RAUDHA 1-END

RAUDHA Page 41 to 50

“Ok mu je”. Zannurain yafaɗa yana yin gaba tare da kanannaɗe hannun rigan sa

Faruk dai yana tsaye yana kallon su har sanda suka tashi wasan, sannan ya juya ya bar wajen.

         ????????????

      Washe gari wajen ƙarfe 10:30am sai ga Suhaib ya zo shi kaɗai, lokacin RAUDHA da Abubakar da Zannurain sun fita zaga gari, sai Faruk ne da be bi su ba, time ɗin ma barci yake yi

Uncle rungume Suhaib yayi kafin suka gaisa, ya soma tambayan sa iyalan sa

Yace, “suna gida, sun ce in gaishe ku sosai”. Sannan ya gaishe da Ammee

Ta’amsa cike da fara’a itama tana tambayan sa iyalan, sannan tace, “meyasaka baka zo da su ba?”

Shafa kansa yayi yace, “babu komi wlh, nima na zo ganin ku ne ai”.

“Ka kyauta ai, amma su ma da kazo da su mun ga juna, tunda ba daɗe wa za mu yi ba, kuma idan mun tafi ba kawo mana su zaka yi har Bayelsa ba”. Ammee tafaɗa hakan da fara’a

“Haka ne Ammee, ban yi tunanin hakan ba wlh”.

Daga nan hira suka ɗan taɓa, inda Suhaib yake tambayan “ina su Faruk?”

Kafin ma su ba shi amsa, Faruk ya fito daga ɗaki

Ammee tace, “ga Faruk ɗin nan ya fito, su kuma sauran sun fita da RAUDHA”.

Faruk gaishe shi yayi, inda ya amsa mishi yana tsokanar sa da faɗin, “har da kai ƙaton kawai aka zo da kai?”

Dariya Faruk yayi yana shafa kansa yace, “ai ban wuce zuwa anguwa ba Yaya Suhaib”.

“Eh naga alama, amma ai ka isa ajiye mata, har yanzu shiru da kai da Dude”.

Uncle yace, “bar su Suhaib, ai na san maganin su, ina gajiya nima auren zan yi musu, ka ga wannan ƙiri-ƙiri ga matar sa a gida, amma har yanzu sai kwana-kwana yake mana, kuma shi ya amsa yana son ta, amma yanzu kuma yana son Wai ya koma karatu ne, abun dai da yaga ɗan uwansa nayi shine shima yake son yayi. Ko sha’awar ka ɗan uwan (yana nufin Rayyan) ba ya ji, ga ka har ka tara iyalan ka gunin sha’awa”.

Daddy na murmushi yace, “ai komi nufin Allah ne, wata rana sai labari, idan lokaci yayi za su yi”.

Uncle sauya maganar yayi suka ci gaba da hiran su, inda Ammee ta tashi ta koma ciki, dama gaisa wa da Suhaib ya fito da ita. Su kuma Suhaib da Faruk suka fita waje suna zanta wa.

    A lokacin ne su RAUDHA suka dawo, duk suka nufi wajen su

RAUDHA rungume sa tayi tana murnan ganin sa, tace, “Yaya ina su Daddy na?”

“Suna gida ban zo da su ba”.

Buga ƙafa ta soma yi tana mishi rigima

Abubakar ya dunguri kanta yace, “ke dai kin cika rigima wlh, ki bari mu gama gaisa wa mana, kin wani ƙwaƙwime sa kin hana shi ya san damu a wajen”.

Dariya suka yi gaba ɗaya

Inda ita kuma tabi sa zata bige sa, ya gudu. Nan suka soma zagaye wajen suna dariya

Zannurain yace, “mu dai ku dena zagaye mu haka”.

Bata ƙyale shi ba kuwa, sai da ta kama shi ta naushe shi a kafaɗa

“Aushh! Wlh Yaya Suhaib wannan yarinyan muguwa ce, ta iya mugun ta”.

Sosai Suhaib yake dariya, musamman yanda ya ga ƙanwar tasa ta saki jikin ta, fara’an ta ma daban ne, shi kansa yasan ƙanwar tasa tana cikin nishaɗi sosai. Family wani abu ne me girma da daraja, me saka nishaɗi a zuciya.

     Anan suka shantake, sai daga baya suka shige gidan.

      Da rana sai ga Rayyan ya zo.

[4/5, 9:31 PM] نفيسة أم طاهرة: ????????????????????????????????????????

????????????????????

????????????????????

      *RAUDHA*

????????????????????

????????????????????

????????????????????????????????????????

*MALLAKAR:* ✍️

              _Nafisat Ismail Lawal Goma._

*بسم الله الرحمن الرحيم*

*FEENAH WRITER’S ASSO*????

”’®Ɗaya tamkar da Dubu”’????✓

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattapad: UmmuDahirah*????

         *F.W.A????/*

*RAMADHAN MUBARAKH*????????????

                     2021.

