Jajayen idanuwansa dasuka sauya tun kafin shigowarta ya dago ya Mata kallo daya dayasa gabanta faduwa Amma batajin zata yarda ta zauna sbd abinda yake gabanta,
Nafada Babu inda Zaki ki
Idan Kuma Zaki tafin ki tafin Amma Kar qafarki ta Isa kofar gidana….
Miqewa yayi tareda daukan wayarsa yabar gurin.
Cikin masifaffen tashin hankali da tsoro harma da firgici Ms Na’ima tabi bayansa da kallo tana shedar da tsananin bacin Rai data hango cikin idonsa,
Karta Isa kofar gidan fa yace????
Batasan lokacinda ta miqe tana neman zunduma ihuba ta fito tana cewa”
Wlh anshiga tsananina da Turaki andau hanyar rabamu….
Ina Zinat ga bala’i Mai zaman kansa na neman sauka rayuwata
Turaki na fadar karna Isa kofar gidan.