RAUDHA Page 41 to 50

“Lafiya Daughter? Me ya faru ne?” Ammee tafaɗa tana riƙe mata ɗaya hannun cikin kulawa
Kallon ta tayi, sai kuma ta saki murmushi tana faɗin, “babu komi Ammee na tuna wani abu ne, bari inje ɗaki ina dawo wa”.
“Kin tabbatar?” Ammee ta sake tambayar ta
Gyaɗa mata kai tayi tana miƙe wa tsaye
“Ok ki kula”.
Kai tsaye ɗakin ta ta wuce, ta soma neman layin Ƙalby, sai dai akashe ake ce mata, ta gwada ya kai fiye da biyar, but the same answer. Runtse idanu tayi tana buɗe wa da sauri, sai kuma ta tashi ta soma zagaye wajen tana tunani kala-kala
Wani Gwauron numfashi taja tana dukan cikin tafin hannun ta da ɗaya hannun, afili ta furta “Nooo impossible!”. Hannun ta ta saka a baki tana cizon yatsan ta, taci gaba da Safa da marwa, sai kuma taja burki da sauri tana riƙe goshin ta
“A’a tunani na ne wannan, amma wlh Ƙalby bazai taɓa zama shi ba! Me zai saka ma yayi min irin wannan wasan? Meye haɗi na dashi? Na tsane shi fa! I hate him so much”. Taƙarike maganar kamar zata yi kuka
Zama tayi daɓas akan gadon ta, ta sake ɗaukan wayan ta ta kira Numban nasa, a time ɗin yana shiga sai dai ba’a ɗauka ba, sai da tayi two missed calls kafin a ɗaga. Tana kara wa a kunne abinda ta soma tambayan sa, “ina ka shiga Ƙalby?”
Murmushi Ray ya saki, yana gyara muryan sa yace, “Pretty Ina aiki ne”.
“Aiki kuma? Wani aiki kenan bayan yau ba ranan aiki bane?” Ta sake tambayar sa da sauri, ita kanta a ruɗe take, so kawai take yi ya bata ƙwaƙƙwaran amsar da zuciyar ta zata iya yarda dashi
Stiil Murmushi yayi yace, “kin manta nace miki muna zuwa Gona Ni da Abba na?”.
Shiru tayi
Ya sake cewa, “lafiya dai Pretty? Me ke damun ki? Ina ji a jiki na akwai abinda ke damun ki?”
“Yeah akwai Ƙalby, Ni na gaji da ɓoye min kanka da kake yi, ina so mu haɗu”. Tayi maganar da tsananin sanyin murya
“Kar ki damu Pretty nayi miki alƙawari Very soon zamu ga juna, amma don Allah ki faɗa min meyasa kike son mu haɗu da wuri?”.
Shagwaɓe murya tayi tace, “Ni ina son ganin ka ne fa, kuma ka ga su Daddy suna ta tambaya na kai, sannan Ni fa ina so mu yi aure nan kusa ne, kai nake jira”.
“Ohhh Pretty Ni kike jira? Ashe kin ƙosa kamar Ni anan?” Yayi maganar cikin dariya
Itama dariyan tayi tana kwanciya kan gadon, ta sake matse wayan a kunnen ta, cikin ƙasa-ƙasa da murya tace, “to dama kai kaɗai ka ƙosa, nima ai har da Ni”.
“Me kika ce Pretty?”
Saurin faɗin, “no ba da kai nake yi ba?”
Dariya ya kece dashi, itama tana taya sa, yace, “ok kenan dama akwai wanda kike magana da shi bayan Ni?”
Turo baki tayi kamar tana ganin shi tace, “a’a babu kowa fa”.
“To nace da Ni kike yi kika ce ba dani ba?”
“Au da kaina nake yi”.
Dariya yayi yace, “kin ganki ko? Zaki sake maimaita abinda kika faɗa duk sanda muka haɗu”.
Dariya tayi kawai tana rufe idanun ta
“Baby in tambaye ki mana?”
“Ina ji Ƙalby”. Tayi maganar tana tashi zaune
“Wai dama kina da kunya haka?”
Turo baki tayi sabida bata yi tunanin tambayan kenan ba, sai da ta harari wayan kafin tace, “ban sani ba”.
“Oh Allah ya baki haƙuri my Pretty, kin san me? Wlh kina saka Ni nishaɗi duk sanda zan kasance ina waya dake”.
Murmushi tayi tace, “buri na da fata na kenan, a koda yaushe ka kasance cikin farin ciki, ina matuƙar matuƙar ƙaunar ka Ƙalby”.
Lumshe idanun sa yayi cike da jin sanyi a ransa yace, “nima haka My Baby, Ina matuƙar ƙaunar ki, fata na ki kasance mata a gare Ni, kuma uwar ƴaƴa na, Allah ya nuna min ranan da zan mallake ki, ina ga ranan ko uhmmm farin ciki na bazai misaltu ba”.
