NAWA BANGAREN

NAWA BANGAREN COMPLETE

NAWA BANGAREN COMPLETE HAUSA NOVEL

Hajiya Maryam ta ce “Ashe abun har ya kai haka , to doctor ya maganar rashin lafiyarta “.

Likita ya ce “to his excellency ya ce min zaku je America , ni dai na shawarce shi da ya bari ayi bone marrow transplant ɗin a nan national hospital Abuja “.

Hajiya Maryam ta ce “to kai doctor kana ganin za a dace nan ɗin?”.

“Eh mana , ai koma ina ne addu’a ake so , asibitin America ba abunda zasu nuna ma national hospital Abuja “.

“To shi kenan likita Allah yasa a dace ” ta faɗa .

Da ameen ya amsa sannan ya fita ya bar nurse ta ma Nahad allura sannan ita ma ta fita .

Anan dasa aya .
Manage plss aiki ya man yawa .

MASOYAN LITTAFIN NASMAWALLATU GOBE ZAKU GA UPDATE INSHA ALLAH .

NAWA ƁANGAREN FANS MU HAƊE JIBI IN ALLAH YA YARDA .

LOVE U ALL .

NASMERH LIMAN
09121873529
[7/21, 9:23 PM] QUEEN-NASMAH ❤️✍️: NAWA ƁANGAREN

HAƘƘIN MALLAKA : QUEEN-NASMAH

????MOONLIGHT WRITER’S ASSOCIATION????
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

”’We are the moonlight writers we shine all over the world.”’
بِسم الله الرحمن الرحيم

????????       ????????        ????????
*Wohoho ! Garin daɗi na nesa ungulu ta leƙa masai . Wani Kaya Sai amale shin kun san k'ayatattun magungunan Mata  na maman Haidar ko kuwa an bar ku baya *
*To ƴar uwa Kayan maman Haidar basu da matsala domin traditional medicine ne Kuma Ana had'asu da ingantattun kuma nagartattun itatuwa masu aminci da karfi da Basu da wata illa  sai ma taimaka miki da zasu yi. Malam bahaushe dai ya ce In kana da kyau ka ƙara da kwalliya* ????????*Akwai wani ingantacce hadin. Manyan Mata  da mamàn  haidar takeyi  bakowa takewa wnnn hadinba sai me matsaloli. Allah ya yaye sabida karfinsa Wanda yasan yanada kudin yi saiyay magana*
*Sannan Akwai wasu mayatattun kayan haɗi masu Matuƙar ƙarin Ni'ima da mamàn  haidar take yi.

 *1 Gumbar kankana da aya* 
3 *Gumbar Madara da kwakwa*
4 *Kaza me ƙwai *
5 *Zabo me zuma*
6 *Kaza me allurai,  sahihiyar hanyar zaki mallake mijinki ƴar uwata ba boka ba malami*
7 *Kwallin idonka inadona*
8 *Tauwadar mata*
9 *ketar larabawa magani me kankarowa mace kima da daraja*
10 *Maganin sanyi me fatattakarsa duk kuwa nacinsa Koda bakya haihuwa indai matsalar sanyice  gwada wnnn*
11 *Maganin nono. Sahihi* 
12 *Maganin hips and bobbs* 
13 *hodar. Ni I'ma koramar mata*
14 *nakasan Mara babban sirri*
15 *kafi jijjibi*
16 *daga Sha Sai wanka kasaitacce magani*
17 *Dan kwankwalati namata da mazajensu Kevin Mata* 
18 *matsin kinfi budurwa dubu ko haihuwa nawa kikai  Babu magana*
19: akwai magani maza , da kuma maganin Feeling both gender Mata da maza .
*Maman haidar Bata tsaya anan ba*
*Tana Saida hijabai da yadikansu akan farashin sari yadika dila dila, hijaban Ƴan gayu sannan*
*ta kawo muku hadaddan sabulun  gyaran jiki da hadin dilka Me sa shek'i da laushin fata,  ga kuma mayukkan kitso Wanda laraba ke amfani dashi inkin gwada sai kin dawo  ku dai ku neme Maman Haidar a wannan number domin neman ƙarin bayani*????????   08146017245

----------------------
_My love for you has no depth, its boundaries are ever-expanding. My love and my life with you will be a never-ending story._ *HABEEB-ALBI*

€pisode 17.................

Garin Zawatu ya cika dam da mutane . Kowa ka gani yayi kyau sosai cikin adonshi . Ƙofar gidan sarki Zimba suka nufa . Kamar yadda sarki Zimba ya faɗa yau sati ɗaya cif da yin nasara akan a ƴan garin bustumbula saboda haka aka shirya gagarumin taron naɗin sarautar gimbiya Naheela .

