RAUDHA Page 41 to 50

A time ɗin ne wata matashiyar budurwa da a ƙalla baza ta fi 21years ba, ta fito daga kichen tana yarfe hannayen ta, ganin sa sai ta kwatsa ihu tana kiran sunan sa
“Yaya Zulain”.
Juyo wa yayi yana kallon ta, sai ya sakar mata murmushi yana buɗe hannayen sa alamun ta zo
Da gudu ta ƙariso cikin tsananin murna ta rungume shi
Ihun ta shine ya fito da mutanen gidan, Abba da Momy da kuma Sharif. ganin Zulain rungume da Sharifa, gaba ɗaya sai suka yo wajen sa suna me nuna murnan su da ganin sa
Nan shi kuma ya sake ta, ya bi su bayan ɗaya yana rungume su cike da fara’a
Abba na murmushi yace, “amma kuma yanzu Drever’n da na aika tare da bodyguard ɗina, suka kira Ni akan ba su ganka ba har yanzu, ashe kai ga ka har ka iso gida, ta ya ka gane hanya da ka taho kai kaɗai?”
Dariya Zulain yayi yace, “Abba kenan, ba fa yau na saba zuwa ba, kasan ba na son mutanen wajen su gane Ni, that’s why na ɓoye fuska ta na fito na hau Taxi ya kawo Ni”.
Momy tace, “ai kuwa kayi kyan kai wlh, Ni ban san ma wanda yake kiran su ba, nan muka zauna a gaban t.v muna jiran mu ga an haska ka, amma muka ji shiru, ashe kai kayi musu wayau ne ka gudo”.
Dariya suka yi gaba ɗaya, kana suka zauna suna sake gaisa wa, Abba na tambayar Iyayen Zulain ɗin da mutanen can ƴan uwa
“Abba kowa lafiya, suna gaishe ku sosai da sosai”.
“Masha Allah muna amsa wa”.
“Sharifa tashi mana ki kawo masa Drinks, kin zauna kin wani maƙale masa”. Cewar Momy tana kallon Sharifa da ta shige masa
Buga ƙafa ta hau yi kana tace, “Um um Momy! Ba ga Yaya ba ya ɗauko masa, Ni ba na son jirga wa kusa da shi”.
Sharif hannu ya saka ya buge mata baki yace, “a aike ki ki aike Ni, ina wasa dake ne?”
Zumɓura baki tayi tana shirin kuka
Zulain ya saka hannu yana shafa mata kai yace, “oh sorry my dear sister, Kar ki biye masa kiyi kuka bar sa ko?”
Tsamm Momy ta tashi tana cewa, “Ni bari in tashi in ɗauko maka”.
“Tun farko ma da hakan kika yi, da baki ɓata bakin ki ba, kin san halin Sharifa tunda ta ga Zulain ba kuma sauran aiki”. Abba ya faɗa yana murmushi
Sharif yace, “Ai Abba ƙyale ta Ni ne maganin ta wlh, in sake ganin an saka ki ki ɗauko wani abun ki ƙi”.
“Kai da baka ɗauko ba, ina ce ai duk halin ku ɗaya?” Momy tace hakan sanda ta dawo ta ajiye babban Plet a saman Centre table, janyo wa tayi ta matso da shi gaban Zulain ɗin, sannan ta koma ta zauna
Sharif dai be ce komi ba, sai saka hannu da yayi yana zaba wa Zulain Coke a cikin glass Cup
Abba ya ce, “mun yi magana da Yaya yace min zaka ɗan jima ko?”
“Yes Abba, Coz anan zan yi hutu na gaba ɗaya ma”.
“To Masha Allah, ka ga ai ka za ga dangi sosai wannan karon, da waɗanda ma suke min ƙorafin ba su sanka ba duk zaku je su sanka, ga Sharif nan tunda shima ya dawo hutun sa gaba ɗaya sai ku riƙa zuwa tare”.
“Abba nima har da Ni”. Cewar Sharifa cike da zumuɗi
Hararan ta Sharif yayi yana cewa, “wa ya saka bakin ki?”
Momy tace, “ka ji ka dai, to idan bata raka ku ba, ai ina ce duk sammakai da kai da shi ɗin, tunda kaima babu inda ka sani a dangin, dole ita zata nuna muku ko ina ku shiga”.
Gwalo Sharifa tayi masa
Shi kuma yayi ƙwafa yana ɗaukan wayan sa ya ce, “wlh Momy duk ke kike saka wa yarinyan nan tana raina Ni, amma babu komi zan yi maganin ta”.
Daga Abba har Zulain murmushi kawai suke musu
Hira suka ɗan taɓa, kafin Abba ya ce su tashi su tafi masallaci ana kiran sallah.
Ba su dawo ba, sai da aka yi sallan isha’i, inda suka zauna a dainning suka ci abinci, sannan suka dawo Parlour suka dasa hira, sai wajen goma suka watse, Zulain da Sharif suka wuce ɗakin Sharif ɗin, sai da Zulain yayi wanka ya sauya kaya sannan ya hayo kan gadon, sai dai tunda ya rufe idanuwan sa ya kasa barci, illa fuskar RAUDHA da ya bayyana masa, gaba ɗaya ya rasa sukunin sa sai faman tunanin ta yake yi, yana fata Allah ya sake haɗa shi da ita, sosai yarinyan ta hana sa sukuni har ya rasa me ke damun sa, daƙyar ya iya samu barci ya ɗauke sa, sabida ba ƙaramin gajiya ne a jikin sa ba.
