NAWA BANGAREN

NAWA BANGAREN COMPLETE

NAWA BANGAREN COMPLETE HAUSA NOVEL

Da gudun bala’i Zamzila ya nufo Sarki Banoto, yayin da Naheela ta ƙara ware ido wani haske ys haske Zamzila, take ya ƙara jin wani ƙarfi ya ƙara gudu, sarki Banoto yayi saurin juyawa ya fara mulmula cikin ƙasa ƙura na tashi, Zamzila kuma bai fasa bin ƙasa.

Wata kibiya ce ta nufi Zamzila ba tare da an ankara ba ta cake Zamzila, nan take gimbiya Naheela ta diro daga sama, dib! Kake ji ƙarar saukar ta, wanda haka ya ba duwatsu damar ɗagawa. Da sauri sarki Banoto ya tunkaro Naheela da a lokacin ba abunda take gani sai rayuwa macijin tsafinta.

Shuuuuuu! Mashi ya nufi Naheela zai cake ta, da sauri ta duƙe ya bi ta Saman kanta ya wuce, wani mashin sarkin Banoto ya sako mata ta ƙare duƙewa, haka ya ci gaba da aiko mata mashi tana kauce musu har ta samu ta isa gaban Zamzila da yake fitar jini a jikinsa, da ƙarfi ta miƙe hannunta zuwa saitin jikin Zamzila ta fara fitar da wata wuta mai matuƙar haske.

“Zamzila! “ta ambaci sunanshi da ƙarfi tana buɗe baki, wasu duwatsu suka riƙa fita a bakinta har gudu sha ɗaya, suna sakin wata danja fari da ja, daidai lokacin Sarki Banoto yayi saitin wani dogon mashi, cak! Wannan mashin ya cake gefen cikin Naheela.


Zumbur Sarki Zawatunduma ya miƙe tsaye daga kan kujerar da yake yana faɗin “ina gimbiyata tafi ƙarfin azzalumi “.

“Me ya faru yallaɓai” Wani bafade ya faɗa.

Ba tare da ya amsa shi ba ya fito waje.

Hannunshi ya naɗe wuri ɗaya ya buɗe su da ƙarfi sai ga wani ƙaton tsuntsu gabanshi.

“Bilbil ka kai ni inda gimbiya take ” sarki Zawatunduma ya faɗa.

Tsuntsun da sarkin teku ya kira da Bilbil ya kwanta sarki ya hau kanshi, nan take ya cira sama da ƙarfi.


“BOBBO!” ya ji ana ta fama kwaɗa mishi kira, juyawa yayi yana kallon mai kiranshi har ta ƙaraso gabanshi tana mishi murmushi.

Fuskarta bata wani bayyana da kai ba domin kuwa dishi-dishi yake ganinta.

“Wacece ke?” ya tambaya .

“Taka ɓangaren!” ta bashi amsa

“Ɓangarena? ” ya sake tambaya

“Eh kai ne Nawa ɓangaren?” ta amsa.

Ido ya ƙura mata yana son ganin Fuskarta amma ina duhu ya lulluɓe ta fuskarta ba a iya gane wacece.

“Wace ce ke? ” ya sake tambaya

“Ɓangarenka ce ni ” ta amsa.

“Na ce miki wace ce ke! ” yayi maganar da ƙarfi.

Da mamakinshi sai yarinyar ta juya ta fara tafiya ba tare da ta amsa mishi ba.

“Ya za ta ce min ita ce ɓangarena, NAWA ƁANGAREN kamar ya?” ya faɗa yana Bin ta da kallo.

Tafiyarta take yi ba tare da ta juyo ba har ta sha kwana.

Firgigit ya farka daga barci da yake yi wanda ya so ganin wacece wannan yarinyar a mafarkinshi.

Mamma ce ta hankaɗa labubulan ɗakin “Bobbonmu ka fito daga wannan ɗakin haka ka zo ka ci abinci ya fara yin sanyi ” ta faɗa.

“Na Ƙoshi Mamma” ya amsa mata yana goge zufar da yayi da manunin farcenshi.

