RAUDHA 1-END

RAUDHA Page 41 to 50

Malam ya ce, “kenan duk ku kuke saka ta shaye-shaye har kuka samu damar haukata ta ko?”

“Wlh ba mu bane, amma dai mun san mun ba ta gudunmuwa, ko tana son bari sai mu hana ta, mu riƙa saka ta tana son sha koda yaushe”.

“To yanzu meyasaka ka aure ta bayan kasan babu aure a tsakanin mu da ku?”

“Ai na ce maka ina son ta ne, tayi min ne”.

Malam ya ce, “to yanzu zaku fita ne ko kuwa kun samu wurin zama ne baku da ninya?”

Shiru tayi tana ci gaba da hawaye

“Ina magana kuna ji na, muna son ku fita a jikin ta, ku bar ta ta huta tunda kun rigada kun azabtar da ita”.

“Malam wlh ina ƙaunar ta, ita matata ce”.

“To shine yanzu na ce ka sake ta ku fita a jikin ta, tun kafin in azabtar da ku”.

Shiru tayi taƙi yin magana.

.

_To ya za’a kaya, shin za su bar ta ko kuwa?_

[3/19, 1:25 PM] نفيسة أم طاهرة: ????????????????????????????????????????

????????????????????

????????????????????

   *RAUDHA*

????????????????????

????????????????????

????????????????????????????????????????

*MALLAKAR:* ✍️

              _Nafisat Isma’il Lawal Goma._

*بسم الله الرحمن الرحيم*

 

*FEENAH WRITER’S ASSO*????

“`®Ɗaya tamkar da Dubu????✓“`

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattapad: UmmuDahirah*????

         *F.W.A????/*

*HIKIMAR FARILTA SALLAH*

      _An farilta sallah domin a cikin ta akwai godiya ga Mani’imcin sarki jalla Ta’ala, wanda yake shi ne macancancin godiya da yabo, kuma shi ne kaɗai muka keɓe shi da ruku’u da sujada. Ba wani mahaluki da ya dace da wannan. Idan wata masifa ta sami mutum yakan yi maza ya fake da Allah ta yin Sallah, kamar dai yadda Allah yayi umurni a cikin suratul Baƙara, aya ta 45 da cewa:_

       _”Kuma ku nemi taimako da yin haƙuri, da Sallah”._

    _Ganawar da bawa yake yi da Ubangijin sa a cikin Sallah ita ce bauta wadda take ƙarfafa zumunta tsakanin bawan da Ubangijin nasa. Ubangiji kuma yana yi wa bawan baiwar darajar samun kusanta da shi. Hikima ce kammalalliya da aka farilta sallah, don kuwa ta yin Sallah ne ake kankare wa bawa zunubai, muddin dai ya yi sallah yadda ake so._

     _An ruwaito cewa annabawan da suka wuce, ko wannen su yana da Sallah da yake ibada da ita. Sallolin suna da lokatai biyar; asuba, azahar, la’asar, lokacin faɗuwar rana da na isha’i. Ashe za mu lura cewa Allah ya tara wa Annabi da al’umma tasa sallolin dukan annabawan da suka gabata._

    _Allah ya sa mu dace._

.

 

*NOT EDITED* ___________________________????

        *SEASON THIRTY EIGHT*

_______???? Daƙyar Malamin ya samu Sa’a suka amsa za su fita, shima sai da ya gama gana musu azaba sosai sannan ne suka ce za su fita, ta hanci suka fice, sai faman atishawa take yi, daga baya kuma ta hau barci babu ji babu gani

Malamin sallaman mutanen yayi, sannan ya soma magana da su Daddy daga shi sai su, anan ya soma ba su shawara akan yanda za su kula da tarbiyyan ta, sabida ya kula kaso saba’in cikin ɗari duk laifin su ne, inda ba ta shigan banza da duk hakan bata faru ba, ita ta soma janyo hankalin su gare ta, kuma ga shi daga ƙarshe ita tasha wahala. Sosai yayi musu nasiha tare da shawarwari, sannan kuma ya ce za su riƙa zuwa ana amsar mata magani don ba zama za’a yi, ko wani lokaci za su iya dawowa idan har ba’a ci gaba da nema mata magani ba, don ya kula taurin kai ne da su, ya san ba su yi nisa ba, tun daga nan ya fara ba su magunguna da za tayi sirace da shi, sannan ya ce musu “idan sun ga ta tashi hankalin ta be da wo ba, dole za su mayar da ita asibiti saboda aci gaba dana asibiti, tunda dama ƙwayoyin da tasha sun birkita mata ƙwaƙwalwa, dalilin aljanun ne har yanzu ana magani babu ci gaba

Sosai suka yi wa Malamin godiya, har waje Daddy ya raka sa tare da ɗumbin alkhairai da ba ya faɗuwa.

