NOVELSUncategorized

RUWAN JAKARA 1

*BRILLIANT WRITERS ASSOCIATION*                  
( _pens of freedom, home of exceptional and magnificent writers_) 

                *RUWAN JAKARA*………….    

                *~LITTAFIN~*???????? 

   _MARYAM HAMISU YUSUF (Maman boy)_
~True life story~
_kyakkyawar gaisuwa zuwa gareka : Muhammad kareem kd, Allah yayi maka sakayyya da mafificin alkhairinsa_“`Page“` *1*
*_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM_*

*_KACE “KUZO, IN KARANTA ABINDA UBAN GIJINKU YA HARAMTA AGAREKU”.  WAJIBINE AKANKU KADA KUHADA ALLAH DA KOMAI, IYAYE KU KYAUTATAMUSU, KADA KU KASHE ‘YAYAYENKU DAN TSORON TALAUCI… MUNE MUKE AZURTAKU DASU (YAYANKU)  KADA KU KUSANCI ALFASHA.. DA ABINDA YA BAYYANA DAGA GARETA DA WANDA YA BOYU… KADA KU KASHE RAI WANDA ALLAH YA HARAMTA FACE DA HAQQI.. WANNAN NE (ALLAH) YAYIMUKU WASIYYA IDAN KUN KASANCE MASU HANKALI (Q 6:V:151)_*
 .______________________________

Ajin yayi shiru!! Yayinda duk macen datake  Ajin ta shagalta da jin amon za    zzakar muryata… Alokacin da nake rairo masu karatun alkur ani mai girma ina Koyar dasu. 

Ban gusheba Saida nayimusu tafsiri akan ayar da nake karanta musu….(suratun_nissa’i aya ta biyu)  Yayinda suke jefomin tambayoyi nikuma ina basu amsa cikin kwarewa da kafa musu hujjoji da sahihan hadisan manzon Allah (SAW)…. 

 Duk macen dake ajin danake koyarwa ayanxu babu wacce bata haifeniba wata ma tayi jika dani duk da  karancin shekarun danake dasu sosai hakan bai hana dalibn nawa mutuntaniba kamr yadda nima nake tsananin mutuntasu…amatsayiinsu na wadanda suka isa su haifeni  

Badan nagaji da amsa tambayoyinsuba na dakatar sakamakon lokacin Rufe makarantar islamiyyar  da yayi (6:00pm) ..ttuni dalibai suka soma fitowa a farfajiyar makarantar Hakan yasa mukayi addua…… 

Staff room na koma nasaka hannu alittafi na cike attedence dinmu na malamai… Sallama mukayi da malamai na fito

Sakin nikabina nayi wanda ke boye tsananin kyau da sigar da Allah yayiwa fuskata… Dara daran fararen idanuna kawai zaka iya hangowa ka shaida nidin kyakkyawa ce

Cikin nutsuwa da takon danakeyi tamkar ina tausayin kasa na karaso bakin gate.din makarantar …


 Saidai kafin wani lokaci tuni garin yayi bakikirin da hadarin da haduwarsa kenan,  nan da nan iska ta fara kadawa yayinda malamai da dalibai kowane ke kokarin sanin inda dare yayi masa dan gudun kada ruwa su jikasu….  Kafin wani lokaci tuni ruwa sun fara sauka tamkar da bakin kwarya kuma da karfin gaske ….. 

Saida najike sosai acikin Ruwan har Allah yasa nakarasa gida…

 Ina shigowa gidan na cikaro da kofar dakin ummah a rufe.. Atake raina yasoma 6aci… Arayuwata na tsani bakin yawon da mahaifiyata takeyi cikin ruwannan kuma ko ina ta nufa??.. Bansamu wannan amsar daga gareni ba nayi saurin nufar dn karamin dakina alokacin gwaggo kwazo ta fito tarbar ruwar sama tanamin sannu… (Dayake gidannamu na hayane.) . Na amsa Mata ina kokarin tura yamutsattsen kyauran dakinnawa….. 