“Ban gane ka Ƙoshi ba, dallah can ta so maza wallahi kar in saɓa maka ” ta faɗa cikin ɗaya murya.

“Mamma wallahi kaina ciwo yake min bazan iya cin komai ba” ya faɗa yana lumshe ido.

Riƙe haɓa mamma tayi ta ce “ to bari na turo Indo ta kawo maka fura da jiƙo ka sha na san kan zai rage “.

Gaɗa kai yayi yana mayar da kan ya jingina da bango a hankali ya ce “NAWA ƁANGAREN” sai kuma ya dafe kai yana jin kamar zai faɗo ƙasa tsabar ciwo.

Ba a yi minti uku ba wata yarinya ta shigo da ƙwarya hannunta da Alama ita ce Indo ta ce “Babbonmu wai Mamma ta ce a kawo maka “, hannun kawai ya iya ɗaga mata alamar ta tafi.

Abun ka da ɗa da mahaifi sai ta matso kusa da shi ta ce “Bobbo baka lafiya ne?” girgiza kai yayi ya ce “a’a barci na tashi bai ishe ni ba “.

“To ka sha furar zaka daina jin barci” ta faɗa tana jawo ƙwaryar furar gabanshi.

“Bana so na sha Aisha ” ya faɗa yana shafa kanta.

“Bari in sha maka kada Mammanka ta maka faɗa” ta faɗa tana buɗe furar.

Jawo ta yayi ya rungume yana jin tausayinta, zai iya tuna ranar da Umman Aisha ta bar mai ita tana cikin zane ko kwana 20 bata yi a duniya ba ga shi yanzu har tayi shekara 8 duniya.

A hankali ya ce “Mamma ba za ta min faɗa ba, ki je kiyi wasa “.

Ɗagowa tayi tana gaɗa kai, sannan ta tashi ta bar ɗakin.

Mamma da kanta ta shigo ta bashi jiƙon da ta dafa mishi, sannan ya sha fura ya kwanta dan yanzu sanyi yake ji sosai, mamma ta ce “Allah ya yaye maka wannan rayuwa ta wahala ina dalili”.

“Ameen ya rabbi ” ya faɗa.

Anan zan daka ta sai mun haɗu a shafi na gaba .

MASOYANA KU SA KAKANA MARIGAYI ALHAJI MUHAMMAD LIMAN (MAI-SHUKURA) ADDU’A, IDAN DA HALI ƳAR UWA KO ƊAN UWA KI/KA KARANTA MISHI SURATUL IKHLAS ƘAFA ƊAYA HAR MAKWANCINSHI. DAN ALLAH BA DAN NI ZA KU YI BA. NA GODE .

LOVE U ALL FANS……………….

(QUEEN NASMAH) NASMAH LIMAN

~JIKAR-MAI-SHUKURA~✍️

09121873529
[7/17, 12:00 AM] QUEEN-NASMAH ❤️✍️: **NAWA ƁANGAREN

HAƘƘIN MALLAKA : QUEEN-NASMAH

????MOONLIGHT WRITER’S ASSOCIATION????
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

”’We are the moonlight writers we shine all over the world.”’
بِسم الله الرحمن الرحيم

_*Wannan littafin daga farkonshi har ƙarshe sadaukarwa ne gare ka Hayateeynah (my Eternal love) ka ji daɗinka*_.
.

-Love is just a word until someone comes along and gives it meaning.HABEEB ALBI._

---------------------



€pisode 8.........................

Cikin daƙiƙa uku Tsuntsu Bilbil ya sauka gabansu na Naheela. 

Cikin kakarin jini ta shiga kiran sunayen dabbobin tsafinta “Binaf! , Mazib, Bunut, kilkila" haka ta dinga kiransu suna sauka gabanta da ɗaɗɗaya, yayin da idonta suka rikiɗa suka yi ja. 

Sarki Zawatunduma kuwa tun da Bilbil ya sauke shi bai motsa ba, sai wuta da kuma idonshi ke saki. 


Dabbobin tsafin Naheela kuwa sai zagaye ta suke yi yayinda take ƙoƙarin tashin Zamzila. 

