NAWA BANGAREN

NAWA BANGAREN COMPLETE

NAWA BANGAREN COMPLETE HAUSA NOVEL

Cikin daƙiƙa da basu wuce biyar ba madubin ya dawo ɗauke da hoton zuciyar .

“Cikinta na ce ba wajenta ba ” ta faɗa tana sakin jar wuta cikin Idonta .

Bayan wasu daƙiƙu madubin ya sake tsayawa daga juyawar da yake .yanzu ma ɗauke yake da hoton zuciyar .

“Cikinta na ce ko baka ji ba ” ta faɗa tana sakin tsanwan haske .

Amma har yanzu hoton zuciyar kawai yake bata .
Nan take jijiyoyin Idonta suka fiffito waje suka bude ƙuru-ƙuru da su .

Furuttanta suka miƙe suka yi zago-zago haƙoranta suka fiffito waje zara-zara da su . Cikin rawar murya da Matuƙar ƙarfi ta ce “Cikin zuciyar Naheel ” wani mahaukacin zafin ya fara bugun madubin .

“Ba Za ki iya ganin Zuciyar Naheel ba ,muddum in Raye ” wata murya ta karɗe ko ina .

Wuta Naheela ta fara saki ko ina duk ta haukace kamar ta ci babu .

“Ba mahalukin da ya isa ya min katanga tsakanina da Naheel ko shi Naheel ɗin da kan shi ballantana ke Zuhuriyya ,ki shirya tarbar bala’in da zai tunkare ki akan shiga gonata da kika yi “Naheela ta faɗa …………………

To masu karatu an zan dasa aya .

Sai jibi in Allah yasa muna da rai .

Alƙalami ya fi takobi .

NASMERH LIMAN
09121873529
[7/17, 12:00 AM] QUEEN-NASMAH ❤️✍️: NAWA ƁANGAREN

HAƘƘIN MALLAKA : QUEEN-NASMAH

????MOONLIGHT WRITER’S ASSOCIATION????
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

”’We are the moonlight writers we shine all over the world.”’
بِسم الله الرحمن الرحيم

*_In a sea of people, my eyes will always be searching for you_* *HABEEB-ALBI*

£pisode -13............
Babban parlorn gidan ya shiga ,masha Allah gidan ya tsaru ƙarshen mataki , parlorn wani irin katafaren parlorn mai ɗauke da manya-manyan kujera in dai ba an faɗa maka mutum yana zaune kai ba to daga nesa ba za ka san akwai mutum zaune ba . Cikin takun da dattako ya shigo tsakiya parlorn da baka jin ƙarar komai sai sautin akwatin talabijin .

Wata hanya ya bi wadda zata sada shi da ɗakimshi . Aka ce idan kana duniya baka gama kallo ba ,a wannan gidan ma kaɗai zaka ga abun al'ajabi dan wajen gidan ba komai ba ne in aka haɗa da cikin . Wasu manya-manya ƙofofi ne aka shiga buɗewa har guda uku ,ko wace ƙofa da maza guda biyu tsaye gefenta . Ƙofar ƙarshe da aka buɗe kuwa ta bayyana wane haske ban mamaki ,wanda sai ka kalla zaka fahimci haske zinari da aka yi amfani da shi ne wajen ƙawata bangon wurin da wasu kallar duwatsu masu mugun ƙyalli .Ɓata lokaci ne bayyana yadda gidan yake .

Wata ƙofa ya buɗe ya shiga  . Kayan jikinshi ya fara ragewa sannan ya shiga toilet yayi wanka. Wata tsadaddar Jallabiya ya saka sannan ya bita da da wasu ni'imtattun turaruka masu ratsa ƙwaƙwalwar wanda ya shaƙa.

------------------
Washe gari 
“Wai ni Allah wai ni Kaina Bobbo har yanzu bai motsa ba " inji Mamma dake zaune tana ta faman gasa mishi jikinshi da ya mugun yin zafi.
Asama ta numfasa ta ce “wai Mamma ba zamu kai Bobbo asibiti ba ta iya yuyywa zafin ciwo ne ke sa shi sambatu ".

“Kuma kin kawo shawara ina ganin haka za a yi ,bari mahaifinsu ya dawo mu gani ya Za a yi"
Manna ta faɗa tana ci gaba da danna mishi goshinshi a hankali da ƙyalle .


“Salamu alaikum " Arɗo yayi sallama ,“wa'alaikumus salam " suka amsa mishi a tare .

Zuwa yayi ya zauna kusa da Bobbo yana faɗin “har yanzu bai samu matsowa ba ".

Mamma ta ce “Ina Fa ,ko ido bai samu ya buɗe ba ".

“Kai amma Bobbo yana jin jiki " Arɗo ya faɗa .
“Bobbo da tun yana ƙarami ko ciwon kai yana jimawa be yi ba " Mamma ta faɗa .
“Wallahi kuwa " Arɗo ya faɗa.


