KWARATA 74

???? —— 72
Bazan fito ba na bashi amsa , dariya ya sakeyi kaɗan cewa he ƙarya ne fa gani nan zuwa , kasan gidan ne ? Ko na sani ko ban sani ba damuwa na ne ina zuwa kuma ki faɗawa Mama ina gaisheta kice mata nine zanzo dan na kirata waya bata
ɗauka ba , da sauri na miƙe ina tunanin yadda zan shirya kafin yazo naji yana cewa bafa sai inyi wanka ba ina zuwa nan da mintuna biyar yana faɗin haka ya tsinke wayarshi.
2gnovel
4medicals
Smidris
Ɗakin da Inna ta shiga na nufa ina taɓa ƙofar najita a rufe , zan juya naji tace Sultana miye ? Inna Dikko ne yace zaizo , wane Dikkon ? Wanda kika sani , tou yanzu ya akayi ne ? Shigowa zanyi inyi wanka , duk kin san zaizo sai yanzu zakiyi wanka ? Nifa bansan zaizo ba Inna yanzu ya faɗamin yana zuwa , tou ki tafi ɗakinki mana , nidai Inna buɗemin don Allah , tsoki tayi tare da tasowa tazo ta buɗe ɗakin ta koma saman gado ta kwanta , bayanta nabi na shiga ciki har yanzu bata daina kuka ba !
Ban mata magana ba na cire kayana na shiga wanka , kafin in fito har Dikko ya iso sai kiran wayata yakeyi , Inna sai faɗa takeyi banda wawanci sai mutum yace zaizo na sirki wanka , ki fito ko baki gama ba , shiru nayi naci gaba da huɗɗar data shafeni , ita kuma Innar fita tayi taima mai gadi magana wai akwai baƙo a waje ya buɗe mishi ya shigo.
Da mai gadi yayi ma Dikko magana cewa yayi ai nan ma yayi suna da yawa ne basai sun shigo ba , mai gadi ya koma ya faɗawa Inna bataji daɗin haka ba , shi kuma Dikko abinda ya hanashi shigowa kar Inna ta sake feƙa mishi rashin mutunci kuma An mata tana fitowa ɗaukar ta zaiyi su tafi idan sun gama ya dawo da ita kar Inna ta fito ta tona mishi asiri cikin bainan nasi…..
Ina fitowa wanka na ɗauki kayana dana cire Inna tace ki ajiyesu dan ubanki ko su zaki maida ne ? Haba nifa ba su zan maida ba , da kika ɗaukesu ina zaki dasu ne ? Zanje in ajiyesu ne , da Allah aje ki wuce ga kaya can ta nuna inda ta ajiyemin kallonta nayi tare da cewa sannu ki daina kuka haka nan kar kanki yayi ciwo , idan yayi ina ruwanki naki ko nawa ? Allah ya baki haƙuri na nufi jikin madubi ina shafa mai sai powder tagumi Inna tayi ta bini da kallo har na saka kaya na shafa tutare kaɗan na ɗauki hijibin da Inna ta ajiyemin na saka na fita ,
Sultana tana fita Inna tayi magana a bayyane cewa wai Dikkon nan nawa ne don Allah ? Nifa na shiga rubibi dan har yanzu wallahi na kasa fahimta shin wai Dikko U DK shine yake zuwa wurin Sultana ko kuwa akwai wani Dikkon bayan shi Dikkon gidan gwamna ne ? Gaskiya ba DK bane tou ita Sultana ina ta samo wannan shi kuma …….?
Cike da zumuɗi na fito na buɗe gaba zan shiga naga ya ajiye filet a saman kujerar da kabeji anyi mishi yanka mai kyau sai cokali mai yatsu babu mai ba magi komai babu a ciki kuma Dikkon waya yakeyi rufewa nayi na koma baya na shiga na zauna , ina zama ya tafi yau bada su Ashiru yazo ba abokanshi ne suke tare , yana gama wayar ya ɗauke filet in yana cewa dawo nan An mata ,
Daga baya na tsallaka na isa gaba na rumgume Dikko sunbatar gefen fuskata yayi zan kwanta jikinshi motar ta fara lilo da sauri ya figi sitirayi dan kaucewa motar gabanshin daya kusa haye mata , zaunar dani yayi saman kujerar daya ɗauke filet in yana cewa zauna An mata karmu faɗi , ƙin zama nayi zan sake tasowa ya danne ni da hannun damarshi ya riƙe sitiyari da hannun haggunshi ya miƙa hankalinshi da natsuwarshi wurin tuƙi yana cewa da nace kar kiyi wanka saida kikayi badai zaki daina raini ba ko ?