Sarki Banoto yayi kukan kura da gudun tsiya ya nufo ta kafin ya kawo ya ji wani ƙarfe ya tokare mishi gaba, da sauri ya ja baya yayi juyi zuwa ɗayan ɓangaren ya nutsar da kanshi cikin Ƙasa.

Sarki Zawatunduma yayi wani ihu mai haɗe da gurnani ya nutsar da kanshi ciki. 


Naheela kuwa jikinta ya sauya launi zuwa tsanwa shar. Dabbobinta sun fi hamsin waɗanda suka sauko sai ƙara rufe ta suke yi dan su ƙara mata ƙarfi. Wuta kawai suke saki ta baki. Daidai lokacin Zamzila ya tashi, shuuuuuuuu ya tashi sama ya sauko da kanshi ta ƙasa dai-dai saiti da gefen ƙirjinta ya ɗora bakinshi tare da ziro harshenshi inda mashin ya cake ta ya fara fitar da dafin da mashin ya sakar mata. 


Idonta sun yi ƙulu-ƙulu kamar zasu faɗo ƙasa jijiyon idon sun yi baƙi ƙirin, zut ta ki fitar wani abu cikin Idonta nan take ta faɗi ƙasa sumammiya. 


Zamzila ya rikiɗa zuwa majiji mai kai shida, yayinda sauran dabbobin suka haɗe kansu wuri ɗaya suka cira sama da ƙarfin gaske Zamzila ya sauko, garin ya ƙara turniƙewa da duhu da hayaƙi. Aka fara girgizar ƙasa a garin Zawatu. 


Mutanen garin sai fitowa suke labarin mutuwar Naheela ya fara zagaye ko ina na garin. 

Da ƙarfi dabbobin suka diro nan take suka dawo kamar mutane. 

Binaf ta rungume Naheela yayinda ta rufe Idonta tana tuno duk abubuwan da tayi ma Naheela da irin taimakon da Naheela ke bata. 

Da sauri ta miƙe tsaye ta rufe idonta tare da kara hannunta saitin kan Naheela ta fara sakar mata ƙarfinta. 


----------------

Ɓangaren sarki Zawatunduma kuwa musayan wuta ake ayi tsakaninshi da Banoto. 

Cikin ƙarewa Sarki Zawatunduma ya sako wani siririn tsinke wanda ya kawar da  Sarki Banoto daga ganin wannan tsinke. Da gudu-gudu tsinke ya nufi sarki Banoto ya cake maƙogwaronshi. 

Ko daƙiƙa ɗaya be ƙara ba ya faɗi ƙasa ba rai. 

--------------------------

Ɗakin Mairo ya shiga da sallama a bakinshi “Assalamu Alaikum ", ciki-ciki ta amsa mishi, bai damu da yadda ta amsa sallamar ba. 

Wuri ya samu ya zauna gefenta, cikin tausasa lafazi ya ce “kin samu kin ci abinci ko?", gaɗa mishi kai kawai tayi alamar eh. 

“Ya Sadauki yake " ya tambaya yana kallon Ibrahim dake hannunta. 

“Yana Lafiya "ta faɗa a taƙaice tana Miƙa mishi Ibrahim da ya kira da suna Sadauki. 

Karɓarshi yayi ya ƙara mishi Addu'a sannan ya Miƙa mata shi yana tambayarta “ba wani abunda ke miki ciwo". 


“Eh" amsa mishi cikin nuna ƙulewa. 

“Allah ya ƙara sauƙi " ya faɗa tare da tashi tsaye. 

Can ƙasa-ƙasa ya ji ta ce “Ameen". 

Bai ce komai ba ya fita. 


Ɗakin Bintoto ya shiga. Washe haƙora tayi tana faɗin “sannu da dawowa ashe ka shigo? ". 

Murmushi ya ɗan yi ya ce “eh yanzu na shigo, ɗakin Mairo kawai na shiga". 

“Allah sarki bari na kawo maka fura yanzu na gama dama ta tana bayan Randa " ta faɗa. 

Numfashi ya sauke, sannan ya ce “a'a ki bar ta barci zan ɗan yi zazzaɓi nake ji". 

