Tsayuwarshi ya gyara ya ci gaba da magana “nayi haka ne saboda girman soyayyar da nake miki , idan har kika tambaye ni gaskiyar zan faɗa miki kuma zaki so barin ɓangarena dan a zuciyarki na ga tarin soyayyarsu a tare da ke wanda ya lunka nawa , a NAWA ƁANGAREN kuma bana son wata ko wani ko buƙatar wani a Rayuwata bayan ke , wannan dalilin ya san ya ni yin haka ” .
Sai yanzu Naheela ta tattara kalamai a bakinta ta ce “Su waye Abbana yake tunanin zan bar shi a kansu ?” , Sarki Zawatunduma ya ce “Mahaifiyarki Naheela “
Naheela ta ce “Ummana tabbas ina nemanta Abbana , na rufe duk wata hanya da zaka gane haka saboda na fahimci tashin hankalinka akan haka , na rufe maka ido daga ganin ina ganinsu neman su , Amma Wallahi babu wannan asubar da bana yawace duniyar Aljanu amma ban ga ko da sawunta ba , ina ji a jikina ina buƙatarta , amma Abba bana tunanin zan bar ka shiyasa ban tilasta ma kaina son ganinta ba ” .
Murmushi yayi wanda ya zo tare da hawaye ya ce “ da ace ban yi ƙoƙarin danne soyayyar da kike mata ba , da wallahi babu wanda ya isa hana ki tunkararta “.
“To Abbana yanzu ka sakar min marata in yi fitsari , ka bani dama in haɗu da cikon Rayuwata ?” ta faɗa .
Sarki Zawatunduma ya ce “Naheela bazai yuyu in baki dama ba dan aiki ne nayi na har abada , dole sai na koma nahiyar macizai sannan aikin zai karye , ki jira nan da ƴan awanni “.
“Abba amma ina Ummana take ?” Naheela ta faɗa .
“Naheela Ummanki tana inda kika fi…………………”
Anan zan dakata
Sai gobe in Allah yasa muna cikin masu kaiwa .
Shin a ina mahaifiyar Naheela take? Ku ci gaba da bin labarin nan komai zai warware ..
LOVE U ALL .
NASMERH LIMAN
09121873529
[7/28, 2:34 PM] QUEEN-NASMAH ❤️✍️: NAWA ƁANGAREN
HAƘƘIN MALLAKA : QUEEN-NASMAH
????MOONLIGHT WRITER’S ASSOCIATION????
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/
”’We are the moonlight writers we shine all over the world.”’
بِسم الله الرحمن الرحيم
???????? ???????? ????????
*Wohoho ! Garin daɗi na nesa ungulu ta leƙa masai . Wani Kaya Sai amale shin kun san k'ayatattun magungunan Mata na maman Haidar ko kuwa an bar ku baya *
*To ƴar uwa Kayan maman Haidar basu da matsala domin traditional medicine ne Kuma Ana had'asu da ingantattun kuma nagartattun itatuwa masu aminci da karfi da Basu da wata illa sai ma taimaka miki da zasu yi. Malam bahaushe dai ya ce In kana da kyau ka ƙara da kwalliya* ????????*Akwai wani ingantacce hadin. Manyan Mata da mamàn haidar takeyi bakowa takewa wnnn hadinba sai me matsaloli. Allah ya yaye sabida karfinsa Wanda yasan yanada kudin yi saiyay magana*
*Sannan Akwai wasu mayatattun kayan haɗi masu Matuƙar ƙarin Ni'ima da mamàn haidar take yi.
*1 Gumbar kankana da aya*
3 *Gumbar Madara da kwakwa*
4 *Kaza me ƙwai *
5 *Zabo me zuma*
6 *Kaza me allurai, sahihiyar hanyar zaki mallake mijinki ƴar uwata ba boka ba malami*
7 *Kwallin idonka inadona*
8 *Tauwadar mata*
9 *ketar larabawa magani me kankarowa mace kima da daraja*
10 *Maganin sanyi me fatattakarsa duk kuwa nacinsa Koda bakya haihuwa indai matsalar sanyice gwada wnnn*
11 *Maganin nono. Sahihi*
12 *Maganin hips and bobbs*
13 *hodar. Ni I'ma koramar mata*
14 *nakasan Mara babban sirri*
15 *kafi jijjibi*
16 *daga Sha Sai wanka kasaitacce magani*
17 *Dan kwankwalati namata da mazajensu Kevin Mata*
18 *matsin kinfi budurwa dubu ko haihuwa nawa kikai Babu magana*
19: akwai magani maza , da kuma maganin Feeling both gender Mata da maza .