Murmusawa tayi idanun ta akan hannayen ta da take wasa da su, ta amsa masa da “ameen” cikin muryan ta me daɗi.
Da haka suka ci gaba da wayan cike da nishaɗi, ko wanne na bayyana ma ɗan uwansa irin farin cikin da yake ji idan suna tare da juna.
Ƙarfe biyar Ray yabar gidan, Suhaib kuma sai zuwa dare ya bi jirgi ya koma Abuja.
A ɗan kwanakin da su Ammee suka yi kafin su tafi, sosai RAUDHA ta shaƙu da su gaba ɗaya, har Faruk da be da yawan magana, shima yanzu sun saba sosai. sati ɗaya suka yi suka soma haraman tafiya, RAUDHA ta so bin su, amma dayake akwai bikin Ramcy sai ta fasa, amma Daddy sai ya ce mata “ta je tunda bikin saura Two weeks ne, sai tayi sati ɗaya ta dawo”.
Murna sosai RAUDHA take yi, nan da nan ta haɗa kayan ta a Trolly tabi su suka tafi.
.
_To Fans mu dai mun tafi Bayelsa, wanda yaga zai iya bin mu ya biyo mu, wanda kuma be da kuɗin Jirgi ya jira mu har mu dawo. Mu dai shhhhhiiii ✈️ mun shilla.????_
[4/6, 8:53 AM] نفيسة أم طاهرة: ????????????????????????????????????????
????????????????????
????????????????????
*RAUDHA*
????????????????????
????????????????????
????????????????????????????????????????
*MALLAKAR:* ✍️
_Nafisat Ismail Lawal Goma._
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER’S ASSO*????
”’®Ɗaya tamkar da Dubu”’????✓
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattapad: UmmuDahirah*????
*F.W.A????/*
*RAMADHAN MUBARAKH*????????????
2021.
.
*NOT EDITED* ___________________________????
*SEASON FORTY SIX*
_______???? Sun Isa Bayelsa wajen gabanin magriba, driver ya zo ya kwashe su ya nufi da su tanƙamemen gidan su, gidan flet ne me kyan gaske
Suna shiga parlour’n matasan duk suka wuce ɗakunan su, inda Ammee ta nuna wa RAUDHA ɗakin da zata zauna, tana fita ta shiga Toilet tayi wanka sannan ta ɗauro alwala, doguwar riga blue ta saka kafin ta gabatar da sallah
Bayan ta idar ta fito Parlour, babu kowa sai Ammee da itama zaman ta kenan
Tace, “ƙariko mana ɗiya ta”.
Taho wa tayi ta zauna a gefen ta
Ammee na murmushi tace, “kin ji sabon wuri, da fatan dai ya miki?”
Itama murmushin tayi tace, “Yayi min Ammee”.
“To Masha Allah haka nake so, bari in saka a kawo miki abinci ko kina jin yunwa”.
“A’a Ammee a bari sai anjima zan ci”.
Ammee tace, “to shikenan, kinga dai gidan mu ko. Nasan yanzu dare yayi ne shiyasa babu wanda zai zo sai zuwa gobe zaki ga ƴan uwa, Family House ɗin mu na nan baya ne, mutanen gidan duk ƙannin Uncle ne da matan su da ƴaƴan su, zuwa gobe insha Allahu sai mu je ku gaisa”.
“To Ammee”. RAUDHA tafaɗa tana murmushi.
A lokacin su Faruk suka shigo da sallaman su
Amsa musu suka yi.
Zannurain sarkin tsokana yace, “Hajiya RAUDHA ga ki ga garin mu, to ya kika ji namu garin? Da fatan dai yayi miki zam-zam ko?”
Dariya tayi tace, “Bro Zannu ai komi zam-zam”. Har da mishi waigi da hannu ????
Wannan karon dukan su suka yi dariyan
Abubakar yace, “ai sai kin gaji da yawo, Allah ya kai mu dai gobe, gaba ɗaya babu inda bazan zaga dake a garin namu ba”.
Ammee tace, “a’a babu inda ɗiya ta zata je gobe, hutu zata yi, idan ma yawon zaku fita sai dai zuwa jibi, yanzu ku tashi ku je ku ci abinci don ga yi can Asabe ta gama jera wa. Ina Uncle ɗin ku?”
“Yana wajen su Baba Iliya a waje”. Abubakar ya bata amsan hakan
Tashi suka yi su ukun zasu nufi kan dainning, har sun yi gaba sai Abubakar ya dawo yana cewa, “Friend ke fa? Baza ki taso mu ci abincin ba?”
Girgiza kanta tayi tace, “ba yanzu ba”.
“Cabb.. don Allah ke kuwa ba kya jin yunwa? Duk uwar daɗewan nan da muka sha a hanya?”
Hararan sa Ammee tayi tace, “dayake ance maka kowa ma irin ka ne, wuce ka tafi kai dai kaje kaci abincin ka”.
Turo baki yayi yayi gaba
Ita dai RAUDHA sai dariya take mishi