“Kaƙi cire damuwa ranka wallahi kar ka mutu cikin damuwa " ta faɗa. 


 “Fatima kin kwashe shekara tare dani ina tauye ki, dan Allah ki faɗa min in zaki iya jure zama dani". Ya faɗa yana ƙara jin zafi cikin ranshi. 

Cikin rashin Fahimta Bintoto ta ce “ban fahimce ka ba? "

Iska mai zafi ya furzar ya ce “kina so mu raba auran nan". 

Da sauri ta ce “eh, eh walla....... "

Bata ƙarasa maganarta ba sanadiyyar kallon da BOBBO ya kafe ta da shi. 

“Yanzu har na kai lokacin da kike gudu na?" ya tambaya. 

Sai yanzu ta ji nauyin abun da ta faɗa, cikin noƙe kai ƙasa ta ce “Kayi haƙuri wallahi ni bazan iya jurewa ba, ina da buƙatar lafiyayyen namiji tun ina da saura na dan Allah Bobbo kayi haƙuri ya sawwaƙe min wallahi na daɗe ina neman ranar da zaka ce ka sake ni " ta kai ƙarshen maganar hawaye na bin kuncinta. 


“Kar ki damu Fateemar Sadauki yau ni Ibrahim Bobbo na sake ki saki biyu, idan kin gama idda kiyi aure Allah ya baki mai sonki wanda zai kare miki haƙƙinki" ya faɗa yana runtse idonshi. 


Hawaye suka biyo kuncinta ta ce “a zamana da kai Bobbo baka taɓa muzguna min, matsalarka ɗaya ce kuma na fahimci lalura ce haka Allah yayi ka dan haka ba wanda ya isa ya canza maka taka ƙaddarar ina Roƙon Allah ya haɗa ka da mahaɗinka, kayi haƙuri na Gaza ". 


Murmushi yayi waɗanda suka zo da hawaye masu zafi ya ce “Fatima da ina da mafita da nayi, bazan iya zama da wata mace ba dan na san cutar da ita zan yi, kiyi haƙuri na san matsalar daga ni take ina miki fatan alkhairi".



Cikin kuka ta fara haɗa kayanta, yayinda zazzaɓi mai zafi ya rufe Bobbo, cikin minti biyar barci yayi awon gaba da shi. 


Bintoto kuwa fita tayi, sai da tayi sallama da duka ƴan gidan, yaran gidan ma sun sha kuka da zata tafi. 



“NAWA ƁANGAREN " ya ji ana faɗa, da sauri ya ɗago daga jikin bishiyar da yake jingine jin muryar wadda ke kira shi da NAWA ƁANGAREN, murmushi ya ga tana mishi, babu abunda yake gani sai fararen haƙoranta. 


“Ki faɗa min wacece ke?"ya faɗa


“Sadauki na faɗa maka ni ɓangarenka ce" ta faɗa. 


“ɓangarena kamar yaya? " ya tambaya, cikin ware hannu ta ce “ iya abun da na sani kenan". 

Matsowa ya fara yi kusa da ita yana faɗi “wacece ke na ce? ". 

“Bobbo ban san ko ni wacece ba" ta faɗa tare da juyawa ta fara tafiya, gudu ya fara yi dan ya samu ya kamo ta amma sai ta dinga noƙe mishi, har ya gaji ya fara haki ita kuma ta wuce ba tare da ta juyo ba. 

Kamar kullum yau ma  Bobbo farkawa yayi ba tare da ya samu ya ga wace ita ba. 

Take ya ƙara jin zazzaɓi ya rufe shi yana jin wani zafi cikin jikinshi. 


“Wacece ke? "ya furta a bayyane. 






Anan zan daka ta sai mun haɗu a shafi na gaba .







_MASOYANA KU SA KAKANA MARIGAYI ALHAJI MUHAMMAD LIMAN (MAI-SHUKURA) ADDU'A, IDAN DA HALI ƳAR UWA KO ƊAN UWA KI/KA KARANTA MISHI SURATUL IKHLAS ƘAFA ƊAYA HAR MAKWANCINSHI. DAN ALLAH BA DAN NI ZA KU YI BA. NA GODE_ .


