RAUDHA 1-END

RAUDHA Page 41 to 50

Addu’o’in da Malamin ke tofa mata, shi yasa ta buɗe idanunta da suka sake matuƙar girma tamkar ba nata ba, sun sauya kala zuwa kore, jajja-jajja, sai kawai ta soma ɓaɓɓaka dariya nan da nan ta tashi tayi sama tana shawagi, take ta tsaga wani uban ihu da ya razana su gaba ɗaya, ba su kaɗai ba gaba ɗaya gidan sai da ya amsa sabida ƙarar ihun nata. Babu shiri Daddy da Suhaib suka miƙe tsaye suna zazzare idanu sabida tsoron da ya shige su, ai nan suka soma addu’a jikin su na rawa, ga shi babu daman fita sabida Malamin sai da ya saka aka kulle ɗakin

Malamin kallon abokan aikin sa yayi, yayi musu nuni su ci gaba da karatun, yayinda shima ya ci gaba da karanto addu’o’i waɗanda zasu saka su bayyana kan su

Kuka ta soma yi sosai a wannan lokacin, sai dai babu hawaye amma gaba ɗaya idanun nata sun sauya kala, ko ɗigon fari ba’a gani, sai shawagi take yi a saman tana wani irin tururi tamkar ana dafa ta, hayaƙi sai fito wa yake yi a jikin ta

Karatun su ke yi, ita kuma tana ƙara yawan ihun nata, gaba ɗaya ta cika ɗakin da kuka ko karatun nasu ba’a ji.

          Malamin sosai ya gane aljanun masu taurin kai ne akanta, sabida duk yanda suka yi karatun, sun ƙi yin magana sai kukan da suke yi, daga ƙarshe ma sai taci gaba da ɓaɓɓaka dariya, idan ta gaji kuma sai ta koma kuka, sun shafe wajen awa biyu ana abu ɗaya, sai daga baya da suka ji ayoyi na ƙona su, sun ji azaba na ratsa su sosai wanda baza su iya jure wa ba, sai ta faɗo ƙasa da ƙarfi ta kurma uban ihu, cikin ƙaton murya na gardi take cewa, “ku dena ƙona mu, ku dena ƙona mu, ku dena ƙona mu”. Abinda take ta ambata kenan, har muryan ma ta koma tana faɗa ahankali sabida tsaban wahala

Gashi sun ƙi dena karatun

Sai ta koma kuka da hawayen ta tana roƙon su sosai

Nan malamin ya ba su daman dakata wa, sannan ya soma tambayan su “su wanene akan ta?”

Amma sai taƙi yin magana ta kafa wa Malamin idanu, idanun ta na zubar da hawaye

“Baza ku yi magana bane?” Cewar Malamin yana kallon ta shi ma

Sai ta ɓarke da dariya me fita muryoyi da yawa, nan ta miƙe da gudu tayi bakin ƙofa ta soma jijjiga ƙofan, kankace me ta kusa cire ƙofan, domin har ya ɓanɓaro tana shirin cire shi, nan suka yi kanta suna riƙe ta, tana bizgewa tana ihu, duk ta gama bibbige su

Su Daddy babu inda jikin su ba ya rawa, yau sun ga tashin hankali.

     Daƙyar suka riƙe ta suka dawo da ita cikin ɗakin, haka suka soma kici-kicin kwantar da ita don su danne ta, amma sun kasa, sai ta fara zagin su tana musu gargaɗin “idan basu sake ta ba, sai ta halaka su”

Malamin ganin dai tana son fin ƙarfin su, sai ya ɗauki waya yayi kiran wasu daga cikin malaman su, sannan ya kalli Daddy yace, “idan da hali ku ƙaro mana mutane, sabida tana ƙoƙarin guduwa ne, kuma tabbas idan har ta fice a ɗakin nan da akwai matsala”.

Jikin Daddy na rawa, ya umarci Suhaib ya kira masu aikin gidan maza su shigo

Dasauri ya fita ya kira su, sai ga su kusan su shida sun shigo

Nan Malam ya saka su duk suka taru wajen kwantar da RAUDHA, amma sun gagara, gaba ɗayan su sun kai su goma sha biyu kenan, amma sun gagara kwantar da RAUDHA ƙasa, ihu kawai take yi tana fizge-fizge, duk wanda ta samu ta mazge shi

Karatu suka ci gaba da yi suna danne ta tana kuka da ihu. Ba su yi nasaran kwantar da ita ba sai da wasu daga cikin malaman suka shigo, kusan su huɗu ne, Malamai ne su ma masu cire aljanu, tare suka dage daƙyar suka danne ta a ƙasa, suka hau karatu babu ji babu gani, sosai suka wahalar da ita, kukan ma wani irin kuka take yi tamkar na mage, gaba ɗaya tayi yaushi sai fitar da huci take yi, amma tsabar taurin kai taƙi magana.

