RAUDHA 1-END

RAUDHA Page 41 to 50

Ad

_____

 Ba don Allah yasa Daddy me saurin yarda da ƙaddara bane, da babu abinda zai sa be zube musu anan ba, sai dai kuma sosai ya dage wajen danne kaso sittin cikin ɗari na daga damuwar sa, amma hakan be sa fuskar sa ta hana bayyanuwar tsantsan damuwa da tashin hankalin da yake ciki ba, idanuwan sa gaba ɗaya sun kaɗa sun yi jazur, muryan sa na rawa ya ce da su, “yanzu tana asibitin ne?”Rayyan ya ba shi amsa da “Eh”.

“Ok ku mu je ku kai Ni”. Yafaɗa yana miƙe wa tsaye da hanzari

Tare suka fice suka shiga motar Suhaib, Rayyan ne ya ja su zuwa asibitin.

    Suna isa ɗakin da aka kwantar da RAUDHA, Daddy yayi saurin ƙarisawa wajen ta, zama yayi ya ɗaura tafukan hannayen sa biyu saman fuskar ta yana shafa wa, ji yake yi tamkar yayi ta kurma kuka sabida tsananin tausayin ɗiyar sa. Wai yau RAUDHA ce kwance cikin wani hali na taɓin hankali, duk a sabida sakacin su

Lumshe idanu yayi yana sake sauke wa akan kyakkyawar fuskar ta, wanda ya rame sosai, sai haske da ta sake yi, barci take yi har yanzu sabida alluran barcin da aka yi mata. Ahankali Daddy ya saka hannun sa ya ɗauke hawayen da ya silalo masa a kuncin sa, sannan ya juyo yana kallon su yace, “ina ne Office ɗin doctorn dake duba ta?”

“Daddy bari in Kai ka”. Rayyan yayi saurin faɗar haka

Gyaɗa kai kawai yayi yabi bayan sa

Shi kuma Suhaib ya koma kusa da ita ya zauna a gefen gadon, ya riƙe hannun ta ɗaya wanda akayi mata ƙarin ruwa aka cire.

     Wajen mintuna ashirin da fitan su Daddy kafin suka dawo, dayake magriba tayi, sai suka wuce gaba ɗaya masallaci, har bayan sallan isha’i suna nan a asibitin, har sannan kuma RAUDHA bata farka ba, dole suka taho gida suka bar ta cikin kulawar likitoci, tunda dama asibitin ba kasafai suke barin mutane suna kwana da mara lafiya ba. Daddy ya so ya kwana amma sai su Rayyan suka taushe shi akan ya koma gida, tunda shima yana buƙatar hutu a wannan lokacin

Sai da suka mayar dashi gidan sa, kafin suka wuce su ma, da zummar gobe Suhaib zai kawo mishi Haneep da Farida, sai su gaisa tunda yau basu samu sun haɗu ba.

Ad

     A taƙaice ranan Daddy be iya runtsa wa ba, kwana yayi a zaune yana nema wa ƴar sa samun lafiya daga wurin mahaliccin mu.

    Washe gari tare suka taho da Farida gidan Daddy ɗin, anan suka gaisa, Daddy ya amshi Haneep yana ta faman mishi wasa, sosai soyayyar yaron ya shiga ransa, kuma ya tausaya mishi da rashin lafiyan da yake yi, yayi masa addu’a sosai kafin ya miƙa ma Farida shi, sannan suka fito suka nufi asibitin, daga can Rayyan ya wuce wurin aikin sa.

     Wajen awanni biyu da zuwan su, sannan ne RAUDHA ta farka, amma kuma gaba ɗaya ta rikita su da koke-koken ta, kuka take yi sosai tana surutu kamar zautacciya, ba ma ta gane wanda ke kanta

Sosai tashin hankali ya sake bayyana a wajen Daddy da Suhaib, sun rasa ya zasu yi, har kuka sai da Suhaib yayi, shi kuma Daddy sai faman sharan ƙwalla yake yi, musamman da ya riƙo ta yana faɗin, “shi ne Daddyn ta, tayi shiru”. Yana rarrashin ta

Sai tahau zagin sa, daga ƙarshe ta soma ɓaɓɓaka masa dariya tana tokarin sa da ƙafa, wai sai ya sake ta ta hau saman silling

Da gudu Suhaib ya fice yana sharan hawaye

Itama Farida dake riƙe da Haneep ta zauna a gefe tana kallon RAUDHA dake jikin Daddy, bata san sanda hawaye yayi ta kwarara a saman fuskar ta ba, sabida tsantsan tausayi

Hauka tuburan RAUDHA take yi, an rasa yanda za’a yi da ita, tunda tuni Suhaib ya kira likitoci sun duƙufa akanta

Ƙiri-ƙiri Daddy ya ƙi fita a ɗakin koda suka buƙaci su ba su wuri

Yanda suka ga hankalin Daddy yayi ƙololuwar tashi, dole suka tausaya mishi suka bar shi a cikin ɗakin, haka suke iya yin su wajen taimaka wa RAUDHA, sai da suka yi mata alluran barci sannan suka samu lafiya, amma ta karaɗe ɗakin da waje da ihun ta

Daddy kasa jure wa yayi ya faɗi ƙasa a sume, ai nan hankalin su Suhaib ya sake tashi da jin abinda ke faruwa

A wani ɗakin aka kai Daddy aka soma ba shi taimakon gaggawa, sosai jinin sa ya hau, ga shi yana buƙatar hutu, dole suka yi masa alluran barci don ya samu ya huta ko jinin sa zai sauka

Abun tausayi idan ku ka ga Suhaib, ya hana kansa sukuni duk ya tsangwami kan sa, shima ba don jarumta da ƙarfin hali ba; da tuni ya zube, sai  Farida da ke ƙarfafa masa gwiwa tana masa nasiha akan ɗaukan ƙaddara. tabbas haka Allah ya so ƙaddaran RAUDHA ce, dole wannan ciwon sai ya same ta, sai dai su yi wa Allah godiya tare da roƙon Allah ya taƙaita abun haka.

      Wajen awanni uku Daddy yayi a kwance, sannan ya farka. duk yanda likitoci suka so ya zauna ya sake huta wa a ɗaura masa drip amma yaƙi, nan ya soma buga waya ya hau yi mata cuku-cukun yanda za’a yi a fita da ita Abroad, sai dai basu samu ba, tunda ko wani ƙasa ance a dakata da zuwa, shi kansa Nigeria an rufe, dole Daddy ya bar ta anan asibitin, sai dai ya samu an yi masa hanyar likitoci ƙwararru waɗanda za su iya kula da RAUDHA

Abun ka da ma su kuɗi, a washe gari sai ga likitocin sun iso, nan aka duƙufa wajen duba RAUDHA, sosai take samun kulawa wajen likitoci, sai dai kamar ma ƙara haukan take yi, domin ciwon ci gaba yake ba baya ba, ta kai yanzu ɗaure ta ake yi a jikin ƙarfen gadon, sabida idan ta tashi daga alluran barcin da ake mata, ta rinƙa hauka kenan tana fashe-fashen kayan ɗaki, ko kuma tayi yinƙurin guduwa dole sai an kamo ta, har kayan jikin ta take yagawa, sai dai a sauya mata wani.

Ad

_____

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Related Articles

Back to top button