                  *NASIHA*

     ”’Muna iya lura cewa ga al’ada in an Kira talaka zuwa fadar sarki yakan gyara fuska, ya yi ado don ya sami kyakykyawar maraba daga Sarki. To, in haka ne, ina ga in ya tashi zuwa tsayuwa gaban  Ubangijin sa? Bawan da aka neme shi ya zo gaban Ubangiji, Sarkin sarakuna, mamallakin mamallaka, lalle kam ya fi kamata ya gyara kansa saboda wannan muhimmin muƙami. Ya kamata ya gyara kansa ta tsarkake tufafin sa da jikin sa, ya fito cikin kama mafi kyawu, kamar dai yadda aka umurci musulmi duka a cikin suratul A’ARAF, aya ta 31:

       _”ya ɗiyan Adam! Ku riƙi ƙawar ku a wurin ko wane masallaci”_

  Allah yasa mu dace.”’

.

  *NOT EDITED* ___________________________????

        *SEASON FORTY FIVE*

_______???? Lokacin da Rayyan ya shigo gidan, time ɗin su Daddy gaba ɗaya suna masallaci, sai Ammee dake zaune a Parlour, RAUDHA ta ɗaura kanta a saman cinyoyin ta suna ta hira suna dariya, sosai RAUDHA ta saki jiki da Ammee, sai tana kallon ta tamkar Mahaifiyar ta, bata taɓa kewar Mahaifiyar ta ba tunda take, sabida Daddy da Suhaib sun ɗauke mata komi, duk abinda uwa zata yi mata suna mata, ba su taɓa barin gurbin da zata ji kewar Maman ta ba, shiyasa ta taso ko kaɗan bata taɓa tuna wa da ita ba, ko a hoto ba ta ganin ta, duk da suna da hoton nata, amma ita ba ta ɓata time ɗin ta wajen ganin ta a hoto. shiyasa yanzu da Ammee take nuna mata ƙauna da kulawa, sai taji sosai take kewar Maman ta, sai taji tana matuƙar ƙaunar ta, har tana jin da ma tana raye ta so ta itama kamar yanda Ammee take mata fa. a jiya da take tunanin nan har sai da tayi kuka sosai, shiyasa a ranta yanzu ta ɗauki Ammee tamkar tana tare da maman ta ne, komi da zata iya faɗa mata zata iya sanar wa Ammee

Yanda RAUDHA ta saki jiki sosai, hakan sai ya faranta ran Ammee matuƙa, sosai take jin soyayyar ta a ranta, kasancewar ta me ƙaunar ɗiya mace, tunda Allah be bata ba.

     Sallaman Ray, shi ya dakatar da su daga hiran da suke yi suna dariya, a tare suka amsa mishi har RAUDHA da tayi tunanin ko Faruk ne, tunda muryan su ba shi da banbanci, sai dai yanda taji ƙamshin turaren sa ya daki hancin ta, sai tayi saurin lumshe idanu tana sake zuƙo turaren sosai, but duk a tunanin ta ba shi bane.

      Allah ya sani turaren sa yana matuƙar mata daɗi, bata san meyasa ba. tana jin sanda suke gaisa wa da Ammee, sai hakan ya bata mamaki tayi saurin ɗago kanta tana sauke idanun ta akan shi, yanda idanun ta suka faɗa cikin nasa sai tayi saurin ɗauke kai tana koma wa ta kwanta

Murmushi shi kuwa yayi, ya kalli Ammee dake shafa kanta a yanzu ɗin yace, “Ammee su Uncle fa?”

“Sun je masallaci”.

“Ok Nima bari inje dama ban yi sallan ba”. Har ya miƙe kuma sai ya kalli RAUDHA da idanun ta ke rufe yace, “pretty babu gaisuwa?”

Wani irin sara wa gaban ta yayi, dasauri ta buɗe idanun ta tana sakin numfashi me ƙarfi, sake mayar da idanun ta tayi, ahankali ta furta, “naharan sa’idan”.

Murmushi yayi ya kalli Ammee da itama take murmushin, don sosai zuciyan ta ta ɗarsa mata wani abu yanzu-yanzu da Rayyan ɗin ya kira RAUDHA da Pretty, sai ta ga sosai suka dace da juna, har tana ji a ranta da ma su kasance mata da miji

Shi kuwa Ray, har ga Allah manta wa yake yi yake kiran ta da suna Pretty a ko ina, sabida bakin sa ya saba. Sallama yayi wa Ammee ya fice

Sai a time ɗin RAUDHA ta buɗe idanun ta, sosai ranta yake kawo mata tunani kala-kala “meyasa yake kiran ta da sunan da Ƙalby ɗin ta ke kiran ta? Shin ba shi da wani sunan da zai iya kiran ta da shi ne sai wannan? Meyasa take jin muryan sa na shige da na Kalby? Ko dai shi ne?” Take ƙirjin ta yayi wani irin buga wa, tayi saurin tashi zaune tana riƙe wajen

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button