Bantsaya wata² ba na fara cire zurmikekiyar hijab Dina da nikab na sauya kaya zuwa wani tsohon leshi na dinkin riga  da skirt..  sai rawar sanyi nakeyi.. 
Alwala na dauro na gabtar da sallar magrib sakamakon Kirayen  kirayen sallah da aka farayi saidai har aka yi sallar issha umma bata shigo ba…

 Lumshe idanuna nayi tare da makurewa akan yar tsohuwar katifa na ina tunanin wannan bakin gantalin na umma Dana taso na ganta a ciki…. 
Shigowar gwaggo kwazo ta saka na bude idanuna… Langa ta ajiyemin agefe na tana fadar “uwar dakina har kinyi bacci bakici abinci. ba? (Dayake sunan jijarrta gareni)  
Yunkurawa nayi ina yimata sannu..tarevda kakaro murmushhi Takuma turomin langar tan fadan kici abinci…. Tana matsamin naci dan ita kanta tasan damuwata 

Godiya nayiwa gwaggo kwazo.. Domin duk lokacin da mahaifiyata ta tafi  bulagoronta.. Itace me kula dani har ta dawo….


  “Gwoggo Tun yaushe ummah tbar gidannan”…. Na dakatar da gwaggo dake kokarin fita. Juyowa tayi tana kallo na kafin tace “ai kina tafiya makaranta ta fita kuma gashi har duhu yafara bata dawoba…. “

Lumshe idanuna nayi ina jinjina kai alokacin gwaggo ta fice sakamakon sallama da mijinta yayi agidan …. “Ya Allah ka yayewa umma wannan jarababben yawon…. “
Na fada ina janyo langar
Bude langar da gwaggo takawomin nayi… Tuwon dawane miyar danyar kubewa duk da kayan miya basu wadaci miyar ba hkan bai hanata fitar da kamshi mai dadi ba……. 

Kadan na ci na mayar na ajiye sakamakon yadda nake jin zuciyata namin zafi…..


  Sai misalin karfe Tara saura kwata ummah ta shigo gidan inajin lokacin data bude dakinta ta shiga hakan ya tilastamin tashi  na nufi dakinta…. 
Tana kokarin ajiye mayafinta na shigo dakin tare da sallama….

 Tunda ummah ta kalleni ta watsar bata kuma bi takaina ba ta cigaba da ninke tsohon mayafinta dan Kuwa tasan abinda ya kawoni…..  

“Sannu da dawowa nayimata……  Ba yabo ba fallasa ta amsamin… 
Ta dora dacewa “kinci abinci Kuwa naga kinyi wani zuru² tamkar an shakare mage”…
  Ta idar da maganr tana kallon yanayina. Kawar da kaina nayi kafin nabata amsa “eh gwaggo kwazo ta bani “… Na dora dacewa “ummah dan Allah ina kikajene haka sai yanxu “….. 

Zama bakin gado ummah tayi tana rabka salati tare da tafa hannayenta “shknan batula zargina kikeyi kenan… Kinaso ki fadawa duniya wato bin maza nakeyi”…. 

 Saurin girgiza kaina nayi na fara kuka jin yadda ummah take Neman lailaiya tambayata.. “Wlh ummah ba haka nake nufi ba
 Naga kin dadene shiyasa….   
“To batula mekike nufi idan ban fita na samo maku abinda zakuci ba amatsayinku na marayun da aka mutu ba abarmin ko sisiba na kula daku,  so kike na zauna bakin cikin duniya ya kasheni da bakin cikin dangin mahaifinki.. Ki dubi dukiyar da Allah yayiwa alhaji mansoor Amma dai² da kwayar shinkafa baitaba taimakamana da ita ba.. Sai azumin bara ne Allah ya taimaka ya kwato mana tiyan masara biyar daga hannunsa .. Shin batula da wannan kikeso na zauna.. Koko zama zanyi ku taru ku cinyeni”.? 

Share hawayen da suka jikamin fuska nayi nasoma magana “ummah ya usman da ya faruq su kadai sun isa su taimaka mana ba sai kindinga yawoba haka umma kefa macece kuma kinada yaya maza “….. 

“Dallah rufemin baki batula su usman da faruq Dinne zasu rikemu… Sudin da jira sukeyi na ajiye su dauke… Agaban idanunki sun sha satarwa kwazo kudadenta… Kwanaki usman sabbin kayan mijina dazai saka a bikin yarsa ya dauke yaje yasiyar yadawomin gida abuge… Shikuwa faruq sai na kwana inwuni bansakasa a idanuna ba ya na can wurin tambada… Ke kadaice ta kirki  acikinsu.. Yadda allah yayiki da kyau hka ga iliminnan naki so nake kisamu wani  basarake ko dan  gwamna.. Ko dan wani mai fada aji akasar nan ya aureki… Dan wlh kin fi karfin talaka”…, 
Umma ta idar da maganr tana murmishi….. 
Takaici ya kuma cikani akan Kala man umma… 
Tashi nayi kawai na fice ina hawaye… Duk Wani buri mahaifiyata ta azasa akaina… Nazamemata jari na ganin takaiga cikar burinta……… 


