LabaraiMalamar CociYaro

Fasto ta Bayyana Bidiyon Jinjira da aka Haifa da Sunan Allah a Kunnuwanta a Cocinta

Wata jarumar masana’antar shirya fina-finai na Nollywood, Mama Rainbow ta wallafa bidiyon wani abun al’ajabi da ya faru a cocinta kwanan nan a shafukan sada zumuntar zamani.

Dattijuwar a cikin farar rigar wankanta ta rike jinjirar tare da bukatar mutane su bude idanuwansu su ga sunan Allah da aka rubutu a yaren larabci a kunnuwanta Legit Hausa ta ruwaito.

Wallafar Iya Rainbow ta janyo cece-kuce a yanar gizo yayin da mutane da dama suka ki yarda da ita tare da tuhumar siddabarun da ke tare da bidiyon.

Fitacciyar jarumar wasan kwaikwayo, Mama Rainbow wacce kuma jagoran wata coci ce, ta wallafa wata mu’ujizar Ubangiji ta hanyar daya daga cikin jinjiran da aka haifa a cocinta.

A wani bidiyo da ya yi yawo a yanar gizo, an ga jarumar rike da wata jinjira, inda ta ke bayanin da Yarbanci yadda wani Musulmi ya nuna wani irin zane a kunnen jinjirar.

Mama Rainbow ta bukaci mutane su bude idanuwansu su ga rubutun ‘Allahu’ a kunnuwan jinjirar da tayi bacci cikin kwanciyar hankali yayin da aka nunata a kafafan sada zumuntar zamani.

Jarumar ta yi godiya ga Ubangiji yayin da ta nuna mu’ujizar da Ubangiji ya albarkaci taron jama’arta.

Jama’a sun yi martani

Martanin jama’a:

jouceisy: “Wadannan kawai surar gurin guntsinta ne ranki shi dade. Addini ba zai kashemu ba a kasar nan!”

united fc99: “Ni ba zan ce komai ba.”

iam_horpeyhemi: “Kila wasan kwaikwayo ne ko wani abu daban.”

mcelvisjcfrn: “Ku taru a nan idan kun lura da kyan jinjirar ba tare da damuwa da sanyin Zobon ba.”

godson21100: “Abun dariya. Wannan shi ne makurar jahilci. Tare da bada girma yadda ya dace ranki shi dade.”

aforchibunduaugustine: “Ni fa ban ga komai ba.. mummy wa… Idan zan ci ki gyara… haka kunnuwa suke!!! wai me addini zai mana ne!!!

[ad_2]

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button