*Maman haidar Bata tsaya anan ba*
*Tana Saida hijabai da yadikansu akan farashin sari yadika dila dila, hijaban Ƴan gayu sannan*
*ta kawo muku hadaddan sabulun gyaran jiki da hadin dilka Me sa shek'i da laushin fata, ga kuma mayukkan kitso Wanda laraba ke amfani dashi inkin gwada sai kin dawo ku dai ku neme Maman Haidar a wannan number domin neman ƙarin bayani*???????? 08146017245
----------------------
_It doesn't matter where you are, and I can always hear your heartbeat when I lay down and see your face when I close my eyes._ *HABEEB-ALBI*
€pisode 19.................
“Naheela Ummanki tana inda kika fi tsana " Sarki Zawatunduma ya faɗa , numfashi Naheela ta saukar tare da faɗin “Amma Taya zan tunkari wurin " , Hannunta Sarki Zawatunduma ya jawo ya riƙe , sannan ya ce “Da kanki zaki tunkari wurin cike da soyayya , kuma zaki gane Mahaifiyarki da zuwanki wurin , idan zaki je ki bi ta cikin dutsin Kimbaya , ni zan wuce lokaci na tafiya ta yayi ", Naheela ta ce “Abbana aron shekaru da kayi ya zaka fanshe su?", murmushi yayi hawaye suka fara gangorowa yana gogewa , “Zan bayar da fansar numfashina ", nan take Naheela ta ƙara matsowa kusa da shi a kiɗime ta ce “Ban fahimci me kake faɗi ba ?".
Hannunta ya saki ya dafa kafaɗunta yana faɗin “na fanshi shekarun kasancewa tare dake ta hanyar sadaukar da jinina ga Gongumba (shugaban macizai )", Hawaye suka fara bin kuncin Naheela cike da jin zafin maganar Abbanta ta ce “Kana nufin bazan sake ganinka ba ?" , “Naheela lokacina yayi na tafiya , ki kula da kanki da kuma sabon ahalin da zaki gina ". Ɓat ya ɓace daga ganin Naheela.
_______________________
Nahad ce zaune kan Kujera tana danna waya lokacin da Umma ta shigo , amma bata ɗago ta kalle ta ba, Hajiya Maryam ta ce “Ke Nahad baki iya gaisuwa ba ", idonta ta ɗago tana kallon Hajiya Maryam sannan ta saukar da su , Hajiya Maryam ta ce “La'ilaha illal lahu Muhammadur rasulillahi ( saw ) , Nahad kin fara halin naki ko ?" , ƙara ɗagowa tayi da kanta yanzu kam idonta sun fito waje sosai jijiyoyin idonta sun yi ja , Hajiya Maryam tayi saurin Ja baya tana jin wani zafi duk ilahirin jikinta .
Zaunawa tayi gefen Nahad ta ce “Nahad wai waya taɓa ki ?" .
“Abbana !" Nahad ta faɗa.
“Abbanki da baya nan ,Nahad ki ji tsoron Allah ,ina ce wata ɗaya da suka wuce kina nan kamar zaki mutu ?".
“Kina ganin zan iya mutuwa ne ?" Nahad ta tambaya .
“Eh mana ai kowa sai ya mutu " Hajiya Maryam ta faɗa . Nahad ta ce “To ni shekerun da zan yi duniya sai kin yi mamaki" , cikin kawar da zance Hajiya maryam ta ce “Faɗa min me Abban naki yayi miki ?", “ an sha jininshi ne " ta faɗa , Hajiya Maryam ta ce “ke kika sha jininko ja'irar yarinya ", “Umma ki Kira Abba ki ji in yana lafiya " ta faɗa .
“Ni bazan iya da shiriritarki ba ta shi ki je ɓangaren Fulani ki ce ta baki saƙona " , tashi Nahad tayi , amma Hajiya Maryam bata ƙara ganin ko walƙiyarta ba . Jinjina kai Hajiya Maryam tayi a hankali ta ce “Allah ka mini maganin abunda bazan iya yima kaina ba ", tashi tayi ta shige ɗaki.
Hajiya Fulani na kitchen sai ji tayi an taɓa ta , a razane ta juyo , sai kuma ta sauke numfashi ganin Nahad “Nahad ba za ki daina firgita mutane ba ko ?" , idonta da suke tsara-tsaye ta ware ta ce “Ko kaɗan ba da niya nake firgita ki ba Maman Muhammad " . Numfashi ta sauke ta ce “Ta ina kika shigo bayan na rufe ko ina " , Nahad ta ce “to ni dai gani na taho , Umma ce ta ce ki bata saƙonta , Fulani ta ce “To bari na ɗauko miki " .
