RAUDHA 1-END

RAUDHA Page 41 to 50

Dariya Suhaib ya saki yana ƙara ba shi hannu suka cafe yace, “gaskiya ka kyauta, Daddy zai yi farin ciki da zuwan ka, to ya Uncle da Ammee, da su Faruk?”

“Alhmadulillah duk suna gaishe ku, akwai babban surprise ma, but bazan sanar maka ba sai muna gaban Daddy”.

Murmushi Suhaib yayi yace, “ok mu je to, mun tsaya a nan”.

Jan hannun sa yayi suka nufi cikin gidan. Har sun kusa ƙarisa wa wajen taron sai wayan Rayyan tayi ƙara, ogan sa ke kiran sa don haka yace ma Suhaib “yayi gaba zai zo”. Wayan ya ɗauka suka soma magana. Daga inda yake yana hango taron mutanen, inda fitilu masu haske suka haske wajen, kasancewar duhun magriba ta gabato, a time ɗin ma shirin tashi suke yi.

      Yana gama wayan sai ya nufi wajen, a time ɗin har wasu sun soma barin wajen sabida an gama.

     Tuni itama RAUDHA taja hannun Ramcy sun shige gida.

     While su Daddy sun tsaya suna sallama da mutane.

    Ƙarisawa Rayyan yayi wajen Suhaib.

            ????????????

     Kai tsaye ɗakin RAUDHA dake sama suka wuce, anan suka zube kan kujera kowa na faɗan gajiyan da ya sha, sai kuma Ramcy ta tashi tana faɗin, “oh na bar su Aunty Nafeesa a waje, kuma sun ce min tafiya za su yi, ina zuwa bari inje”.

RAUDHA tace, “miƙo min wayan ki, but kar su tafi yanzu zan sauko sai mu gaisa, in yaso drever ya mayar da su, but ke nan zaki kwana ko?”

Dariya Ramcy tayi tana zaro ido, “No ai nima tafiya zan yi zuwa anjima kaɗan, sabida Baba na gari kuma sai da yayi min gargaɗin in dawo, ina tunanin ma zamu tafi tare kawai da su ne”.

“Ok mu je to sai mu yi sallama”. cewar RAUDHA tana miƙe wa tare da wayan ta dana Ramcy dake hannun ta

Ramcy kuma ɗaukar jakan ta tayi suka fice.

     RAUDHA tafiya take yi tana latsa wayoyin, kasancewar tana son tura pictures and videos ɗin da Ramcy tayi mata ne a wayan ta, kuma tana son tura wa *Ƙalby* a yanzu ɗin.

    Sai da suka fita waje, kafin suka haɗu da su Amarya da Aunty Nafeesa suna shirin shigowa

Anan RAUDHA tayi musu godiya sosai, inda tasaka masu aiki suka kwaso musu kayan party ɗin. har wajen motan da za’a tafi da su ta raka su, kasancewar gaba ɗaya an gama watse wa, wasu sun wuce masallaci.

       Su sun shiga mota, ita kuma ta tsaya da Ramcy suna ɗan Surutu, har sanda ta gama tura wa kafin ta miƙa mata wayan. Sai da ta jira suka tafi tana ɗaga musu hannu kafin ta juyo cikin gidan. Da ɗan tazara tafiyan, ahankali take taka wa tana latsa wayan ta, inda take karanta text ɗin da Ƙalbyn ta ya turo mata, tana sakin murmushi cike da nishaɗi, har sanda ta iso cikin gidan, ta hau Lifter ya wuce da ita sama. ɗakin ta takoma ta shiga Toilet tayi wanka kafin ta ɗauro alwala, kayan ta ta saka farar less mara nauyi tamkar yadi, doguwar riga akayi mata fitet amma me guntun hannu, sai ta tufke gashin ta ta saka hula Robber ja, ta ɗaura Hijab tayi Sallah, sai da ta gama ta cire ta ɗauki wayan ta tafito parlour’n sama, anan ta haɗu da Farida da yaran ta tana buɗe musu Chocolates suna sha

“My guys how far?” RAUDHA tayi maganar tana murmushi bayan da ta ƙariso wajen su

Nan suka tashi suka nufo ta, sai ta soma ba ma Abdul hannu suka cafe, sai kuma ta miƙa wa Haneep da ya miƙo mata nasa yana dariya da zilalar da yawu

Murmushi tayi ta saka nata hannun cikin nasa, sannan ta sumbaci goshin sa ta ce, “My Daddy , I love you so much”.

Washe baki yayi cike da murna, cikin muryan sa da ba ya fita maganar sosai ya ce, “I lobi u Baby”.

Shima wai yayi irin na Suhaib da yake kiran ta Baby

Sai suka saka mishi dariya daga ita har Farida dake kallon su

“Wow My Daddy wa ya koya maka faɗan suna na?”

