RAUDHA 1-END

RAUDHA Page 41 to 50

     A mazhabobin maliki da shafi’i da Hambali nafila ita ce duk abin da yake ba farilla ba. Watau, abubuwan da Hanifawa suke ɗauka wajibi ne don kansu, a wurin sauran mazhabobi suna cikin sunna ko mustahabbi sabida cewa wajabcin ba don zatin su ba ne, illa dai sabuban da aka ambata.

     Ita nafila ɗin an kasa ta gida biyu:

_1. Nafila mu’akkada,_ watau wadda aka ƙarfafa sunnancin ta, kamar su sallolin idi da wuturi da raka’o’in ɗawafi, waɗanda Hanafawa suke kira wajibi.

_2. Nafila wadda ba mu’akkada ba,_ watau wadda ba a ƙarfafa sunnancin ta ba, kamar su nafilolin da ake yi gabanin azahar ko bayanta, da waɗanda ake yi gabanin la’asar da bayan magriba da kuma gabanin isha’i da bayan ta.

        Allah yasa mu dace.“`

.

  *NOT EDITED* ___________________________????

        *SEASON FORTY TWO*

_______???? Yanda take jin wani iri da kallon ƙwayar idanun sa, hakan yasa tayi saurin ɗauke kai daga kallon sa, a lokaci ɗaya ta taɓe baki don bata yi tunanin shi ɗin zata gani ba, tun barin ta Abuja rabon ta da shi, sabida koda ya zo Hospital gaishe ta sanda tana jinya, ba ta sanin kowa. Sosai ya sauya mata fiye da tunanin ta, ba don ta sanshi sosai ba baza ta iya gane sa ba, ya sake ƙiba da ya ƙara masa kyau matuƙa, ga haske da ya sake wanda kowa ya kalle sa zai san hutu ya zauna masa, ya sha aski da yayi masa kyau ya sake fito da shi, kasancewar ba hula a kansa, yana sanye cikin faran gezna shara-shara, har Singlet ɗin da ya saka a ciki ana gani. Yanzu bata san meyasa ba, kaso sittin a cikin ɗari na daga tsanar da tayi masa a baya, yanzu kuma sai taji babu shi, ya ragu sosai.

   Juya wa tayi zata bar wajen, sai ta tsinkayi muryan sa da yasa ta sake tsaya wa cakk, zuciyarta ta na wani irin bugawa da ƙarfi, sakamakon sunan da ya kira ta da shi. Dasauri ta juyo tana kallon sa

Shima idanun sa akanta suke, sai ya saki murmushi ya sake cewa, “pretty babu gaisuwa?”

Waro idanuwan ta waje tayi, sosai zuciyar ta take tsananin bugawa a yanzu ɗin, domin kuwa the same sunan da Ƙalby ɗin ta yake kiran ta da shi ne, ita in ba ma makuwa tayi ba, muryan sa na mata shige da muryan sa. Ji take yi tamkar tace ya sake maimaita sunan, sai kuma tayi dauriya tana kau da idanun ta daga kallon sa, ta sake juya wa tayi hanyar ɗakin Daddy.

     Da kallo Ray ya bi ta da shi, yasan sarai abinda ke cikin ranta, don haka tuni ya saki murmushi zuciyar sa cike da farin ciki.

     Har ta kusa ƙule wa, sai Suhaib da ya shigo yanzu ya kira sunan ta. juyo wa tayi tana kallon sa, sai kuma ta tako tana faɗin, “Yaya ina kuka shiga, ina neman ku? An ce kaima kana nema na”.

“Eh Baby, dama Dude ne ya zo musamman don taya ki murna, shine na ce bari in Kira ki ku gaisa. Dude ga Baby ɗin; ko kun gaisa?” Suhaib ya sauya akalan tambayar nasa ga Rayyan yana kallon sa

“Yaya mun gaisa”. RAUDHA tayi saurin faɗar maganar idanun ta kan Suhaib tana murmushi, tana juya wayan hannun ta

Murmushi shima yayi ya ce, “ok mu je mu zauna to, yanzu Daddy zai shigo ya sauka downstairs raka baƙin da yayi ne”.

Gyaɗa kanta tayi, suka nufi inda Rayyan ke zaune, Suhaib ya zauna gefen sa, ita kuma ta zauna can kujeran dake kallon nasu, zata yi magana kenan taji shigowar message a wayan ta, ɗagowa tayi tana karanta wa

         _”Pretty kin Yi matuƙar kyau fiye da ko yaushe, har kin saka naji na ƙosa na mallake ki a matsayin matata, wlh pretty ina son ki, ƙaunar ki zai zauta Ni, ji nake yi kullum kamar ana ƙara min wutan ƙaunar ki a raina, I love You so Much my pretty”._

     Murmushi kawai take zuba wa, sabida sosai message ɗin yayi mata daɗi. Itama sai ta soma typing don mayar masa da reply.