     Sanye Naheela take cikin wata doguwar riga fara wadda ta sauka har ƙasa, wuyar rigar dogo ne har Saman maƙogwaronta. Da wani farin mayafi dogo sosai wanda ya lulluɓe mata duk ilahirin jikinta . Tafiya take yi mayafi yana tashi sama . Hannunta kawai zaka iya gani da fuskarta.


      Sarki Zawatunduma kuwa yana tsaye gefe yana kallon ƴarshi cike da farinciki da annashuwa . Daidai lokacin sarki Zimba ya fito tare da fadawanshi. Duka sauran aljanun dake tsaye suka durƙusar da kansu . Sannan suka ɗago. Har sau uku suna yin hakan . Sannan suka tsaya da ƙafafunsu.


   Hannu yayi ma Gimbiya Naheela alamar ta zo . Takowa tayi cikin isa da nuna izza ta tsaya gaban Sarki Zimba . Babban yatsanshi da manunin yatsanshi ya haɗa wuri ɗaya suka bada wata ƙara . Sai kuma ya rufe idonshi . Ya miƙa Hannayenshi biyu . Wata doguwa takobi mai Matuƙar sheƙi ta sauka kan hannu sarki Zimba . Buɗe idonshi yayi jin saukar wannan takobin a hannunshi .


Kallon al'ummar garin Zawatu yayi ya fara magana “Tabbas lokaci yayi da zan ba da sauratar garin nan , dan lokacina a duniyarku ya ƙare. Sanin Kanku shekara ta 2500 a kan mulkin nan . Kuma lokaci yayi da zata bar gidanmu ta koma wani gida. A kaf faɗin garin Zawatu babu wanda ya cancanci hawa mulkin nan kamar Naheela . Saboda haka ku shaida takobin sarauta ta bar hannuna ta dawo hannu gimbiya Naheela " ya kai ƙarshen maganar yana miƙa mata takobin .

Da hannu biyu ta karɓa tare ɗaga takobin sama , hawaye suka fara gangaro mata . Yayinda ta rufe Idonta kamar yadda yake a ƙa'idar garin duk wanda ya karɓi takobin saurata sai ya cika sharuɗa . Takobin dake hannunta ta riƙa girgiza amma Naheela ta riƙe ta gam . Nan take kayan jikin Naheela suka sauya zuwa ta jar riga wadda ta sha ado da zanen ɗawisu . Bayan rigar kuwa wasu manyan fika-fikai ne .

Kowa a garin yayi mamakin Yadda Naheela tayi saurin karɓar sarauta . Kowane sarki kafin ya hau mulki sai ya ci baƙar wuya sannan takobin ta ba shi kayan sarauta . Amma Naheela ko awa ɗaya bata yi ba har ta karɓi kayan sarauta . “Barka da karɓar sarauta sarauniya Naheela " duka aljanun suka faɗa a tare .

Idonta ta buɗe wanda wani haske mai mugun ƙarfi ya bayyana cikin idonta tare da wata Koriyar danja cikin ƙwayar idonta .

Sarki Zawatunduma ya tako gabanta ya miƙa mata hannu “Sabuwar sarauniyar garin Zawatu . Kuma sarauniyata ". Murmushi tayi ta ce “Masoyina tilo " . “Ina taya ki murnar zama sarauniyar garin Zawatu " ya faɗa . “Na gode Abbana " ta faɗa .


“Ina taya ki murna Naheela " Naheela ta jiyo muryar Naheel daga can nesa da ita . Murmushi tayi tare da girgiza kai . ta ce “ Na gode mijina " . Juyawa akalar dokinshi yayi daga inda yake ya wuce .

------------------------------

Tun daga ranar da malam Jafar ya bar gidan yau kimanin kwana bakwai kenan Bobbo bai sake jin wani abu da ya shafi Nahad ba . Amma dai raɗaɗin ƙunar bai wuce ba . Kamar yadda tabon ƙunar ya bayyana a jikinshi. 

Yana zaune tare da yaranshi da aka kwashe tun da Binto ta tafi aka maida su gidan Jauro abokinshi .  “Bobbonmu fuskarka ta ƙone ne ?" Maryama ta faɗa . Bobbo ya ce “Eh Maryama ruwan zafi na zuba ma jikina " , “to amma ......" bata samu damar ƙarasa maganar ba Mamma ta fito daga ɗaki da ƙwarya a hannunta ta ce “Ke kin cika surutu , zo ki ɗauki wannan ƙwayar ki ja yaran can ku je ɗakin wurin ɗakin Asama ku zauna ku sha . Kar ku dame Bobbonku ". “To Mamma" Maryam ta faɗa . Miƙewa tayi ta ɗauki Ƙwaryar ta aje kan tabarmar kabar dake wurin ɗakin Asama . Sannan ta juyo ta kalli ƙannenta ta ce “ku zo ga fura " ,duk suka taso kamar ƙwari suka nufi Maryama.