Ɗaki ta wuce tana jinjina al'amarin Nahad “Wani lokaci sai ka ga kamar yarinyar can ba mutum ba ce "Fulani ta faɗa, Nahad dake nesa da ita ta ce “Amma kuma mutum ce ni ba " ,Hajiya Fulani ta sha jinin jikinta dan ta san duk inda tayi magana Nahad sai ta ji , saboda haka ta shige ɗaki a tsorace ta ɗauko wata leda babba ta fito da ita.
Nahad na tsaye tana kallon yadda take yin ƙasa kamar zata nutse cikin ƙasa , ta ji fitowar Hajiya Fulani , mayar da idonta tayi ga Hajiya Fulani , tare da tsayawa cak kamar ba ita ba ce ke shirin nutsewa cikin ƙasa .
Ledar Hajiya Fulani ta miƙa mata tare da faɗin “ki ce mata lace ɗin kawai aka samu . Gyalen kuma sai gobe zai iso ", karɓa Nahad tayi tana faɗin “to shi kenan" juyawa tayi ta wuce .Hajiya Fulani kuma ta shige kitchen .
___________________
Mamma ce ta fito daga ɗakinta riƙe da matakaɗin fura wanda kowa ya riga ya san dakan fura ya auri Mamma , dan kullum sai ta daka fura ta dama . Kallon Bobbo tayi da yake zaune Ƙofar ɗakinta ta girgiza kai , sannan nufi turmin dakan fura ta aje matakaɗin , tare da jawo kujerar katako ta zauna , “Wai kai Sadauki wane irin mutum ne , a ce mutum ya riƙa zama shi kaɗai , ko dai zuwa za a yi dawo maka da yaranka ?" , girgiza kai Bobbo yayi ya ce “Mamma kowane yaro mahaifoyarshi ita ce garkuwarshi , ni kaina ban gama kula da kaina ballantana Yarana , ina ganin Zaman kowannensu wurin Mahaifiyarshi ya fi " , Mamma ta ce “Amma wannan zaman kaɗaicin bai yi ba " . Numfashi Bobbo ya sauke ya ce “Haka Allah ya ƙaddara , ban isa in yi jayayya da abunda Allah ya ƙaddara min ba ". Mamma zata yi magana kenan Mairo ta shigo “Salamu alaikum " , “wa'alaikumus salam " Bobbo ya amsa . “Ina wuninku " ta faɗa , Mamma da Bobbo suka amsa mata .
“Na same ku lafiya " Mairo ta faɗa , Mamma ta ce "lafiya ƙalau" , Bobbo ya kalli Mairo ya ce “Ina Sadaukina ?" , Mairo ta ce “Yana wurin Inna na baro ", Bobbo ya ce “to ki shafa min kanshi ",“in sha Allah " ta faɗa , numfashi Bobbo ya sauke sannan ya ce “Na ji saƙon da kika bar min na gode sosai , kuma ko kaɗan ban ga laifinki , ina so ki sani har abada bazan daina girmama ɗaya daga cikin matan da na aura ba , na aure ku ne dan so ba dan muzgunawa ba , dan haka kina da damar nema ma kanki farinciki " , tun da Bobbo ya fara magana Jikin Mairo yayi sanyi kamar ta ce kar yayi . Amma ta san ba za ta iya zama da shi ba .
“Kafin mu je ko ina Mairo ina roƙonki da ki yafe min duk abunda na miki ina sane da kuma wanda ban sani ba , ko kaɗan ban yi haka dan in muzguna miki ba, kuma ban taɓa ji a raina ina son cutar da ke ba , ni kaina ban san me yake damuna ba , dan Allah ki yafe min a matsayin mahaifin ɗanki ", Mairo da hawaye suka cika ma ido cikin rawar murya ta ce “Na yafe maka duniya da lahira ".
