
Cikin mintuna da basu wuce talatin ba Wuta ta kama ko ina na garin ya fara ci da wuta bal-bal-bal.
Sarki Banoto yayi wata irin ƙara ya cira sama, sannan ya ɓace ɓat. Cikin garin Zawatu ya dira.
Tun kafin ya shigo cikin garin an sanar da Naheela zuwan shi saboda haka ta shirya kai mishi hari.
Bobbo bai dawo gida ba sai bayan isha’i. Mal. Jaɓɓo da sauran ƴan gidan duk suna zaune suna cin tuwo.
Yaran dake zaune kan ɗayar tabarmar suka tashi da gudu suka rungume Bobbo “sannu da zuwa Bobbonmu” kansu ya shafa da ɗaɗɗaya yana amsa musu, sannan ya nufi su Mamma.
“Ina wuni Abba ” BOBBO ya faɗa, “lafiya lau Bobbon Abba ya kake ina fatan komai lafiya”, “Alhamdulillahi “ya faɗa, Sannan ya kalli Mamma ya ce “ina wuni Mamma”.
“Lafiya lau Bobbonmu “ta faɗa.
Sai da ya gama gaisawa da kowa sannan ya tashi zai wuce, Mal. Jaɓɓo ya ce “ga wannan ka sha da safe, kasha da rana, da daddare ma kasha” ya faɗa yana Miƙa mishi wani galam, karɓa yayi ba tare da yayi gardama ba.
“Mahaifiyarka ta faɗa min abunda ya faru, kayi haƙuri na san ba abu bane mai sauƙi gare ka, Allah zai yaye maka, wannan maganin ni na Haɗa shi da kaina ka sha dan Allah kar kayi wasa da shi “.
“Ina Allah” Bobbo ya faɗa yana tashi tsaye.
“Allah ya maka albarka ” Mal. Jaɓɓo ya faɗa.
“Ameen” ya amsa tare da wuce ya nufi ɗakin Mairo.
Kwance ya same ta tana ba jaririn nono, tana jin ya shigo ta rufe idonta. Duƙawa yayi kaɗan ya sumbaci jaririn, tare sha mishi kanshi. Sannan ya cire rigar jikinshi ya rataye a ƙofa, ya dawo ya kwanta ƙasa yana tunanin rayuwa irin wadda yake yi.
Wannan somun taɓa ne a cikin labarin Nawa ɓangaren,
A littafin NAWA ƁANGAREN zaku ji yadda ƴan garin Zawatu zasu fafata da Sarki Banoto. Anan zaku ga yadda ake wasar ƙarfi, anan ne zaku ga yadda Naheela ke da ƙarfin iko, duk a nan ne zaku ga Ƙarfin ikon sarki Banoto, da kuma jarumtarsa.
A cikin littafin NAWA ƁANGAREN zaku ga yadda Bobbo zai yi rayuwa ba mahaɗin rayuwarsa.
A littafin NAWA ƁANGAREN zaku ga soyayya mai ƙarfin gaske.
Yanzu ma aka fara taɓo ɓangarora.
MASOYANA KU SA KAKANA MARIGAYI ALHAJI MUHAMMAD LIMAN (MAI-SHUKURA) ADDU’A, IDAN DA HALI ƳAR UWA KO ƊAN UWA KI/KA KARANTA MISHI SURATUL IKHLAS ƘAFA ƊAYA HAR MAKWANCINSHI. DAN ALLAH BA DAN NI ZA KU YI BA. NA GODE .
LOVE U ALL FANS……………….
NASMAH LIMAN
~JIKAR-MAI-SHUKURA~✍️
09121873529
[7/17, 12:00 AM] QUEEN-NASMAH ❤️✍️: NAWA ƁANGAREN
HAƘƘIN MALLAKA : QUEEN-NASMAH
????MOONLIGHT WRITER’S ASSOCIATION????
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/
”’We are the moonlight writers we shine all over the world.”’
بِسم الله الرحمن الرحيم
_*Wannan littafin daga farkonshi har ƙarshe sadaukarwa ne gare ka Hayateeynah (my Eternal love) ka ji daɗinka*_.
_I love you, in ways you've never been loved, for reasons you've never been told, for longer than you think you deserved and with more than you will ever know existed inside me HABEEB-ALBI_
_____________________
€pisode 9................✍️
Duka ƙarfinta take sakar ma Naheela amma ina, jikin Naheela ya rikiɗe ya koma fari tas kamar farin takarda, dai-dai lokacin sarki Zawatunduma ya diro dab, ƙasa ta tsage wani haske ya ɓullo mai matuƙar kaifi shaaaaaaa ko ina na wurin ya ƙara haske banda cikin garin Zawatu.
