NOVELSUncategorized

SOORAJ 17

????????????????????????????????????????

               *SOORAJ !!!*

    *Written By*
Phatymasardauna

*Dedicated To My Life (Sardauna)*

*????KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*
_{United we stand and succeed; Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}_


           *WATTPAD*
    @fatymasardauna

#romance

          *Chapter 17*

Buɗe murfin motar yayi  ya shiga, batare da yace wa Mas’oud dake tsaye ƙala ba, zai rufe murfin motar ne,  Mas’oud yayi saurin riƙe murfin  ransa aɗan ɓace yace.
 “Wai hakan da ka keyi me yake nufi ne Sooraj? me kake tunani idan su Abba sukaji abun da ka aikata? menene amfanin hakan!!”  

Wani iska ya fesar daga bakinsa, tare da jingina bayanshi da jikin kujeran motar.  
“Mai kakeson ji daga gareni Mas’oud?”  yafaɗi haka cikin wata murya mai sanyi.

A ƙufule Mas’oud yace.  
“Bansani ba”  Juyawa Mas’oud yayi afusace yabar wajen, da ƙafansa ya nufi hanyar fita daga cikin asibitin, Sooraj na kallonsa ya tari taxi ya shiga, yana ganin tashin taxi ɗin  ya jawo murfin motarsa ya rufe, kifa kansa yayi akan steering motar, tare da sauƙe wata ƙaƙƙarfan ajiyar zuciya, ya ɗauki kusan mintuna 6 ahaka,  kafun daga bisani ya ta da motarsa ya fice daga cikin asibitin.    Direct wani super market ya nufa, zama yayi akan wata kujera, tare da umartan wata ma aikaciyar wajen da ta haɗa masa duk wani abu da tasan mace na da buƙata, kama daga kan suturun sawa da dai sauransu, take ita kuwa tashiga aikinta, kaya masu kyau ta jidar masa hadda su pants, kasancewar tasan duk wata mace indai ta girma to tana da buƙatarsu,  bai da mu da yawan kuɗin kayan ba haka ya cire ya biya,  yaran dake aiki a wajen su suka  kwashe kayan suka kai mishi cikin mota. 

Kafun ya koma asibitin saida ya biya ta wani hotel yayi take away,  sannan ya ɗauki hanyar komawa asibitin. Yana shiga asibitin direct ɗakin da aka kwantar da ita ya nufa. 
Tana kwance tana baccinta cikin kwanciyar hankali. 
Zama yayi akan wata kujera dake gefen gadon tare da lumshe idanunsa.   Kamar jiran zuwansa take ahankali ta ɗan soma motsawa, jin motsinta da yanda numfashinta ke fita ne, ya san yashi buɗe idanunsa,  haɗe da maida kallonshi gareta. 

 Ahankali ta soma ɗan ware manyan idanunta harta buɗesu tarwai,  saidai kuma kallo ɗaya zakayi mata kasan taji jiki, domin kuwa hatta ƙwayan idanunta saida suka sauya kala, sunyi wani fari fat dasu. 
 Tashi tayi ta zauna tana mai ɗan cije laɓɓanta,  sam batasan da cewa yana cikin ɗakin ba.   “Aushhh” taɗan saki wani ƙara, saka makon murɗawan da taji maranta yayi,  ɗan yarfe hannuwanta ta somayi,  tare da soma yunƙurin sauƙa daga kan gadon,   Idanunsu ne ya sarƙe acikin na juna, ji tayi gabanta ya wani irin faɗuwa, da sauri tayi ƙasa da kanta,  tare da haɗiyan wani yawu dake maƙale a maƙoshinta. 
Aƙalla yaɗauki kusan 50 second yana kallonta,  abun da bai taɓa yi ba kenan, ahankali ya janye idanunsa daga kanta tare da kawar da kanshi gefe.

Shiru ne ya shiga tsakaninsu na kusan mintuna 2,  jin wani abu  me ɗumi tayi ya fito daga jikinta, hakan yasa ta ƙosa ta je banɗaki ta duba ko menene,    ganin zaman bazai kaita ba yasa ta sauƙa daga kan gadon, banɗaki’n dake cikin ɗakin ta shiga tare da rufo ƙofar,   tashi shima yayi ya fita daga cikin ɗakin.

