NOVELSYAR RAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

YAR RAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

YAR RAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

Assalamu alaikum warahmatullah, ‘yan uwana makaranta, ga sabon novel mai suna ‘YAR RAWA, zan fara, ina fatan zaku karbe shi, ku bini kamar yanda ko fiye da ku kaima novels dina na baya, ina roqon Allah daya sanya albarka a ciki, ya bani ikon rubuta daidai, duk abinda zan fada in ba zai zama alkairi garemu duka ba Allah ya karkatar dani da barin shi, Allah ya yafen kurakuren da zan yi har i zuwa qarshen kammalawa. HAERMEEN HAERMMAERH NA SON DUKKAB MASOYAN TA DA MASOYAN NOVELS DIN TA DUK INDA KUKE, ME LOVE U XX❤

” Sannu Tabawa, Allah zai baki lfy, da kan ki za ki reni abinda kk haifa, shi ciwo ai ba mutuwa bane” Yana fada yana share kwallar dake maqale a manyan idanun shi, shigowar yar budurwar yarinyar su da bazata wuce shekaru sha 12 ba, ne yasa Tabawa ta daga kai da kyar ta kalle ta, miqa mata hannu tai akan ta isa gareta, da kyar cikin azabar ciwo da kanta yake mata, tare da zafin da take ji a qirjin ta, wanda ji take kamar hucin garwashin wuta take fiddawa, ta fara magana, bayan yarinyar ta bata ruwan da ta debo mata,” Ameenee,….. ki ji tsoron Allah a duk inda kk,…. ki ma mahaifin ki biyayya, shida abokiyar zamana,….ki kasance yarinyar kirki da kowa zai sha’awar zaman ki tashi…… ki kiyaye dokokin Allah Ameenee…. Allah zai kiyaye ki da zuri’ar ki har qarshen rayuwar ki,…. Malam ka riqe amanar yarinyar nan,…… kar ka bari a cutar mana ita…… ka saka ta tai ilimi…. domin kai mai ilimi ne…..” tari ne mai qarfi ya sarqe ta, yi take ba qaqqautawa, cikin tashin hankali, Malam Muhammad ya miqe ya dakko ruwan zai bata, sai yaji diyar su Ameenee, tana kalmar shahada,mahaifiyar ta na mainaitawa, idon Ameenee na zubar da hawaye, kamar an bude famfo, Malam kasa motsi yar, ganin dagawar da girjin matar shi yai, tare da jan wani nunfashi, ta kwanta, hannun ta Ameenee ta daga, ta ga alamar ya sake, kuka ta fara can qasan maqoshin ta, mara sauti, ta farama mahaifiyar ta addu’a” Ya Rab Ya ilahy, Allah ina roqon ka ka gafarta ma mahaifiyata, ka kai rahama qabarin ta, Allah ka tada ta cikin bayin ka muminai salihai, Allah ka bata ikon amsa tambayoyin qabari,” Malam Muhammad da yai mutuwar durqushe ne , kama kanshi yana juya shi, hawaye masu mugun zafi, suke fama kwarara a idon shi, amsa addu’ar diyarshi yai wadda gaba daya bai san me take cewa ba sai daga qarshe ya fahimta, qanqame matar tashi yai kamar zai maida ta cikin shi, hawaye ke zuba, cikin ranshi yana nema mata rahamar Allah, daga baya ya sake ta ya kwantar da ita, ya rufe mata ido, sannan ya lullube ta da abin rufar da ta rufa da shi, tashi yai ya fita tsakar gidan nasu, wata gambasheshiyar mata na gani tana ma yaran ta wanda suke dika maza magana,akan suyi su gama cin abinci su debo mata ruwa, turo baki suke suna su ba inda za su, ganin malam ya fito cikin tashin hankali fuskar shi duk hawaye yasa ta qarasawa wajen shi da gudu2 sauri2, daurin qirjin ta na rai da rai na neman faduwa, ta damqe shi, ” Delu, Allah daya ban tabawa ya fini son ta, a yau ya amshi abar shi,ta tafi ta barnu cikin kewar ta, da quncin zuci, wannan qunci daja shiga ban san ranar fita ba Delu” wani tuquqin baqin ciki ne ya tokare mata wuya, jin kalaman shi, amma dake makira ce,sai ta fake da kukan mutuwar da taji ta saka hannu a ka ta kurma ihu ta fadi qasa dabar, tana turje2n kafa da hannaye, tare da cire dankwalin ta kanta da ya cure dan datti ya bayyana,” wayyo ni Delu na shiga ukuna, na rasa ‘yar uwata, mai sona da qaunata, Tabawa kar ki tafi ki bar mu, muna tsananin son ki, ki yafe mana laifin da mukai maki” Malam ne ya sunkuya ya daga ta, yana qara jin wanu tausayin kansu dika, dan rasa mace kamar Tabawa babban asara sukai,mace ce mai kunya, kawaici, tsafta, rufin asiri, da kuma juriya da hakuri, ga rufa asirin mijin ta, in basu da shi zatai duk qoqarin ta tai providing masi kamar itace mijin, daga mijin har kishiyar tata suna morar ta ba ladan ba, ya fifita ta da kowa a zuciyar shi fiye da kowa, ya bata mazauni mara misalin fada a cikin zuciyar shi da ruhin shi, ta zama wanu bangare na jikin shi, lokacin da sukai aure suka dare basu haihu ba, ita ta matsa mai ya auro Delu, tana zuwa ta fara da haihuwar maza, taso ta fito da iskancin ta fili Malam yai mata barazanar saki, ko nace ya sake ta ma, amma dake Tabawa mutuniyar kirki ce ta bashi hakuri, ta fada mai duk randa ya saki Delu itama ta bar zama da shi kenan, hakuri ya bata suka je ita da shi suka dawo da Delu,kowa na mamakin hali irin nata na kyautayi da kyautatawa, dan haaka sai ita Delu ta fara yi mata kisan mummuqe, a haka har sai da ta haifi yara biyu maza, masu suna Habeebu da Hamza, sannan Allah ya azurta, Tabawa da cikin Ameena, wadda ta sha gata wajen malam, kamar mai sabuwar haihuwa, hakan ne ya qara dasa qiyayyar Tabawa da duk abinda zata haifa a ran Delu,tayi iya qoqarin ta na ganin ta zubda cikin amma Allah bai bata dama ba, ran da kuwa taga mace aka haifa tai rawa tai juyi a daka tana waqoqin samun nasarar kasamcewar yaranta maza kuma sune manya, a haka rayuwa ta ci gaba sai ta dauki Ameenee da niyyae raino da ta kauce tai ta mata azaba, tana kuka, sai tace daga dan matsawa yara suka dake ta, ta hau sababi ma yaran, in Tabawa ta karbe ta tai ta mata fadan dan me zata ma yara fada, suma ai qanana ne,haka dai har Ameenee ta girma ta gane halayen Delu tsaf, mahaifiyar ta bata gano ba, Malam ma haka, ran da ko ta sanar ma da mahaifiyar ta ta sha duka sosai, a haka ta ja bakin ta tai shiru, dan yarinya ce mai biyayya sosai.
Daga ta Malam yai ya gyara mata zanin ya miqa mata dankwalin ta yana mai lallashin ta, daki ya kaita, ya miqo mata rigar kayan akan ta saka da hijab, ta saka tana wanai kuka kamar na gaske, can qasan ran ta kalaman da ya fada suna qara yunquro mata kamar kumallo. A haka aka gyara Tabawa akai mata wanka da sallah aka kaita gidan ta na gaskiya, Ameenee ta sha kuka tin tana iyawa har taji ba zata iya ba, daki ta koma ta kwanta inda Innar ta ke kwanciya,ya rungume filo tana hawaye, addu’a take ta mata a ranta ta samun rahamar Allah.

