RAUDHA 1-END

RAUDHA Page 41 to 50

Daga Zulain har Sharif kallon ta kawai suke yi, babu wanda yake jin abinda take faɗa kasancewar ta juya harshe zuwa larabci ganin suna kallon ta. Zulain in ban da Hello ɗin da tace ba ya jin komi, haka shima Sharif, gwara shima Ƙalby ɗin da ta faɗa ya gane me take nufi, a ransa ya ce, “lallai kam! wannan yarinya anya ba mu kawo kan mu inda za’a wulaƙanta mu ba?” (A raina na ce da sauƙi dai Sharif, da abaya kazo ina tunanin baza a baka wurin zama ba bare a kalle ka na arziƙi, ko ba haka ba Fans?????)

Duk abinda take yi sosai take ƙara shigan zuciyan Zulain, be taɓa ganin yarinyan da ta burge shi irin ta ba, duk da kasancewar sa bature amma wayewar ta sosai ya burge sa, ba ta da maraba da su. Be dena tunanin ba har sanda ta gama wayan

Ta kalle su tana faɗin, “afuwan na tsai da ku ko? I’m sorry”.

“No problem Cuty, girman ki ne ai”. Zulain ya faɗa yana murmushi

Itama murmushin tayi idanun ta akansa tace, “ok me ke tafe da ku?”

“Soyayya”. Cewar Zulain still yana murmusawa

Ɗan waro ido tayi, sai dai bata kai ga magana ba yaci gaba da faɗa mata yanda ya kamu da tsananin ƙaunar ta, ko kaɗan babu ɓoye-ɓoye a lamarin shi, tunda dama su turawa ba kunya suka cika ba

Har ya dire maganar shi RAUDHA kallon shi take yi, a rayuwan da tayi a Madina ta samu mutanen da suka sha sanar mata suna ƙaunar ta, sai dai yanda ta ƙi ba su dama ne, yasa dole suka haƙura. tuni Ƙalby ɗin ta ya sace mata zuciya, kuma ba ta tunanin koda da wasa zata iya haɗa soyayyar shi da wani, duk da tana ganin waɗanda suka burge ta matuƙa, musamman ma yanzu Zulain ɗin nan, sosai taji a ranta yayi mata, ya haɗa komi ne wanda ɗiya mace idan ta ganshi dole ta so shi…

    Shigowar Daddy da sallaman shi, shi ne ya katse musu gaba ɗaya tunanin su, wanda Zulain da Sharif sun tsaya ne su ji amsar da zata ba su, yayinda ita kuma ta faɗa kogin tunani

Miƙe wa gaba ɗaya suka yi har RAUDHA, su Sharif suna masa sannu da zuwa

Sai a time ɗin ne ma ya gane su, nan da nan ya washe baki yana faɗin, “a’ahh ku ne ashe? Sharif and Zulain ko?”

Murmushi suka yi suna amsa mishi da “Eh”.

“To ku zauna mana, Sannun ku da zuwa”.

Zama suka yi kamar yanda ya ba su umarni, shima ya zauna akan sofa, inda itama RAUDHA ta koma ta zauna

“My daughter ko wajen ki suka zo ne?” Daddy ya tambaye ta yana murmusa wa

“Na’am Daddy”. Ta amsa mishi tana murmushi

“Ok Masha Allah, bari in Baku waje to?” Yayi maganar da fara’a yana shirin tashi

Sai ta langaɓe kai tana cewa, “Daddy da ma kayi zaman ka”.

“No daughter, KU dai gama maganar ku, in ya so sai ki kira Ni daga baya mu gaisa sosai”.

Gyaɗa masa kai kawai tayi, shi kuma ya wuce ciki.

     Kallon su tayi tace, “ku daure ku ci wani abun mana, ga shi baku taɓa komi ba?”

Murmushi Zulain yayi yace, “no ba ma buƙatar komi ɗin ne a yanzu, illa amsar ki, ki daure ki sanar da Ni abinda ke zuciyar ki ko da nima tawa zuciyar zata samu sukuni daga zugin da ta daɗe tana min”.

Sharif Ya amshe zancen da faɗin, “Please RAUDHA, ɗan uwana na matuƙar ƙaunar ki fiye da yanda kike zato, tun haɗuwar da kuka yi a airport ya kamu da soyayyar ki. A taƙaice dai ya kasa samun sukuni tun zuwan sa ƙasan nan, sai kuma Allah yasa bazai sha wahala ba, ya haɗu dake cikin sauƙi anan gidan, ina ga Allah ya ƙulla wani alaƙa a tsakanin ku ne shiyasa har ya sake haɗa ku batare da ya sha wahala haka ba, ki duba magana ta RAUDHA, Zulain na ƙaunar ki matuƙa”.

Murmusa wa tayi sabida maganar Sharif ɗin, idanun ta a kansu tace, “eyya gaskiya ban san me zan ce muku ba yanzu, amma dai zan iya sanar muku da cewa na rigada na ba wa wani..”