Dai-dai lokacin Asama da ta tashi bayan shigowar Arɗo ta dawo ɗauke da ƙwarya ta miƙa mishi “Mai gida ga fura ka sha " .

Karɓa yayi yana faɗin “Yauwa Allah ya miki albarka Asama" .

“Ameen ya Allah " ta faɗa .


----------------

Zumbur Sarki Zawatunduma ya miƙe tsaye yana faɗin “Me ka ce ?"

Bafaden ya ce “Wai garin Bustumbul zasu kawo mana hari anjima da yamma "

Sarki Zawatunduma ya ce “Ka sanar da Sarkin garin Zawatu (Wato Sarki zimba mahaifin Naheel ) ya kamata a haɗu a je yaƙin Domin ɗaga tutar garin Zawatu .

“To Sarkin Teku mai mulkin duk wata halitta a teku an gama " Bafaden ya faɗa .

Sarki Zawatunduma ya ce “mulkin hallitu sai Allah ,bana son surutun banza ".

“Ayi min aikin gafara ,kuskure ne kuma bazan sake maimaita shi ba".

Hannu sarki Zawatunduma ya ɗaga mishi sannan ya juya ya ɓace ɓat da ganinshi .


----------------------

MASARAUTAR ZIMBA.........
Zaune yake ya ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya yana lilo da ita ,yayinda fadawa ke ta mishi fadanci suna kirari .

“Jinjina Sarki Jinnu . An buga an bar ka . Da wani ya taɓa ka gara ya jefa kanshi cikin wuta . Allah ya ja zamanin sarki Zimba shugaban shugabanni    , ......." basu ƙarasa ba Sallamar wani ta dakatar da su .


Amsawa suka yi yayinda sarki ya ɗaga hannu kawai .


“Me ke tafe da kai Alumu " wani Bafade ya faɗa .


Wanda suka kira da Alumu ya amsa musu da cewa “Saƙo ne daga MASARAUTAR BUSTUMBULA ,sarkin Bahulandu ya ce anjima da faɗuwar rana zasu kawo hari garin Zawatu " 

Da ƙarfin Sarki Zimba ya miƙe yana faɗin “Gafara dai raggwayen maza garin Zawatu gagara gasa ne gare ku  ,a haɗa mana dakarun yaƙi kafin rana ta faɗi zamu hallara filin daga " 

Yana faɗin haka ya cira sama cikin daƙiƙa biyu ya ɓace .


Alumu ya tashi ya fita dan ya sanar da Sarki Zawatunduma yadda suka yi da Sarki Zimba .


------------------------


Bayan Sarki Zawatunduma ya ɓace da ganin Alumu ɗakin gimbiya Naheela ya dira wanda ita ma dawowarta kenan daga gidan sihirinta.

“Masoyi wurinka na ɗaura niyyar zuwa ,aka yi sa'a ka zo " Naheela ta faɗa.

Sarki Zawatunduma ya ce “Ƴata ƴar lelena gani na zo"

Murmushi ta yi ta ce “kunnena ya kasa gazgata min abinda ya jiyo lokacin da ina gidan sihiri "(idan na Naheela na gidan sihiri takan ga abubuwa kuma ta ji su a cikin madubin sihirinta)

“Me kunnuwan ƴata suka jiyo mata da har ta gagara gasgatawa " ya faɗa .

“Labarin zuwan sarki Bahulandu " Ta faɗa .

Jinjina kai yayi sannan ya ce “Tabbas Madubinki bai miki ƙarya ba "



Nan take idonta ya canza kala zuwa Koren launi ,har wani juyawa suke yi “Garin Zawatu ba na yara ba ne Abbana ,ka sanar da shi kar yayi hasarar rayuwarshi da ta al'ummar Bustumbula ,   yau fa tunda na tashi nake son shan jini ".


Murmushi Sarki Zawatunduma yayi ya ce “Na ji a jikina gimbiyar sarkin teku na buƙatar jini shiyasa dana ji labarin zuwan shi na zo gare ki da sauri dan ki yi shirin shan jini iya yadda zaki iya ".

Idonta na walwalniya wani haske na fita ,ta ce “ai ba a gayyatar shege ranar shegantaka , Yau jinin Ƴan Bustumbula shi ne abincina kuma ruwan shana ,sai nayi hani'an ".

Wata Doguwar siririyar sandar ƙarfe ce ta fito daga idonta mai mugun tsinin gaske ,sai sheƙi take yi .

Tsayawa tayi cak ita ba sama ba ita ba ƙasa ba .

Naheela ta matso kusa da Sarki Zawatunduma ta ce “ Masoyi wannan sandar ita ce ƙwarin guiwata ,zan sakar mata duka ƙarfina idan har ta faɗi bazan sha jinin kowa ba ,domin kuwa na rasa ƙwarin guiwata" .