Cikin garin Zawatu kuwa duk wani aljani da ya mallaki gida a cikin gari ya ruguje, duk sun fito waje kowa yana tunanin yadda zata kasance da da shi, idan dai har ta tabbata Naheela ta mutu sun san basu da zaman lafiya har abada.
Ɓangaren Naheel kuwa wani mahaukacin zafi Yake ji a zuciyarshi da ilahirin jikinshi kamar ana zuba mishi ruwan zafi, da sauri ya miƙe tsaye tare da buɗe tafukan hannunshi guda biyu ya ware su “A ci ba a sayar ba, kwai ya fi doki, waya isa ya ja da mu, har wani ya isa ya kawo mana hari a garin Zawatu kuma a zauna lafiya " ya faɗa, sannan ya juyar da Hannayenshi da ƙarfi ya ƙara juyar da su, sannan ya miƙe babban farcenshi tare da faɗin “Baharadi!", nan take kukan wani Tsuntsu ya karaɗe daƙin, da alama shi ne Baharadi.
“Kana ji kana gani ka bari Banoto ya zo Zawatu, maza da gaggawa ka dira garin Mubanuwa ka hargitsa su, ka janyo musu hasara" ya faɗa.
Nan take tsuntsun nan ya tashi sama.
“Barhana " ya faɗa yana ɗaga farcenshi sama, sai ga wata ƙatuwar tsuntsuwa girmanta ya ɗara na doki.
“Kai ni ga Gimbiya Naheela, mu je kina fitar da jin bakinki" ya faɗa, tare da yin ƙasa da hannunshi.
Cak ya ji yayi sama, ya hau kan Barhana, wani ƙarfe ya fitar daga farcenshi, ya ɗaga shi dai-dai saitin Rufin ɗakinshi, nan take ɗakin ya buɗe, tsuntsuwar ta tashi sama bakinta buɗe.
Jini ya dinga zuba daga bakinta, nan take aka fara ambaliyar jini a garin Zawatu, ran ɗan sarki ya ɓaci dole kowa ya san da ɓacin ran Naheel. Dan Naheel mugun aljani ne.
-----------------
“Naheela!, Naheela!, Naheelaaaaaa! " Sarki Zawatunduma ya faɗa da ƙarfin tsiya.
Sarki duk ya rikice ya rasa ta ina zai fara, da ƙarfin tsiya ya fara magana “ na rantse da Allah sarki mai sama, wanda yayi ni yayi kowa da kowa garin sai garin Mubanuwa sai ya zama labari babu mahaluƙin da ya isa ya rayuwa ko kuma ya zauna in dai garin Mubanuwa ne, garin Mubanuwa sai ya zama guba ga duk wanda ya tunkari garin, rayuwa duk wani ɗan Mubanuwa fansar rayuwarki Naheela".
Hannayenshi guda biyu ya ɗaga sama da ƙarfin gaske, ya ce “Sukam kayi ɓarin manyan duwatsu cikin garin Mubanuwa ".
-------------------------
Babbo duk ya zare saboda duk inda ya tafi sai ya riƙa ganin ana rubuta NAWA ƁANGAREN a bango. Tafiya yake yi hanyar da dawowa daga kasuwa ya ɗaga kanshi ya kalli wani doki fari ƙal da shi, da wani rubutu a kai da ya gagara karantawa, ci gaba da tafiya yayi yana tunkaro dokin.
NAWA ƁANGAREN ya ga an rubuta jikin dokin da sauri ya kawar da kanshi, yana faɗin “innalillahi wa'inna ilaihir raju'un", kallon inda dokin yake amma da mamakinshi dokin yayi tafiyarshi, juyawa yayi sai ya hangi dokin na gudu kamar zai tashi Sama, juyar da kanshi yayi.
“Da alama na fara zarewa " ya faɗa, sannan ya ci gaba da tafiya.
-----------------------
“Mairo Kin cika taurin kai wallahi, miye amfanin rashin ba ƙaramin Sadauki nono" Mamma ta faɗa tana girgiza Sadauki dake faman kuka.
“Abin cikin kwai, ya fi kwai dadi, me zai hana ku bashi madarar Shanu " Mairo ta faɗa.
Mamma ta riƙe haɓa, tana faɗin “Abin mamaki! Kare da tallan tsire, in bada abun ki ina aka taɓa ba yaro madarar shanu bayan yana da abincinshi, a rashin uwa ne ake yin ta ɗaki".
Mairo da ta turo ɗan kwali gaban kanta ta ce “to ni dai bazan bada ba, ya je yayi uwar ɗakin ".
Mamma ta ce “ ba komai ɗan kuka mai ja ma uwarshi zagi, yanzu in ba dan Bobbo ko an ce ki min rashin kunya ai ba za ki yi min ba" tana gama maganar ta bar ɗakin tare da Sadauki.