Ni ? Waye yace maka nayi wanka ? Nayi wanka a ina ? Ko kana tunanin zanyi ne dan na burge ka ? Sauke hannunshi yayi daga riƙon da yayi min ya ɗauko filet in kabejin daga inda ya ajiyeshi ya ɗoro shi saman jikina yana gyara rigarshi yace ci , me zanci ne ? Koma miye idan kinci bakinki zai faɗa miki , wai kana nufin ni zanci kabeji kamar wata akuya ? Koma dai mece ce ke bai shafeni ba cewa nayi ki ci , haba Dikko ni gaskiya bana ci , cikin ɓacin rai ya kalleni yace ke….. Ɗauka kici , cikin sanyin murya nace haba kabeji ne fa har yanzu ni yake kallo yace kabejin ci ya ƙarasa maganar fuskarshi ba wasa.
Ina gunguni na ɗauki cokali na fara ci , a dai² lokacin da muka iso goruba , amma yau ba gidanshi yaje ba wata kyakkyawar santa suka yanka suka haɗa majalissar su a saman titi sun kashe hanyar ta yadda wani baya wucewa dan duk a saman titin suka ajiye motocinsu su ishashshi duk wani abokin Dikko da nasan yana majalissa a gidanshi na ganshi har dai Yazeed na gani kuma naga irin “yan matan da Inna ta bani labarinsu daren jiya , kallon Dikko nayi da hankalinshi yake kan wayarshi naci gaba dacin kabejin ina yunƙurin amai bai kalleni ba yace idan kikaimin amai a mota saina zaneki , to ai na ƙoshi babu daɗi , ai a ba daɗin zaki cinyeshi kisha ruwa gashi nan a gefenki ,
Salaf ne fa , salaf ɗin An mata cinye shi da sauri , maganin mi to ? Ra’ayi nane kawai na tareki da kabeji kuma ki rufemin bakinki na fara gajiya da magana , Allah ya isa na faɗa ƙasa² naci gaba daci saida na cinye kabejin nan duka , ansar filet in yayi ya duƙo kusa dani yace to me ne ne ? Ngode na bashi ansa to yayi kyau sha ruwa ina zuwa ya ƙarasa maganar yana fita daga motar da filet in yana fita wani ɗan cika sheda ya ansa , shi kuma aka ɗaukeshi a mota suka tafi….. Kuma na kirashi a waya bai ɗauka ba , raina ya ɓaci kuma na ƙufula da yawa.
Gaba ɗaya ɗakin yayi shiru kasancewar ƙarar saukar marin da Momy ta tsinkawa Dikko duk ƙannenshi dake wurin da gudu suka tashi , yayin da ita kuma Momy ke cewa saidai ka zaɓa ko yarinyar nan Dikko ko ni saboda ba so ɗaya ba biyu ba na rabaka da ita baka bari , kai da bala’e ma zaka rabu da ita dan duk duniyar nan idan zata taru bisa kaina bazaka auri karuwa ba sakaran banza da baka san inda duniya ta nufa ba yaushe ka koma sakarai ban sani ba ? Ina tantama anya ma kaine Dikkon dana haifa da ciki na ? Karuwa Dikko ? Me ka gani jikinta wanda harya gigita ka yasa kake neman ka zama wani zararre ?
