NAWA BANGAREN

NAWA BANGAREN COMPLETE

NAWA BANGAREN COMPLETE HAUSA NOVEL

Kuka Mamma ta fashe da shi tana faɗin “ Na rantse da Allah bazan yarda ba ,ku ƙyale ta kar ɗana ya mutu “.

Baffa ya dakawa Mamma tsawa yana faɗin “yi mana shiru dan Allah , malam yi aikinka”.

Malam Jafar ya ce “kina ganin so ne ya kawo ki jikin Ibrahim “.

Ta ce“Ni ban taɓa shiga jikinshi ba ,yau ma dole ce ta sa saboda ka kira ni da ayoyin Allah “.

Malam Jafar ya ce “ idan har abunda nayi shi ya kawo ki nan kenan kina da alaƙa da halin da Ibrahim yake ciki ?”.

Ta ce “Eh malam ,ni ce cikon ɓangaren Ibrahim ,duk inda babu ni a wurin Ibrahim zai zama shi da matacce duk ɗaya kamar yadda ka same shi “.

Malam Jafar ya ce “to ki yiwa Allah ki bar azabtar da shi ko in ƙona ki da ayoyin ubangiji ,kuma kin ga na zo da ruwan magarya zan watsa miki su “.

Ta ce “Malam zaɓin biyu ne nima bani da wani sai shi ,wallahi in ina kusa da shi dole sai ya ganni kuma hakan yana azabtarshi , idan nayi nesa da shi kuma bazai iya motsi ba, idan kuma ka ce ko ƙona ni hakan zai nuna jikin Bobbo kuma yadda zan ji zafi haka Shi ma zai ji ” .

Malam Jafar ya ce “ shiyasa kika zaɓi ki yi nesa da shi “.

Ta ce “ eh malam ,kuma nima ina azabtuwa da hakan ,na gaya maka Shi ne Nawa ɓangaren “.

Malam Jafar ya ce “kina mana ƙarya dai ,ni zan ƙona ki yanzun nan “

Ruwan magarya ya ɗauka cikin wata kwalba ya buɗe …………………………….

To masu karatu anan zan dasa aya .

Na gode sosai da goyon baya.

NASMAH LIMAN .
09121873529
[7/18, 12:07 PM] QUEEN-NASMAH ❤️✍️: NAWA ƁANGAREN

HAƘƘIN MALLAKA : QUEEN-NASMAH

????MOONLIGHT WRITER’S ASSOCIATION????
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

”’We are the moonlight writers we shine all over the world.”’
بِسم الله الرحمن الرحيم

_I love you as certain dark things are to be loved in secret, between the shadow and the soul._ *HABEEB-ALBI*

€pisode 15..................

Ruwan magarya ya ɗauka cikin wata kwalba ya buɗe , sannan ya yaye lulluɓin da yayi ma Bobbo ya kai zai watsa mishi ruwan magaryar Bobbo ya miƙe da ƙarfin tsiya ,cikin muryar da ba tashi ba  ,wanda aljanar ce da kanta ta ce “Malam " , ta kalli mamma ta ce “kar ki bari ƙonani ya zama mafarin tashin hankalinku " .

Zumbur Mamma ta miƙe tana faɗin “Malam Jafar , shin Bobbo ɗana ne ko , to ku ƙyale shi idan har sai an ƙona aljanar nan "

Arɗo ya ce “ Haba Mamma ki bari yayi aikinshi ,ba a yiwa aljani yadda yake so ".


Da ƙarfi Bobbo ya juya wanda ba shi yayi hakan ba aljanar da ke jikinshi ce , wata wuta ta saki mai ƙarfin gaske sai saitin fuskar Arɗo  ,cikin muryar da ke nuna hasala ta ce “Ka fita a sha'anin nan ".


Malam Jafar ya ce “To yanzu dai zauna ki faɗa mama sunanki ?"