“Na gode da yafiyar da kika min , Allah ya saka miki da mafificin alkhairi " ya faɗa , Mairo ta ce “Ameen , nima ka yafe min duk abun da na maka " , “Ko akwai abun da kika min na yafe miki , ballanta baki yi hakan ba "ya faɗa ,Mamma dai har yanzu bata ce komai ba illa ma hankalinta da ta mayar wurin dakan fura . Bobbo ya ja numfashi mai nauyi ya sauki , sannan ya ɗago ya kalli Mairo ya ce “Allah shaida ne ina jin nauyin furta Kalmar saki amma kuma dole ne gare ni , Allah ka min afuwa " ya faɗa yana runtse ido , Mairo ta ce “Bobbo ka...... " ,katse ta yayi cikin Dakiya ya ce “Mairo na sake ki saki ɗaya ,idan kin gama idda miji ya zo ki yi aurenki , ina miki fatan miji na gari wanda zai riƙe ki amana " yana faɗin haka Mairo ta fashe da wani irin kuka mai ratsa zuciya tana faɗin “,Wayyo ni Allah wai ni kaina , na shiga uku , yau ƙaddara ta raba ni da mai sona da gaskiya " Bobbo tashi yayi ya shige ɗaki .
Mamma ta tsagaita dakan ta kalli Mairo ta ce “Abun rabo ya ƙare miƙa hannu na mine ne, ki tashi ki tafi gida kar ki cika mu da kuka " . Tashi Mairo tayi tana share ƙwalla ta wuce . Mamma ta bita da kallo har ta fita , sannan ta ce “Yau ni na ga abunda ya ture ma buzu naɗi , matar nan da kanta ta ce a sake ta wai kuma ta zo tana kuka , to Allah ya kyauta " tayi maganar tana riƙe haɓa , sannan ta ci gaba da dakan da take yi .
Nan zan dakata sai kuma Asabar in Allah yasa muna da rai .
LOVE U ALL .
NASMERH LIMAN
09121873529
[7/31, 8:42 AM] QUEEN-NASMAH ❤️✍️: *NAWA ƁANGAREN*
HAƘƘIN MALLAKA : QUEEN-NASMAH
*????MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION????*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/
*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.'''*
بِسم الله الرحمن الرحيم
???????? ???????? ????????
*Wohoho ! Garin daɗi na nesa ungulu ta leƙa masai . Wani Kaya Sai amale shin kun san k’ayatattun magungunan Mata na maman Haidar ko kuwa an bar ku baya *
To ƴar uwa Kayan maman Haidar basu da matsala domin traditional medicine ne Kuma Ana had’asu da ingantattun kuma nagartattun itatuwa masu aminci da karfi da Basu da wata illa sai ma taimaka miki da zasu yi. Malam bahaushe dai ya ce In kana da kyau ka ƙara da kwalliya ????????Akwai wani ingantacce hadin. Manyan Mata da mamàn haidar takeyi bakowa takewa wnnn hadinba sai me matsaloli. Allah ya yaye sabida karfinsa Wanda yasan yanada kudin yi saiyay magana
*Sannan Akwai wasu mayatattun kayan haɗi masu Matuƙar ƙarin Ni’ima da mamàn haidar take yi.
1 Gumbar kankana da aya
3 Gumbar Madara da kwakwa
4 *Kaza me ƙwai *
5 Zabo me zuma
6 Kaza me allurai, sahihiyar hanyar zaki mallake mijinki ƴar uwata ba boka ba malami
7 Kwallin idonka inadona
8 Tauwadar mata
9 ketar larabawa magani me kankarowa mace kima da daraja
10 Maganin sanyi me fatattakarsa duk kuwa nacinsa Koda bakya haihuwa indai matsalar sanyice gwada wnnn
11 Maganin nono. Sahihi
12 Maganin hips and bobbs
13 hodar. Ni I’ma koramar mata
14 nakasan Mara babban sirri
15 kafi jijjibi
16 daga Sha Sai wanka kasaitacce magani
17 Dan kwankwalati namata da mazajensu Kevin Mata
18 matsin kinfi budurwa dubu ko haihuwa nawa kikai Babu magana
19: akwai magani maza , da kuma maganin Feeling both gender Mata da maza .
Maman haidar Bata tsaya anan ba
Tana Saida hijabai da yadikansu akan farashin sari yadika dila dila, hijaban Ƴan gayu sannan
ta kawo muku hadaddan sabulun gyaran jiki da hadin dilka Me sa shek’i da laushin fata, ga kuma mayukkan kitso Wanda laraba ke amfani dashi inkin gwada sai kin dawo ku dai ku neme Maman Haidar a wannan number domin neman ƙarin bayani???????? 08146017245
Your warmth fulfils my heart. Nothing in this world could ever satisfy me the way you do. Thank you for being exceptional someone. HABEEB-ALBI
€pisode 20……………..
Yau bobbo ya tashi da matsanancin zazzaɓi sabon mafarkin Nahad da yayi , Mamma dake gefenshi zaune ta ce “Kai kam Bobbo wannan abu da ya same ka Allah ya maka maganinshi ” , daga ɗayan gefen Asama ta amsa da Ameen .