Fatima ko fadima,  sayyada ko batula ko Zarah babu sunan da Bana amsawa musamman abakin mahaifina….. 
 Mahiafina dan asalin jihar katsina   ne ba fullacen mutum ne sosai.. Hausa.ma bata zauna bakin sa yadda yakamata ba… Su shidda ne awurin iyayensu mansoor shine babba sai sa’eed wato mahaifina.. Sai sa’adatu mai bimasa da umma jamila.. Sai habu da baba saratu…….


Alhaji mansoor yanada Mata daya salamatu yayansu uku anwar, saiyya… da nazifa… 
Mutum ne mai arziki sosai da ya shahra ta fanni shigo da shinkafa a kasar… Da kuma harkar shigo da suturu daga kasashe daban daban….

 Mutum ne mai tsananin son yaynsa da sngartasu… Hkan yasa alokacin da anwar ya kammala secondary school.. Ya fitar dashi jamiar america  acan yayi karatunsa fannin kasuwanci..  Ya hada degree da masters,dayadawo Nigeria babban office mahaifinsa ya ba a fannin kasuwancinsa Amatsayin general  manager na company n na  kera robobi wqnda baijima da budesaba
Shekarunsa bazasu Gaza ashirin da tara ba… Fari ne sosai  yanada kakkarfan jiki da cikakkiyar siga ta da namiji da kuma kyau.. Saidai idanunsa sunfi Kama Dana jaraba bun mazannan wato sexy eyes.. Dan basu cika hhasskeba.. Suna da girma kuma alumshe suke   Sangartaccene awurin abbansa da haji ya salamatu… Tataccen  marar kunya ne… Duk wata dabia ta Muslimin kwarai baida ita..  Shahrarrene wurin kawo Mata agidan nasu… Kamar yadda zaman clubs ya zame masa jiki.. Duk abinnan da yakeyi Alhaji mansoor ya ki hantararsa wai kuruciya ce ko wa kuma da irin yadda ya yi kuruciyarsa…sumaiyya da nazifa Kuwa kusan kansu daya suna a secondary tsadaddiyar private school sukeyi zamuzo kai daga da nazifa… Duk da shekara daya da rabi ne tsakaninsu.. 
 Yarane yan kwalisa da suka raina kowa da suke tutiya da kyau da naira.. Basa ganin kowa da mutunci… Wannan yasamo asaline daga mahaifinsu… Dan ko kadan baya kaunar dan uwansa ya rabe sa bare ya ya taimaka masa… Daga matarsa sai yayansa…. Kuma Alhaji mansoor shikadaine mutumin da Allah yayiwa arziki acikin family dinmu…  kannen mahaifina Mata Kuwa duka mazajen da suke aure ba masu karfi bane… Har kara baba habu ba laifi yana, da rufin ssiri…yarsa daya da Mata biyu. 

 Bakidaya sunja jikinsu daga alhaji mansoor sun rike talaucinsu..saidai ghakkin zumunci da suke kokarin cikawa . 


Wannan yasa mahaifinmu yaja jiki daga lamurransa saidai Sauke hakkin zumunci da ba’a rasa ba… Mahaifina malam sa’eed mutum ne mai wadatar zuci… Da sanaar sayar da tukane da murahu Da ita yke kokarin rikemu. 

Mahaifina bai taba zuwa wurin alhaji mansoor da Neman ya taimaka masa ba haka shima bai taba, yunkurin .ya taimaka masa ba…  Saidai mahaifiyata(hajara)  tunda ta kyalla ido taga gidan Alhaji mansoor da maiko tafara kokarin kutsa kanta gidan… Duk da fada da abbahnmu yake Mata amma taki harma wani lokacin takan rufesa da masifa wai girman kai ne dashi da baya iya zuwa ya nemi Abu agidan alhaji mansoor inda aka fika an riga an fika….. Baitaba bi takanta ba idan tana masifa dan mahaifiyata macece mai kwadayi da hangen na wani ga masifar fada… Hka Allah ya jarrabi mahaifina da ummah dan shi mutum ne mai sanyin hali ga hakuri… Bakomai yake daga kai yayi magana ba…… 
 Kwata² mu uku ne  awurin iyayenmu… Ya faruq shine babba shekarunsa ashirn da hudu sai mai binsa usman sai da mahaifiyata ta kwashe shekaru bakwai kafin ta haife ni kuma, ni kadai ce mace daga kaina ta tsayar da haihuwar wai bazata iya cigaba da haihuwa da mahaifina da talaucinsa ba..    

