NAWA BANGAREN

NAWA BANGAREN COMPLETE

NAWA BANGAREN COMPLETE HAUSA NOVEL

Murmushi ta mishi ta ce “na san abun da kake ƙiyastawa a ranka ya masoyina”.

Sarki Zawatundma ya ce “ina duba gaskiyar abun da ya faɗa ne “.

Numfashi ta sauke ta ce “to me ka gani”.

“Da gaske ne yana ƙonewa idan mace ta kusance shi ” ya faɗa.

Zuwa tayi ta jera da Mahaifinta, tare da gaɗa mishi kai ta ce “ na san wannan, amma kuma ina so ya saba da ni a tare da shi”.

Gaɗa kai Sarki Zawatunduma yayi ya ce “Eh na ga gaskiyarki ai, na fahimci zaki iya “.

“Ka san zan iya, amma kuma ta yaya?” ta tambaya, suna ƙara matsawa gaba.

Numfashi ya sauke ya ce “ƙarfin da kike da shi zai iya yin komai, kawai ki san yadda zaki yi amfani da shi”.

“Haka ne Abbana zan yi yadda ya dace “.


Yaran Bobbo ne waje suna zana Ƴar gala-gala, suka hango Bobbo riƙe da ƙaramin Sadauki, da sauri suka nufo shi suna faɗin “Sannu da zuwa Bobbonmu”, shafa kansu ya dinga yi da ɗaɗ-ɗaya, sannan ya ba ko Wannensu naira goma-goma.

Dama can abunda ya saba musu kenan ko wace ranar Juma’a, yau ma haka yayi, sai tsalle suke yi.

Da gudu suka nufi wurin Ade mai aya. Wata tsohuwa ce ke kasa kayan ƙwalam a wajen gidanta.

Aka yi sa’a lokacin da gama ƙulla Ayar, ai ko nan take suka siye ƙullin Ayar da tayi.

Ɓangaren Bobbo kuwa cikin gida ya shiga, kai tsaye ɗakin Mamma ya nufa, in da ya tarar da Mamma………………….

MASOYANA KU SA KAKANA MARIGAYI ALHAJI MUHAMMAD LIMAN (MAI-SHUKURA) ADDU’A, IDAN DA HALI ƳAR UWA KO ƊAN UWA KI/KA KARANTA MISHI SURATUL IKHLAS ƘAFA ƊAYA HAR MAKWANCINSHI. DAN ALLAH BA DAN NI ZA KU YI BA. NA GODE .

LOVE U ALL FANS……………….

(QUEEN NASMAH)NASMAH LIMAN

~JIKAR-MAI-SHUKURA~✍️

09121873529
[7/17, 12:00 AM] QUEEN-NASMAH ❤️✍️: NAWA ƁANGAREN
(NW-B)

HAƘƘIN MALLAKA : QUEEN-NASMAH
????MOONLIGHT WRITER’S ASSOCIATION????
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

”’We are the moonlight writers we shine all over the world.”’
بِسم الله الرحمن الرحيم

*_Your voice is my favorite sound_ HABEEB-ALBI* 



£pisode ~11

Cak ko ina na garin Zawatu ya tsaya , haske ya bayyana ko ina alamar gimbiya Naheela ta dawo hayyacinta.

Sarki Zawatunduma da Naheela kuwa ɓacewa suka yi ɓata . Sai gaban Teku . Wani tsalle suka yi a tare suka shige cikin ruwan .


Garin Mubanuwa kuwa babu wanda ke motsi ,ruwan duwatsun da aka yi sun yi musu muguwar illa ,wasu da yawa lokacin girgiza ƙasa sun faɗa cikin ƙasa .


 Ko ina labarin garin Mubanuwa ake yi domin kuwa  cikin ɗan ƙanƙanin lokacin labari ya zagaye ko ina .


---------------------

Bayan wasu kwanaki .