Baffa ne ya shigo cikin gidan ,tun safe da ya fita . “Assalamu Alaikum ” ya faɗa yayin shigowa , “wa’alaikumus salam ” suka amsa tare ban da bobbo da yake jin kamar ranshi zai fita .
“Har yanzu jikin ne ?”Baffa ya tambaya , Tashi Asama tayi daga inda take ta ba Bobbo wuri . Mamma ta ce “ijaba ce ta riga ta sauka , sai ranar da Allah ya iyakance “, Baffa ya ce “To Allah ya iyakance ” . A tare su Mamma suka ce Ameen .
“Yau Malam Rabi’u zai dawo , an ce gobe mu kai Bobbo wurinshi ” Mamma ta faɗa , Baffa ya ce “Eh mun yi magana da Arɗo ” , Mamma ta ce “Duk tare zamu babu wanda za a bari cikinmu ” , Asama ta ce “Ba matsala Mamma ni zan tsaya gida “, Baffa ya ce “A’a ba damuwa zamu je tare “, “Allah ya kai mu ” Asama ta faɗa tare da tashi ta shige cikin ɗaki . Mamma kuma ta tashi ta ɗauko ma Baffa tuwon da ta ɗumama mishi . Karɓa yayi ya ce “Allah ya miki albarka ” , “Ameen ya rabbi ” ta faɗa tare da gyara ma Bobbo pillownshi da ta ga ya koma gefe ɗaya .
“Nahad tashi daga wurin nan ” Ahmad ya faɗa ganin Nahad bakin Swimming pool , Wanda Kowa a gidan ya riga ya san ɗabi’ar ta ce zama cikin kuwa , dan idan har ka nemi Nahad baka ganta ba tabbas ka neme ta a banɗaki koma cikin swimming pool , tana ji yana mata magana Amma yarinyar nan tayi kunnen uwar Shegu da Ahmad .
“Nahad baki ji ina miki magana ” ya sake yin magana yana ɗaga murya , ido ta ƙura mishi na ƴan daƙiƙu sannan ta miƙe cikin tafiyar da kai ba za ka gane ko tafiya ba ce ko a’a ta tunkaro shi “Yaya Ahmad mine ne kake damuna “, Ahmad ya ce “ba na hana ki zama nan ba “, Nahad ta ce “Nan fa gidana ne ” , Ahmad ya ce “gidanki kamar yaya ?” , juyawa tayi ta koma cikin ruwan tsundum , daga ƙirjinta zuwa fuskarta ne kawai bai shiga ruwa ba , kallon Ahmad tayi ta ce “Bari ni ɗin nan na nuna maka wani abu da nake jin daɗi idan na shiga ruwa bayan minti biyar ” , Ahmad ya ce “mine ne wannan “, “Yaya Ahmad na fahimci ruwa su ne cikar Rayuwata , idan nayi nesa da ruwa ji nake mutuwa tana tunkara ta , yanzu da na fara rayuwa cikin ruwa bana jin ko Abba da kanshi zai iya hana ni , abu ɗaya yake bani tsoro kuma yanzu na saba da ganin hakan ” , Ahmad ya ce cikin rashin fahimta dan shi duk ya daburce “mine ne wannan abun ?”, “Shi nake shirin nuna maka “. Bayan minti biyar jikin Nahad ya koma sak irin na kifi amma daga ƙirjinta zuwa fuskarta halittar mutum ce . Ido Ahmad ya zaro kamar zasu faɗo ya ce “Nahad !” sai kuma ya faɗi ƙasa sumamme , da sauri Nahad ta saki wata wuta daga cikin idonta nan take ta dawo yadda take , fitowa tayi ta ɗaga Ahmad sai parlorn su . Hajiya Maryam na zaune Nahad ta shigo tare da Ahmad a hannunta . Tashi Hajiya Maryam tayi cikin tashin hankali ta ce “Nahad ba na ce ki riƙa ɓoye ƙarfinki ba ,so kike ki tona min asiri ko , to kin ɗauko shi kin ji daɗi , kuma abu ne da ke da kanki kin san a asalin ƙarfi na ɗan adam ba za ki iya ɗaukar Ahmad ba ” ,Nahad ta ce “to yanzu ba gashi nayi ba “, hannu Hajiya Maryam ta ɗaga zata daki Nahad , Nahad ta kalle ta ai ko nan take hannun ya ƙame wuri ɗaya yana mata zugi. Nahad kuma wucewa tayi cikin ɗaki .