Mom….. Ƙara yanka mishi mari tayi tace idan ka sake min magana saina shaƙeka ka mutu na huta da baƙin ciki tashi ka fita ka bani wuri kuma kaci gaba da yawo da ita a garin nan ana bani labari , duk ranar dana sake jin labarin ka ɗauki yarinyar nan a motarka saina je har gidansu naci uwar uwarta na faɗa maka sakaran banza marar kishin kanshi tashi ka fita ta faɗa a tsawace , jiki a sanyaye Dikko ya miƙe ya fito daga palon ,
A waje ya samu Nabeela tana ganinshi zata ruga yace ke zo nan , cike da fargaba tazo ta tsaya gabanshi ta fara kuka , kallonta yayi na wani lokaci sannan yace waye yace ya ganni da An mata ? Cikin kuka tace wallahi Yaya bansan waye ba ina toilet ina alwalla naji ta tana magana a waya tana faɗa , bayan na fito ne na sameta tana tura maka text ,
Amma a tunaninki waye ya kirata ? Yaya wallahi ban sani ba , na baki nan da mintuna 5 ya nuna da hannunshi yana ci gaba da cewa ki ganomin ko waye idan kuma ba haka ba zaki shiga3n ki…. Yana faɗin haka ya nufi wurin mota ya shiga abokinshi yaja suka bar gidan!
Lokacin da Dikko ya dawo har na fara bacci shigowarshi cikin mota ya farkar dani , ina tashi na ganshi nace sai in kiraka baza ka ɗauki waya ba ? An mata da Allah bazan ɗauka ba kiyi magani na mana , ai baka dai kyauta ba kuma haka rashin adalci ne ka barni a mota kamar sakara idan kuma na tafi kace na tafi saika shanyani ka kama huɗɗoɗin gaban ka ? Ke kalli idona , kallonshi nayi yace baki lura da yanayi ba ? Ai ni naga lura da yanayin yasa ka barni ni taya ma zan iya ganewa bayan duk yanayin iri ɗaya ne ? Rufe idanuwa yayi dan haka na kame bakina nayi shiru ,
Shi kuma idonshi a rufe yace na shanyaki sai zakiyi ya ya dani ne ? Shiru nayi ban sake magana ba dan yadda ya ɗauki zafin nan yana iya tsintsinka min mari , tafiya ya farayi da motar yana faɗa cewa ni bansan irin iskancinki gaba ɗaya na lura so kike ki mayar dani wani sa’ar wasanki wai me yasa ke kike san cin moriyar rauni na ne ? Kici gaba da haye man ƙaramar yarinya dake. Nidai ban sake mishi magana ba ,
Har muka iso ƙofar gidan Inna Dikko faɗa yake min yana cewa idan kinajin taurin kan ki sake magana kiga yadda zanyi parking nan in lalata miki fata , banza nayi dashi bance masa umm׳ ba , yanayin parking na fice da sauri bayan nayi mishi godiya kamar yadda yake so , har na kusa shiga gida ya kirani , dawowa nayi amma ban shiga motar ba , An mata kin yafemin ? Ya tambaye ni , da Eh na bashi amsa , tou zagayo nan kiji wata magana , zagayawa nayi saitin inda yake na tsaya ina kallon ƙasa…..
Idan Allah ya kaimu gobe zanje kaduna , Allah ya tsare hanya na bashi ansa , to bazaki tambayeni me zanyi ba ? Da kamar ince masa ai bani na aike ka ba , amma sai nace ɗin me zakayo ? Murmushi yayi yace An mata baiwar Allah ba kai tsaye zaki riƙamin magana ba na faɗa miki ki riƙa lanƙwasa min harshe wai ke ni haka nake miki magana ba sanyi ? A shagwaɓe zakice zakaje kaduna ka abarni ne , shiru nayi na kasa magana , ina saurarenki , ni dan Allah bacci nakeji , ai kowa ma yanajin bacci sai kin faɗa zaki tafi idan kuwa ba haka ba zamu kwana a titi , sai kin faɗa da shagwaɓa sannan zaki tafi , nidai kunya ta hanani kallon Dikko bare na maimaita abinda yasa na faɗa , text ɗin da Nabeela ta turo mishi yake dubawa bayan ya ajiye wayar yace ina saurarenki.
