Daidai lokacin Hajiya Mabaruka ta shigo a hargitse tana faɗin “Me aka yiwa Ahmad? Na ga Hatsabibiyar yarinyar can ta ɗauko shi , Hajiya Maryam dake ji wani irin zugi a hannunta ta ce “ni taya zan sani tunda nan ta zo ta same ni kuma ta a je shi ta tafiyarta ” .
Hajiya Mabaruka ta ce “ bari Alhaji ya dawo yau sai an yi zama kin faɗi inda kika samo wannan yarinyar ” . Juyawa Hajiya Mabaruka tayi ta fita rai ɓace .
Naheel ne ɗaure a masarautar Sarauniya Naheela , shigowa tayi cikin ɗakin tana kallon Naheel , Naheel ya ce “Miyasa kika ƙoƙarin tilasta Rayuwarki gare ni “, Naheela ta durƙusa gaban Naheel hawaye suka ciko mata ido ta ce “Naheela tun daga ranar da na zo duniya Ban taɓa jin ina son wani kamar yadda nake sonka ba , yadda nake ji game da kai da a ce ciwo ne da tuni na zama tarihi , ina sonka da duk wani bugu na zuciyata , ina sonka a duk wani fita da shiga na numfashina da zan yi . Ina sonka so wanda nake ji a yanzu idan ban same ka ba zan rasa numfashina gaba ɗaya ” Numfashi ta ja wanda ya ba hawayen da ke kwance cikin ƙwayar idonta damar gangarowa.
Ido Naheel ya Zuba mata Yana mamaki yadda zaka ji Kana son wani haka , “Naheel da zan Iya nesanta kaina daga gare ka da yanzu baka sake gani na ba , nakan yi yunƙurin yin nesa da Rayuwarka amma kuma bazan iya ba , numfashina Yankewa yake yi , kai ne kaɗai cikar farincikina ,kayi haƙuri ka jure kwana uku tare da ni hakan shi zai baka damar yin rayuwa tare da ni ba tare na takura maka ba” ta faɗa.
“Nakan zauna ni kaɗai nayi tunanin cikin halittun da Ubangiji yayi ke wace halitta ce , ɗabi’unki da halayyarki suna nuni da yadda kike ba abubuwa mahimmanci ” Naheel ya faɗa .
Hawayen dake gangaro mata ta share ta ce cikin muryar kuka “kayi haƙuri ! Kayi haƙuri ! Samunka shi ne ƙarfin guiwa da nake da ita na tunkarar mahaifiyata ” .
Naheel ya ce “Ban san miyasa ba , bana jin zafi kamar yadda na saba ji ” , murmushi ta ɗan yi ta ce “Na mayar da zafin a jikina ne , dan na ji irin yadda kake ji ” , numfashi ya sauke ya ce “zaki cutar da kanki na kwana uku ?” ,Naheela ta ce “idan dai zafin da nake ji yanzu shi ne abunda kake ji a can baya idan na tunkare ka to wallahi ba komai ba ne gare ni kamar yadda rashinka yake ƙona duk ilahirin jikina “. Shiru yayi yana kallon yadda take share hawaye amma wani na bin wani .
“Kwana uku zaki ɗauka kina kukan nan? ” ya tambaye , murmushi tayi wanda ya zo tare da hawaye ta ce “na ɗauki lokaci tun daga ranar da na san ina sonka kuma na fara furta maka haka duk dare kafin barcina sai nayi kuka ,dan nayi na kwanan uku ai na san bankwana muke yi”, gaɗa kai yayi alamar ya fahimta .
Nan zan dakata sai kuma gobe in Allah yasa muna da rai .
LOVE U ALL .
NASMERH LIMAN
09121873529
[8/1, 12:30 PM] QUEEN-NASMAH ❤️✍️: NAWA ƁANGAREN
HAƘƘIN MALLAKA : QUEEN-NASMAH
????MOONLIGHT WRITER’S ASSOCIATION????
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/
”’We are the moonlight writers we shine all over the world.”’
بِسم الله الرحمن الرحيم
???????? ???????? ????????