Zama Bobbo yayi kamar yadda malam ya ce “ sunana Nahad Sulaiman , malam ku daina ce min aljana ni mutum ce kamar ku ".


Mamaki ƙarara ya bayyana a fuskokinsu ,kowa da tambaya a fuskarshi .


Malam Jafar ya ce “kina mutum taya kika iya zama a jikin wani ,wannan ba gaskiya ba ne ,yanzu kiyi abu ɗaya ki bar shi ya huta ".


Aljanar ta ce “To malam zan tafi ,amma Bobbo bazai tashi ba ".Baffa ya ce “Na gaji da wannan wasar kwaikwayon , Malam Jafar yi aikinka ".


Ruwan magarya da malam ya rufe ya ƙara buɗewa ya watsa mata .


Da ƙarfi ta gantsare “Ahhhhhhhhhhhhhhhhhhh !"
Sai kuma ta ƙame , idonta suka ƙaƙƙafe , yayinda hannunta suka murɗe , Mamma ta miƙe cikin kuka tana faɗin “La'ilaha ilallahu Muhammadur rasulullahi (saw) shi kenan kun kashe shi " ta ƙara fashewa da kuka , yayinda Malam Jafar ya shiga karanta ayoyinda Allah amma ko motsi bata ƙara yi ba . Arɗo da Baffa mamakin duniya ya cika su .

Jin Mamma na kuka ya saka Asama zuwa cikin sauri tana faɗin “wa suka kashe ".


Mamma ta ce “wa in ba Ibrahim ba ,sun kashe min ɗa " .

--------------------------
Cikin ruɗewa Hajiya Maryam ta juya tana kallon Nahad dake ihu tana faɗin “ya ƙona ni" , kallon yadda idon Nahad suka ƙaƙƙafe take yi, hannunta ya wani murɗe , ta wani ƙame , tashi Hajiya Maryam tayi ta dawo kusa da Nahad domin tabbatar da yanayin da take ciki   , a firgice ta ja baya tana rufe ido tare da faɗin “Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un ,Nahad me zan gani haka " . Da sauri ta ɗauki waya ta kira Ahmad da bai daɗe da Fita ba shi da Abbansu  .


Ahmad yana zaune parlor tare da Ammynshi suna fira , wayarshi ta hau ruri , “Hello Aunty " ya faɗa , “Ahmad ka zo ba lafiya fuskar Nahad ba ......... " bai ma bari ta ƙarasa zance ba zare wayar daga kunne ya miƙe zai fita duk ya rikice ,Ammy ta ce “Ahmad lafiya kuwa ", Ahmad “Ammy Nahad ce ba lafiya " yayi maganar yana ƙara sauri .

Ammy ta ce “ kai dai ka sani , kayi ta rawar jiki akan waccan yarinyar mara kunya " .


Ba tsaya ba ya fita , part ɗin da ke kusa da nasu ya shige , gani yake ma ba sauri yake ba , dan sai ya ta buɗe ƙofofi zai shiga parlorn in dai ta gaban gidan zaka bi to haka ne a ko wane ɓangaren na gidan .


Gudu ya fara yi yana haɗawa da sauri , har samu ya buɗe Ƙofar parlorn kamar wanda aka bankaɗo ya shigo . “Aunty me ya sami Nahad ", cikin rawar baki ta ce “du...duba ka ganii " .


Matsawa yayi kusa da Nahad , da sauri ya ja da baya yana kallon Hajiya Maryam “waya ƙona mata jiki " .


Hajiya Maryam ta ce “nima ban sani ba , yadda take kwance haka na ganta " , Matsawa Ahmad ya sake yi ya kallonta , “Aunty har da wuyanta duk ya ƙone ,kuma Abba ya fita muna fita shugaban ƙasa ya kira shi wai meeting ɗin gaggawa , ya hau jirgi zuwa Abuja , Yaya Muhammad da Yaya Adam kuma sun fita bari in kira yaya Babangida ina tunanin yana gida ".