Murmushi yayi ya ce “ƴata baki san iya ƙarfin da kike da shi ba ,amma ki yi da iya ƙarfin da kika san kina da shi ".

Kallonshi tayi cike da tarin tambayoyi amma sanin bazai amsa mata ba yasa ta maida dubanta ga sandar tare da rufe ido ta miƙe Hannayenta guda biyu ya dai-daita su daidai da saitin Sandar ,tana juya hannun da ƙarfi .




To masu Karatu a nan zan tsaya .
Sai mun haɗu gobe .

Comments ɗinku nada mahimmanci matuƙa.






NASMERH LIMAN
09121873529
[7/17, 12:00 AM] QUEEN-NASMAH ❤️✍️: *NAWA ƁANGAREN*


HAƘƘIN MALLAKA : QUEEN-NASMAH 


*????MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION????*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.'''* 
بِسم الله الرحمن الرحيم

I’m much more me when I’m with you. HABEEB-ALBI

€pisode 14……………

Bayan ya gama shiri tsaf ya dawo ya zauna gefen gado tare da jawo wayarshi ya fara taɓawa ,kara wayar yayi alamar kira yake yi . Bugu biyu kawai tayi aka ɗaga . “your excellency yanzu nake shirin kiranka ” Hajiya Maryam ta faɗa .

His excellency ya ce “Lafiya dai ko ?”

Hajiya Maryam “Wallahi Jikin Nahad ne ba sauƙi”

His excellency Alhaji Sulaima ya ce “Amma ɗazu na kira Muhammad ya ce min yanzu zai kai ta asibiti nayi tunanin da sauƙi, shi ne dalilin kiran naki ma “.

Numfashi ta ja ta ce “eh shi da Babangida da Adam suka je , allurai aka mata abun kamar da sauƙi yanzu ta ƙara rifcewa ko ido bata iya Buɗewa “.

“Okay bari na zo ” ya faɗa yana sauke wayar daga kunnenshi .

Tashi yayi ya saka takalmi ya buɗe wata ƙofa ta bayan gida ya shiga ɗaya daga cikin ɓangaroran.

Hajiya Maryam na zaune kan kujera tana shafa kan Nahad da take kwance tana birgima .

Alhaji Sulaiman ya ƙaraso gabansu yana faɗin “Hajiya Maryama tashi bani wuri ” .

Tashi tayi tana komawa kan ɗayar kujerar .

Zama yayi kan kujerar da Nahad take tana birgima ya ce “Nahad !”da ɗan ƙarfi .

Idonta ta ware da suka fiffito waje ta kafe shi da ido .

“Me yake damunki ?” ya faɗa da ɗan ƙarfi .

Rufe ido ta sake yi tare da ƙara ƙamewa tana faɗin “Ban sani ba ,na faɗa muku ban sani ba ,wayyo Abba zuciyata zata fashe ,Abba zafi nake ji ,wayyo ni Yaya Muhammad , Yaya Ahmad kayi haƙuri bazan ƙara maka rashin kunya ba , Ummana bazan ƙara miki rashin kunya , wallahi nima bana sanin ina yi , Abbana kayi haƙuri bazan ƙara ba ” ta ci gaba da ihu .

Jawota yayi jikinshi ya rungume ta yana hura mata iska “Kiyi shiru Nahad “.

Cikin kuka da kuma rauni da ya bayyana ƙarara a muryata ta ce “To Abbana ,ka kira min yaya Ahmad “.

Hajiya Maryam ta ce “ya je siyo mata magani fa ,ki bari ya dawo mana “.

Nahad “Ummana ki ce ya dawo zan mutu ,wallahi zan mutu , wayyo zuciyata Abbana kira shi muyi bankwana “

“Assalamu alaikum ” Ahmad yayi sallama , Alhaji Sulaiman ya ce “Ga shi nan ya dawo kiyu shiru ki bar kuka “.

Hannu Nahad ta miƙa mishi tana faɗin “Yaya Ahmad ka dawo ” sai kuma ta fara yin ƙasa da hannunta da sauri ya taro hannun yana kallonta . “Haba Autar Abbanmu ki daina kuka zaki samu sauƙi ” .

Rufe ido tayi tana ji kamar barci zai ɗauke ta , “Abba ga su nan sun zo , Yaya Ahmad dan Allah kar ka bari su tafi ne , wayyo ni Allah ,Yaya Ahmad kayi haƙuri da abunda na maka wayyo ni , ga su nan , ga su nan dab dani ” ta runtse ido ta ƙarfi ,tana ci gaba da faɗin “Raina zai fita Ummana ,wayyo ni ku ji tausayi na “tun tana iya maganar ma ta kai ko bakin baya motsawa ,duk ta sandare tayi mugun haske duk da dama Nahad Fara ce tass .