*Wohoho ! Garin daɗi na nesa ungulu ta leƙa masai . Wani Kaya Sai amale shin kun san k'ayatattun magungunan Mata na maman Haidar ko kuwa an bar ku baya *
*To ƴar uwa Kayan maman Haidar basu da matsala domin traditional medicine ne Kuma Ana had'asu da ingantattun kuma nagartattun itatuwa masu aminci da karfi da Basu da wata illa sai ma taimaka miki da zasu yi. Malam bahaushe dai ya ce In kana da kyau ka ƙara da kwalliya* ????????*Akwai wani ingantacce hadin. Manyan Mata da mamàn haidar takeyi bakowa takewa wnnn hadinba sai me matsaloli. Allah ya yaye sabida karfinsa Wanda yasan yanada kudin yi saiyay magana*
*Sannan Akwai wasu mayatattun kayan haɗi masu Matuƙar ƙarin Ni'ima da mamàn haidar take yi.
*1 Gumbar kankana da aya*
3 *Gumbar Madara da kwakwa*
4 *Kaza me ƙwai *
5 *Zabo me zuma*
6 *Kaza me allurai, sahihiyar hanyar zaki mallake mijinki ƴar uwata ba boka ba malami*
7 *Kwallin idonka inadona*
8 *Tauwadar mata*
9 *ketar larabawa magani me kankarowa mace kima da daraja*
10 *Maganin sanyi me fatattakarsa duk kuwa nacinsa Koda bakya haihuwa indai matsalar sanyice gwada wnnn*
11 *Maganin nono. Sahihi*
12 *Maganin hips and bobbs*
13 *hodar. Ni I'ma koramar mata*
14 *nakasan Mara babban sirri*
15 *kafi jijjibi*
16 *daga Sha Sai wanka kasaitacce magani*
17 *Dan kwankwalati namata da mazajensu Kevin Mata*
18 *matsin kinfi budurwa dubu ko haihuwa nawa kikai Babu magana*
19: akwai magani maza , da kuma maganin Feeling both gender Mata da maza .
*Maman haidar Bata tsaya anan ba*
*Tana Saida hijabai da yadikansu akan farashin sari yadika dila dila, hijaban Ƴan gayu sannan*
*ta kawo muku hadaddan sabulun gyaran jiki da hadin dilka Me sa shek'i da laushin fata, ga kuma mayukkan kitso Wanda laraba ke amfani dashi inkin gwada sai kin dawo ku dai ku neme Maman Haidar a wannan number domin neman ƙarin bayani*???????? 08146017245
----------------------
_I will choose no other person than you to walk down this love lane with. You're my choice, today, tomorrow, always and forever._ *HABEEB-ALBI*
€pisode 21.................
His excellency Alhaji Sulaiman bai dawo gida ba sai 9:00 na dare , wanda ya nufi part ɗin Hajiya Maryam kai tsaye domin ya ƙara duba lafiyar Nahad , tsaye ya sami Hajiya Fulani , Hajiya Maryam , Hajiya Mabaruka , Muhammad , Babangida , Adam , Abubakar , da Aliyu tsaye sunyi cirko-cirko suna kallon Ahmad da har yanzu a firgice yake yana karkarwa . Nahad kuma na daga gefe tana kallonsu a kaikaice .
“Me yake faruwa ne ?" His excellency ya tambaya , Hajiya Mabaruka tayi karaf ta ce “Dama kai nake jira ka dawo , so nake ka san Nahad ba mutum ba ce " , Nahad ta miƙe tsaye da ƙarfi ta ce “ni mutum ce kamar kowa ki daina suffantani da wata halittar " ,cikin Rashin Fahimtar zancen his excellency ya ce “ ban gane ba mutum ba ce ".
Hajiya Maryam kuwa tuni jikinta ya ɗauki rawa tana sosa ƙeya dan ta san yau dole ta fallasa sirrin da ta daɗe tana ɓoyewa iya Rayuwarta .
Hajiya Mabaruka ta ce “ka san dai tagar ɗakina ta bayan swimming pool ɗin Gidan Nan take ko " gaɗa mata kai yayi , yayinda su Muhammad suka maida hankalinsu gare ta , “Ba tun yau ba ni da idona na sha ganin Nahad ta zama kifi cikin ruwa " Hajiya Mabaruka ta faɗa , his excellency ya ce “Kifi kamar ya?" , Hajiya Mabaruka ta ce “kifi dai da ka sani , yau haka tayi ma Ahmad dalilin da yasa ka gan mu nan kenan ".
Nahad ta ce “to mine ne ciki dan na zama kifi , amma dai ni mutum ce " ,jin maganar Nahad yasa His excellency kallon Hajiya Maryam wadda tuni rashin gaskiya ya bayyana a fuskarta , duk zufa ta karyo mata . His excellency ya ce “kina da masaniya akan abun da ke faruwa ne ?".