Hajiya Maryam “to kira shi mu ji ".

Hannu yasa cikin aljihu , ya laluba amma ba waya ciki , dafe goshi yayi tunawa da yayi ya bar wayar parlorn Ammy , Hajiya Maryam ta ce “me ya faru ", “lokacin da kika kira ni sai na kiɗime ashe na jefar da wayar parlorn Ammy ".

Hajiya Maryam ta ce “ga wayata kira shi da ita " ta kai ƙarshen zancen tana nuna mishi wayar kan standard table ɗinta na talabijin .

-----------------------------

Garin Zawatu cike yake dam da rundunar Aljanu kowa da ƙungiyarshi , duk wanda ka gani zaka ganshi Saman doki Yana , sai wucewa ake yi zuwa filin da za a yi yaƙi , sai da aka gama hallara ba ɗaya Sarki Zimba da Sarki Zawatunduma suka shigo tare da ayarinsu , kowannensu ɗaure da takobi a ƙugun. Naheel ya shigo daga ƙarshe ,duk da tare yake da Mahaifinshi. Sarki Bahulandu ma da ayarinshi sun hallara wuri , a taƙaice ma su suka fara hallara wurin yaƙin.

Sarki Zawatunduma kuwa tun da ya iso filin daga yake raba ido ,amma har yanzu bai ga gimbiyarshi Naheela ba , duk yadda ya kai ga bincike yau dai ya gagara ganin komai game da gimbiyarshi.

“Mu kai musu hari " Sarkin garin Bustumbula wato sarki Bahulandu ya faɗa .

Riiiiii! Ayarin sarki Bahulandu suka yi cikin ƴan Zawatu . 


Shuuuuu shuuu ! Kukan wata ƙatuwar tsuntsuwa ya ruɗe wurin ,maimakon a yi faɗa sai kowa ya ɗaga kanshi sama dan ganin mine ne .


Wata irin ƙatuwar tsuntsuwa ce da Naheela ke kira Ruhaina , tsuntsuwar ta sha ado na ban mamaki duk ilahirin jikinta duwatsu sai ƙyalli take yi , a hankali ta fara saukowa in da aka fahimci akwai wata kan tsuntsuwar , takalminta baƙaƙe masu ado da dutsuna kamar irin na jikin tsuntsuwar .

Sai da da ta sauko gaba ɗaya sannan kowa a wurin ya tabbatar macece , Naheela ce sanye cikin baƙaƙen kaya riga da wando waɗanda suka zauna matuƙa a jikinta , jambakin bakinta baƙi , sannan rabin fuskarta daga hancinta  har zuwa goshinta duk ta shafa baƙi . Idonta sai fitar da wuta yake yi wal-wal-wal . Tuni kowa a wurin ya sha jinin cikinshi ganin Naheela .


Tsananin fushi da ɓacin rai duk ya bayyana tare da ita .  Hannu ta ɗaga ta juya ,cikin tsawa mai ƙarfi ta ce “Ruhaina ki saki macizai yanzun nan "


Baki Ruhaina ta buɗe wasu zara-zaran macizai masu kai uku suka fara fitowa daga bakinta .

“Kun san su wa zaku kaiwa hari "Naheela ta ce da macizan .

Nan take macizan suka nufi Ƴan Bustumbula , yayinda Naheela ta ce “Sarki Bahulandu ni ce daidai kai ,dan haka matso gani ".


Da azama ya nufo Naheela yayinda ya ɗaga takobinshi sama ,yana isowa rafka mata ita a kai , cikin rashin sa'a ashe ..........Anan zan dakata .

