Noor AlbiNOVELS

NOOR ALBI 39

Mamuhgee 39_*
Daqyar taga asuba tayi ta tashi tayo alwala tazo tayi sallah tana idarwa ta danyi karatun Qur’an tasamu nauyin zuciyarta ya sauka kafin ta miqe takoma gadonta ta Haye Tareda komawa cikin bargo sai alokacin bacci ya iya daukanta mai nauyi.

Bata fito breakfast ba sbd baccin datakeyi sai 12 ta farka tayi wanka ta fito taje ta gaida mum tadawo dakinta tayi zamanta anan tasa Cindy ta kawo Mata abincin taci tana gamawa takira Anty Sa’adah suna fira sama sama dan tasamu tasake sakewa.

Anyi Sa’adah data fahimci tana cikin yanayi Mara Dadi ta saki Ajiyar zuciya tareda Kiran sunanta tace”

Laylah kinsa yanayinki dai yanzu ba’a son damuwa ko?
Karki saka damuwar komai a ranki sbd lafiyanki Dana cikinki Dan kuwa qaramin ciki bayason saka damuwa arai zai iya fita,

Kinsamu Allah yasa daga haduwar qaddara so daya da Turaki yayi dake kin samu cikin gwara ki lallaba abinku ki haife kinsamu naki jinin,
Hakama su Anne da Turakin kin saka musu da dukkanin alkhairansu akanmu….

Nidai banason wani Abu ya samu cikin Nan Laylah sbd bakisan yaushe Allah zai Kuma kawo wannan rabonba na yaqara zuwa ya nemeki harki samu wani rabon Dan Haka gwara ki lallaba wannan din tunda kince so dayane Kuma bada saniba.

Kunyar qaryar dataiwa anty Sa’adah tun farko datake maimaita Mata yanzu da damuwar Jin cikinta zai iya zubewa sanadin damuwa yasa taqarajin duk batajin dadin komai.
Haka suka Gama wayar ba wani walwala ta miqe tayo alwala tayi asr prayer ta koma ta miqe a kujera tana chatting da Sofia itama taji ko zata sake.

Wuni tayi a daki Bata fito ko kofar palon ba hakama washe gari wuni tayi a daki taqi fitowa komai a daki Cindy ke kawo Mata.

Kwananta biyar Bata zuwa cin abinci dasu wasan boyo ma takeyi dasu gabaki dayansu sbd ko mum din datake zuwa gaidawa zuciyarta Shiga wani Hali takeyi sbd yanda mum din koyaushe take nuni da wani alamun mijinta Yana Mata yanda takeso,
a tafin hannunta yake,
Kullum biya Mata buqatanta yake, dadai sauran makamantansu duk da ba ita take fadawaba Amma koyaushe alamominta da wayarta da Haj Zinat na nuni da hakan Dan Haka sai kawai ta taqaita zuwa dakin mum din
Qarshema Bayan kwana biyu cewa tayi batada lafiya Dan Haka saita daina fitowama kwata kwata Dan wani radadi takeji cikin zuciyarta bakuma dama ko halin nunawa.

Shi kansa Abban ko txt dinsa dayake Mata ada kullum ya daina Yi itama batai Masa ba saidai kullum dare saitayi kukan data tabbatarda na mugun kishine Dake cinta Amma ba dalilinta na yin hakan shiyasa abun yake cin ranta.

Daqyar taga anyi sati biyu ta koma cigaba da zuwa makaranta sai tazama Bata wani zama gidan dama mum ko anan Atlanta ba wani zama gida takeba kullum tana gurin yawo.

Tunda Suka koma school sofia datasan da sabon cikin data samu koyaushe itace ke kokarin cheering dinta kayan ciye ciye harma da maganinda Aunt siya ta rubuto Mata na masu cikin kullum sofia ke Kai Mata school acan take Sha itakuma ta koma da sauran gidansu Dan bazasu Bari Laylan taje gida da maganinba a samu matsala.

Yau da wuri tadawo daga makarantar sbd gajiya da bacci ma kawai ita takeji Dan Haka ko data shigo harabar gidan tayi parking motarta ta fito rataye da qaramar Gucci quilted shoulder bag dinta ta,
Jikinta Kuma Diva abaya ce ajikinta maroon sai gyalen abayan data daura akanta yayi gefe daya.

Palon tashigo kai tsaye batasan dasuba a palon saidata shigo tayi Ido biyu dashi daidai shigowarta daidai dagowarsa ya kalli kofar sbd qamshinta dayaji hancinsa ya shaqo.