Rufe ido tayi ta dafe kunnenta yayin da maganar da aka faɗa mata shekarun baya ta shiga dawo mata cikin kunne _*Ƴarki zata riƙa abubuwan da ba na mutane ba , zata riƙa zama maciji , kifi , mage , da kuma kaɗangare , dole ki sa mata ido ko kuma asirinki ya tonu*_ . Da ƙarfi ta ce “Ina a'a ".
His excellency ya ce “Maryam magana nake yi kin yi min shiru fa " , Nahad ta ce“ to me zata ve muku tunda haka Allah ya halicce ni , ita ai bata yin halitta ", hawaye suka fara bin kuncin Hajiya Maryam .
Fulani ta ce “Hajiya Maryam ki buɗe baki ki faɗi gaskiya , dan ko ni bazan manta ba gaba na Nahad ta zama macijiya , kuma ranar ina tsaye ta tagar kitchen ɗina ga ta zama mage ta haye katanga , alama suna nuna kin san wani abu game da haka ".
Nahad kamar an tsikare ta , ta ce “Abba me haka ke nufi , ranar fa har ƙadangare na zama ".
His excellency da ya gama gigicewa ya ce “wai ba da ke nake magana ba ", “Kayi haƙuri ur excellency , am so sorry plss " Hajiya Maryam ta faɗa cikin kuka , “haƙurin me kike ba ni , ki min bayani " ya faɗa yana zama gefen Ahmad da har yanzu bai daina karkarwa ba.
“So kake in buɗe baki in faɗa maka Nahad ba ƴarka ba ce , ko kana ganin ina da ƙwarin guiwar da zan faɗa maka ba hanyar da ya dace na samu Nahad ba ?" Hajiya ta faɗa tana durƙusawa Gaban Alhaji Sulaiman .
Cikin rashin Fahimtar zancen ta wanda yake jin hakan tamkar barazana ce gare shi ya ce “Kina so ki ce min Nahad ba Jinina ba ce taya haka ta faru ,ina so ki min bayani " yayi maganar cikin raunin dake nuna ya kaɗu da maganar Hajiya Maryam .
Su Muhammad kam sun zama ƴan kallo , dan mamaki ya dabaibaye su .
Nahad ta ce “Eh haka ne Umma ,wani sarki ya faɗa min shi mahaifina ne , ba na faɗa miki ya min laifi ba ya bada jininshi " ita har ga Allah magana take yi ko a jikinta kawai gaskiya take faɗi.
Hajiya Maryam ta ce “Eh Nahad wannan sarkin shi ne asalin mahaifinki " , “To umma wace ce Naheela ?" Nahad ta tambaya tana gyara zama cikin nuna son jin labarin , Hajiya Maryam ta ce “ƴar uwarki ce kuma ƴan biyunki ", “To ita tana ina? " Nahad ta sake tambaya , Hajiya Maryam zata yi magana Alhaji Sulaiman ya dakatar da ita “All is enough (ya isa haka ), wannan wasar kwaikwayon ta ishe ni , ki min bayani na ce ".
“Rana bata ƙarya sai dai uwar ɗiya tayi kunya , yau dole na faɗa muku sirrin da na binne tsakanin kaina , sirrin da ko Nahad bata san shi ba , a lokuta da dama Nahad kan tambaye ni , _Umma miyasa abubuwana suka bambanta da na kowa ,Umma miyasa nake ji kamar bazan iya rayuwa a wannan duniyar ba , shi akwai wasu halitta ne bayan mu , Umma miyasa nake yawan son shiga ruwa , miyasa nake jin son teku , miyasa nake jin soyayyar wani gurin da ban sani ba_ na kan bata amsa na ce Nahad haka Allah ya halicce ki , kuma akwai wasu irinki , amma yau wannan sirrin zai bayyana , zan faɗa miki wace ce ke , sannan zan faɗa ma kowa yadda na same ki " .
Sosai kowa ya natsu a parlorn yana son jin wannan abun al'ajabin banda Babangida da ya juyar da fuska kamar baya cikin parlorn .