Ganin zamu dawwa a haka yasa na rufe fuskata na faɗa kamar yadda yace , buɗe fuskar ki , sauke hannuna nayi , matso nan , matsawa nayi kwantar da kanshi yayi samman murfin mota ya ƙara cewa matso , matsawa nayi da hannunshi ya nunamin nima na kwantar da kaina kamar yadda yayi , ɗaura kaina nayi ina kallon idonshi , shima kallon nawa idon yayi yace tou faɗamin ko baki so inji daɗi ? Ina so , kina so ko ? Eh , yimin magana a shagwaɓe yadda nace ki faɗa , dakel na iya faɗa cikin jin kunya bayan na rufe idona , buɗe idonki ba’a furta zancen so yayin da ido yake rufe ki faɗa a yayin da muke kallon idanuwan junanmu dan martaba soyayya , kallon idon abun soyayyarka yayin furta masa wata kalma da zaiji shauƙi yakan ƙara tabbatar da son mai magana a zuciyarshi , faɗa min kina kallon cikin idanuwana , dakel dai na faɗa , murmushi yayi tare da cewa jeki zanzo kafin in tafi badai haka yaso yaji ba , saida safe na faɗa tare da wucewa gida , saida na shiga gida Dikko ya tafi da tunanin wai me yasa yawancin mata basu iya magana mai tafiya da tunanin namiji ? Ba kallo mai burgewa magana mai laushi babu dai wani salo na tafiya da tunani wai a haka ma ita kunya ta takeji lallai yarinya kina da aiki kima tattara wannan kunyar gefe ɗaya ki ajiyeta saboda Dikko baya ma mace kawaici.
Dakel Dady yaja jikinshi ya leƙo yana ma mai gadin dake faman tsaron su babu dare kuma ba rana magana cewa da Allah ɗan sammin aron wayarka , ba wani damuwa ko tunanin abinda zai faru ya miƙa mishi waya , lambar matarshi yasa ya kirata , saida ya tsinke ya sake kiranta ana biyun ta ɗauka , ko gaisawa basuyi ba yace mata ɗan ƙawarki yana nan yana cin mutunci mu akan wannan tsinanniyar yarinyar dana faɗa miki tana san ta anshi kuɗin gadon su dan haka ki faɗawa ƙawarki tasa Dikko ya sakemu dan wallahi idan na ƙara biyu awurin nan mutuwa zanyi , cike da damuwa tace Dikko bai sanka ba ? Ya sanni mana ɗan iskan saida yacemin ma albarkacinki naci cikin kuka Dady ya ida cewa amma duk aya sanni yake ta ganamin azaba ba dare ba rana !
Maman Hafsa tace amma dai Dikko baida mutunci , bara zan kira Maryam ɗin dan na tabbata duk iskancin da Dikko keyi garin nan bata da labari ɗan iska mara mutunci dako bakin duniya bai kamashi , Dady yace dama banda abinki ya za’ayi bakin duniya ya kama irinsu wanda basu fito ba saida suka shiryama duniyar , ki kirata an fara kashedi kuɗin zai ƙare ya tsinke wayar.
Ina shiga gida a saman idon Inna na shiga kuma ta zageni sosai sannan ta shatamin layi karna sake bin Dikko fira idan ba’a ƙofar gida ba cikin palonta idan bayayi nan tou ya kama gabanshi , nace to na canja maganar da cewa kin daina kukan ne ? Dan bana so azo inda zata zagi Dikko , bata bani ansa ba dan haka nahau saman gado na kwanta kusa da ita ban daɗe da kwanciya ba bacci ya ɗaukeni da tunanin rigimar Dikko.
Misalin ƙarfe 7:45am Momyn Hafsa ta kira Momyn DK tana ɗauka Momyn Hafsa tace tuba nake dai na tasheki bacci da safiyar nan dan Allah ina tare da damuwa ne nake ta Allah² gari ya waye , Momy tace ba komai , Mom Hafsa tace Hajjaju Dikko ne da mai gidana , Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un nan kuma ya dawo ? Eh , meya haɗa Dikko da mijinki Mariya ? Wata karuwars….. Ah ah Momy ta faɗa dan dakatar da Maman Hafsa tace Dikko bashi da karuwa ni kuma ban haifi mazinaci ba Allah ya tsaremin ɗana baya huɗɗar mata , me kuwa zai haɗashi da karuwa da har zaiyi riƙici da wani akanta ? Allah ya baki haƙuri ba haka nake nufi ba , Momy tace duk ma yadda kike nufi ki bari zan kira Dikko yanzu….