Dai-dai lokacin Bobbo ya shigo cikin gidan, turus ya tsaya yana kallon Mamma.
“Yauwa Alhamdulillahi, faɗuwa ta zo daidau da zama tunda gaka ka zo ai sai ka ji da ɗan ka ni bani da abun ba shi " ta faɗa.
Matsowa yayi kusa da Mamma ya ce “me ke faruwa ne".
“karɓi abunka sannan muyi magana " ta faɗa tana miƙa mishi Sadauki da ke shan hannu.
Karɓar Sadauki yayi, yana kallon Mamma da tambaya a idonshi.
“Ga shi nan ka cire riga ka bashi nononka tunda uwarshi ta hana shi abinci, tun safe yake kuka, kai da ka ja mishi sai ka bashi ya ja naka" Mamma ta faɗa.
“Hhhhmm, Mamma kenan, ai namiji baya shayarwa " ya faɗa.
Mere tayi ta ce “ ina na sani ko yau kanka za a fara".
Murmushi yayi wanda ya fi kuka ciwo ya ce “ ba damuwa Mamma bari in je wurin shanu in tatso mishi madara ya sha ".
Mamma ta ce “to yayi kawo shi in riƙe maka".
“Ba damuwa ai ni janyo mishi komai bari in je da shi sai in ba shi ya sha na gode " ya faɗa yana juyawa da yaron.
------------------
Ɓangaren da suke kiwo ya zagaya ya shiga ciki, Saman wani dakali ya ɗora yaron, sannan ya ɗauki wani kofi da suke tatsar madara da shi ya tatso madarar, sannan ya dawo ya ɗauki yaron.
Zama yayi tare da ɗora yaron kan cinyarshi ya ce “yi haƙuri mai sunan Manya, komai zai wuce, na san ban maka adalci ba da har na janyo aka maka horo da yunwa, amma wata rana sai ya zama labari insha Allah"
Madarar ya dinga bashi yana sha, sosai tausayi ya kama shi, yadda yaron ke shan nono zai tabbatar maka da yunwa yake ji, kanshi ya ɗan sha, sannan ya manna shi a ƙirjinshi ya ce “kai ma kamar sauran yarana kake, ina fatan yanayin halittata kar ta cutar da ku, kar ku samu nakasu kamar ni ".
Anan Zan dakata dai kuma gobe in Allah ya kai mu.
_MASOYANA KU SA KAKANA MARIGAYI ALHAJI MUHAMMAD LIMAN (MAI-SHUKURA) ADDU'A, IDAN DA HALI ƳAR UWA KO ƊAN UWA KI/KA KARANTA MISHI SURATUL IKHLAS ƘAFA ƊAYA HAR MAKWANCINSHI. DAN ALLAH BA DAN NI ZA KU YI BA. NA GODE_ .
LOVE U ALL FANS...................
*(QUEEN NASMAH)NASMAH LIMAN*
~*JIKAR-MAI-SHUKURA*~✍️
*09121873529*
[7/17, 12:00 AM] QUEEN-NASMAH ❤️✍️: *NAWA ƁANGAREN*
HAƘƘIN MALLAKA : QUEEN-NASMAH
*????MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION????*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/
*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.'''*
بِسم الله الرحمن الرحيم
Wannan littafin daga farkonshi har ƙarshe sadaukarwa ne gare ka Hayateeynah (my Eternal love) ka ji daɗinka.
I didn’t have a life before I met you. I was merely existing, then you came and set my heart sour on fire. I’m bound to you forever, sweetheart. You made my life colorful I love you Habeeb Albi
€pisode 10…………….✍️
Barhana da sarki Zawatundma ya aika zuwa garin Mubanuwa kuwa da sauri ta fara keta hazo har ta isa garin Mubanuwa inda wani mahaukacin iska mai matuƙar ƙarfi ya fara girgiza manyan duwatsun dake cikin garin. Cikin ɗan ƙanƙanin lokaci duwatsun suka fara tsagewa, garin ya rikiɗe, sai iska da ke ta kaɗa abubuwa, yana kwasar kayansu zuwa sama.
Take ƴan garin suka fara gudu suna neman mafaka, musamman da labari ya zo musu cewa babban dutsin garin wanda wani bai taɓa hawa ba saboda yadda suke girmama dutsin, akasari ma wasu daga cikin ƴan garin wannan dutsin suke bauta ma, tun da suka ji labarin ya rabe biyu kowa ya san yau tashin hankali zai afku a wannan garin, dan duk wanda ya girma ya tashi ya san da zaman wannan dutsin da suke kira MIRACLE STONE.