Hajiya Maryam ta numfasa sannan ta ci gaba da faɗin “a gidan kowa ya san yadda nake so Allah ya bani haihuwa , kuma kowa ya san wahalar da na sha Hannu Hajiya Tsohuwa (wato Mahaifiyar Alhaji Sulaiman ) kafin ta bar duniya . A nan kowa babu wanda bai san irin Gorin da na sha ba , wannan abun ne yasa na ji babu abunda bazan iya yi ba matuƙar zan samu haihuwa , kwatsam sai tafiya ta kama ni zuwa Gwarzo , a can ne nake ba wata Ƙawata Hasina labarin matsalar da nake fuskanta , a lokacin ne ta bani shawara muka je wurin wani boka , shi ne ya min aiki ya tabbatar min ranar da duk na sa ƙafa Adamawa zasu sakar min jinin wata ɗaya , kuma zan yi rashin lafiyar sati uku bayan jinin ya ɗauke , idan sati uku ya cika cif Sarki Zawatunduma zai sadu dani , haka ko aka yi bayan na dawo Adamawa idan baka manta ba an yi haka " ta ƙarasa maganar tana kallon Alhaji Sulaiman , sannan ta ci gaba da magana “a ranar da sarki Zawatunduma yayi amfani da ni a ranar ciki ya shiga , dan da kaina na ji saukar ajiya mai Matuƙar nauyi a cikina , da cikin su Nahad yayi wata huɗu na koma Gwarzo wanda ya kasance umurnin boka ne , amma sai na ce maka Hajiyata ce ke nema , da na je sai aka sa nayi alƙawari idan na haife su zan bayar da wadda ba mutum ba , na ɗauki rabi mutum rabi aljan , wannan dalilin yasa na ɗauki Nahad saboda ita ce rabinta mutum rabinta kuma aljan , Naheela kuma gaba ɗayanta jinsin jinnu ne bazai yuyu ta rayu tare da mu ba , haka yasa Sarki ya mantar da ita ni , duk da ina yawan ganinta kusa da ni , wanda ita bata san wace ce ni ba " Hajiya Maryam ta kai ƙarshen maganar tana kallon Alhaji Sulaiman da rashin ya kai ƙololuwa wurin ɓaci.
His excellency ya numfashi tare da Furzar da wani iska mai Matuƙar zafi ya ce “Hajiya Maryam Na........................
Anan zan dakata sai mun baɗu a next chapter dan jin yadda zata kasance a wannan littafin mai suna NAWA ƁANGAREN.
LOVE U ALL .
NASMERH LIMAN
09121873529
[8/2, 4:46 PM] QUEEN-NASMAH ❤️✍️: *NAWA ƁANGAREN*
HAƘƘIN MALLAKA : QUEEN-NASMAH
*????MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION????*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/
*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.'''*
بِسم الله الرحمن الرحيم
???????? ???????? ????????
*Wohoho ! Garin daɗi na nesa ungulu ta leƙa masai . Wani Kaya Sai amale shin kun san k’ayatattun magungunan Mata na maman Haidar ko kuwa an bar ku baya *
To ƴar uwa Kayan maman Haidar basu da matsala domin traditional medicine ne Kuma Ana had’asu da ingantattun kuma nagartattun itatuwa masu aminci da karfi da Basu da wata illa sai ma taimaka miki da zasu yi. Malam bahaushe dai ya ce In kana da kyau ka ƙara da kwalliya ????????Akwai wani ingantacce hadin. Manyan Mata da mamàn haidar takeyi bakowa takewa wnnn hadinba sai me matsaloli. Allah ya yaye sabida karfinsa Wanda yasan yanada kudin yi saiyay magana
*Sannan Akwai wasu mayatattun kayan haɗi masu Matuƙar ƙarin Ni’ima da mamàn haidar take yi.
1 Gumbar kankana da aya
3 Gumbar Madara da kwakwa
4 *Kaza me ƙwai *
5 Zabo me zuma
6 Kaza me allurai, sahihiyar hanyar zaki mallake mijinki ƴar uwata ba boka ba malami
7 Kwallin idonka inadona
8 Tauwadar mata
9 ketar larabawa magani me kankarowa mace kima da daraja
10 Maganin sanyi me fatattakarsa duk kuwa nacinsa Koda bakya haihuwa indai matsalar sanyice gwada wnnn
11 Maganin nono. Sahihi
12 Maganin hips and bobbs
13 hodar. Ni I’ma koramar mata
14 nakasan Mara babban sirri
15 kafi jijjibi
16 daga Sha Sai wanka kasaitacce magani
17 Dan kwankwalati namata da mazajensu Kevin Mata
18 matsin kinfi budurwa dubu ko haihuwa nawa kikai Babu magana
19: akwai magani maza , da kuma maganin Feeling both gender Mata da maza .
