RAUDHA Page 41 to 50

Kasancewar Daddy yana yawan zuwa gidan su Uncle Hassan, anan kusa da gidan su ya haɗu da mahaifiyar su RAUDHA, suna maƙotaka ne da gidan su Uncle Hassan, inda babu ɓata lokaci soyayya me ƙarfi ya shiga tsakanin su, koda ya tashi aure sai Allah yasa ita ɗin rabon sa ne, a time ɗin iyayen sa suna raye, har can suka je nema masa auren Ruƙayyah, inda aka ba shi babu wani ja’inja
Anan Zaria suka soma zama, cikin ƙofan doka, Allah da ikon sa rayuwa taci gaba da gudana, inda a gefe ɗaya suna Abotan su sosai da Uncle Hassan, shima be daɗe ba yayi aure a can Bayelsa
Babu jima wa Matan nasu suka haihu a tare, inda yaran suka ci sunan Rayyan da Suhaib. Haka rayuwa taci gaba da gudana, Ruƙayya dai bata sake haihuwa ba, sai matar Uncle Hassan Hansa’u da ta haifi Umar Faruk, suna kiran sa da Faruk tunda sunan mahaifin ta ne, wani lokacin kuma su kira sa da Abba, daga shi kuma sai Usman da suke kiran sa da Zannurain, sai kuma Abubakar autan su, shi ne sa’an RAUDHA, an haife shi babu daɗe wa aka haifi RAUDHA, shekarun ta biyar a duniya Ruƙayya ta rasu a wajen haihuwar ƙanwar ta, lokacin tana cikin naƙuda, domin har ta kusa haihuwa, da ita da abun da ke cikin ta gaba ɗaya suka koma ga Allah saboda ta sha wahala a lokacin. Wannan dalilin ne Daddy da Suhaib suka ɗauki son duniya suka aza wa RAUDHA, ga tsaban tausayin ta da suke ji.
????????????
Drever yaje ya ɗauko su a airport sanda suka sauka, suna iso wa Uncle da Daddy suka rungume juna, ko wannen su cike da farin cikin ganin Abokin sa, domin sun jima rabon da su haɗu sai yanzu, shiyasa Uncle Hassan ya shirya zuwa gaba ɗaya har iyalan sa
Sai da suka daɗe suna gaisa wa cike da barkwanci kafin suka samu wuri suka zauna, inda su Faruk ɗaya bayan ɗaya suka hau gaishe shi. Ya amsa musu cike da fara’a yana tambayan su school da aikin su. Sannan suka gaisa da Ammee cikin mutunci
Uncle ne ya soma tambayan RAUDHA, kasancewar shi kaɗai ya san ta, ita kanta Ammee tun tana yarinya rabon da ta sake ganin ta
Daddy na murmushi yace, “yanzun nan zata dawo, ta je gidan ƙawar ta ne (Ramcy)”.
“To Masha Allah, Allah ya dawo da ita lafiya”.
“Ameen ameen”. Daddy yafaɗa still yana murmusa wa. sai kuma ya kalli su Faruk ya ce, “Abba sai kuma ga ku a Nigeria ko?”
Dariya suka yi gaba ɗaya, inda Abubakar yayi tsalan ɗin cewa, “wlh kuwa Daddy, wannan shi ne zuwa ta na farko ƙasar ku, ashe dai yana da daɗi”.
Daddy dariya yayi yace, “sosai ma Habu, ai zan sa a zaga da ku zaku fi jin daɗin garin sosai”.
Duka suka yi dariya
“Ya kamata Ku yi wanka ku huta, bari in saka a nuna muku masaukin ku”. Daddy ya faɗa yana kallon su da murmushi
Gyaɗa masa kai suka yi, don su ma sun fi buƙatar hakan
Daddy da kansa ya nuna musu, be ma bari an nuna musu ba, har Ammee itama ɗaki ta wuce, inda Daddy ya dawo suka ci gaba da hira da Uncle suna ta dariya, babu abinda suke yi sai tuna baya, idan sun tuno abinda yayi musu daɗi da ba su dariya har kashe hannu suke yi.
A lokacin ne RAUDHA ta shigo gidan
Daddy na ganin ta yace, “yauwa Baby kin ga har su Uncle ɗin ki sun ƙariso baki dawo ba, sai tambayan ki yake yi”.
“My daughter ƙariso mana”. Uncle yafaɗa yana nuna mata kusa da shi
Da murmushi a fuskar ta ta ƙariso wajen sa ta zauna, sannan ta gaishe sa cikin mutunci sosai
Hakan sai ya faranta ran sa, ya saka hannu a kanta yana shafa wa ya ce, “Allah ya miki albarka my daughter”.
“Ameen Uncle”.
Murmushi yayi yace, “kin girma sosai my daughter, rabo na da ke tun kina ƙarama, amma kuma kina nan a yanda kike, domin ko aina na ganki sai na shaida wannan ɗiya ta ce”.