------------------------

Kamar yadda His excellency ya ce yau aka yi ma Nahad bone marrow Transplant (dashen ɓargo). Alhamdulillahi an yi sa'a . Ahmad ne ya bata ɓargonshi aka yi mata dashi.

Likitoci ne suka fito da ita daga ɗakin theater zuwa ɗakin jinya . Ɗakinta na kusa da na Ahmad .

Hajiya Fulani  (wato mommynsu Babangida ) da kuma Hajiya Mabaruka (wato Ammynsu Ahmad )  suka shigo asibitin ,ɗakin da Ahmad yake suka nufa kai tsaye . Hajiya Fulani ta mishi ya jiki sannan ta nufi ɗakin da aka kwantar da Nahad .


Anan zan dakata . 

Kuyi haƙuri da wannan page ɗin abubuwa sun mini yawa .am so sorry my dearies

LOVE U ALL .


NASMERH LIMAN
09121873529
[7/24, 1:27 PM] QUEEN-NASMAH ❤️✍️: *NAWA ƁANGAREN*

HAƘƘIN MALLAKA : QUEEN-NASMAH 


*????MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION????*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.'''* 
بِسم الله الرحمن الرحيم

???????? ???????? ????????
*Wohoho ! Garin daɗi na nesa ungulu ta leƙa masai . Wani Kaya Sai amale shin kun san k’ayatattun magungunan Mata na maman Haidar ko kuwa an bar ku baya *
To ƴar uwa Kayan maman Haidar basu da matsala domin traditional medicine ne Kuma Ana had’asu da ingantattun kuma nagartattun itatuwa masu aminci da karfi da Basu da wata illa sai ma taimaka miki da zasu yi. Malam bahaushe dai ya ce In kana da kyau ka ƙara da kwalliya ????????Akwai wani ingantacce hadin. Manyan Mata da mamàn haidar takeyi bakowa takewa wnnn hadinba sai me matsaloli. Allah ya yaye sabida karfinsa Wanda yasan yanada kudin yi saiyay magana
*Sannan Akwai wasu mayatattun kayan haɗi masu Matuƙar ƙarin Ni’ima da mamàn haidar take yi.

1 Gumbar kankana da aya
3 Gumbar Madara da kwakwa
4 *Kaza me ƙwai *
5 Zabo me zuma
6 Kaza me allurai, sahihiyar hanyar zaki mallake mijinki ƴar uwata ba boka ba malami
7 Kwallin idonka inadona
8 Tauwadar mata
9 ketar larabawa magani me kankarowa mace kima da daraja
10 Maganin sanyi me fatattakarsa duk kuwa nacinsa Koda bakya haihuwa indai matsalar sanyice gwada wnnn
11 Maganin nono. Sahihi
12 Maganin hips and bobbs
13 hodar. Ni I’ma koramar mata
14 nakasan Mara babban sirri
15 kafi jijjibi
16 daga Sha Sai wanka kasaitacce magani
17 Dan kwankwalati namata da mazajensu Kevin Mata
18 matsin kinfi budurwa dubu ko haihuwa nawa kikai Babu magana
19: akwai magani maza , da kuma maganin Feeling both gender Mata da maza .
Maman haidar Bata tsaya anan ba
Tana Saida hijabai da yadikansu akan farashin sari yadika dila dila, hijaban Ƴan gayu sannan
ta kawo muku hadaddan sabulun gyaran jiki da hadin dilka Me sa shek’i da laushin fata, ga kuma mayukkan kitso Wanda laraba ke amfani dashi inkin gwada sai kin dawo ku dai ku neme Maman Haidar a wannan number domin neman ƙarin bayani???????? 08146017245


I never thought love could be so magnificent until I saw the sincere look in your eyes, telling me that this time¦ I would never shed another tear.. HABEEB-ALBI

€pisode 18……………..
Bayan wata ɗaya .

Tun daga Ranar da Naheela ta karɓi mulkin Garin Zawatu wani a garin bai ƙara yin wani yunƙuri ba , haka ma daga sauran garuruwa ma sun shaida da sarautar gimbiya Naheela , dan sosai aka kawo sauyi garin . Sarki Zimba ya kwashe komai nashi shi da matarshi sun koma Nahiyar macizai dan lokaci yayi da zai koma maciji , a al’adar garin Zawatu idan har kayi shekara dubu ɗari a duniyar Aljanu to dole ne ka koma Nahiyar macizai ka ci gaba da bauta ma Allah a matsayin maciji daga lokacin baka da wani ƙarfi har da zaka cutar da wani .

