Noor AlbiNOVELS

NOOR ALBI 38

Zainab“”

yakira sunanta cikin sauti Mara alamar Wasa ko kadan acikinsa.

Dakatawa tayi daga inda taye ta tsaya cak zuciyarta ta Dan harba sbd idan bashine yakira sunanta ba har mantawa takeyi da sunanta na asalin kuma sunan mahaifiyarta.

Ahankali ta juyo jikinta amace ta tako tadawo inda suke ta kalli fuskarsa taga ko dagowa baiyiba ya kalleta
Duk sai taji jikinta ya qara mutuwa,

Mum ma dataji yanda ya Kira sunan Laylan dakatawa tayi daga shigewa ta waiwayo tana kallonsa.

Sai daya aje tab din hannunsa gefe ya dago ya zubawa laylan su a fuska ganin lipstick dinta data shafa Yana Nan daram a bakinta har lokacin kamar ma lokacin ta shafa,
Ya gangaro da idanuwansa Kan suturar jikinta,

Skinny jeans ne ajikinta da doguwar pencil gown Wanda take tsage gefe gefe daga qasa har zuwa gurin qugunta sai Ana ganin jeans din ta inda yake yanken…

Siraran cinyoyinta lafe jeans din yake jikinsu sai silky scarf datai rolling dashi akanta ko wuyanta ba Sosai ya sauka ba…..ya dauke idanuwansa dasuka sauya take da wani bacin ran fitarta daga kanta…

Gabanta ya sake mummunan faduwa tana cigaba da shiga sanyin jikin ganin yanayinsa.

Kai tsaye batareda yakuma kallon gefentaba yace”

Meye time yanzu?
Bana fada karki Kuma fita idan ba school ba?
Akwai school ne yau?

Girgiza Kai tayi tana sauke kanta qasa jikinta na mutuwa da ganin bacin ransa.

And menene wanann a jikinki da Kika saka Kika fita dashi?
Wannan kayane?

Hawayen idonta dasuka taru ne Suka gangaro ta bude Baki ahankali tace”

I’m sorry Abba,
Zan kiyaye Inshallah bazan karaba.

Miqewa yayi yabar gurin batareda ya tanka hakurinta ba ya wuce sama.

Da mamakin Mai girman gaske Ms Na’ima tabi bayansa da kallo har yashige kafin ta maido kallonta Kan Laylah Dake tsiyayan hawaye sosai tadawo gabanta tace”

Baby kinwa Abbanki laifine da bana Nan harya hanaki fita anyhow yanzu?

Laifin me kikai?

Kinje yawone kinyi dare sosai ba?

Girgiza Kai tayi Ahankali hawayenta na sake gudu tace”

Siyayya naje tareda Sofia mukai dare shine yace karna Kuma zuwa koina sai school.

Da mamaki Ms Na’ima tace”

To ai wannan baya cikin dalilin hanaki fita gskia,
Ina nakejin Hana fita a turai saikace Muna Nigeria,
Lallai wannan saidai ke Amma Kam Ni ba magana irin wannan a tarihina….wuce kije daki Zan magana dashi anjima idan mun kwanta Zaki cigaba da fitarki koina kikeso,
Zan lallasar Miki shi anjima idan naje……

Maganar mum din ta qarasa dama lissafinta taji nauyin zuciyarta na tsananta yanda mum din keta nanata idan taje sun kwanta..

Dan Haka juyawa tayi tabar gurin ta nufi dakinta tashige tareda rufo kofar sai lokacin taji kuka na son zuwar Mata Amma ta danne ta qarasa tsakiyar dakin ta aje handbag dinta tareda cire kayan jikinta suka tayi wurgi dasu ta shige toilet.

Wanka tayo tana fitowa sallah kawai tayi ta Haye gado ta kwanta tareda dunqulewa ta rufe ido saidai zuciyarta Dake cikin Hali na qunci Babu yanda zata iya bacci musamman da kunnuwanta Suka jiyo Mata karar rufe kofar bedroom din mum data San sama zata gurin Abban koba komai tafiya tayi ta dawo yau Kam Dole gurinsa zata kwana ga gyara anyo masa…..

Wasu hawaye ne Suka gangaro gefen idonta ta rufe idon tana sake duqunqunewa cikin bargo zuciyarta na Mata nauyi.

MAMUH

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button