Abdul yayi saurin cewa, “Aunty ai yaji Daddy na faɗa miki ne, kuma yanzu yace mu kira ki, sai ya ce miki i love You Baby, shi ne shima ya faɗa, but be iya sanar da ke sauran ba”.

Murmushi RAUDHA tayi ta shafa kan Abdul tana faɗin, “kai kuma me wayau ga shi ka faɗa”.

Ya washe baki yana tsalle

Still murmushin tayi; tayi musu peck a kumatu, sanan ta shafa kansu, ta miƙe tana kallon Farida tace, “Aunty bari in zo”.

Tashi za su yi su bi ta, sai Farida ta riƙe su tana ce musu “su zo ta gama ɓare musu biscuits and Chocolates ɗin”.

    RAUDHA tuni ta bar wurin, ta Steps ta nufi ƙasa, a hawa na biyu ta tsaya ta shiga parlour’n don duba Daddy, don tasan baza su wuce suna nan ba dukan su. Tana shiga wani ƙamshi ya doki hancin ta, lumshe ido tayi tana buɗe wa, tabbas kamar ta taɓa sanin me turaren nan, kamar ta taɓa jin sa a wani waje, amma aina? Wurga idanu ta soma yi cikin parlour’n. Can ta hangi mutum saman kujera, sai dai bayan sa take hanga tunda kujeran da ya zauna a kai ya juya wa ƙofa baya ne

Kamar ta wuce sai kuma wani zuciyan nata ya bata umarnin zuwa ta ga ko waye, domin dai tana ji a ranta ta san koma waye ne, kuma farin sani tunda turaren sa ya tabbatar mata da hakan, amma kuma ta kasa tuna inda ta sani. Takowa tayi ta nufo wajen

Kasancewar bata da takalmi a ƙafafuwan ta sai Socks, shiyasa Rayyan be San da zuwan ta ba, ya ƙuƙe sai kallon zafafan hotunan ta da ta turo masa yake yi, yana zuba murmushi

Gab ta kusa isa wajen, inda ƙiris ya rage ta hangi abinda yake yi a wayan, sai ya juyo da sauri, sabida ajikin sa sai da yaji kamar da mutum a wajen, kuma take yaji ƙamshin turaren ta ya bugi hancin sa.

    Haɗa idon da suka yi, sai ta tsaya cakkk tana bin sa da kallo, ƙure sa da idanu kawai tayi ta kasa tunanin komi

Haka zalika shima idanun ya zuba mata, yana kallon ta cike da tsantsan ƙauna a idanun nasa, tare da tsatsan kewar ta gami da muradin ta cikin ransa. Komi nata ya sauya fiye da Da, ta sake girma da tsananin kyau.

[3/23, 3:29 PM] نفيسة أم طاهرة: ????????????????????????????????????????

????????????????????

????????????????????

   *RAUDHA*

????????????????????

????????????????????

????????????????????????????????????????

*MALLAKAR:* ✍️

              _Nafisat Isma’il_

*بسم الله الرحمن الرحيم*

 

*FEENAH WRITER’S ASSO*????

“`®Ɗaya tamkar da Dubu????✓“`

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattapad: UmmuDahirah*????

         *F.W.A????/*

 

*SHAR’ANTATTUN SALLOLI*

        “`A dukan mazhabobi sallolin da aka shar’anta sun kasu kashi biyu ne, farilla da nafila. Amma shi kuwa Abu Hanifa ya ce uku ne: farilla, wajiba da nafila. Ita farilla ɗin ta kasu biyu.

_1. Farlu aini._ Wannan ita ce sallar da take kama baligi kansa, ba wani da zai iya ɗauke masa yinta, kamar dai su sallolin nan biyar da sallar juma’a.

_2. Farlu kifaya._ Ita ce sallar da take kama baligi, amma idan wani ɓangare na mutane suka yi ta, ta faɗi ga sauran jama’a, misali sallar jana’iza. Idan sashin mutane kuwa ba su yi ba, jama’a duk sun yi laifi.

      A mazhabar Abu Hanifa wajibi kashi biyu ne:

_1. Wajibi don kansa-_ watau abin da wajabcin sa bai dogara akan wani abu daban ba, kamar sallar wuturi da sallar idi da sujadar tilawa.

_2. Wajibi don wani abu-_ wannan shi ne abin da wajabcin sa yake dogara ga wani abu daban, kamar sujadar rafkannuwa da raka’o’in ɗawafi da bakantacciyar sallah da ramakon sallah wadda ta ɓaci. Watau, sujadar rafkannuwa ba ta wajaba sai don rafkanar wani abu a cikin sallah. Su kuma raka’o’in ɗawafi ba sa wajaba sai don ɗawafi, bakantacciyar sallah ma ta wajaba ne saboda bakance. Ita nafila kuwa ramakon ta bai zama farilla ba sai da ɓacin tun farko.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button