RAUDHA Page 41 to 50

Ramcy dake zaune saman sofan ɗakin ta, sakin baki tayi tana kallon ta
Sai da RAUDHA ta matso kusa da ita, ta sanya hannun ta ta shafa fuskar ta tana murmusawa. Sannan a time ɗin Ramcy ta rufe bakin ta bayan ta dawo da tunanin ta jikin ta
“What happened Besty?”
Gwauron numfashi Ramcy ta sauke kafin tace, “ban san me zan ce bane wlh Besty, haɗuwar ki yayi yawa. Masha Allah gaskiya ki gode Allah”.
Murmushin ta me kyau ta saki kafin ta lumshe ido ahankali ta furta, “Shukran Lak, linazhab”.
Da ido Ramcy tayi mata magana, “wai what?”
“Let’s go”.
Miƙe wa Ramcy tayi tana gyara zaman gyalen ta, itama tayi shiga ne cikin baƙin yadi me santsi, ɗinkin doguwar riga, duk da kasancewar ta baƙa but sosai tayi kyau matuƙa, kasancewar an yi wa rigan ado da jan zare sai Stones, kuma tayi amfani da jan ɗankwali ne sai farin gyale.
Fita suka yi, inda tuni an gama taruwa su kaɗai ake jira a wajen. A hanya suka haɗu da Farida ta zo kiran su, sai suka tafi tare, itama kanta sai ya ba kwalliyan RAUDHAN take yi
Ita kuwa sai murmushi take saki me fid da sihirtaccen kyawun ta, tana takun nan nata ɗai-ɗai me ban sha’awa, kasancewar bata yafa gyale ba, shiyasa duk inda jikin ta ya juya ana ganin komi ta yanda take sarrafa jikin ta.
Tun doso wan su wajen sai idanun mutane kawai ya koma kanta, hakan yasa wasu da hankalin su be kai kanta ba, sai duk suka kallo wajen
Tana tsakiyar Farida da Ramcy ne, suna taho wa wajen
Nan da nan aka soma tafi sabida sanar wan da MC ke yi na zuwan ta, nan ya soma koɗa ta yana kambama ta
Ita kuwa idanuwan ta na kan su Daddy da ta hange su, su ma suna mata murmushi, Suhaib har da ɗaga mata babban yatsan sa alamun tayi zam-zam. ita kuwa ta saki murmushin nan da ke ƙara wa fuskar ta kyawu.
“Kai man juyo ka ga wata halitta don Allah”. Cewar Sharif da yayi maganar a hankali kusa da kunnen Zulain dake waya ya karkace kai
Juyo wa yayi kuwa, yana shirin hararan sa sai idon sa suka sauka kan RAUDHA dake tafiya zuwa wajen zaman ta, take anan komi nasa ya tsaya illa idanun sa da ya lumshe ya sake buɗe wa akanta, yana son tabbatar wa kansa itan ce ko kuwa?. Maganar Sharif ya sake dawo da shi hayyacin sa
“Ni wlh da na san S. Makamashi yana da ƙanwa irin wannan, ai da tuni ita na nema, me zai kai Ni zuwa waje gida be ƙoshi ba”.
Shiru Zulain yayi don hankalin sa be gama dawo wa kan Sharif ba, bare ya tantance me yake faɗa, idanun sa ƙyam akan RAUDHA har ta zauna ta yanda yanzu yake ganin fuskar ta sosai. A take ya saki wani irin ajiyan zuciya yana sake lumshe ido
A tare Sharif da Mom ɗin sa da suke waya, suka je ho masa tambaya the same
Buɗe idanun sa yayi yana kallon Sharif da ya tsaya kallon sa shima, sai kuma yayi saurin kara wayan a kunnen sa sosai yana faɗin, “Mom zan kira ki letter please”. Ya Yi saurin katse wayan be jira cewar ta ba, nan ya sake mayar da idanun sa kan RAUDHA gaba ɗaya ya mayar da hankalin sa gare ta, sosai yaji daɗin ganin ta da baki ma bazai iya furta wa ba, har wani sakin murmushi yake yi batare da ya sani ba
Sharif dake faman kallon sa baki sake, ya jinjina kansa ya ce, “cab ɗijam.. Kar dai har ta sace maka zuciya daga kallon farko?”
Zulain be kalle sa ba don ba ya son abunda zai gilma ga kallon kyakykyawar nan, amma kuma sai ya ɓata fuska yana kumbura shi irin maganar Sharif ɗin fa ya fara isar sa
Murmushi kawai Sharif yayi be ce komi ba, ya mayar da hankalin sa shima ga abinda ake yi.