LOVE U ALL FANS...................




*NASMAH LIMAN*

~*JIKAR-MAI-SHUKURA*~✍️

*09121873529*
[7/17, 12:00 AM] QUEEN-NASMAH ❤️✍️: *NAWA ƁANGAREN* 


HAƘIN MALLAKA : QUEEN NASMERH


*????MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION????*


*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.'''*

بِسم الله الرحمن الرحيم

Wannan littafin daga farkonshi har ƙarshe sadaukarwa ne gare ka Hayateeynah (my Eternal love) ka ji daɗinka.
-You’re that part of me I’ll always need.HABEEB ALBI._


€pisode 6…………………….

Mahaifin BOBBO (wato Mal. Jaɓɓo) ne ya shigo riƙe da wata jaka a hannunshi. Mamaki ne ya dabaibaye shi lokacin da ya ga gidan shi cike da mutane, da sauri Mamma ta aje dakan furar da take yi ta tarbe shi cikin far’a tana faɗin “Maraba da Ƴan tafiya”, “yauwa sannunki da ƙoƙari “yayi maganar cikin sakin fuska, idan ka ga mahaifin Bobbo zaka ga tsantsar kamar da suke yi da Ibrahim Bobbo kamar a tsaga kara. Ɗaki ya shiga, yayin da Mamma ta shigo mishi da jakarshi ciki.

“Ya na ga gidan ya cika da mutane lafiya dai ko?” Mal. Jaɓɓo ya jefi Mamma da zancen lokacin da take shirin fita.

Juyowa tayi ta ce “Mairo ce ta haihu”.

“To, to Madalla, me aka samu? ” ya tambaya.

“Ɗa namiji Ibrahim” ta amsa mishi.

Mal. Jaɓɓo yayi murmushi ya ce “miskilin ɗana kenan. To Allah ya raya shi, halin mahaifinshi ya bi shi “.

“A’a wallahi, wa yake burin hali irin na Bobbo, yaro sai taurin kai yadda ka san ɗan tauri” Mamma ta faɗa.

“In banda ke da abunki minene aibun Ibrahim, haka kawai kin sa min yaro gaba ” ya faɗa.

Mamma ta ce “ai kai baka taɓa ganin baƙin Bobbo, kullum yabon shi kake yi, bari in kawo maka ruwa ni kam”.

Bata jira mai zai ce ba ta fita tana jinini.


“Yau ce ranar da za a yi ɓarin ruwan bala’i biyu, na fi so mu ƙarar da rijiyar bala’i biyu kowa ya hutu, wallahi sai na ɗau fansar ran Barhim da aka ɗauke, Rai akan rai ” Sarki Banoto yayi maganar da ƙarfi dai-dai lokacin da yake jawo ruwa daga rijiyar bala’i biyu.

“ku yi ma garin Zawatu dirar mikiya, ku hanasu zama lafiya” ya faɗa yana kallon ruwan.


Firgigit Naheela ta tashi tare da furta “ina, ƙaryar duk wani ɗan Mubanuwa da garin baki ɗaya, ba mai wannan ƙarfin ikon ” ta kai ƙarshen maganar wata mahaukaciyar wuƙa mai kaifin gaske ta fito daga tsakan goshinta.

Wani irin haske ne ke fita daga idonta zuwa ga wuƙar, yayin da take magana “binaf da gaggawa nake so kiyi ambaliyar ruwan bala’i biyu a garin Mubanuwa”.

Wuƙar (binaf) dake shillo gaban Naheela ce ta cira sama, shuuuuu ta dinga bin bango. Tana fita ta rikiɗa ta zama macijiya mai kai uku, nan take ta ɓace ɓat sai garin Mubanuwa, ruwan da ke cikin ƙwaryar da Sarki Banoto ya ɗiba ta yi ɓari da su, yayinda ta fara hura ruwan da ke malala ƙasa (wato ruwan bala’i biyu) nan take ruwan suke gauraye garin Mubanuwa da kewaye.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Leave a Reply

Back to top button