RAUDHA 1-END

RAUDHA Page 41 to 50

      Haka rayuwan taci gaba da gudana, har sanda ya nemi ta tura masa hotunan ta, sabida yana matuƙar kewar ta yana son ganin ta. Anan ne tayi masa maganar itama tana son sanin shi, tana nufin ya faɗa mata komi a kan sa. Amma sai yayi mata daɗin baki inda ya ƙi yin mata duk abinda ta buƙata. Ita dai ta tura masa pictures ɗin ta, kuma bata sake tambayan sa ba tunda ta lura ba ya son ya nuna mata kanshi ne, har ga Allah ta yarda dashi ɗari bisa ɗari, kuma tana ƙaunar sa, ta saka a ranta ko waye shi zata iya auran sa. Dama akace duk wanda be taɓa soyayya ba, idan har ya tashi yi ba ya ɗaukar ta da wasa, tabbas haka ne a wajen RAUDHA, domin mahaukacin so take yi wa Rayyan, gaba ɗaya ta ɗau yardan ta ta ba shi, a cikin duk wanda ya san ta babu wanda be san labarin sa ba, su Daddy tuni sun san da irin ƙaunar da take mishi, sun buƙaci ganin sa amma sai tace musu watarana zasu gansa kamar yanda shima yake sanar mata, itama hakan ta sanar musu, sunan sa kawai ta gaya musu, inda yace mata sunan sa Muhammad. Yayi mata alƙawari duk sanda ta gama karatun ta, idan ta dawo Nigeria za su haɗu.

         ????????????

     Shigowar Daddy ya saka RAUDHA ta ɗago kai tana kallon sa, sai kuma ta ajiye wayan tana tashi ta nufe sa tana kiran sunan sa

Tarban ta yayi yana murmushi, inda ya shafa kanta ya riƙe hannun ta suka dawo suka zauna a inda ta tashi

Anan Rayyan ya gaishe shi, ya amsa cike da fara’a yana tambayan sa aiki kafin ya ce, “nayi mamaki, wai yaushe ka shigo ƙasar?”

Dayake tuni an sake musu sauyin wajen aiki, dama shekara uku za su yi a Abuja, sai su dawo Kaduna inda anan ne dama yake aikin sa, to sun samu hutu sai ya tafi ƙasar su Bayelsa, sai yau ya dawo, kuma ya hana kansa sukuni sai da ya shigo Zaria don ganin muradin ransa.

    “Daddy yau na shigo”.

Jinjina kansa Daddy yayi yace, “Weldon Captain kana ƙoƙari wlh, ya mutanen gida, ɗazu muna magana da Mahaifinka sai kuma muka katse akan ana jiran sa, zamu yi waya anjima, kuma ka ga hidima ya mantar dani ban sake kira ba, shima be kira ba”.

Murmushi Rayyan yayi yace, “lafiya ƙalau suke, amm. Uncle babban surprise ne da shi, duk da ban yi tunanin zai sanar maka ba, ya bari zuwa Friday, Coz ranan Saturday za su shigo gaba ɗaya”.

“Haba dai? Are You serious?” Daddy ya faɗa cikin fara’a

“Yes Daddy”.

Take anan shi da Suhaib suka nuna matuƙar farin cikin su

Ita dai RAUDHA tana jin su bata ce uffan ba, sai faman taɓe baki take yi tana kallon Rayyan da shima ke kallon ta ta ƙasan ido

“Baby kina ji Uncle ɗin ku zai zo, baki taya Ni farin ciki ba?”

Yaƙe tayi tace, “Daddy I’m so happy, Allah ya kawo su lafiya”.

“Emeen Baby”.

Hira suka ci gaba da yi. Inda RAUDHA ta bar su tana ta faman latsa wayan ta, don bata san ma me suke cewa ba.

        Sai ga Farida itama ta shigo ta zauna cikin su, lokacin su Abdul duk sun barci. 

     Ba su tashi ba sai da aka kira isha’i.

     Bayan sun dawo suka yi dinner a parlour’n ƙasa, inda Rayyan yace musu zai wuce, don shi be damu da tafiyan dare ba, kasancewar sa jami’in tsaro

But Sam Daddy ya ƙi barin sa, dole yace masa sai ya kwana, in yaso washe gari sai ya tafi da wuri

Be musa masa ba kuwa, anan ɗin ya kwana, washe gari zuwa ƙarfe 08:30am. Yayi sallama da su ya tafi, ya so ganin RAUDHA sai dai be samu dama ba, domin dai tana can tana barci, kuma ba ya kyautata zaton zata iya tashi yanzu don yasan halin ta sosai.

     Sai ƙarfe 12:40am ta farka kuwa.

     Zuwa dare su ma su Suhaib suka wuce Abuja, inda suka bi jirgi.