Bugun zuciyarta ne ya tsananta,  duk da kasancewar tasan abun da ta gani ajikinta mai yake nufi,  amma sai da ta ɗan tsorita. 
“Yanzu yazatayi kenan? wa zata faɗawa ya taimaketa?” Tambayar da tayiwa kanta kenan.  Ji tayi ana knocking ƙofar banɗakin, ai saura ƙiris ta zame awajen da take tsaye saboda tsoro,  atunaninta Sooraj ne ke buga ƙofar,   ƙafafunta ne suka soma rawa.    “Taya zata fara faɗa masa matsalanta?”  still ta kuma sake tambayar kanta,  jin anata buga ƙofar ba a tsaya ba,  ya sa ta taho cikin sanɗa ta buɗe ƙofar,  wata ƙatuwar ajiyar zuciya ta sauƙe,  sakamakon ganin wata likita mace da tayi tsaye abakin ƙofar, ashe ma ita ke buga ƙofar ba Mai taimako ba, saɓanin tunaninta. 

“Sannu ya jikinnaki?” nurse ɗin ta tambayeta.

“Da sauƙi” Ziyada ta bata amsa tana ɗan ƙaƙalo murmushin dole.  

“Masha Allah haka ake so ae, ga wannan saiki kimtsa kanki ko” nurse ɗin ta faɗi haka tana me miƙo mata wata baƙar leda dake hanunta. 
Karɓan ledan tayi tare da komawa cikin ban ɗakin,  tana buɗe ledan taga pad’s da kuma pant’s ne aciki, wani ƙaton ajiyar zuciya ta sauƙe, gefe guda kuwa tsananin mamaki haɗi da kunya ne ke ɗawainiya da ita, da farko dai mamakin yanda akayi nurse ɗin tasan halin da take ciki take, na biyu kuma tsantsar kunyar nurse ɗin ne ya kamata,  wani pant ta ɗauko wanda anriga da an maƙala pad ɗin ajikinsa, kallon yanda aka maƙala pad ɗin tayi da kyau, sai da ta ciro wani pant ɗin ta gwada maƙalawa taga yayi sannan ta sauƙe ajiyar zuciya, kasancewar dama bata san ya ake amfani dashi ba.    Aɗaɗare ta fito daga banɗakin sai dai rashin ganin kowa da tayi acikin ɗakin hakan sosai yayi mata daɗi.  Tana zama akan gado, akaturo ƙofar ɗakin, wannan nurse ɗin ce dai ta kuma dawowa,  bayani tayi mata sosai akan yanda zata kula da kanta, da kuma yanda za tana tsabtace jikinta, sannan tace mata taje yayanta na jiranta a mota.  Ɗaukan ledan da nurse ɗin ta bata tayi,  sannan suka fito atare da nurse ɗin, har bakin motar Sooraj nurse ɗin ta rakota sannan sukayi sallama. 

Tana shiga cikin motar ko gama gyara zamanta batayi ba ya yiwa motar key.  Saida suka hau titi sannan ta ɗan saci kallonsa ta gefen idanunta,  maganane abakinta, amma yanda fuskarsa take babu alaman wargi, yasa taja bakinta tayi gum,  ita ayanda ta fuskanta ma shine, shi ko da yaushe ahaka fuskarsa take. 

Basu yi wani tafiya sosai ba, ta ga  ya gangara gefen titi tare da tsaida motar cak,  juyawa yayi ya ɗauko wata leda dake  aje a sit ɗin baya, miƙo mata ledan yayi  tare da cewa.
 “Kici yanzu yanzun nan sai kisha magani”