Na gode muku sosai da soyayyar da kuke nuna ma Littafin nan . Ina jin daɗin comment ɗinku matuƙa , da yadda kuke nuna son littafin nan .
Bani da wani bakin magana sai dai na ce Allah ya saka muku da alkhairi . Ubangiji ya biya ku .
NASMERH LIMAN
09121873529
[7/19, 5:54 PM] QUEEN-NASMAH ❤️✍️: *NAWA ƁANGAREN*

HAƘƘIN MALLAKA : QUEEN-NASMAH 


*????MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION????*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.'''* 
بِسم الله الرحمن الرحيم

???????? ???????? ????????
*Wohoho ! Garin daɗi na nesa ungulu ta leƙa masai . Wani Kaya Sai amale shin kun san k’ayatattun magungunan Mata na maman Haidar ko kuwa an bar ku baya *
To ƴar uwa Kayan maman Haidar basu da matsala domin traditional medicine ne Kuma Ana had’asu da ingantattun kuma nagartattun itatuwa masu aminci da karfi da Basu da wata illa sai ma taimaka miki da zasu yi. Malam bahaushe dai ya ce In kana da kyau ka ƙara da kwalliya ????????
*Akwai wasu mayatattun kayan haɗi masu Matuƙar ƙarin Ni’ima da mamàn haidar take yi.

1 Gumbar kankana da aya
3 Gumbar Madara da kwakwa
4 *Kaza me ƙwai *
5 Zabo me zuma
6 Kaza me allurai, sahihiyar hanyar zaki mallake mijinki ƴar uwata ba boka ba malami
7 Kwallin idonka inadona
8 Tauwadar mata
9 ketar larabawa magani me kankarowa mace kima da daraja
10 Maganin sanyi me fatattakarsa duk kuwa nacinsa Koda bakya haihuwa indai matsalar sanyice gwada wnnn
11 Maganin nono. Sahihi
12 Maganin hips and bobbs
13 hodar. Ni I’ma koramar mata
14 nakasan Mara babban sirri
15 kafi jijjibi
16 daga Sha Sai wanka kasaitacce magani
17 Dan kwankwalati namata da mazajensu Kevin Mata
18 matsin kinfi budurwa dubu ko haihuwa nawa kikai Babu magana
Maman haidar Bata tsaya anan ba
Tana Saida hijabai da yadikansu akan farashin sari yadika dila dila, hijaban Ƴan gayu sannan
ta kawo muku hadaddan sabulun gyaran jiki da hadin dilka Me sa shek’i da laushin fata, ga kuma mayukkan kitso Wanda laraba ke amfani dashi inkin gwada sai kin dawo ku dai ku neme Maman Haidar a wannan number domin neman ƙarin bayani???????? 08146017245


I never thought love could be so magnificent until I saw the sincere look in your eyes, telling me that this time¦ I would never shed another tear. HABEEB-ALBI

€pisode 16……………..

Da azama ya Nufo Naheela , yayinda ya ɗaga takobinshi sama, yana isowa ya rafka mata ita a kai , cikin rashin Sa’a ashe ba ita ya sama ba ta kauce. Ɗagowa tayi cikin ɓacin rai ta cira sama da ƙarfi ta buga mishi wani ƙaramin ƙarfe wanda gara a watse maka kai da a buga maka irin wannan ƙarfen , ƙarami ne amma kuma idan aka buga maka shi yana durƙusar dai kai . A gigice Sarki Bahulandu yake , nan take ya faɗi ƙasa . Da ƙarfi Naheela ta biyo shi ƙasa , tare da kara hannayenta guda biyu ta saitin zuciyarshi , idonta suka fito daga mazauninsu suka zazzalo har suna shirin taɓa ƙasa , gantsarewa yayinda wani ɓakin haske ke fita daga jikin sarki Bahulandu yana shiga ta hannun Naheela , yana gama shiga ta miƙe kamar wadda aka tsikara . Sannan ta juya ta saki wata ƙwallon wuta daga idonta zuwa cikin Ƴan gari Bustumbula .