Bayan an yi sadakar arba’in ne na rasuwar Tabawa, komai jin shi suke ba dadi, tsakanin Malam kenan da Ameenee, wadda Delu ta mayar baiwa,a bayan idon mahaifin ta, amma in yana nan, har rungumar ta take a jikin nan nata mai dankaren tsami, tana nuna mata kulawa,dan haka suke qara bama Malam tausayi, in ya fita tun safe sai dare, baya jure ganin su cikin quncin da shima ya addabe shi, hakan ne ya ba Delu da yaran ta damar musgunawa marainiyar Allah, ga horon yunwa, da ya dawo sai kuji tana” zaki qara abincin ne Ameeneenaa, na kula ba ki son cin abinci, ki taimake ni kina ci, dubi yanda kk rame? Mutuwar nan duk muma a cikin dacin ta muke….” sai ta kasa qarasawa ta hau kuka, Malam ne zai rarrashe ta, ya karbi dan abincin ya ba yar tashi, ta wuni da yunwa amma gudun kar ya gane komai, dam an mata warning mai girma akan kae ta bari ya gane daidai da rana daya kashin ta ya bushe, daki take komawa ta hau ci kamar mahaukaciyar data shekara ba abincin, tana ci tana hawaye.

Mai gari ne yace a kira Malam Muhammad, sabida ya ga tunda akai rasuwar ya daina hada2r shi na Islamiyyun da ya taimaka aka bude a qarin nasu na Rimin Gata, hakuri ya ba mai garin, ya kuma tabbatar mai zai koma normal, daga wannan satin.

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button