Cikin Ido Suka kalla juna kafin ta dauke Kai ahankali tareda qarasowa tana kallon mum Dake zaune kusa dashi sosai Sosai hakama tana riqeda hannunsa tana zuba Masa soyayya da kudin datakeson yasaka hannu A Abdoul ya Bata.

Ahankali ta Dan sauke kanta daga kallonsu cikin murya Mai taushi da nutsuwa tace”

Abba Ina wuni?
Mum barka da rana.

Yanda ya amsa Kai tsaye batareda yabar duba wayan dayakeba yasake sakata Jin wani iri ta wucewarta Dan dama ba wani tsayawa tayi ba.

Mum dakeson kudi gurin Turakin ta kalli Laylan cikin kulawan kissa tace”

Baby yau kifito kici abinci damu anjima kadan sbd munyi kewan cin abinci as happy family dukanmu.

Dagowa yayi ya zuba Mata idanuwansa da tanajinsu akanta suke
Sai Bata waiwayoba ta gyada Kai kawai Dan batada dalilin cewa aa.

Tana shiga daki wanka tafara Yi tayi sallar la’asar da akai ta Kira Cindy a waya tace takawo Mata fruits masu sanyi.

Tana Gama cin fruits dinta waya dasu Anne tayita Yi suna debe Mata kewansu data qaru tasa Jin qasar ta isheta.
A daki tayi wuninta sai dare Bayan tagama sallar isha tayi wanka kamar bazata fitoba sbd zamanta dakin yafi Mata nutsuwa yanzu Amma sbd batada dalilin qin fitar yasata zuro slippers ta fito ta nufi dining room din.

Tun a kofar shiga ciki ta tabbatarda Yana cikin sbd hancinta daya Bata tabbacin,

Numfashi ta sauke ahankali tareda Dan rufe ido ta bude tana hadawa da Ajiyar zuciya zuciyarta na neman narkewa Amma ta daure ta qaraso ciki.

Dagowa yayi ya zuba Mata idanuwansa Dake kokarin bada kamewarsa..

Doguwar fitted pencil gown ce a jikinta red Mai zib a gaba daga sama har Wasa,
Yanda rigar ta lafe a jikinta ta kwanta ne ya fidda asalin shape Dinta Sosai
Abin dabata lura dashiba cikinta ya Dan kumbura kadan ajikin rigar yafita saidai ba a ganewa ko kadan…
Ga wani irin Hasken gaske data qara har wani glowing takeyi.

Jin idonsa akanta yasa zuciyarta takasa hakuri ta dago ta kallesa itama
Idanuwansu suka shiga cikin na juna take taji kamar zata sakar Masa kukan tsananin kewarsa datai agurin saidai ba wannan damar Dan Haka ta dauke idonta tareda zaunawa gefen mum da taketa fama zuba Masa abinci tana Masa wasu salo salon daukan hankali duk Dan samun biyan buqatarta dataketa bi ayau din na kudin.

Murmushin yaqe tasake tana kallon mum da har lokacin Bata zaunaba tana serving dinsa da kasalalliyar murya tace”

Sannu da aiki mum.

Batareda ta waiwayo ba muryarta duk a washe tace”

Thank you baby.

Har Lokacin Bai dauke idonsa daga kantaba duk sai takasa komai ta aje cup din madarar data dauka batareda Tasha ba ta dago ta kallesa yanayi na Rasa abin Yi dakuma rashin mafita ta zuba Masa idonta Dake neman cikowa da hawaye.

Wani irin rufe ido yayi ya bude ahankali cikin Jin cin abincin ya fita kansa gabaki daya ganin hawayen idon nata,

Miqewa tsaye yayi ya juya yabar dining room din
Mum tabisa da kallo da gudu ta aje serving spoon din hannunta tabisa tana Kiran sunansa cikin firgicin karta Rasa damarta na abinda takeso.

Suna fita itama ta miqe batareda taci komaiba tabar dining room din tana share hawayenta da bayan hannunta.

Har bedroom dinsa Ms Na’ima tabisa jiki na rawa hankali tashe Dan kuwa zuwa gobe da safe idan Bata turawa Zinat kudinba akwai matsala,
Shagunan kasuwancinsu da boutiques dinsu komai na neman lalacewa kudi suke nema sosai Ido rufe Dan kila sai ta danganta da zuwa Nigeria din da kanta.

Baya buqatan hayaniya ko wace irice a yanzun Dan Haka tana shigowa tun kafin tafara Masa hayaniyar ya janyo takardarda tun safe takawo Masa take bibiyarsa ya zari pen ya saka Mata hannu akai ya miqa Mata.

Maganar dataso fada na nuna damuwar barowar da yayi baici abincinba Yana miqa Mata takardar ta shanye maganar da cewa”

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button