RAUDHA 1-END

RAUDHA Page 31 to 40

Ad

_____

_______📖 𝗧𝗼𝗺𝗼𝗿𝗿𝗼𝘄 𝗠𝗼𝗻𝗱𝗮𝘆

Ƙarfe 10:00am. Yau RAUDHA suke da Lectures, zuwa ƙarfe 09:20am. Har ta gama shirin ta, ta saka riga da wando, dack blue Jeans pencil crazy, sai ta saka ƙaramar riga t. Shirt me gajeren hannu baby blue colour, sannan ta ɗaura baƙar Kimono akai, yau har da Facing cap ta saka a kanta sannan ta saka hill shoes, taɗau jakar ta tafito

Sai da tashiga har ɗakin Farida ta yiwa Haneep kisses kafin tafito tafice, mota tahau tabar gidan da gudun da ta saba.

🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐

     Zuwa ƙarfe 02:30pm. Suhaib ya nufi airport ɗauko abokin sa, time ɗin yazo babu daɗe wa sai ga jirgin su ya sauka, don haka yafito yanufi haraban airport ɗin.

     A cikin waɗanda suke sauko wa na farko-farko, Suhaib ya hangi babban Amininsa wanda tuni yanzu ya zame masa ɗan uwa, *Captain Rayyan Hassan* kenan

Shima tuni ya hange sa, don haka tun sanda ya sauko a matattaƙalan benen jaye da Trolly ɗin sa yanufo sa fuskar sa cike da fara’a

Yayinda shima Suhaib ɗin ya tako zuwa gare sa dasauri, yana zuwa suka rungume juna ko wannen su yana me nuna farin cikin ganin ɗan uwan sa, sai kuma suka saki juna suna me cafe hannaye bakin su a washe

Sai da suka gama gaisawa kafin Suhaib ya amshi Trolly ɗin yaja, suka nufi inda yayi parcking motan sa riƙe da hannun juna.

       Ko a motan ma hira ne ta ɓarke a tsakanin su har suka isa gida.

Ad

     Farida na jin su tafito daga ɗaki cikin fara’an ta ta tarbe shi, dama tuni ita da kukun ta sun shirya masa girkin tarba, don haka koda suka gaisa sai Suhaib yaja sa zuwa sama, ya nuna masa ɗakin sa don yayi wanka kafin yazo yaci abincin.

     Bayan yayi wankan ya sauya kaya, sannan ya sauko ƙasa suka zauna da Suhaib a saman dainning

Farida tayi saving ɗin su kafin ta wuce ɗaki tabar su don su sake.

    Bayan sun gama cin abincin Parlour suka dawo suka dasa wani hiran

Lokacin Farida tafito ta kawo masa Haneep don ya ganshi

Miƙa masa tayi tana faɗin, “wannan ɗan dai ya taki Sa’a, yazo duniya da ƙafan Nasara tunda ya haɗu da Mahaifin shi batare da ya sha wahala ba, ko in ce ba sai ya girma ba ya soma tambayan mu Daddyn sa”.

Dariya suka yi gaba ɗaya

Rayyan yace, “kar ki saka in ji kunya mana Momyn Dady, kin san fa an ce yara kunne ne dasu, kar kuma ace yana jin k..”

Maganar tasa ne ta ƙaƙare sabida kukan da Haneep ya tsandara, dasauri yasake riƙe yaron sosai sabida ganin zai kubce masa, hakan yasa ya sake ɗaura hannun sa a ciwon sa, sai ya sake tsandara masa ihu

Taso wa Farida tayi ta amshe shi tana cewa, “kayi haƙuri Captain na manta ban sanar maka yana da tsira a cikin sa ba, idan aka taɓa masa shine yake kuka”. Taƙarishe maganar tana girgiza yaron bayan ta buɗe wajen ta gani

Sosai Rayyan yaji tausayin yaron ganin girman ƙulun dake cikin sa, sai ya kalli Suhaib yace, “Dude menene wannan ɗin? Ya akayi baku nema masa magani ba?”

       Farida juyawa tayi ta wuce ɗaki don ta rarrashe shi.

     Nan Suhaib ya sanar masa da halin da ake ciki, kafin ya ƙara da faɗa masa “sun samu DOCTOR a India zasu je can ya duba sa”.

Numfashi Ray yasaki a hankali yana jinjina kansa, sai kuma yayi masa addu’an samun lafiya yana sake nuna tausayin sa.

     Daga nan sun ɗan taɓa hira kafin shi Rayyan ɗin ya tashi, yace masa “zai je Barrack ɗin su”

Tare suka tashi suka fita bayan sun ɗaura alwala a Toilet ɗin parlour’n, sai da suka yi sallah suka komo gidan kafin drever ya ɗauki Rayyan zuwa Barrack, Kasancewar daga can zai taho da motar sa that’s why drever zai kai shi.

🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐

      Ƙarfe 05:00pm. RAUDHA tashigo gida agajiye, yau Lecture ɗaya suka yi a school ɗin, sai suka fantsama yawo da su Rash, bata dawo ba sai yanzu, tana shiga wanka tasoma yi, ta saka Biri da wando mara hannu kalan sararin samaniya, sai ta ɗaure gashin ta da Ribom baƙi ta saka room Slippers me kamar Socks, ta sauko ƙasa

Abinci ta ɗibo ta zauna gefen yayan ta dake aiki cikin Lapton, tana ci suna taɓa hira duk da shine ke maganar, ita iyakan sauraron sa take yi tana saka loma.

      Bayan ta gama ajiye Plate ɗin tayi saman Centre table, ta ɗauki Remote tare da gyara zaman ta ta ɗaura ƙafafu saman kujeran, sannan tasoma sanja channels, idan tasaka wannan be mata ba, sai ta sauya da wannan, ahaka har ta samo tashan da ake yin wrestling, tunda yau Monday ne sai dare MBC Action zasu yi.

“Yaya wai ina baƙon da kace zamu yi?” Tayi maganar idanun ta na kan t.v

Shima batare da ya ɗago kansa ba ya bata amsan “ya fita zuwa Barrack ɗin su”.

Be fi kamar minti goma da maganar nasu ba, Rayyan yadawo shima.

      Yana shigowa parlour’n, RAUDHA tayi zumbur ta tashi tamkar ta ga abun tsoro

Hakan yasa Suhaib ya kalle ta da mamaki, sai kuma ya maida idanun sa kan Rayyan ɗin da take kallo

Yana takowa cikin parlour’n ne shima idanun sa kan ta, zuciyar sa cike fall da mamakin ganin ta anan ɗin, domin dai bazai taɓa manta ta ba a rayuwan sa, yanda ya santa a baya haka take har yanzu, sai dai raman da yake kallo a kyakkyawar fuskar ta

Bakin ta na rawa tace, “You..”. Sai kuma ta datse bakin tana ƙara ware idanun ta kan shi

“Ikon Allah! Baby kin san shi ne?” Cewar Suhaib yana kallon ta fuskar sa cike da fara’a

“Yaya kar dai ace shi ne abokin ka da zai zauna tare damu?”

Ad

_____

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Related Articles

Back to top button