Mun taso cikin kula daga mahaifinmu ya tsaya tsayin daka kanmu wurin ganin ya kyuatata mana…dukkan family dinmu kyawawane sosan gaske dan takoina munyi gadon kyau kamanninmu sun kusa zuwa daya.. Dan dakaga dan familynmu kanaganewa wannan yasamo nasaba daga kammaninsa da iyayenmu sukeyi da junansu..  Tun daga ilimin mu har cinmu da shanmu da suturmu Mahaifinmu ya tsaya akanmu… 

Saidai fa karatun su ya faruq yatsaya daga secondary school… Dan mahaifinmu baida kudin dazai tallafa masu Suci gaba da karatu….. Sai ya zamana ni kadaice ke karatu ina jss one…. Duk yadda mahaifina yaso su ya faruq suyi karatun addini suka watsar.. Sune. biyewa batagarin unguwa sune shaye²…  Mahaifina yayi kukan bakin ciki sosai.. Saidai yakan samu nutsuwa idanyana tare dani.. Babu inda nabaro halayen mahaifina.. Inada son addini da son Neman ilimin addini sosai… Duka Dana boko ina mayar da hankali sosai… Allah ya  bani kwazo da saurin  fahimtar duk karatun da akayimin Tun daga Boko har islamiyya… 


Inada shekara 13 nasauke alkur’ani mai girma… Nasha kyautttuka da yawa daga wurin mahaifina da sauran mutanen unguwarmu saboda ni macece mai farin jinin mutane.. Sainazama abun kwatance awurin iyaye idan zasuyiwa yayansu fada, kowace uwa burinta yarta tayi koyi da halayena.. Duk da mutane da dama na cewa Banyi dacen mahaifiyata ba dan kowa, yasan mahaifiyata macece mai gantali yau tna can gobe tana nan……. 

Tsararrakuna Kuwa, so sukeyi suyi abota dani… inada ilimi gwargwado 
duk da karancin shekaruna  inada kaifn hankali ga nutsuwa… Zama daya zakayi dani na shiga ranka…. 
Ina da shekaru goma sha biyar Allah yayiwa mahaifina  rasuwa, asthma itace tayi ajalinsa….

Allahu akbar naji imutuwar mabaifna domin Kuwa yadda na shaku da mahaifina banshaku da mahaifiyata haka ba.. 
Mahaifina baibar mana komai ba sai  dan karamin gidan da muke ciki… Syar da gidan umma tayi bayan ta kammala takaba.. Zawarawa sukayo kanta… Bayan rasuwar mahaifina da, watanni bakwai ummah ta auri malam kabiru… Matansa biyu yayansa takwas maza biyu Mata shidda duk ya aurar dasu…. Gidan haya ya Kama Mata….damuna uku manta guda biyu sai dan karamin wanda baiwuce akirashi da store ba. Wanda nake kwana acikinsa..  Bisa sharadin zama da marayun da aka barmata…. Malam kabiru namamajon mutum ne idanunsa tarr akan Mata…. Babu wanda baisan yana bin matan banza ba  a unguwartasu. Sam baida halin kirki kuma yayansa maza duka babu na kirki…. Sau tari nasha Kama malam kabiru yana kallon sassan jkina idan Bana cikin hijab.. Hakan yasa matukar yana gidan inatare da kton hijab Dina har saiya fita dan alokacin nake gautsan budurcina.. Hallituna na cikakkiyar mace suka fara bayyana inada Kira mai daukar hankalin duk wani lafiyayyen namiji.. Duk da bani da kiba amma shape din coca cola dani ga wani fitanannen kyau danake kadawa …. A wannan lokacin kuma na kara zurfi acikin ilimin addini islama nasan litattafaida dama da hadisan manzon Allah saw… Su kansu malamai makarantar jinjina kokarinda sukeyi…. Hakan yasa suka, waremin azuzuwn dazan dinga koyarwa alokacin Dana gama  (sanawiyya)  da karancin shekaruna ina aji biyar a, secondary school…  Ina koyar da matan aure da ajujuwan yn Mata…… _Wannan kenan_

Pls share and comment 
_maman boy_

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button