      Ray dake hira da Suhaib, hankalin sa na gare ta, ta ƙasan ido yake kallon ta, ta yanda babu wanda zai fahimci yana kallon ta.

         Tun tafiyan ta ƙasar Madina, hankalin Rayyan ya tashi matuƙa, gani yake yi gaba ɗaya ya gama rasa ta, shi da yake burin da zaran ta samu lafiya, ya bayyana mata ƙaunar da yake mata, sai gashi wai zata tafi karatu, hakan ya saka sa damuwa tsantsa. Haka ya danne wa ransa yaci gaba da al’amuran sa, sai dai ya rasa ta ya ya zai samu gana wa da ita ko da ta waya ne kamar yanda yake tura mata saƙo, tunda tuni ta dena amfani da wayan ta, anan Abuja ma ta bar shi, kuma da ta tashi tafiya sai dai aka siya mata wani, ga shi ba shi da Numban ta, ya rasa ya zai yi ya samu, ba ya son tambayan Suhaib kar ya zargi wani abu.

     Ahaka dai Allah ya basa Sa’a, inda watarana suna zaune suna hira da Suhaib ɗin, ya ce “ya ara masa wayan sa zai tura wani abu” to anan ne ya lalubo Numban ta na can yayi saurin kofe wa.

      Tun daga ranan Ya samu damar waya da ita, da fari text ya soma tura mata, ita kuma lokacin da ta gani, ta sha mamaki kasancewar yayi mata bayanin shine Masoyin ta da ke tura mata text a baya. Ta so ta share sa, sai kuma mamakin abun ya ƙi barin ta, tambayan da ta soma masa, “shin aina ya ƙara samun Numban ta? Kuma taya ya san ba ta ƙasar Nigeria?”

Shi kuma be bayyana mata komi ba, sai ya ce mata “duk inda take a faɗin duniya, idan har yana numfashi, to tabbas sai ya lalubo ta, ƙaunar da yake mata ya wuce tunanin ta”.

Hakan sai ya saka ta shiga tunani tsantsa, tana tunanin shin wanene shi? Aina ya santa? Tunani kala-kala take yi a kansa. Kuma tun daga ranan bata sake mishi reply ba, duk da kuwa tana karanta saƙon sa, sosai yake saka ta tunani duk idan ta gama karanta saƙon sa, sabida kalaman sa ba ƙaramin taɓa mata zuciya yake yi ba, da haka ya soma kiran ta wai “yana son jin muryan ta”. Tun bata ɗauka, har dai ta soma ɗauka, inda ta sha mamaki, domin kuwa muryan sa sak yayi mata kama da wanda ta sani, sai dai ta rasa aina? Koda wasa bata taɓa kawo cewa Captain Rayyan bane, to taya ma zata yi tunanin hakan bayan ta san ba sa shiri, ya tsane ta itama ta tsane shi, ita ta manta da shi ma tuni.

     Haka rayuwan taci gaba, inda Rayyan be ƙasa a gwiwa ba wajen yin nasaran sace zuciyar RAUDHA, sai dai fa ya sha matuƙar wahala, domin sai da ya dage da gaske, da jure duk wani wulaƙanci nata kafin yaci nasara, don da farko ma har block ɗin sa ta koma take yi, sai ya sauya sim ya sake neman ta. Sosai take mamakin naci irin na mutumin da bata ma sanshi ba.

     Kusan shekaru biyu da zuwan ta ƙasan, sannan ta amince ta karɓi soyayyar shi, don tuni ta saba dashi fiye da tunanin mutum, tabbas RAUDHA tana da wuyan sha’ani, babu wanda yake iya shiga jikin ta ta daɗi, tana da wuyan sabo, idan kuma ta saba da kai, tana baka yardan ta ne ɗari bisa ɗari, idan tace tana sonka, to tana son ka ne har cikin zuciyar ta.

  Sun saba sosai matuƙa, koda yaushe suna tare maƙale a waya ko a chart, idan tana school zata ijiye duk wani soyayyar sa a gefe, shima haka idan yana aiki be cika takura mata ba, ahaka dai rayuwan taci gaba, inda sosai RAUDHA ta tsunduma a soyayyar Rayyan batare da ta san waye shi ba, kuma bata taɓa tambayan sa don ta sani ba, ba wai don ba ta son sani ba, a’a, sai don shi be bayyana mata kansa ba, ita kuma jan aji da miskilanci irin nata, ya hana ta tambayan sa, musamman ya buɗe sabon account na facebook suke charting, ko su yi a WhatsApp da Numban sa personal, Wanda don ita kaɗai yake amfani da shi, ko kuma su yi ta inbox message.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button