WUTSIYAR RAKUMI 44

*_NO. 44_*
……….Sai kusan ƙarfe ɗaya su Ummi suka dawo gidan, lokacin itama Bily ta tashi suna kicin suna haɗa abincin rana da ƴar hirarsu.
Ummi data shigo tana faɗin, “Ummm autocina duk kun cika mana gidan da ƙamshi”.
Dariya sukai suna juyowa, duk sukazo suka rungumeta suna mata sannu da zuwa.
Sai da ta buɗe komai taga mi suke girkawa sannan ta fita danta watsa ruwa.
Ummi na fita maman Ahmad ta shigo, dama kunyar Ummi ta sata maƙalewa.
“Habawa yara, inacan inata tattalin yanda za’a shiryaku amma na dawo ko ɗan ruwa baku kawo minba?”.
Dariya duk sukayi, Bily tace, “Aunty wai dan ALLAH ina kukaje?”.
“Gidan wata hajiya ce wlhy, kai-kai angunan nan zasu more fa, yara ina tausaya muku”.
Kafin su bata amsa yaya Zaid ya shigo. Sannu da zuwa sukai masa.
Ya amsa yana buɗe firij ya ɗauki ruwa da faɗin, “Wai dan ALLAH baku gama abinci ba? ALLAH yunwa nakeji.
Cikin tsokana Ummu tace, “Tofa, yaya Zaid kuda kukaje kuka ciwo kajin ɗaurin aure?”.
“Kajin wahala ba, wanifa ƙauyene can Abba ya kaimu, ni bammasan miye dangan takarsu ba, ko ruwa ban shaba harmuka taho, garama Ameer da Yaa Attahir sunsha fura, dan su dama mayun tane”.
“Oh wai harda Yaya Ameer kukaje?” cewar Bily.
“Eh, harma da Dad da yaa Amaan da Bassam fa”.
“To, to ALLAH ya sanya alkairi”.
“Amin dai, ammafa naci dariya, kunga angon kuwa? ALLAH Bassam ya girmesa sosai, bai wuce 20years ba”.
Maman Ahmad tace, “20years fa? Kai Zaid banda sharri”.
“Wlhy babu wani sharri Aunty Hafsat, bara kiga hotonsa”.
Wayarsa ya zaro ya miƙa musu bayan ya lalubo hoton, sai mamaki sukeyi, amma banda Ummukulsoom da tai murmushi kawai, dan ita wannan ai ba sabon abu bane a wajen ta, garinsu har ƴan 18 yima aure ake kuma maza.
Ranar dai yini sukai a gida suna shan hira hankali kwance.
Sai washe gari da yamma suka koma legos tare da tarin kayan gyaran jiki da Ummi ta haɗasu dashi, sai maganin sanyi da aganinta shine mafi muhimmanci a garesu, garama Ummukulsoom ita ance ta fara shan wasu kayan ƙarin ni’ima dana matsewa, dan ita Ummi duk zatonta Ummu tasan komai tunda dai an kaita gidan miji.
Sai dai koda suka dawo sai Maman Ahmad bata bataba, dan tasan ita dai yanda Ummukulsoom ta rayu a gidan Amaan a wancan zaman.
Su Ummukulsoom ba tare suka dawo da Amaan ba, shi sai safiyar litinin ya dawo saboda wani uzuri daya tsaidasa na zuwa Ajiwa.
⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡
Washe garin litinin da wuri Ummukulsoom tai shirin makaranta, tea kawai tasha a tsai-tsaye, shima sai da Maman Ahmad tai mata jan ido, tana gama sha ta miƙe ta tattara kayanta domin tafiya.
Sanye take da doguwar riga ja mai taushi, rigar robace, dan haka ta ɗan kama jikinta, amma ba sosai ba, sai dai saboda kasantuwarta mace mai cikar halittar jiki za’ai saurin fahimtar yanda rigar tabi jikinta, gyale baƙi madaidaici ta naɗa a kanta.
Maman Ahmad nason mata maganar ta canja gyale sai ta shafa’a har Ummukulsoom ta fice.
Abbas ta iske a ƙofar gidan Attahir tsaye jikin mota.
Cike da girmamawa ya gaisheta, ita harma abin yaso bata mamaki, sai dai bata ja zancenba tai shirin wucesa.
“Uhm auntyn mu ai nine zan kaiki”.
Juyowa tai tana kallonsa da mamaki, kamar bazatai magana ba sai kuma tace, “A’a Abbas nagode wlhy kaje abinka, dana fita zan samu taxi”.
Ganin zata cigaba da tafiya yay sauri cewa, “Ai boss ne yace a kaiki”.