Katse ta Sharif yayi da faɗin, “ba sai kin faɗa ba RAUDHA, don Allah ki dai ba wa Ɗan uwana dama ko sau ɗaya ne, ta hakan ne kaɗai zaki fahimci wanene shi, kuma zaki so shi wlh, domin shi ɗin na daban ne, ba ko wace mace take samun Sa’a wajen mallakar irin su ba”.

Wannan karon dariya RAUDHA tayi tace, “uhmmm Sharif kenan! Na ga alamu kana son ɗan uwanka da yawa ko?”

Murmushi duka suka yi

Jinjina kanta tayi tace, “amma Ni ba na so mu ja zancen da tsawo haka, ina da Masoyi na, ina son shi yana so na, so babu amfanin mu ɓata lokaci akan abinda bazai yiwu ba”.

Lumshe ido Zulain yayi, sai kuma ya buɗe akanta, cikin ido suke kallon juna ya ce, “I love You RAUDHA, bazan iya haƙura da ke ba har sanda na ga kin zama mallakin wani, ma’ana an ɗaura miki aure. Yanzu ma na soma son ki, idan har baki kore Ni ba, Ni kuma zan ci gaba da gwagwarmayan samun ki har sanda Allah zai yi ikon sa”.

Kau da kanta tayi, sai dai bata iya cewa komi ba, sai ta tashi tana faɗin, “bari in Kira muku Daddy”.

Ta juya ta tafi abun ta.

      Koda ta kira musu Daddy, ɗakin ta ta wuce bata sake bi ta kansu ba, don bata san ma sanda suka tafi ba. Sai da Daddy ya kira ta sannan ta fito, anan yake tambayar ta “me suka zo yi wajen ta?” Ta sanar mishi da komi tunda babu ƴar kunyan haka a tsakanin su

Murmushi Daddy yayi yace, “Baby in baki shawara?”

Gyaɗa masa kai tayi tana cewa, “Yes Dad”.

“Ok gaskiya yaron nan yayi matuƙar dacewa da ke, ki daure ki duba son da yake miki kar ki yi watsi da shi akan wani”.

Murmushi tayi idanun ta akan sa tace, “Daddy kai ma kasan ina da saurayi na, ban ga abinda zai saka na ɓata lokaci na kan wanda bazan taɓa son shi ba idan har Ƙalby na tare dani. So Daddy Kar ma su biyo ta hannun ka su ba ka cin hanci ka ce shi zan aura”.

Waro ido yayi yana dariya yace, “Baby?”

“Yes Daddy.” Tafaɗa tana dariya itama

Shafa kanta yayi yace, “ki dena maganar haka kin ji Baby na? Domin wanda kike so shi nima nake so, duk wanda kika kawo a matsayin Mijin ki, shi ne zai kasance Mijin ki, ba zan taɓa baki wanda ba ke ne kika kawo ba”.

Dariya tayi tana ɗaura kanta saman kafaɗan sa tace, “Daddy Nima Wasa nake maka fa”.

Hancin ta ya ja yace, “i know Baby, but yaushe ne zaki kawo min suruki na in ganshi, yakamata kema ki zo kiyi auren nan ko da nima zan soma ganin Jikoki na ta wajen ki”.

Ƙyalƙyale wa tayi da dariya tana cusa kanta a hannun sa tace, “Daddy”.

“Umm Babyn Daddy, ai gaskiya na faɗa”.

Murmushi kawai tayi bata yi magana ba

Shima sai be sake cewa komi ba ya sauya maganar suka ci gaba da hira.

[3/23, 7:48 PM] نفيسة أم طاهرة: ????????????????????????????????????????

????????????????????

????????????????????

      *RAUDHA*

????????????????????

????????????????????

????????????????????????????????????????

*MALLAKAR:* ✍️

              _Nafisat Ismail Lawal Goma._

*بسم الله الرحمن الرحيم*

 

*FEENAH WRITER’S ASSO*????

“`®Ɗaya tamkar da Dubu“`????✓

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattapad: UmmuDahirah*????

         *F.W.A????/*

*RAMADHAN MUBARAKH*????????????

                     2021.

.

  *NOT EDITED* ___________________________????

        *SEASON FORTY FOUR*

_______???? Daddy ya saka ana ta shirye-shiryen tarban iyayen Rayyan da za su zo, an gyara musu ɗakunan ƙasa da ba a amfani da su, duk wani abubuwan jin daɗi ya saka an zuba musu

Alh. Hassan da suke kiran sa da Uncle Hassan, shine Abokin Daddy. Asalin Abotan su ya fara ne sanda Daddy yayi zaman Bayelsa yin wani course, to anan suka haɗu da Uncle Hassan Wanda gaba ɗaya ahalin su sunan da suke kiran sa da shi kenan, tun yana ƙarami, kasancewar sunan Kawun sa shima ya ci, to lokacin da aka haife sa a lokacin ne Kawun nasu ya rasu, shiyasa da aka mayar da sunan Kawun shi ne suke kiran sa da Uncle Hassan kamar yanda suke kiran Kawun, har Allah yasa ya girma da sunan ake kiran sa, yanzu haka har iyalan sa duk Uncle suke kiran sa, su Rayyan ba sa kiran sa da Baba sai dai Uncle.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button