Tun Cindy na Jin tsoro da shakka harta daina sai itama gidan yafi Dadi daga ita saisu ba hayaniya ba tashin hankali,
Tareda Laylan koyaushe suke abincin Rana da dare banda na safe sbd Basa tashi da wuri.
Babban fargabar data fara kamata shine yanda cikinta yafara tasawa alamar fitowa ga Abban ya lura da tasawar cikinta Amma Bai taba tunanin ciki ajikinta ba Dan Bata Raina kanta ba Saida tafiya ta kamasa ya wuce Australia yabarta da kewa Allah yasa Cindy na Nan tana kulawa da ita sosai sbd itama tagano cikin jikin Laylan daya sakata cikin tashin hankali da tsoron ranarda Ms Na’ima zatasan cikin da uban cikin.
Daga Ceddi Plaza anty Sa’adah ta fito gurin siyayyar tafiyar da zatai ganin gida Za’ayi bikin rantsar dasu Alhaji Qarami yayan Momy matsayin dasuka samu na siyasa,
Bataso zuwaba sbd tsoro da fargabar kada su Gane gaskia da aketa boye musu Dan kuwa suna ganowa tabbas batasan masifarsu ko ta Ms Na’ima wanne za’a fi Jin fargaba,
Su umma Jamila Babu abinda bazasu iya yiwa Laylah ba da dama Kawu saidun data daura auren ya wargaza dadadden burinsu,
Haryanzu alwashinsu na Kan takurawar momy dasukai tadawo Nigeria su samu su Shiga cikin arzikin Turaki da Anne tunda Sa’adah taqi bada dama umma Jamila ta tsine Mata yafi so dubu dari Akan yanda take cewan tana Amarica taqi dawowa su kutsa cikin dukiya,
Duk wasu manyan malamai da bokaye sungama shirinsu akan yanda zasu Dora Sa’adah a zuciyar Anne dashi kansa Turakin Dan samun abinda sukeso shiyasa batason zuwa Inda suken gashi yanzu Dole zata sbd ranar data dawo daga last tafiyar datai Suka hade airport da Haj Karima Dole ta sanar cewan dawowarta kenan yanzu tana Nigeria ta dawo shiyasa suka takura tazo wannan bikin da za’ai.
Motarta ta bude tasaka siyayyar datai bayan motar ta zagayo zata shiga…..
Haj Karima data Gama abinda take itama acikin gurin tana cikin motarta tana waya da Ms Na’ima da shigarta gida kenan ta koma Laylah dake fama da zazzabi Mai qarfi ta fito tana Mata sannu da dawowa….
Haj Karima ta zubawa Sa’adah Ido tana kallonta da kyau Dan ta tabbatarda ita din ce
Cikin tsananin tsana da baqin cikin ganin Sa’adahn tace”
Na’ima ga matsiyaciyar kishiyarki Nan gabana Kamar na taketa da mota…
Dakatawa Ms Na’ima tayi daga tafiyar datake zuwa daki ta miqawa Laylah handbag dinta zuciyarta na tsananin Kuna da zafi sbd da baqin cikin Turaki tadawo khairat Chiroma ta sanar Mata tagansa last month a LA da mace Kuma yarinyace,
Ayanda tace tagansu tamkar Mata da miji sbd yanda yake riqe da hannunta….
Sai data Bata rantsuwa ta tabbar Mata da abinda ta fadan shiyasa ba shiri ta baro yau din tadawo Dan kuwa saita Gane ko wacece Koda komai nata zai qare,
Tafasar da zuciyarta keyi yasa a qule tace”
Kibi kanta da mota Zinat narage masifar Dake gabana akan Turaki,
Kibi kanta da motar yanzu Nan nafada Miki Zinat Dan wlh zuciyata balbalin wuta takemun.
Tana daf da shigewa motarta Haj Zinat ta bawa motarta wuta tayi kanta da motar take kuwa Sa’adahn tayi sama ta Fado gurin ya dauki ihu da salatin jama’a akayo gurin..
Securities ne Suka taso da sauri duk Suka nufo gurin
Sai alokacin Haj Zinat ta fahimci zata iya samun matsala Dan Haka ta sauya shawara ta bude motarta ta fito da sauri ta nufi Sa’adahn tana cewa”
Innalillahi wainna ilaihirrajiun,
Ban luraba wlh,
Na Shiga uku,
Please ku taimaka min nakaita asibiti
Innalillahi….
Kama Sa’adah akai aka Sanya motar Haj Zinat tareda Mai aikin Haj Zinat din tunda tace ta santa sai securities guda biyu dasuka ja motar Sa’adah din itama Suka tafi..
Wani private hospital takaita aka karba Sa’adah din wadda taji rauni sosai take fidda jini akai ciki da ita.
Sun Jima agurin kafin aka gama dressing ciwukan Sa’adah da sauran Taimakon da aka Bata aka kaita wani lafiyayyan dakin hutawa.
Tsinuwar da Haj Zinat ta ringa sheqawa Sa’adah batada adadi Ms Na’ima kuwa acan gida daga hankalinta tayi tana Kira tana tambayar ko Sa’adahn ta mutu Dan buqatan ace ta mutu kawai takeyi.
Handbag din Sa’adah da Mai aikinta ta miqo Mata ta kalla Mai aikin cikin tsananin girmamawa tace”
Ma’am anata Kiran wayarta acikin jakarnan tun dazu.
Kallon wulaqanci Haj Zinat tayiwa jakar tareda cewa”
Bude ki dauka wayar ki sanar idan gidane suzo asibitin Dan Ni tafiyata zanyi Allah yasa kafin suzo tagama Isa lahira.
Bude jakar nafisa Mai aikin tayi ta zura hannu ciki tana neman wayar cikin jakar Amma tayi qasa
Dan Haka saita fara Ciro takardar Dake sama ta riqe hannunta daya ta maida hannu zata dauko wayar idon Haj Zinat ya sauka Kan takardar hannun nafisar da sunan asibitin data sani a LA ke rubuce barobaro.
Hannu takai ta karbi takardar tareda budewa Kai tsaye idonta Bai fara sauka koina ba sai Kan 7weeks pregnancy.
Zare Ido tayi hannuwanta na rawa
A gigice takai idonta Kan date tagani….
Qafafunta wannan karon suka dauki rawa da sauri ta kalli sunan Wanda yake da cikin taga MRS AB TURAKI kawai aka saka kenan matar Turakin ce Mai ciki ita Sa’adahn harna sati 7,kenan yanzu yakai wata hudu cikin…