi Na gode sosai Mamma, ki tashi kiyi wanka ga hadari nan kar a yi ruwa sanyi ya sauka ” , “To” Mamma ta faɗa sannan ta miƙe ta fita . Wani wankan ta sake yi tana fitowa aka kece da ruwa kamar da bakin ƙwarya da gudu Mamma ta shige ɗaki ta shirya sannan ta ci ɗumamen tuwon da Asama ta aje mata , ta kawo fura ta sha , sai ta ji kamar ba ita zazzaɓi ya rufe jiya ba , dama harda firici.

Ɓangaren su Hajiya Maryam ita ma tana dawowa ciwon kai ya buge ta ta kwanta sai barci , Ahmad bai shiga gida ba sai washe gari ,yana shiga ɓangaren Ammynshi ta ce “To Alhamdulillahi an samu dai an rabu da ƙaya , nima in samu a bar min ɗana ya huta ” , Ɗan murmushi yayi yana girgiza kai ya ce “Ammyn kenan ” , harara ta watsa mishi tana “Ammyn gidanku ” , “Yanzu dai ina abincina” ya faɗa , “Ai da wannan aljannar ta yanko mata namanta ka ci ” , “Ya Ahmad ka ci abincin da na dafa maka ” Suka ji muryar Nahad , da sauri ya juya yana kallonta ita da Naheela tsaye . Miƙewa yayi ya karɓi kular dake hannunta ya ce “Na gode miki ƙanwata ” , murmushi Nahad tayi sannan suka ɓace ita da Nahad sai ɗakin Hajiya Maryam .

Rungumeta suka yi suna faɗin “A zahiri Umma ke ce ginshiƙinmu , ki bi mu mu je duniyarmu ” , girgiza kai tayi ta ce “Nan ma Alhamdulillahi , bazan iya Rayuwa cikinku ba “. Naheela ta miƙe ta ce “Naheel !”, Hajiya Maryam ta ce “Yayi me ” , “Na ji a jikina ya zo nan ” ,Nahad ta ce “Ga su ma har da Bobbo ” , zuwa su Bobbo suka yi suka rungume Hajiya Maryam duk su huɗu “Muna sonki Umma” suka faɗa , murmushi tayi ta ce “Ina sonku nima “, sumbatarta Naheela da Nahad suka yi a Kumatu ,sannan Nahad ta juya ta sumbaci Bobbo , Naheela ma sumbatarta Naheel ta yi sannan suka ƙara rungume Hajiya Maryam cikin soyayya sai dariya suke yi tsabar son da suke ma juna.

ALHAMDULILLAH ! Allah abun godiya . Ba dan na so ba sai dan haka Allah ya so . A yau dai na kawo ƙarshen littafin NAWA ƁANGAREN .

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Leave a Reply

Back to top button