Dariya suka yi daga ita har su ɗin
Anan ne itama Ammee ta fito, ta ƙariso ta zauna idanun ta akan RAUDHA da itama take kallon ta
Kafin ma tayi magana RAUDHA tayi ƙoƙarin gaishe ta, sabida ba ƙaramin kamannin Rayyan ta gani a tare da ita ba, kamar an tsaga kara, wannan dalilin ne yasa ta gane mahaifiyar shi ce
Cikin fara’a Ammee ta amsa ta tana cewa, “taho nan kusa dani mana ɗiya ta in ji ɗumin ki”.
Taso wa tayi tana murmushi ta dawo kusa da ita, sosai taji farin ciki da wannan ƙauna da iyayen Rayyan suka nuna mata, har sai da ta tuno sa, a ranta tana cewa, “shi kuwa be da kirki kamar su, ko wa ya biyo oho masa”.
Anan ne su ma su Faruk duk suka fito, inda Daddy duk ya gabatar mata da sunayen su
Farin ciki duk ya cika RAUDHA, musamman da tagan su har su uku, sai ta washe baki ta soma ba ma Abubakar hannu wai su gaisa
Sai hakan gaba ɗaya ya burge su har su Ammee, duka suka saki murmushi
Abubakar kuwa hannun ya miƙa mata yana dariya yace, “Abubakar Sadiq your friend”.
Gyaɗa kanta tayi tana sake washe baki tace, “ana RAUDHA”
Duk dariya suka sake yi
Sai shima Zannurain ya miƙo mata hannu yana dariya yace, “Ni dai ba friend ɗin ki bane, Yayan ki ne, Ki kira Ni Bro Zannu”.
Kasancewar yayi maganar ne cikin barkwanci, duk sai suka yi dariya gaba ɗaya
“Bro Zannu”. Itama ta faɗa cikin dishewar muryan ta me daɗi tana murmushi, sannan sai kuma ta kalli Faruk dake tsaye ya harɗe hannayen sa yana kallon ta yana murmushi. Sosai gaban ta ya faɗi sabida ganin kamannin su ɗaya da Ray, har ta Yi tunanin ko shi ne, sai taga kuma wannan be kai shi haske ba, sannan be da jiki kamar shi, Faruk siriri ne sosai
Hannu ta miƙa masa tana murmushi
Sai ya saka nashi shima yana murmushin yace, “kina lafiya?”.
“Ana bikhair.. ant?” Tayi maganar idanun ta a kansa tana ci gaba da murmushin ta me kyau
“Ana jayyidan”.
Dainning suka wuce gaba ɗaya suka ci abinci, ita dai RAUDHA ba ci take yi ba tana zaune gefen Abubakar suna zuba surutu, sai dariya take yi
Cike da nishaɗi haka suka kasance a ranan har yamma, anan ne RAUDHA taja hannun Abubakar suka nufi bayan gidan, inda anan ne aka saka basketball, da kuma abubuwan Game dai kala-kala
Tare suka soma ƙwallon suna ta dariya, fara wa da iya wa har ya ci ta biyu, nan ta saka mishi rigima wai bata yarda ba
Sai kawai ya faɗi ƙasa yana ta mata dariya, shi kawai dariya ta bashi sabida yanda take shagwaɓan ta tamkar yarinya, baza ka taɓa tunanin ƴar shekara 24 bane
Kaɗa kai tayi, ta zuƙuna ta soma kanannaɗe farar wandon ta, sai ta kama gashin ta ta sake ɗaure shi da kyau, ta tashi tana tsalle tace, “to taso mu ci gaba, yanzu sai na sa ka kayi kuka”.
Dariya ya sake kwashe wa dashi.
Daga nesa Faruk na tsaye yana kallon ta yana murmushi, gaba ɗaya RAUDHA ta gama tafiya da imanin sa, salon ta da komi nata burge sa yake yi, yana nan yana kallon yanda suke ƙwallon, duk RAUDHA bata iya ba amma ta dage sai ta ci Abubakar, shi kuma sai saka mata ƙwallo yake yi ta kasa cin ko guda ɗaya, duk ta gama gajiya sai nishi take yi, don daƙyar take gudu ma
Kamar ance ta kalli inda yake tsaye, ta hange shi kuwa ya kafa mata idanu, da gudu ta nufe sa ta ƙariso wajen sa tana nishi, idanun ta a kansa tace, “Plz Brother taimaka min in ci shi, wlh wayau yake ta min duk ya gajiyar dani”.
Dariya maganar nata ya ba shi, wai wayau yake mata, bayan bata iya bane
“Kaji?”. Tayi maganar tana riƙe masa hannu
Murmushi yayi yace, “wa yace miki na iya? Nima irin ki ne ai”.
Langaɓe kai tayi kamar zata yi kuka
Zannurain ne ya ƙariso wajen yana tambayan me ke faruwa
“Yauwa Dear Zannu, zo mu je ka taya Ni cin Friend, ka ga sai cinye ni yake yi”.