Yau ake taron sunan ƙaramin Sadauki .inda aka yanzu mishi ɗaya daga cikin shanun da suke kiwo da kuma rago ɗaya , dama Bobbo duk aka mishi haihuwa cikin dabbobin da yake kiwo ake ɗiba . Bobbo mutum ne da Allah yayiwa arzikin kiwo , yana da garken dabbobi sun fi a ƙirga , duk garke ɗaya ba za ka iya gane yawansu ,dan ko shi da yake kiwon bai san iya adadinsu ba .iya abinda kawai ya sani rago guda ɗaya ya siye amma da shi yayi arzikin da ya tara duk waɗannan dabbobin .


Mutane sai shiga suke yi gidan taron suna . Duk wanda ya shigo sai ya fita yana gulmar Mairo ,dan duk baƙon da ya shigo bata bashi ko ruwa ba ,ko wanka Mairo bata yi ba ,ga Sadauki sai kuka yake yi kamar ranshi zai fita ta ƙi da ɗaukarshi .

 “Ke ko Mairo ki ɗauki yaron nan ki bashi nono ya sha mana" wata Tsohuwa ta faɗa ,wadda bata wani daɗe da shigowa ba. Kallon tsohuwar Mairo tayi a kaikaice ta ce “ai ki ɗauke shi ki bashi nonon ban hana ki ba ".

“A'a aha ,raba ni da yari bani auren sarki ,gani nayi yaron sai kuka yake yi " tsohuwar ta faɗa.

Mamma ta shigo cikin ɗakin jin kukan Sadauki ya ƙi ci ya ƙi canyewa .

“Miƙo min shi nan tun da bata da imani "Mamma ta faɗa .

Wata yarinya dake zaune gefen katifa ta miƙa hannu ta ɗauki Sadauki ,sannan ta miƙa ma Mamma shi .

Mairo ta kalli Ƴan ɗakin ta ce “ku fitar min daga ɗaki ga yaron can an fita da shi ".

Tashi suka yi suka fita
Mairo ta ci gaba da bambami “ba wanda aka gayyata amma da yake harkar ci ce duk kun zo ".

Ba su kula ta ba suka fita suka bar ɗakin .


_________________

“NAWA ƁANGAREN " Bobbo ya ji ana faɗi da ƙarfi duk muryar ta karaɗe jejin .

Da sauri ya juya dan jin daga ina sautin yake amma bai ga kowa ba .

Ta ɓangaren hagu ya ƙara jiyo sautin “Nawa ɓangaren ,Nawa ɓangaren ,Nawa ɓangarennnnnn !!!!!!!" da sauri ya juya ta ɓangaren hagu amma bai ga mai maganar ba .

Miƙewa tayi daga Saman kujerar da yake zauns . Take ya fara jin jiri ,da sauri ya dafe kanshi yana jin duniya na mishi yawo , gami da jin ana mai-maita abu ɗau .“NAWA ƁANGAREN ". Dafe kunnenshi yayi yana ji zuciyarshi na mishi barazanar tarwatsewa .

Da wani irin mugun ƙarfi yake jin zuciyarshi na bugawa , yayinda yake ganin alamar mutum  na wucewa ta gabanshi da sauri ,sai kuma a dawo da sauri ,haka ya dinga ganin abu kamar wani shirin wasar kwaikwayo .


Yafi ƙarfin minti goma a wannan yanayin sannan daga baya komai ya tsaya cak ,a hankali ya fara buɗe idonshi ,in da ya sauke su kan wata Kyakkyawar yarinya mai Matuƙar kyau ,murmushi kawai take yi . Fuskarta bata da maraba da ta Naheela ,sai bambancin halitta .

Take jikin Bobbo ya ɗauki wani irin rawa ,zufa ta karyo mishi , wacece wannan yarinyar ? Ya ayyana a ranshi .

Murmushinta ya faɗaɗa yayinda fararen haƙoranta masu ƙyalli suka bayyana , “Ibrahim!" ta furta a hankali tana murmushi .


Rufe ido ya sake yi ,ya kuma buɗe su da sauri yana murza idon ,domin ƙara tabbatar da abunda idonshi ke nuna mishi .


“Ni ce ɓangarenka da kake gani a mafarki " Ta faɗa .