[3/23, 7:33 PM] نفيسة أم طاهرة: ????????????????????????????????????????

????????????????????

????????????????????

   ????????????????????????

????????????????????

????????????????????

????????????????????????????????????????

????????????????????????????????: ✍️

              ???????????????????????????? ????????????????’???????? ???????????????????? ????????????????.

*بسم الله الرحمن الرحيم*

 

???????????????????????? ????????????????????????’???? ????????????????????

®Ɗ???????????? ???????????????????????? ???????? ????????????????????✓

???????????????????? ???????????????????????? ????????✍️

????????????????????????????: ????????????????????????????????????????????????

         ????.????.????????/

???????????????????????????????? ????????????????????????????????????????????

                     2021.

.

  ???????????? ???????????????????????? ___________________________????

        ???????????????????????? ???????????????????? ????????????????????

_______???? Washe gari ƙarfe 11:00am. RAUDHA ta tashi, bakin ta kawai ta wanke ta ɗauraye fuska ta fito Parlour, part ɗin Daddy ta wuce, sai dai bata same shi ba, sai ta tambayi ɗaya daga cikin ma’aikatan dake gyara Part ɗin, suka ce mata “ya fita ne”

Ɗakin ta ta koma ta ɗauki waya ta kira sa, nan yake sanar mata “ya fita, but bazai daɗe ba zai dawo”. Sake fitowa tayi da wayan a hannun ta, inda ta kira ɗaya a cikin masu aikin ta bata umarnin kawo mata Breakfast ɗin ta saman

Bata jima ba kuwa ta haɗo mata

zama tayi saman dainning tana ci tana latsa wayan ta. Kamar shuɗewar mintuna ashirin sai wata acikin masu aikin ta shigo take sanar mata tayi baƙi. maimaita kalman baƙin tayi a fili, idanun ta kan ƴar aikin, sai kuma tace, “su wane ne?”

“Ranki ya daɗe wasu samari ne su biyu”.

Shiru RAUDHA ta sake yi zuciyarta cike da mamaki, kafin kuma tace, “ok CE musu su jira Ni, ki sauke su parlour’n ƙasa”.

“To ranki ya daɗe”. Tayi maganar cikin girmamawa tana juya wa don isar da saƙon ta

RAUDHA ci gaba tayi da harkan ta, tamkar bata san jiran ta ake yi ba, sai da ta ɓata time kafin ta miƙe tsaye, wayan ta ta ɗaga tayi Selfie ???? tana turo baki gaba, sannan sai ta shiga WhatsApp ta tura wa Rayyan, a ƙasan ta rubuta, “Good morning Ƙalby, I Love you xoxoxo” ta saka emojis na love ta tura masa”.

Murmushi tayi kafin ta kama hanyan barin parlour’n, ko kaɗan bata yi tunanin sauya kayan jikin ta ba, tana sanye cikin kayan barci riga da wando masu santsi, kalan ruwan Powder, wandon Three qwater ne amma burgujeje tamkar skert, sai rigan ɗan shimi me hannun vest da kwalliyan bakin leshi a gaban, kanta da baƙin hula me raga-raga, ƙafanta kuma babu takalmi sai Socks

 

Duk da yanzu ba ta fita da irin shigan nan, amma har yanzu bata dena yin sa ba in dai a gida ne.

     Lifter ta hau ya kai ta ƙasa. Tana sauka ta shiga cikin parlour’n

Zulain da Sharif dake zaune, suka hange ta tana nufo su, sai gaba ɗayan su suka ƙura mata idanu, ko wanne a ransa yana yaba tsantsan kyan da Allah yayi mata, gaba ɗayan su ganin dirin jikin ta sai da ya tafi da duk natsuwar su. har ta iso wajen ta zauna kan sofan dake kallon su, ta ɗaura ƙafan ta ɗaya kan ɗaya tana bin su da ido, amma su gaba ɗaya hankalin su ya fita jikin su

Itama sai da ta gama ƙare musu  kallo, musamman Zulain ganin sa da tayi Bature, duk da kasancewar sa ba fari ba, domin ko kama ƙafan hasken ta be yi ba, amma kuma gashin kanshi fari ne irin na turawa, da ganin shi dai kasan Bature ne shi. Taɓe baki tayi kafin tace, “ku ne kuke nema na?”

Sai a time ɗin suka dawo hayyacin su, yayinda duka suka yi murmushi, Zulain na shirin magana wayan ta ta soma ƙara

Ɗago wayan tayi tana kallo, sai ta saki murmushi tana peacking Call ɗin ta kara a kunne, sai a time ɗin ne ta kalle su ta ɗaga musu hannu alamun tana zuwa, “Hello Ƙalby”. Tafaɗa still tana murmusawa

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button