Kiyi haƙuri ki fahimci maganar tawa , Momy tace nafa fahimta kawai dai banji daɗi ba kike cewa wai karuwarshi kamar ba ɗanki ba ? Haba Mariya , haƙuri dai Mariya ta ƙara bawa Maryam sannan suka ajiye waya Momy bata bar Mariya ta gama maganarta ba , tsoki Momy tayi bayan ta tsinke wayarta , taci gaba da faɗa ita dai Dikko yana so ya kasheta ya hana mata zaman lafiya , idan ta rabashi da nan sai kuma ya koma nan Dikko ba ƙaramin yaro ba amma ya hana mata kwanciyar hankali , yanzu banda iskanci kuma meya haɗashi da mijin Mariya Jabeer , wayar Dikko ta fara kira tana faɗa amma sai Jiddah ta ɗauka tace mata tunda ya fita masallaci har yanzu bai dawo ba ,
Tun tsakar dare Bello ya fara tanɗar harshe kamar kwarton da yaga wawan zama , yana dariya ma Dady cewa saina tona maka asiri ׳ harararshi Dady yayi tare da cewa to ka tonamin dan wutsiyar gyatimin ka , dariya Bello yayi ta irin ya saki layi yana ci gaba da cewa saina tona maka asiri , a haka Dikko ya sami Bello yana ta abu kamar dai yaɗan zare haka….
Yana ganin Dikko yace Baba wannan Baban ne , Dikko rai babu haƙuri yayi ma Bello wani irin kallo yace nine Baban naka …..? Umm ya faɗa tare da gaggaɓewa da dariya yace ba kaine ka kamoni ba kayi man duka , kallonshi Dikko yayi tare da cewa ko kana so na ƙara maka ne ? A , a Baba na bari , tou me kayimin na dake ka ? Dan abinda shi Dikko ya fahimta kila kamar Bello ya tsorata da yawa yasa ya ruɗe , shi kuma Bello cewa yayi in faɗa maka gaskiya ? Da ƙarya ka faɗamin ? Inji Dikko , Bello yace wallahi nine nake so ta zama karuwa ,
Kuma nine na kashe Binna sa’ar caca na yana tafiya da rayuwar cacarsa dama boka yace zai haɗa sa’a tane a ta Binna danshi mai sa’a ne yacemin kuma idan har Binna ya daina caca shine komai zai lalace min bazan sake samun sa’ar caca ba kuma rayuwata zata zama kamar walƙiya idan har Binna ya daina caca , shine Binna ya fita a caca komai nawa yaja baya ,
Dana koma na faɗawa boka cewa komai ya taɓarɓare min kuma mutane suna gudu na , shine boka yace idan Binna bai dawo caca ba rigar da zan saka komai na rayuwa saina nema na rasa , dana ce Binna ya dawo caca ya ƙiya , shine na sake komawa na faɗawa boka shine ya tura aljannu suna bawa Binna tsoro a bacci ko zai dawo amma ya ƙiya.
Mafita na ƙarshe shine boka yace mutuwar Binna itace tsira da kuma salama a rayuwata shine na kashe shi , Dikko yace ai bashi ka kashe ba kaine ka kashe kanka , labarin kwalba ya akayi yazo wurinka ?
Malami karuwa da mawaƙi duk basu da amana , yayin da suka kama wani a lokacin suke watsi da duk wani mutunci dake tsakaninku , malamin da suka ba kwalbar ni malami na ne kuma nine na haɗashi da Mamy , da kwalbar tazo hannunshi shine ya kirani mukayi ciniki ita Mamy ta bashi naira dubu hamsin akan ya warware matsalar shine ya faɗamin ni kuma nace zan bashi naira dubu ɗari biyar ya bani kwalbar , shine nakai na anso ,
Aljannu goma ne a saman kwalbar suna gadinta daga nan har illah masha Allah , wannan sammu makarinsa ɗaya ne inji boka , saukar alƙur’ani mai girma tsawon wata ɗaya kullum sai an sauke alƙur’ani sau goma duk rana ɗaya a yanka raguna goma bayan an buɗe kwalbar kuma ba fasata za’ayi ba domin kwalbar itace matsayin ƙwalwar ita Sultana shi yasa akayi cushe² a cikinta an tosheta ta yadda iska baya shiga , buɗe kwalbar za’ayi a barta a buɗe daga ranar da aka san za’a fara sauka , sau goma za’a sauke fa kuma har tsawon kwana 30 za’a yanka raguna goma duk rana a raba ɗanyen naman sadaka…..