Hannunshi ya miƙar yana ƙoƙarin taɓa ta ,amma sai ya ga da sauri ta cira sama . Ɗaga kai yayi yana kallonta .

Murmushi take sakar mishi, da ɗan ƙarfi yadda zai jiyo ta ta ce “Ibrahim ni wadda ba a iya taɓawa ce ,kuma ni ɓangarenka ce . Lokaci zai yi da zan baka dama ka taɓa ni, sai wata rana". Bobbo na tsaye yana kallon ikon Allah har ta ɓace mishi da gani kamar hoto haka ta dinga dishewa har wurin ya koma ba kowa .


Saukar da kanshi Bobbo yayi daga kallon Saman da yake , wani mugun ciwon kai ya dabaibaye shi , jikin shi ya fara kakkwarwa ,haƙoranshi na gamewa .

Da ƙyar yake taka ƙasa a daddafe yana bin bango har ya samu ya shigo inda mutane suke .


Jatau mai Faskare yayi sauri a je gatarin da yake Faskare da shi ,ya nufo Bobbo da sauri ganin yana layi kamar zai faɗi ya taro shi yana faɗin “Lafiya dai Bobbo " , cikin ƙarfi hali ya ce “ lafiya alhamdulillahi ,kama ni mu je gida dan Allah " muryarshi sai rawa take yi .


Riƙa shi yayi har suka isa ,Jatau ya cika da mamakin ganin yanayin Bobbo .


Kewayensu Bobbo ya zagaya da shi . Mamma na goye da ƙaramin Sadauki aka shigo mata da Bobbo . Salati ta fara yi ,tana mamakin yau Sadauki ne aka riƙo haka ,da ƙyar Jatau ya ƙaraso da shi gaban Mamma dan Bobbo ya riga ya galabaita . Tabarmar kabar da Mamma ta shimfiɗa ,Jatau ya kwantar da Bobbo .


“Ina ka haɗu da shi Jatau ?" Mamma ta tambaya .

“Kin san ba a raba Bobbo da zama jeji ,ta wurina na ga ya gifto ,da alama daga can yake " ya faɗa .


Mamma ta ce “Mun gode Jatau Allah ya biya ka "
Matsawa tayi kusa da Bobbo da jikinshi yayi wani mugun zafi kamar garwashi ,amma kuma sai zufa yake yi da rawar sanyi ,wannan wane irin al'amari ne .

“Sannu ka ji Bobbo " ta faɗa .

Ba zai iya magana ba ban da bakin shi dake haɗewa tsabar sanyi da yake ji.


Da sauri Mamma ta shiga ɗakin ta ta ɗauko zani ta lulluɓe shi , sannan ta zauna gefenshi .

Tana zaunawa Sadauki ya ƙara fashewa da kuka ,da sauri ta miƙe tana jijjiga shi .

“Wannan wace jarabawa ce take tunkaro mu ?" Mamma ta faɗa .


Asama ta fito daga ɗakinta tana faɗin “Wai kukan me ƙaramin Sadauki ke yi  da tsakar ra..... " maganar ta tokare ganin an lulluɓe Bobbo .

“Me ? Me nake shirin gani haka ?" ta faɗa cikin ruɗani.

Mamma ta ce “ke ki zo ki gane mini wannan al'amari ,ɗa kwance uwa kwance haihuwar guzuma ".

Asama ta ce “Subahanallahi ,to me ya sami Bobbo ?".

Mamma ta ce “yadda kika ganshi to nima haka na gashi . Ki mishi fatan Allah ya ba shi lafiya mu ji me ya same shi ,ni yanzu riƙe min Sadauki ".


“To Allah ya ba shi lafiya " Asama ta faɗa .

Mamma ta miƙawa Asama Sadauki . Sannan ta duƙa gaban Bobbo . Kanshi ta kama tana mishi addu'a ,shi kuma ya rufe ido yana jin kamar zai yi barci .


Anan zan daka ta ......✍️

Na san kuna da tarin tambayoyi da zaku min ƙofa a buɗe take zaku iya yi .