Tsuntsun da Naheel ke kira Baharadi ne ya shigo da guguwar zuma mai matuƙar yawa da dafi, zuuuuu zuuuuu haka zumar suka dinga kuka, sun fi ƙarfin minti talatin kafin suka fara saukowa, domin har gitsa garin Mubanuwa kamar yadda Yareema Naheel ya umurta.
Zuma nan ta dinga shiga kunnuwan aljanun garin tana gigita musu lissafi, yayinda duwatsun da Barhana ta suka suka fara gangarowa suna danne ƴan garin, gidaje suka riƙa rushewa, duk yadda aljanun garin suka kai ga tsafi yau sun ga wutar dafa kansu, dan komai ya gagare su sai gudu.
Wasu sai gudu suke, amma duk yadda ka kai ga gudu wannan dutsin sai ya cimma maka. Cikin mintuna da basu wace talatin ba Barhana da Baharadi suka shafe tarihin garin baki ɗaya. Babu ko halitta ɗaya da ta rage a garin ko da kuwa halittar tsuntsu ce.
“Naheela! ” Naheel ya kira sunanta da ƙarfi, kamar an taɓata ta buɗe Idonta ƙyar ta fara yunƙurin tashi ganin abun ƙaunarta tsaye gabanta.
Hannunshi ya kai Saiti da inda mashi ya cake ta ya rufe idonshi, a hankali ya jaye hannun, da kallo ta bi wurin da Naheel ya taɓa, bata yi mamaki ba dan ta ga babu Ko alamar tabo a gurin, miƙewa tayi yayinda Naheel ya juya zai wuce.
“Abbana ka mishi godiya na san bazai saurare ni ba ” tayi maganar Idonta na zubar da ƙwalla.
Juyowa Naheel yayi ya ce “ki Adana kalamanki, zasu miki amfani wani wurin ba nan ba, bana buƙatar godiyarki”.
Wani farin haske Naheela ta aika ma Naheel daga cikin Idonta nan take ya tsaya cak.
Cikin taku na isa ta ƙarasa gabanshi, wanda yake jin wani mugun zafi na tunkaro shi.
“Ka san miyasa ban tilaska zuwa gare ni ba yau? ” tayi maganar tana shafa mishi ƙirji da yatsunta guda ɗaya.
Ta san ba zai iya yin magana ba saboda ta dakatar da shi daga yin motsi haka yasa ta ci gaba da magana.
“Saboda ka zo ceton raina ne, ya kamata na saka maka da alkhairi ba akasin haka ba, ka sani ni Naheela ba a haife ni dan in gaza ba, burina na zama ɓangarenka sai ya cika, kai NAWA ƁANGAREN ne, babu kowa a ɓangaren Naheela sai kai ” tana kai ƙarshen maganar ta hura mishi iska a fuska.
Hannunshi ya ɗaga ya nuna ta da shi “kin san ba dan ke na zo nan ba, na zo nan ne Saboda al’ummar garin Zawatu, na san idan kika bar duniya Zawatu zata samu jakadu, dan haka ne cece numfashinki ne saboda al’ummar Zawatu ” ya faɗa
“Hahahahahahahaaaaaaa!” Naheela ta ƙyalƙyale da wata mahaukaciyar dariya, da ta saka dajin ruɗewa.
“A ɗaga sama! An yi wa wada ƙwace, In ban da abunka waya ce maka ƙarfinka ne ya ceci numfashina ” ta faɗa, sannan ta girgiza kanta “samsam ba haka ba ne, da ace ƙarfi ke ceton rayuwata da Binaf ta cece ni kafin ka zo, da ƙarfi zai iya ceton rayuwata da Abbana Masoyina ya bani rayuwarshi da iya ƙarfin da yake da shi” ta faɗa tana ƙara taku, sannan ta ce “soyayyarka ita ce bugun Numfashina, kusantata da kayi shi ne Maƙasun yin numfashina a yanzu ƙarfinka bashi da tasiri a kaina, ba wani mai wannan ƙarfin “
Ji yake kamar ana soya shi da ruwan mai, ga wani mugun zafi da yake ji har cikin jijiyoyinshi. Da ƙarfi ya ce “Wannan wane irin bala’i ne, na tsane ki, wallahi na tsane ki, ke ba wata ba, ke dai Naheela wallahi, wallahi bazan iya rayuwa ba ki daina kusanta ta mutuwa ita ce aminiyata idan kina kusanta, me na miki da kike azabtar da ni”.
Murmushi tayi, sannan ta ce “zaka saba da ni a matsayin abokiyar rayuwa “ta faɗa.
Ɓat ya ɓace dan bazai iya ƙara fitar da numfashi ba in dai Naheela na a gefenshi.
Juyawa tayi ta kalli Abbanta da tun ɗazu yake kallonta.