Tsaf ta gane wanda yake nufi, kuma tajishi sarai, amma saita share tai gaba abinta tamkar bata jiba.
Abbas ya rasa yanda zaiyi, sai kawai ya zuba mata idanu harta fara nisa.
★★★★
Cikin nutsuwa take tafiya tamkar yanda ta saba, wanda bai mata farin saniba saiya ɗauka yanga ce ko salon iya shege, amma sam ba haka baneba, tunma ba yanzu ba wannan shine asalin takun tafiyar Ummukulsoom tun tana a Ɗilau, tana tafiya tana kallon agogo, fatanta ta fita daga Barrack ɗin akan lokacin kawai.
Cak ta tsaya ganin ansha gabanta, ta ɗago a fusace dan son ganin wane ɗan iskane? Dan ita ba sakarma mazan Barrack ɗinnan fuska takeba.
Tsaye yake a ainahin sojansa, da alama daga motsa jiki yake, dan sanye yake da kayan training na Adidas farare tas, fuskarnan a ɗaure babu walwala kamar ko yaushe, duka hannayensa biyu zube a aljihun wando, sai earpiece daya maƙala a kunne wanda batasan mi yake jiba.
Duk da taji wani iri sai ta janye idanunta itama tana kuma ɗaure fuska ta ratsa ta gefensa zata wuce.
Hannunsa dake cikin wanda ya zaro tare da kamo nata ya maidota gabansa yana kuma haɗe fuska.
Waige-waige Ummukulsoom ta fara, babu yawan mutane sosai, amma akwai ɗaiɗaikun sojoji irinsa masu fitowa motsa jiki da sanyin safiya, yanda baiyi magana ba itama sai bata tankaba, sai hannunta da take kici-kicin ƙwacewa wani haushi na kuma cikata, gashi yanata ɓata mata lokaci.
“Banason abinda kakemin wlhy, ka sakarmin hannu malam”.
Banza yay mata tamkar bai jiba, baikuma sake mata hannunba, sai da ya shaƙi iska ya fesar sannan ya watsa mata manyan idanun nan nasa masu matuƙar tasiri a gareta, itama hararsa tayi ta ɗauke kai.
Murya ƙasa-ƙasa yace, “Ki koma ki canja waɗannan kayan, kokuma ki fasa zuwa makarantar, kuma daga yau Abbas zai kaiki ya ɗakkoki, ya rage naki kiyi yanda nace, kokuma kiyi naki tsarin”. ‘Ya ƙare maganar da sakin hannunta yay gaba abinsa ko wai-wayenta bai sake yiba’.
Harara tabi bayansa dashi, itama ta juya taci gaba da tafiyarta batare da ta koma ɗinba.
Tana tsaye a hanya danta samu taxi, mota tazo ta tsaya a gabanta, ƙin ɗaga kai tai ta kalli motar balle wanda ke a ciki…..
Jitai kawai an fisgeta an tura a motar, tana niyyar yin ihu ya maida murfin ya rufe ya zagaya mazaunin driver ya zauna.
yana shiga ta buɗe zata fita, fisgota yayi ya maida murfin ya rufe tare da saka luck.
Duk yanda taso haɗiye kukanta ta kasa, saida hawaye suka silalo mata a kumatu, hankalin sa dake kan tuƙine ya hanashi ganin kuka take.
Ita kuma taƙi kallonsa, takumaƙi magana dan zuciyarta a maƙoshi take.
Har suka isa makarantar babu wanda ya tankama ɗan uwansa, kowa ya ɗauke kai ya haɗe fuska.
Koda yay fakin sai bai cire luck ɗinba, hijjab ɗin dake bayan motar ya jawo ya ɗora mata akan cinya, cikin kakkausar murya yace, “Wlhy wannan yazama first and last da zan miki magana kiyi ignoring ɗina, dan zakisha wahalane wlhy. Fitarmin a mota”.
Ko kallon inda yake bataiba ta buɗe ta fice abinta.
Shikuma yaja motar tare da bula mata ƙura ya bar wajen.
Tsaki Ummukulsoom taja tana harar hijjab ɗin, ta tsani mulkin mallaka a rayuwarta, wlhy badan furucin baba a kantaba da bazata sakaba sai taga yanda zaiyi.
A fili tace “Sai shegen zuciya da faɗin rai kamar kuturu”.
Hijjab ɗin ta warware ta saka kafin ta karasa class.