Comment is very important ❤️

Idan aka yi nisa kar ki ce in turo daga farko .

Ki bibiya lokacin da ana yi .


Na gode sosai .


Love U all my dearies .


✍️
[7/17, 12:00 AM] QUEEN-NASMAH ❤️✍️: *NAWA ƁANGAREN* 

HAƘƘIN MALLAKA : QUEEN-NASMAH 

*????MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION????*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.'''* 
بِسم الله الرحمن الرحيم

I wasn’t expecting you. I didn’t think that we would end up together. The single most extraordinary thing I’ve ever done with my life is fall in love with you. I’ve never been seen so completely, loved so passionately and protected so fiercely HABEEB ALBI .

£pisode ~12

GANYE…….
Iskan da ke kaɗawa ko ina zai tabbatar maka da ruwan sama ke shirin sauka musamman yadda hadari ya taso yake ta majaujawa da ledodi a sararin samaniya.

Unguwar Ngurori
Wani tamfatseten gida ne na ji na gani a unguwar , motocin dake cikin gidan idan ka gani zaka yi tunanin kamfanin motoci ne , ga furanni ko ina na gida .

Oda aka fara yi tare da jiniya alamar mota na ƙoƙarin shigowa cikin gidan ,da sauri Burhama ya tashi sanye da kakinshi ya leƙa ta gate ɗin . Ta sauri ya kara wata waya me kamar radiyo ya ce “Excellency ne ya dawo ku matso ” .

Nan take duk ma’aikatan masu kaki suka fito daga inda suke . Ma’aikatan kan su sun fi a ƙirga .

Duk suka jera kansu kamar waɗanda zasu yi assembly .

Gate ɗin Burhama ya tura ya buɗe .

Motoci guda biyar suka shigo inda duka sojojin suka ƙame wuri ɗaya tare da sarewa .

Dai-dai ma’ajiyar motoci suka yi parking motoci . Yayin da sojoji suka diddiro daga cikin motar suka nufi wata farar mota mai tinted (glass ɗinta baƙi).

Buɗe motar suka yi suna ƙamewa kamar ɗazu yayin da dattijon dake cikin motar ya fito ,sanye da babbar Riga ,yana ta ɗaga musu hannu cikin takun ƙasaita ,da ganinshi kuɗi sun samu wurin zama a gidan . Bai yi taku uku masu kyau ba ruwan sama suka sauko . Da sauri ɗaya Daga cikin sojan ya buɗe Lemar da ke hannunshi ya kara ma Excellency har ya shige cikin gida .


Yadda Su Mamma suka ga safiya haka suka ga dare ko kaɗan Bobbo be yi rutsa ba sai sambatu da yake ta yi yana ihun Wacece ɓangarenshi .

Baffa ne ya shigo da wasu ruwan magani ya miƙawa Mamma yana faɗin “ tashi ki tafasa maganin nan ina ganin gamo Bobbo yayi “.

Arɗo ya ce “wallahi ko ,ni abun har tsoro yake bani “.

Mamma zata Karɓi maganin daga hannu Baffa kenan Asama ta ce a bari ta dafa .

Tashi tayi ta ɗora shi akan wuta ta dawo .

“Kin dame ni da kalmaminki guda biyu ,ni ba ɓangarenki ba ne .kina azabtar da ni kawai “.

Babbo ya faɗa da ƙarfi .

Mamma ta fara mishi addu’a tana tofa mishi yayi da jikinshi ke ta kakkarwa .

Asama ta tashi ta juye maganin cikin kwano ta kawo .

Baffa karɓa ya ɗauki wani ƙyalle dake gefenshi ya tsoma yana matsewa yana shafa mishi a goshi .

Bobbo dai ji yake kamar ana zarar ranshi tsabar raɗaɗi .

Da ƙarfi ya ce “Nawa ɓangaren ,nawa ɓangaren kin takura min da Nawa ɓargaren ,dan Allah ki ƙyale ni ” ya kai ƙarshen maganar hawaye na gangaro mishi .