Yanzu ina kwalbar take ne ? Tana ɓoye a wani wurin sirri nine kaɗai nasan wurin , na ɓoyeta tun bayan lokacin dana anso ta daga hannun malam , fita Dikko yayi ya nufi gidanshi , bayan yaje yace Ashiru yaje ya ɗauki Bello ya kaishi gidanshi ya ɗauko saƙo , Ashiru yace to , Dikko ya wuce ciki.
Da wani irin ciwon kai yau Inna ta tashi ko motsin kirki bata iyawa tun jiya take kwarara amai kafin gari ya waye tayi laushi ko magana bata iyawa , ina zaune kusa da ita sai sannu nake mata bata min magana tadai bini da ido tana min kallo mai nuni da tanajin tausayin rayuwata ,
Mai gadi naji yana ta sallama daga waje dan haka na tashi na fita , nayi baƙi a waje shine abinda ya faɗamin , kai tsaye na nufi ƙofar gida wani mutum ne zaune a saman machine kusa dashi naje muka gaisa bayan mun gaisa ya ciro takadda daga aljihunshi yace gashi , nace ta miye ne ? Yace ki ansa ki kiranta mana , kaida ka kawota kaine zaka buɗe ka karanta , kallona yayi sannan yace sammaci ne ƙanin Babanki yana tuhumarki da sa hannunki a lalacewar tarbiyar “yar sa sai kuma maganar kuɗin gadonsu daya ji labari kin ansa kin handamesu…….
Kallonshi nayi amma ban anshi takaddar ba nace ina zuwa , komawa nayi ciki na ɗauki wayata na kira Dikko , saida kiran ya kusa ƙarewa ya ɗauka , fita nayi waje babu ko gaisuwa na fara rattafa mishi damuwata , shima yana cikin damuwa domin bayan ya koma gida Jiddah ta faɗa mishi Momy tayi waya , bayan ya kira Momyn ne tace yaje tana kiranshi , da yaje tayi mishi zagin girgizar “ya “yan magarya tare da faɗa masa cewa kashedi na ƙarshe tayi masa akan Sultana idan ya kuskura ta sake kiranshi akan Sultana zata mishi wulaƙancin da katsina bazata iya ɗauka ba , yana cikin tashin hankalin zagi da tunanin taya zaiyi ya rabu da An mata ita kuma ta kirashi tana faɗa mishi tata matsalar kuma shine take so ya sama mata natsuwa , ashe shine ma ya kamata ya koyi aje damuwa 2 a zuciyarshi ba An mata ba , damuwar shi , damuwar An mata , ajiyar zuciya ya sauke sannan yace kina ina yanzu ?
Ina Barhim , ina shi mutumin yake ? Yana waje , tou ki taho dashi mu haɗu daku wurin government house yanzu zan fito , ciki na koma na ɗauki hijabi na ko Inna ban faɗa mawa ba saboda na gani tana cikin damuwa bai kamata na ƙara mata wata damuwar ba amma nasan dole zan mata laifi tunda tace na daina bin Dikko kuma gashi zan bishi , kuɗin napep na ɗauka na fita waje ,
Ina zuwa wurin mutumin nace masa tou muje , ai ba yau ake nemanki ba sai sati mai zuwa zakije , Ey wurin Babana zamuje ka bashi kaga bai kamata ni na anshi sammaci a hannuna ba , kuma kaga daka zo bani ya kamata ka nema ba , iyayena zaka nema idan kuma ina da aure mijina , ina Baban naki ne ? Muje ai wurinshi zamuje yanzu , tada mashin inshi yayi yace in hau nace masa mu fita waje dai na samu napep.