Tun daga wannan ranar Abbas ya koma kaita maƙaranta, dan Attahir da kansa ya kirata yay mata faɗa akan hakan, yakuma ja kunnenta akan kayan da zata ringa fita dasu, dan ya kula ran Amaan yakai ƙolluwar ɓaci da abinda Ummukulsoom tai masa aranar, ba komai ya hasala shiba kuwa sai kishi mai tsanani da ya dade da karantar Ajiwa na dashi.
Tabi dukkan shawarar Attahir kuwa, danshi matsayin uba yake a gareta, sai dai kuma bata sake ganin Amaan ba tun ranar, bata damuba, dan ba buƙatar ganinsa takeba, hankalinta ma gaba ɗaya yana kan exams ɗinta da yazo gangara.
Tana saura kwana biyu ta kammala exams Attahir da Amaan sukayi tafiya.
⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡
Biki ya tashi lafiya su Suhailat dai basu kai ga komawa ba sai yau, taget nasu na gaba shine haɗuwar Zulfah da Basiru, dan haka suka sanya Abu duk yanda zaiyi yayi ya saka Basiru fitowa gida a yau.
Kasancewar Suna tare da Meenal sai Abu bai wani sha wahala akan hakanba.
Wajen wani hutawa na ƴaƴan manya sukaje, tunda suka shigo Zulfah na kallonsu, tana zaune a rukunin kujeru nacan gefe tana danna waya da shan Ice-creem.
Kusan mintuna goma da shigowar su taga sun nufota, ɗauke kai tai tamkar bata gansu ba, Abu ne ya fara jan kujera ya zauna a wajrn yana faɗin “Assalamu alaikum, ƴammata ko zamu iya zama dan ALLAH”.
Saida taja lokaci kafin ta amsa masa batare data kallesu ba.
Basiru kam Uffan bai ceba, yama ɗauke kansa gaba ɗaya shima, shi adole mai aji mijin ƴar gwamna????.
Suna zama Zulfah ta miƙe tana tattara kayanta.
Da sauri Abu yace, “Haba ƴammata ya zaki gudu? Komun takuraki ne?”.
“Kusan haka”. Ta faɗa cike da yanga da salo.
Hakanne ya saka Basiru ɗagowa yaga wace uwar iya ce.
Cikin tsantsar mamaki yace, “k!”.
Kallonsa tai itama tamkar yanzu ne ta gansa, ta ɗan fido ido, “Oh wai kune?”.
Shima Abu saiya washe baki, “Lah ashema Friend ɗinmu ce? Ni ai bamma ganeki ba, Please zauna to”.
Komawa Zulfah tai ta zauna tana wani shegen murmushi, musamman da taga basiru ya kafeta da ido.
“Haba Friend daga ranar kuma saiki ɓata ɓat?”.
Murmushi tayi batare da tace komaiba.
Hakan yasa ta kuma birge basiru, amma saiya basar, cikin gadara yace, “Bani Accaunt Number naki na maida miki kuɗinki na ranar”.
kallonsa tai tana wani narke murya, “Babie ai ni duk abinda na bada ya badu, bana taɓa jeka ka dawo, sai dai kaimin tukuyci da Number wayanka”. Ta faɗa tana zare wayarsa dake hannunsa.
Sosai gabansa ya fadi, dan wayar da Number meenal ce kawai a ciki ta amsa.
“Uhm kinga kawo na baki wannan” yay maganar da kai hannu zai karɓa wayar daga hannunta.
Gocewa tayi tana wani munafikin murmushi da ita kaɗai tasan fassarar kayanta, “Saboda banida muhimmanci ko? Toni wannan itace tafi kwantamin arai”.
Dama tanada Number, sai kawai ta saka tata tai save, takuma shiga inda bazai taɓa blocking nata ba, harda wasu tarkuna ta kafa masa, dan zulfah mayyace a wajen sanin sirrin waya.
Wayar ta miƙa masa tana faɗin, “Thanks babie”.
Bai iya cewa komaiba, dan shikam ko motsima ya kasa yi.
Hirarsu suka cigaba dayi da Abu kusan awa ɗaya kafin tai musu sallama ta tafi.
★★★★
Washe gari suka koma gida, tun daga lokacin kuma suka tasa rayuwar basiru gaba ta waya, musamman a chart, duk wadda tai masa magana kuma a cikinsu saita nuna masa Meenal.
Yasan halin Meenal da shegen siyan layikan waya kamar dangin ɓarayi ko kidinafa haka take. Sosai yake sakin jiki da kowaccensu suna hira har maganar banza ta shigo.
Shiko daɗi yakeji Meenal ta dawo gareshi, tana zuba masa kalaman soyayya fiyema da na da.
Zulfah kuwa idan tai masa magana ba sosai yake kulata ba.