      Suhaib na ɗakin da RAUDHA take kwance ya tasa ta gaba yana ta kallo, har Daddy ya dawo shima ya zauna kusa da shi, tsawon lokaci suna ahaka idanuwan su akanta, kafin Daddy yaja numfashi yace, “tabbas mun aikata babban kuskure tun farko, ga shi son zuciya ya saka mun yi wasa da tarbiyyan ta, soyayya ya rufe mana idanu daga Ni har kai mun kasa wa Baby tarbiyya irin ta addinin musulunci, duka laifin mu ne, kuma insha Allahu daga yau za mu gyara, Allah mun gode maka da ka taƙaita abun haka”.

“Gaskiya ne Daddy, laifin mu ne gaba ɗaya, sabida son da muke ma Sweetheart yasa ba ma hana ta, shiyasa ta tashi bata san bari ba, duk abinda take so shi take yi, ga shi abinda ya faru daga ƙarshe, Allah ka yafe mana”. Suhaib yafaɗa yana share hawayen sa

Daddy hannu ya saka yana buga bayan sa tare da ba shi baki. Sun jima a ɗakin ba su tashi ba, har sai da aka kira sallah tukunna suka fito suka tafi masallaci, bayan sun saka su Saude su zauna a ɗakin da RAUDHA take ɗin.

     Bayan sun dawo ne ta farka, sai dai yanda take yi ne suka gane da akwai matsala har yanzu, dole suka ɗauke ta suka yi da ita asibiti, anan aka sake duba wa aka gane har yanzu tana da matsala a ƙwaƙwalwan ta, amma kuma ba wani sosai bane, don ba sai an dangana dana asibitin mahaukata ba

Duk wani abinda Yakamata an yi mata, daga ƙarshe aka ba ta gado har zuwa sanda za ta warke.

      Haka rayuwa taci gaba da gudana, inda RAUDHA tana kwance a asibiti tana amsar magani, kuma ana kan mata na Islamic, da sannu-sannu suka soma ganin sauyi a gare ta, tunda har tana iya gane su tana banbance su, sai dai magana ne ba ta yi sai dariya, to an dai ci gaba da yin mata magani har zuwa sanda ta shafe tsawon watanni biyu a Hospital ɗin, kafin ta samu lafiya.

    Su Daddy sun yi murna matuƙa sai godiyar Allah suke yi

A zaman ta a Hospital ɗin, zuwan Captain Rayyan sau uku yana duba ta, shima don babu time ne aiki na hana sa zuwa sosai, amma da Suhaib ya kira sa ya sanar masa samuwar lafiyan ta har za’a sallame su, ya ji daɗi sosai, sai dai babu damar zuwa ya duba ta, haka yayi mata fatar alheri suka rabu.

      Koda suka koma gida an dai ci gaba da yin mata magunguna don ba’a zauna haka nan ba, tun ba ta saba wa har ta saba, ita da kanta take yin kayan ta, irin su sirace, shafa magani a jiki, shan zuma, shan wannan da wannan duk ta saba

Sosai RAUDHA ta sauya gaba ɗaya tamkar ba ita ba, duk da dama ba ta da hayaniya sosai, amma yanzu ta sake zama so silent, wuni tana maƙale jikin Daddy ko jikin Suhaib, haka za su zauna su yi ta mata hira ita kuma tana murmushi, har su gama hiran na su, daƙyar take iya yin magana sau ɗaya ko sau biyu

Kayan sakawan ta, gaba ɗaya Daddy ya saka an kwashe, an sauya mata da sababbi, dogayen riguna duk aka siyo mata, sai kuma irin Pakistan ɗin nan riga da wando, tunda dama bata iya shigan Hausawa ba shiyasa ma be haɗo mata da atamfofi ba, amma ƴan kanti da Arabian gown duk su aka siyo mata.

     Itama Ramcy sosai take zuwa duba ta, tunda ta ji labarin dawowar ta, har waya suna yi yanzu

Farida ce me kula da ita sosai, sai da ta sake samun lafiya sosai da sosai sannan Suhaib ya tarkata suka koma Abuja

Dayake ana hutun Corona babu school sai zaman gida, haka rayuwan taci gaba da gudana har sanda aka shafe kusan shekara ɗaya da samuwar cutar, sannan aka soma buɗe makarantu anan Zaria da sauran garuruwa, wasu ma garin sun daɗe da buɗe wa, don haka itama RAUDHA ta sanar da Daddy tana son koma wa school, sai dai tace ba ta son zaman Abuja tafi son Nan kusa da Daddy, tunda shima yana gida ba ya zuwa ko ina

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button