Abba Ƙani ne wajen mahaifin Zulain, haifaffun nan Zaria ne, inda Mahaifin Zulain karatu ya kai sa can American, anan suka haɗu da ƴar Sarkin American ya aure ta, kuma suka ci gaba da zama a can, ɗan su ɗaya suka mallaka a duniya wato Zulain, idan ya samu hutu suna kawo sa nan wajen Abba yayi mishi hutu, har zuwa yanzu da ya girma yana aikin sa a can, sai dai yanzu ɗin be cika zuwa sosai ba sai idan ya samu hutun shekara.
Abba babban mutum ne a nan Zaria, kuma ɗan siyasa ne wanda ya ci jiya yana cin yau, kuma yana fata gobe ma a dama dashi a ƙasar, yanzu haka shi aka tsayar a takarar mataimakin Gwamnan Kaduna, yaran sa uku, Hauwa’u me sunan Maman Abba, suna kiran ta Aunty Mimi, tayi aure har da yaran ta biyu, sai Sharif da yanzu yake aiki a Abuja, shima yanzu haka an saka mishi rana, sai kuma Sharifa da yanzu ne take aji na biyu a A.B.U Zaria
Tun farko ita Allah ya ɗaura mata ƙaunar Zulain sosai, shiyasa take shige masa sosai har suka saba matuƙa, idan ta samu hutun school can American take zuwa tayi hutun ta, hakan ya sa suka sake shaƙuwa fiye da tunanin mutum, har wasu suna musu kallon akwai soyayya a tsakanin su, ba su san cewa shi Zulain yana mata kallon ƙanwa ce kaɗai, shi a rayuwa babu ruwan sa da mata idan har ba ƴan uwan sa ba, sai dai ya taɓa yin soyayya da daɗe wa, har ya so ya auri yarinyan, sai dai Allah be yi ba ta mutu, yarinyan dangin sa ce a can American, kuma Christian ce, tunda dama itama har yanzu mahaifiyar sa bata musulunta ba, to su a wajen su babu komi idan har ya auri ko wace irin yare ce.
????????????????????????????????????????
*SATURDAY*
Yau ce ranan da za’a yi wa RAUDHA partyn kammala karatun ta. Gaba ɗaya gidan an yi masa decorations, sosai ko ina yayi kyau gunun sha’awa, a bayan gidan a cikin Garden ɗin wajen za’a yi, sosai wajen ya matuƙar haɗuwa, ga shi an kashe kuɗi, komi green and red aka sanya a wajen.
Zuwa ƙarfe 04:00pm. Har mutane sun soma zuwa gidan, duk da ba wasu gayya ne a kayi ba, domin dai RAUDHA bata da ƙawaye illa Ramcy kaɗai, sai ita Ramcy ɗin da ta gayyaci ƴan gidan su, sai kuma Daddy da Suhaib su ma da suka gayyaci mutanen su na nan Zaria kaɗai, ciki kuwa har da Abba za su zo da su Sharif, tunda dama Abba abokin Daddy ne, tare suka yi Siyasa kafin Daddy ya fita, jam’iyyar su ɗaya, ta dalilin hakan ne Sharif da Suhaib suka san juna har suka zama abokai, to abokan takan nasu tayi ƙarfi ne sanda Sharif ya koma Abuja da zama yana aiki, shiyasa suka ci gaba da zumunci sosai.
.
_More Comments more page, idan har babu Comments da zai faranta min, to tabbas na ɗau hutu domin baza ku ji Ni ba._
[3/21, 12:36 PM] نفيسة أم طاهرة: ????????????????????????????????????????
????????????????????
????????????????????
*RAUDHA*
????????????????????
????????????????????
????????????????????????????????????????
*MALLAKAR:*✍️
_Nafisat Isma’il Lawal Goma._
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER’S ASSO*????
“`®Ɗaya tamkar da Dubu????✓“`
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattapad: UmmuDahirah*????
*F.W.A????/*
.
*NOT EDITED* ___________________________????
*SEASON FORTY ONE*
_______???? Biri da wando ta saka me santsi Light orange, ƙasan wandon me fela ne sosai, sai ta saka top fari iya gwiwar ta, me kwalliyan stones, sannan sai ta naɗa blue ɗin ɗankwali a kanta, wanda ya fito mata da gashin ta ta ƙasan ƙeya, Light makeup tayi da ya fito da tsantsan kyawun ta, kai Masha Allah duk wanda ya ga RAUDHA wannan lokacin bazai so ya ɗauke idanun sa ba, ta haɗu iya haɗuwa sai wanda ya gani, takalmin da ta saka me tsinin gaske ne cover me igiya, kalan Light blue da farin Socks a ciki, sai tashin ƙamshi take yi irin turaren nan na Arabian