Ahmad ya kalli Hajiya Maryam ya ce “Auntynmu wai yanzu ba yadda za a yi da Nahad ni wallahi abun nan yana ɗaure min kai ” .

Hajiya Maryam ta ce “ ƙaddara ce masu ciwon sickle cell haka suke fama , your excellency duk yadda baka so mu kwanta asibiti fa dole ne “

Alhaji Sulaiman ya ce “A’a ku bari ayi booking flight mu je America ina tunanin a nema mata lafiya zai fi “.

Ahmad ya ce “Ɗazu ma abunda Yaya Muhammad ya ce kenan wai gara a mata bone marrow transplant duk a huta , Ammy ma haka ta ce ” .

Alhaji Sulaiman ya ce “ Eh Haka Fulani ma ta ce min jiya “

Hajiya Maryam ta ce “To Allah yasa a dace ,Amma Nahad kam tana jin jiki “.

Da ameen Ahmad da Alhaji Sulaiman suka amsa

“Mamma Baffa ya ce ku gyara yanzu zai shigo da malami ” Arɗo ya faɗa .

Mamma na dakan fura wanda ya riga ya zame mata jiki ta ce “To ni gyaran Me zan yi , mayafi kawai zan lulluɓa miƙo min shi nan ” ta kai ƙarshen maganar tana nuna wa Arɗo mayafin da ke laƙe a ƙofar ɗakinta .

Jawo shi yayi ya miƙa mata ,sannan ya bi ta gefen Bobbo dake kwance saman tabarmar wundi ya raɓa shi ya fita . Bayan minti biyar sai ga su Baffa sun shigo da sallama ,Mamma ta amsa tana aje taɓaryar hannunta .

Baffa na gaba Shi da Malam Jafar , Arɗo na biye da su har suka iso inda aka shimfiɗe Bobbo , Mamma karkaɗe zanenta tayi ita ma ta zo ta zauna gefensu .

“Sannu da shigowa mai gida , malam ina wuni ” Mamma ta faɗa ,Baffa ya amsa da yauwa ,malam Jafar ya ce “Lafiya Lau “.

Baffa ya ce “Miƙo mishi ruwa Mamman Bobbo “

“To ” ta faɗa tare da miƙewa ta ɗauko moɗa ta buɗe randar ruwa ta ɗibi ruwa sannan ta kawo mishi .

Malam Jafar ya karɓi ruwan ya fara karanta ayatul kursiyyu ƙafa bakwai , suratul iklas ƙafa uku , suratul nas ƙafa uku , suratul falaƙ ma ƙafa uku , amanar-rasulu ƙafa ɗaya ya tofa a ruwan ,sannan ya shafa mishi a ƙafa , sannan ya shafa mishi a hannun , ya shafa mishi a fuska , wanda haka yasa Bobbo sauke wata wahalalliyar ajiyar Zuciya .

Mamma ta ce “Ya motsa ,laaaa Bobbo na motsi ” ta faɗa da farinciki ƙarara a fuskarta .

Malam Jafar ya jawo Jakar dake rataye a bayanshi ya ɗauko wani kasko ya aje , sannan ya kalli Baffa ya ce “A bani garwashi” .

Mamma ta kwalawa Asama dake suyar ƙosai kira , sai ga ta tazo.

Mamma ta ce “ ɗan zubo mana garwasu cikin wannan kaskon “.

“To Mamma” Asama ta faɗa tana ɗaukar kaskon .

Malam Jafar kuma ya fitar da ƙullukan magani ya aje da wasu robi da magani ciki ya aje .

Bata ɓata lokaci ba ta dawo ɗauke da kaskon da ta zuba ma garwashi ta aje , sannan ta juya ta wuce .

Wani garin magani ya buɗe ya zuba cikin kasko ,sannan yasa su Arɗo suka ɗaga mishi Bobbo zaune ,ya lulluɓe shi da wani zani ya tura kaskon ciki .

Nan take idon Bobbo suka fiffito waje yana faɗin “Kar ku rabani da Nawa ɓangaren Wallahil Azim ina son Ibrahim ,bazan iya rayuwa babu shi ba, idan kuka kashe ni bazai ƙara minti ɗaya a doron ƙasa ba “.

Mamaki ya cika su Baffa jin murya mace a jikin Bobbo , Mamma kuwa zare ido tayi , “na bani aljana jikin ɗana “.

Malam Jafar ya ce “Ke wace irin halitta ce me kike yi jikin wannan bawan Allah “.

“Malam ina maka magiya ne saboda soyayyar da nake ma Bobbo bazan so ya mutu ba ” aka sake yin magana ta jikin Bobbo .

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Leave a Reply

Back to top button