Ƴan garin Zawatu kuwa dawowa suka yi Ƴan kallon dan gefe suka koma suna kallon yadda macizai ke ta watsar da jini .yayinda wannan ƙwallon wutar da Naheela ta saki ke ta ƙona wasu . Cikin awa biyu Ƴan garin Bustumbula suka dawo ƙasa , wasu duk sun ji raunuka wasu kuma duk sun mutu .

Nan take a wurin sarki Zimba ya fara magana cikin muryar Babba “A yau ni Sarki Zimba na sauka daga kujerar Mulkina na barwa Naheela ƴar sarki Zawatunduma , taron Naɗin sarautar wani sati ne da izinin Allah ” yana faɗin haka ya ja doki , sauran Ƴan garin suka bi bayanta sarkin . Naheela kuwa matsowa tayi kusa da Naheel ta . Yayinda ya mata murmushi yana faɗin “Jinjina ga sauraniyar Zawatu , ina taya ki murna “.

Murmushi ta sakar mishi ,sannan ta ce “Na gode masoyin Ruhina ,ga shi dai kai ne ka fara taya ni murna “.

“Eh ni ne ” ya faɗa yana juya akalar dokinshi .

Naheela ta ce “Yaushe kai ɗin nan zaka so ni ?”

Ba tare da ya juyo ba ya ce “ so tarin yawa ina yunƙurin in ga na kyautata miki . Amma kiyi haƙuri bazan iya rayuwa tare da mace ba “

“Zan koya maka rayuwa tare da ni Naheel ” ta faɗa .
Bai ce da ita komai ba ya wuce .
Ruhaina ta matso kusa da Naheela ta durƙusa domin ta ba Naheela damar hawa bayanta .
Hawa Naheela tayi , sannan Ruhaina ta cira sama .


Ba yadda malam Jafar bai yi da Mamma akan ta bari yayi abun da ya dace amma fir Mamma taƙi amincewa . Dole Baffa ya ba shi haƙuri ya tafi .

Kuka Bobbo ya fara yi “Mamma zafi nake ji “.
Da sauri Mamma ta matso tana faɗin “Ka farka ?” , cikin kuka kamar ƙaramin yaro ya ce “Mamma zan mutu , ji nake kamar raina zai fita , Mamma an ƙona wani ɓangare na jikina , fuskata da wuyana zafi “. Mamma ta ce “ƙyale su Bobbo Allah ya zai saka maka , sai da na ce kar su yi , amma wancan yayan naka mai taurin rai da Baffanku suka nace sai an yi , ai ga irinta nan Allah dai ya isar maka wallahi “.Rufe ido yayi ,yayinda hawaye masu zafin gaske ke sauka kan kuncinshi .

Baffa na jin Mamma bai ce mata ko ci kanki ba sai ma tashi da yayi ya fita tare da Arɗo.


ASIBITI

Hajiya Maryam ce ke kai da kawo kusa da ɗakin da aka shiga da Nahad , yayinda Ahmad ke ta zirga-zirgar siyo wancan, mayar da wancan kawo wancan . Likita fito ,sauran nurses ɗin suka turo Gadon da Nahad take kwance kai ,duk fuskarta an naɗe ta da bandage har zuwa wuyanta . Idonta kawai aka bari buɗe ,da kuma hancinta da aka bar mata buɗe domin numfashi . Sai baki saboda cin abinci .

Hajiya Maryam na ganin an fito da Nahad ta matso da sauri tare da saurin riƙe hannun Nahad ,ta ce “Allah ya baki lafiya ƴata “. Ɗakin jinya aka shiga da ita aka kwantar ita ,duk Hajiya Maryam na riƙe da hannunta . Kan Nahad ta shiga shafawa lokacin da likita ke mata bayani .

“Gaskiya ban taɓa ganin ƙonewa mai abun al’ajibi irin wannan ba , abun mamakin ma sai an gama gyarawa kamar ana mata feshin jini sai komai ya dawo sabo , sai mun sake gyarawa , dalilin ma da yasa muka ɗauki lokaci kenan”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Leave a Reply

Back to top button