Maman haidar Bata tsaya anan ba
Tana Saida hijabai da yadikansu akan farashin sari yadika dila dila, hijaban Ƴan gayu sannan
ta kawo muku hadaddan sabulun gyaran jiki da hadin dilka Me sa shek’i da laushin fata, ga kuma mayukkan kitso Wanda laraba ke amfani dashi inkin gwada sai kin dawo ku dai ku neme Maman Haidar a wannan number domin neman ƙarin bayani???????? 08146017245
As long as you’re in my heart and I am in yours, there is no distance great enough that our affection can’t travel. HABEEB-ALBI
€pisode 22……………..
His excellency ya numfasa tare da furzar da wani iska mai Matuƙar zafi ya ce “Hajiya Maryam Nayi Matuƙar mamakin jin haka , yau a duniyar nan da a ce wani ya ce min zaki aikata abu makamancin haka wallahi bazan yarda ba , kin fi duka matana addini da ilimi , kuma ga su nan gabansu na faɗa , amma kuma kin aikata babban kuskuren da a cikinsu babu wanda yayi ko da kaɗan ne na abun da kika yi ” , cikin kuka Hajiyar Maryam ta ce “Kayi haƙuri , wallahi ba halina ba ne , kuma ƙaddara ce ta riga fata , dan Allah kayi min afuwa daga cikin ni’imomin da Allah ya maka ” , Numfashi Alhaji Sulaiman ya sauke ya ce “Kul ! Maryam kar ki ma fara danganta hakan da ƙaddara , wannan tsabar son zuciya ne “, “Gaskiya Alhaji mu mun gaji da wannan zancen kawai kayi hukunci , tun ɗazu sai zirititi kuke yi ” Hajiya Mabaruka ta faɗa .
Murmushi ya ɗan yi ya ce “Mabaruka ke nake aure ko ke kike aurena ?”, Mabaruka ta ce “Kai ke aurena mana ” , Jinjina kai yayi ya ce “to wannan ba huruminki ba ne , kar ki sake tsoma baki ” , ai ko maganar His excellency ba ƙaramin baƙantawa Hajiya Mabaruka tayi ba , nan ta ƙara hakincewa sai wani cika take yi tana batsewa .
Alhaji Sulaiman ya ce “Ba halina ba ne saki , kuma ban taɓa ayyanawa a raina zan saki wata ba , har Abada Allah ina roƙonka da ka min tsari da furta kalmar saki ga matana , Hajiya Maryam bazan iya ce miki komai ba sai dai kawai in miki addu’a a matsayina na mijinki Allah ya shirya min ke , ya shiryar da duk wata mace mai irin kuskuren nan ” , “Ameen Your Excellency Allah ya ƙara maka girma ” Hajiya Fulani ta faɗa , murmushi ya mata ya ce “Fulani Allah ya miki albarka mace mai haƙuri da sanin ya kamata ” , Hajiya Mabaruka ta miƙe cikin tsananin ɓacin rai dan ba haka ta so ta ce “Mu da bamu da haƙuri a ce mu bi gari ” , girgiza kai yayi yana ƴar dariya ya ce “Allah ya shirya min ke , Allah ya bar ni tare da ku baki ɗaya ” , bata tanka shi ba ta wuce , sai Fulani ce ta amsa da “Ameen adalin Mijinmu “.
Hajiya Maryam da farinciki ya ƙara sata fashewa da kuka ta ce “Allah ya saka maka da gidan Aljanna , Allah ya haɗa mu baki ɗaya a aljanna ,na gode maka fiye da tuninka , Allah ya ɗaukaka ka ɗaukaka ta ban mamaki , Allah yasa kayi shugaban ƙasa a zaɓe na gaba , na gode Allah ya saka da alkhairi “, His excellency ya ce “Ameen Ya rabbi Amaryata , kowa ma zai iya tashi ya tafi , Allah ya maku albarka “, Nahad ta fara miƙewa ta ce “Kayi ma Ummata Halacci , kuma a yau ka rufa mata asiri , yadda kayi mata Allah ya maka babban alkhairi har abada”, Da ameen ya amsa ,kallon Hajiya Maryam Nahad tayi ta ce “Ana mini kiran gaggawa zan tafi sai na dawo” ɓat ta ɓace da ganinsu .