“Bazan jure hawayenka ba sadauki ” ɓangaren Bobbo ta faɗa tana ɓacewa .

Rufe idonshi yayi yana ji kamar an cire mishi rabin shashen jikinshi .

” Bobbo ” Mamma ta faɗa ganin baya motsi .

Yana jinta amma ba zai iya ɗaga hannunshi ba ,haka ma bazai Iya buɗe ido ba .

“Mamma ” ya faɗa . Abun mamaki Mamma har yanzu sunanshi take kira .

Arɗo ya ce “ Ya na ga kamar baya numfashi “

Bobbo ya ce “Ina numfashi mana ,idona ne bana iya buɗewa ” amma duk da haka babu wanda ya ji abun da ya ce .

Mamma ta ce “Kamar baya numfashi , me gida duba mana shi “

Matsowa Baffa yayi kusa da Bobbo ya ƙara hannunshi dai-dai saitin hancinshi .

Kallon Mamma yayi ya ce “Yana numfashi mana “

Asama ta ce “Miyasa baya buɗe ido “

Baffa ya ce “wataƙila yayi barci”

Mamma ta ce “Allah yasa “

Da ameen suka amsa .

Dai-dai lokacin Mairo ta fito daga ɗaki goye da Sadauki .

Zuwa tayi ta duƙusa gaban su Mamma ta ce “Na san ba kowa ne zai fahimci ni ba ,amma ina da buƙatar namijin da zai biya min Buƙatuna ,Bazan iya zaman aure da Bobbo ba . Saboda haka zan tafi gida da Sadauki ,nayi alƙawari zan ci gaba da shayar da shi har na yaye shi .ina so idan Bobbo ya samu iya buɗe baki in nayi kwana ki arba’in nayi wankan tsarki a sanar da ni zan zo in karɓi takarda ta . Ina mishi Addu’a Allah ya bashi lafiya Allah ya mishi mafita ” .

Mamma ta ce “to kalama a baki dan bakinki “

Arɗo ya ce “Mamma ki bar yin irin haka Mairo na da gaskiya wallahi “

Baffa ya ce “haka ne ,Allah dai ya ba Bobbo lafiya “


Madubin sihiri Naheela ke kallo tana taɓa madubin da wata sanda .

Rufe ido tayi tana jan hanci .

“Naheel ” ta faɗa .

“Na jiyo ƙamshinka masoyi ” ta ƙara faɗa tana lumshe ido .

Tsalle ta daka nan take rufin ɗakin da take ya buɗe ta fita .

Idonta ne suka yi mata tozali da abin begenta Naheel .
Da ƙarfi ta diro
“Na ji a raina wuta na tunkaro ni ashe ke ce ” ya faɗa ba tare da ya juyo ba .

Naheela ta ɗan yi murmushi ta ce “shin ko zan iya sani me yareema ke yi cikin dokar dajin nan “

Har yanzu bai juyo ba ya ce “yawon miƙe ƙafa “.

“Ba wurin miƙe ƙafa sai wurin dubana” ta faɗa .

“Ki daina tunkaroni zaki ƙona ni wai baki fahimta ba ne ” yanzu kam cikin ɓacin rai yake maganar .

Murmushi ta ɗan yi tana “faɗin zaka saba dani a gefenka Yareemana ,ka amsa mini tambayata “.

“Ke kika ɗauki nan wurin duba ni wurin shan iska na ɗauke shi “.

Zata yi magana kenan ya ɓace .

Murmushi tayi ta ce “da sannu zaka saba da bugun numfashina a kusa da kai “

Juyawa tayi itama ta kalli gidan sihirinta nan take ta ɓace .sai gaban madubin ɗakin .

Rufe ido tayi kamar ɗazu .

Da wata gigitacciyar tsawa ta ce “Mudubin Sihiri ka haska min cikin zuciya Naheela “.

Warrrrrrr ! Ta buɗe ido wani koren haske ya fara fitowa daga idon ,nan take madubin yayi wani rame ya dinga juyawa kamar majaujawa .

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Leave a Reply

Back to top button