Yau sarki Zawatunduma zai yi sallama da Naheela . Dan haka a babbar fadar da takobin sarauta ta gina mata ya sauka . Masarautar tafi duk wata masarauta ta sauran sarakunan kyau . “Allah ya ja da zamaninki Masoyiyar ƴata ” ya faɗa tare da ɓacewa sai cikin fadar , ta bayar da baya tana kallon madubi ta ce “Na ji a jikina masoyina zai zo nan , Abba sannu ta zuwa ” , sarkin Teku ya ce “Jikinki madubi ne gare ki baya haska abunda ba gaskiya tabbas ni ne ƴata ” , juyowa tayi ta ce “Tabbas haka ne , amma ban san me yasa nake a jikina bankwana ka zo muyi ba “.

Numfashi sarki Zawatunduma ya sauke tare da kama hannun Naheela ya ce “Lokaci tafiya ta yayi , ya kamata na wuce tun shekarun baya , amma bazan iya barinki kina ƙanƙanuwa ba , haka ne ya sanya na je Nahiyar macizai nayi Aron shekera 27 har ki mallaki hankalinki , Yanzu da kika mallaki hankalinki ni zan juya na tafi ” , Naheela ta ce “Tabbas Haka ne Abbana , na gode da kulawa da kayi dani , ka zame min uwa da uba ” sai kuma hawaye suka fara bin kuncinta .

Rungume ta sarki yayi sannan ya ce “Ina alfahari da ke ƴarta , yanzu zan miki kyautar cikar farincikinki ” , ido ta ƙura mishi tana son jin me zai faɗa .

“Naheel ne kaɗai mai farar zuciyar da zai zauna dake ya kula da ke kamar ni , amma kuma kin gagara gano mafitar . Haka Naheel yake , ma’ana tun da ya zo duniya ko Mahaifiyarshi baya son ta matso shi haka yasa ya katange kanshi daga gare ta da duk wata mace ” sarki Zawatunduma ya faɗa .

Naheela ta ce “Amma akwai irin su a duniya ” ,Sarki Zawatunduma ya ce “a nan nahiyar da muke akwai su birjik Naheela ,kuma dukansu zasu iya dawowa dai-dai “, Naheela ta ce “Ta yaya “.

Sarki Zawatunduma ya ce “Idan har zasu iya yin awa 72 tare da ke dukansu wannan ciwon ya zama tarihi ” . Naheela ta ce “awanni 72 ? kwana uku kenan , Abba kana ganin Naheel zai iya jure ƙonewa ta kwana uku? “.

Sarki Zawatunduma ya ce “Ko kaɗan irinsu ba za su iya jure komai ba “.

“To kenan Abbana ba za su taɓa dawowa dai-dai ba ” ta tambaya . “Zasu dawo idan har kin yi niya ƴar ta , da farko ki rage musu jin zafin , sannan ki ƙwace ƙarfin ikon yin tsafi daga gare su sannan sai ki kasance tare da su na tsawon awanni saba’in da biyu”.

Wata nannauyar ajiyar zuciya tayi ta ce “to shi kenan zan yi hakan Abbana “. Murmushi yayi ya ce “idan awannin da na faɗa miki sun cika ki haɗa bakinki da nashi na tsawon awa ɗaya , sannan ki ɗora zamzila a wuyanshi sannan ki cire bakinki daga nashi komai na tsanar ƴa mace ga Naheel ya zama tarihi ” , Naheela ta ce “to sauran mutanen fa ” , “ko wannensu mai sonshi zata sumbace shi na awa ɗaya sai ki ɗora zamzila a wuyanshi , sai budurwar ta cire bakinta “, Naheela ta gaɗa kai alamar ta gane , sannan ta ce “Kenan dole sai Zamzila zai yi aikin “, “Zamzila ne MATAKIN ƘARSHE a wannan aikin ” ya faɗa .

Naheela ta ce “Tabbas ka cika min farincikina” , sarki Zawatunduma ya ce “Sai ɗayan !” , Naheela ta ɗago ta kalle shi da mamaki , “kina da wani buri da na hana ki furtawa tun kina jinjira Naheela , na ga hakan a ƙwayar idonki Naheela , wasu lokuta har hotunan abunda kike son tambaya ke bayyana a ƙwayar idonki , hakan kuwa ha ƙaramin ɗaga min hankali yake yi ba , dalili kuwa ban san da wani ido zan kalle ki ba , bazan iya miki ƙarya ba kuma na san ko nayi zaki gano ƙarya nayi , girmana na mahaifi a gare ki zai zube , wannan dalilin yasa nayi amfani da ƙarfin iko kanki na mantar da ke su ” ,numfashi ya ja tare da fitar da shi ya kalli Naheela da ta bayar da natsuwarta gaba ɗaya gare shi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Leave a Reply

Back to top button