A lokacin RAUDHA ta miƙe ne tana speech da muryan ta me daɗi da ya karaɗe wajen. Sosai duk mahalukin dake wajen ya mayar da hankalin sa gare ta cike da sha’awa. Har ta gama aka soma mata tafi Raf.. Raf… Raf
Sannan sai Suhaib ya amsa ya sake ma kowa godiya tare da yaba wa ƙanwar sa, da nuna irin tsantsan ƙaunar da yake mata. daga nan kuma Daddy ne ya amsa shima ya soma yabon ta sosai, da abun mamakin da ta ba su, tare da nuna wa mutane tsantsan alfaharin da yake yi da ɗiyar sa
Haka ake ta tafa wa cike da tsananin burge su da suka yi, don sosai iyalan suka burge kowa. Haka dai aka ci gaba da gudanar da partyn cike da sha’awa, inda daga baya MC ya kira RAUDHA domin ta taka
Murmushi kawai ta soma zuba wa, domin har yanzu ƙaunar ta da rawa yana nan, sai dai yanzu ba kamar da ba, duk da a yanzu ta koyo irin rawan larabawa ne, ko tana yi zaka ka bata cika yin irin na nan ba saboda ya zame mata jiki na larabawan. Tashi tayi ta fita ta soma taka wa a hankali tana dariya bakin ta ya ƙi rufuwa
Nan Suhaib ya taso ya soma taya ta
Yanda yake rawan ne sai da ya ba kowa dariya, sai tafi ake musu
Ita RAUDHA ta saka a sauya musu, don ta kasa yi sosai sabida waƙar Hausa ce, sai ta ce a saka mata na Laraba wa, ai nan ta soma taka wa irin nasu sosai, sai shima Suhaib ya biye mata suna yi tare, har da riƙe hannu irin na laraba wa yanda suke yi
Sosai yanzu ɗin Suhaib yafi ba wa kowa dariya, kowa ka gani wajen nishaɗi yake yi.
Lumshe idanu Zulain yayi saboda tsantsan wani farin ciki da yake ziyartan sa, sosai yarinyan ta matuƙar burge sa fiye da tunanin mutum, nan da nan ya ji soyayyar ta me tsananin ƙarfi ya kama sa. Har wani buga tagumi yayi da hannu biyu yana bin ta da kallo.
While sauran samarin, abokan Suhaib duk haka ne a wajen su, kowa fatan sa ya dace da mallakan kyakykyawar balarabiyyan nan.
????????????????????????????????????????
Wata farar mota ce ta shigo cikin gidan a wannan lokacin, ahankali motan take tafiya har zuwa inda akayi parcking motoci, kamar mintuna biyu da tsayuwar motan aka buɗe ƙofan, sai dai wanda ke ciki be fito ba, illa ziro fararen ƙafafuwan sa dake cikin baƙin sandal Shoes da yayi waje
Daga inda yake duk da akwai tazara sosai da inda ake partyn, amma kuma hakan be sa tattausan waƙar larabawan dake tashi a wajen kasa ratsa masa kunnuwa ba, take anan ya lumshe idanun sa cike da jin daɗin waƙan, kamar shuɗewar mintuna biyar ya buɗe su yana aza idanun sa kan wayan sa dake saman cinyan sa, ɗauka yayi ya soma dubo Numban Suhaib da yayi masa serving da Dude yayi kira
While Suhaib na filin rawa yana tiƙan rawa tare da RAUDHA, sai yaji wayan sa na ruri, dasauri ya saki hannun ta yana zira wa cikin aljihu ya ciro wayan, ganin sunan Dude a screen ɗin wayan na yawo, sai nan da nan fara’an sa ya ƙaru, matsawa yayi gefe yana answer call ɗin ya kara a kunne, “Dude”.
“Surprise! Gani a cikin gidan ku”.
Waro ido Suhaib yayi, “haba don Allah”.
Murmushi yayi shi kuma yace, “ka zo ka gani, ina nan wajen parcking space”. Daga haka ya katse wayan
Da sauri Suhaib yayi hanyar barin wajen
Inda RAUDHA ta kira sunan sa
Juyo wa yayi yana kallon ta. Ta ɗage masa gira akan “ina zai je?”
Nuna mata yayi da hannu wai “yanzu zai dawo”.
Ta marairaice fuska kafin ta juya ta nufi wajen zaman ta. A lokacin ne aka soma bata kyaututtuka.
????????????
Suhaib na isa wajen parcking space, Rayyan dake mota ya fito yana rufe wa. Rungume juna suka yi cike da tsananin murna, kafin kuma su saki juna suna cafe hannayen su ko wanne baki a washe
“Dude wlh ka shammace Ni, nayi tunanin ba yanzu zaka dawo ba”.
Murmushi Rayyan yayi yace, “dama wannan week ɗin zan shigo, but sai naga dacewar shigowa yau ɗin tunda naga yau ce ranan ƙanwar ta mu, sai in Taya ta murna”.