      Wani magani malamin ya samu ya fesa mata, take ta sandare tamkar ranta ya fita, sai kuma ta fashe da sabon kuka tana buɗe idanuwan ta daƙyar, ta hau roƙon sa wai “za su fita”.

“Ƙarya kuke yi mugaye azzalumai, uban me tayi muku da kuka shiga jikin ta, ku ka wahalar da ita har haka, tsawon lokaci kun haukatar da ita, shin ku wasu irin mugaye ne, na ce uban me tayi muku ne?” Yaƙarike maganar cikin tsawa

Cikin kuka tana nishi tace, “wlh babu abinda tayi mana, kawai muna son ta ne, tayi mana ne shine yasa muka shige ta”.

“Tayi muku? Dama akwai wani abun da ya haɗa jinsin mutum dana aljanu ne?”

Tari ta soma yi babu ƙaƙƙauta wa, gaba ɗaya idanuwan ta sun gama juye wa, sun ƙara tsananin ja har babu kyan gani

“Shin zaku sanar damu ne meyasaka kuka shige ta? Ko kuwa sai mun ci gaba da gana muku azaba?”.

Shiru tayi taci gaba da tarin ta, yi take yi babu ƙaƙƙauta wa

Malamin kaɗa kansa yayi, kafin ya kalli sauran ya ce, “ku ci gaba”.

Nan da nan suka ci gaba da karatun Alqur’ani, shima yana ci gaba da addu’o’i

Atake anan taci gaba da kuka tana shirin bige su ta gudu, haka suka danne ta sosai suka hana ta tashi, kuka take yi sosai tana ihu, har da su majinu, ta jigata iya jigata sai ta hau zagin su tana faɗin, “wlh idan basu sake ta ba, sai ta kashe su”. Amma ko sauraron ta basu yi ba. Sun shafe tsawon lokuta suna karatun, kafin ta soma ba su haƙuri akan zata yi magana, amma malamin ya hana su dakata wa, sai da ta sha baƙar wahala ta sake yin yaushi sosai, ta yanda duk wani taurin kanta sai da suka yi maganin shi, kafin malamin ya saurare ta ya ce, “to ina ji zaku faɗa dalilin da yasa kuka shiga jikin ta ne ko kuwa sai na ƙona ku gaba ɗaya na kashe ku? Shin ku nawa ne ma ajikin nata?”

Cike da tarin wahala cikin wani irin babban murya tace, “muna da yawa a jikin ta, kuma Ni ne mijin ta, Ni na fara shiga jikin ta, sannan sai na jawo ƴan uwana su ma suka shiga jikin ta”.

Jinjina kansa Malamin yayi kafin ya ce, “har ma ka zama mijin ta kenan, sannan saboda tsaban mugunta sai ka jawo ƴan uwanka suka shiga jikinta don ku cutar da ita ko?”

Girgiza kai ta soma yi tana hawaye, sai tayi shiru taƙi magana

“Ina jin ka zaku yi magana ne ko sai na ƙona ku?”

“Zamu yi Malam, zamu yi”. Tafaɗa cikin mawuyacin hali tana juya idanuwa

“Kar ku sume mana anan, ina sauraron ka yi magana”.

Shiru tayi tana rufe idanuwan ta tamkar ba ta numfashi

Malam ya sake watsa mata wani farin magani

Sai ta buɗe idanunta, sun koma fari a yanzu ɗin tamkar nata, cikin siririyan muryan ta da ya gama dishewa tace, “Daddy”. Idanun ta akansa

Ai da sauri Daddy ya nufo wajen shima yana kiran sunan ta

Malamin ya dakatar da shi yana faɗin, “ba ita ba ce, suna son Raina mana hankali ne, ku muci gaba da karatun”.

Karatun suka ci gaba da yi, sai ta soma kuka, sai da taji azaba kafin ta ce, “kuyi haƙuri don Allah, wlh baza mu ƙara muku taurin kai ba, duk zan faɗa maka abinda ya sa muka shiga jikin ta”.

“To ina sauraron ku”.

“Tun farko abinda ya fara jan hankali na akanta sabida ba ta ibada, sannan tana shigan banza, tana barin kanta a buɗe, shine yasa na kamu da sonta, kuma na shiga jikin ta, sai na jawo ƴan uwana muka shiga, sannan sai suka ɗaura mana aure dani da ita”.

“Shin kai Musulmi ne ko kafiri?” Malamin ya sake tambayar sa

“Ni ba kafiri bane, amma ba mu Sallah, kuma tunda muka shiga jikin ta mu ke hana ta yin Sallah, tunda dama ba ta yi sai ta ga dama, wannan dalilin ne muka sake mayar da ita me wasa da Sallah, daga ƙarshe muka rinjaye ta muka hana ta Sallah”.

“To tun yaushe kuke jikin ta?”

“Mun daɗe sosai, tun tana ƙarama”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button