Ina gaba yana bayana saman machine har muka fito wajen estate in , na samu napep na shige ko a napep mune a gaba yana bin bayanmu da machine har muka isa daga nesa na hango motar Dikko dan haka na sauka a napep bayan na bashi kuɗinshi…
Dikko yana hangoni ya matso inda muke tsaye , ta wurina ya tsaya tare da sauke gilashi , matsawa nayi kusa da motar ina cewa mutumin tou taho , ƙin tahowa yayi , ni kuma na sake cewa kazo ka kawo mishi yana jiranka ,tada machine ɗin shi ya farayi Dikko yace ya akayi ne ? Ya nuna kamar baima san abinda ya faru ba , wai kotu ake ƙarata wai ana tuhumata da lalata tarbiyar wata kuɗin gado duk ni ɗaya , a dai² lokacin da mutumin ya tashi machine ɗin shi Dikko yace kai zo nan , kashe machine ɗin yayi ya sauko dan yasa ko ya tafi zai bishi ne kuma idan ya bishi da damuwa.
Daga ɗan can gefe ya tsaya ya gaishe da Dikko , bai ansa gaisuwar ba yace ya akayi ne ? E dama ranka ya daɗe wai ita ake nema a kotu dan ansa wasu “yan tambayoyi , wane irin “yan tambayoyi ? Wani ƙanin Babanta ne yake ƙararta , biro Dikko ya ɗauko gefenshi ya bani yace miƙa mishi ya goge sunanki yasa nawa , ai ranka ya daɗe ba kai ake nema ba , Dikko yace wanda ya kira uwa ya kira ɗanta ne , haka zalika duk wanda ya nemi mata mijinta ya nema rubuta suna na ,
Ƙin ansar biron yayi tare da cewa tuba nake ranka ya daɗe , miƙo hannu Dikko yayi cewa tou kawomin , miƙomin takaddar yayi Dikko yace kai zaka kawota da kanka , matsawa yayi ya miƙa mishi , duba takardar yayi bayan ya ansa yace to jeka zamu zo rana irin na yau ko ? Yace E ba damuwa kuɗi Dikko ya bashi masu yawa godiya yayi sannan ya tafi…
Taho mu tafi , zagayawa nayi na shiga muka tafi gida , a hanya nake faɗa masa Inna bata da lafiya kuma tana ta amai tun jiya kuma na faɗa mishi kuka tayi sosai shi yasa bata lafiya , addu’ar neman samun lafiya yayi mata daga haka bai sake magana ba saini dana isheshi da surutu har muka iso gida , bayan munzo ne yake cemin ya fasa tafiya saboda wani uziri daya taso mishi ,
Sannan kuma ya tambayeni wai zan iya zama da Jiddah ? Ina zan zauna da ita ? G R A kinga ban gama aiki goruba ba kuma ni inaso muyi muyi aure , kallon gefe nayi nace idan munyi auren ka riƙa bani kabeji ? Murmushi yayi yace ke wallahi wannan kabejin nine nakecin shi a yadda kika jishi , babu daɗi ne ? Umm ba daɗi , zaki zaune da Jiddah ? Idan nayi maka laifi saika dakeni a gabanta ? A , a sai mun shiga ɗaki zan zaneki a saman gado kina so ko ? Tsoki nayi zan fita motar ya riƙoni yace An matana yi haƙuri kar kiyi fushi wasa nake miki fa , tafiya zanyi kar Inna ta tashi bana nan , naji zaki tafi amma kalloni , kallonshi nayi yace kin gode ? Ey , idan munyi aure ma idan kika zanu zaki gode ya ƙarasa maganar yanamin kallon tsakiyar fage…..
Fizge hannuna nayi na fita , dariya Dikko yayi yana An mata zo , ban dawo ba yace ki gashemin Mama zan dawo anjima ki ajiyemin abun daɗi kinji ko……? Ban juyo ba kuma ban bashi ansa ba na shige gida , murmushi yayi ya rufe ƙofar da Sultana ta bari buɗe sannan ya wuce , yana tunanin anya bazai bari ya gama aikinshi ba ? Kamar idan ya haɗa An mata da Jiddah zata sha wahala kuma gashi shi ba mazauni ba , wata zuciyar tace kawai cakuɗesu tayi hankali ma……..
Mutumin daya kawo ma Sultana sammaci gidan Baba ƙarami ya nufa ,
08/11/2019 ????????
*JAMILA MUSA….* ????????