 Baijirayi mai zata ceba ya buɗe murfin motar ya fita, tana kallonsa ya shige cikin wani waje mai kama da kamfani, wanda yake gaba kaɗan da inda ya aje motar tasa,  ledan ta buɗe ta ciro take away ɗin, rubber spoon ɗin dake jikin  take away ɗin, ta zare haɗe da sanyawa acikin abincin.   ahankali take tsakalan abincin, gaba ɗaya bata wani jin daɗin bakinta, duk da cewa tana jin yunwa amma batajin abinci zai wani samu shiga cikinta sosai,  bata wani ci abincin sosai ba,  ta rufe take away ɗin tare da maidashi cikin ledan, goran ruwan da tagani a inda ya tashi tasanya hanu ta ɗauka,  buɗewa tayi tare da kai bakin  goran bakinta,  lumshe idanunta tayi, tare da sauƙe wani irin ajiyar zuciya, tayi imani duk wani abu da zai fito daga gareshi to ƙamshi yake, hatta goran ƙamshinsa take, tana son wannan ƙamshin nashi har acikin ranta, bama ita kaɗai ba ta tabbatar duk wanda yaji ƙamshin nashi dole zai so sa.  Bata fargaba sai kawai jin motsinsa  tayi a gefenta, da sauri ta kalleshi don sam batasan da zuwanshi ba,    buɗe wani waje mai kama da ɗan ƙaramin drawer dake cikin motar yayi, magungunanta ya ciro, da kansa ya ɓare magungunan ya miƙa mata, aƙoƙarinsa na ya zuba mata magungunan acikin hanunta ne hannayensu suka haɗe waje guda,  da sauri ya zuba mata magungunan acikin tafin hanunta, tare da zare nashi hanun,  ba don taso ba haka tasha magungunan kasancewar suna da ɗan ɗaci, tana sha ta jingina bayanta ajikin kujera tare da lumshe idanunta.    Tuƙi yake amma gaba ɗaya hankalinshi na ga wayarsa yana duba wani saƙo da aka turo masa, ahaka har suka isa gida. 
Yana danna horn mai gadi ya wangale masa gate ya tura hancin motar ciki.  

Jin sun tsaya ne yasa ta buɗe idanunta ahankali,   ganin yana ƙoƙarin fita daga cikin motar ne, yasa itama ta buɗe murfin motar ta fita.  Sawa yayi Kamalu driver ya shigar masa da kayan da ya sayo ciki. 

 Yana shiga cikin ɗakinsa ya kwanta flat akan gado tare da lumshe idanunsa,  kamar an tsikareshi haka ya buɗe idanunsa da sauri, bakomai yasa hakan ba face, ganin oily eyes ɗinta da ya keyi  suna yi  masa yawo acikin nasa idanun, hakan kuwa na sawa yaji wani iri ajikinsa.
Ban ɗaki ya wuce ya haɗawa kansa ruwan wanka..


Itama tana shiga cikin ɗakinta,  gado ta hau ta kwanta, tare da cusa kanta acikin pillow, abu kamar wasa sai ga wani sabon bacci ya sake ɗaukanta…

***   Tsakanin  jiya da yau Alhamdulillah ciwon ya ɗanyi mata sauƙi,  kwana biyunnan jinta take atakure, zuwa yanzu ta saba da makaranta,  shiyasa takejin zaman gidan gaba ɗaya bayayi mata daɗi, gashi shima Ogan gidan ba ganinshi take ba, ita kaɗai take rayuwarta,  jakar makaramtarta ta ɗauko ta shiga haɗa littatafanta, tana gamawa ta jawo ledan abincin da aka kawo mata ta soma ci, bata wani ci mai yawa ba ta ture abincin gefe, jin gidan ya ɗauki shiru babu alaman motsin kowa acikinsa ne yasa ta fita zuwa falo,  kusan kullum TV plasma’n dake cikin falon a kashe yake, amma yau ga mamakinta akunne ta sa meshi, zama tayi akan sofa tare da maida hankalinta ga TV’n,  tana nan zaune acikin falon har aka ƙira sallan Isha sai alokacin ta tashi ta koma ɗaki, tana shiga tayi kwanciyarta, kasancewar ba sallah takeyi ba.  

 1:30 na dare,  ƙaran taɓa gate ɗin gidan da ake,  shine yayi sanadiyar tashinta daga bacci, ahankali ta sauƙo daga kan gadon,  bakin window ta nufa don ganin wake taɓa gate ɗin, duk da babu wadataccen haske aharabar gidan, amma inuwarsa kaɗai yasanya tagane wanene,  domin akaf gidan babu wani mai irin yanayin jikinsa shi kaɗai ne,  tana ganinsa da kansa ya buɗe gate ɗin gidan,  sannan ya koma ya shigo da motarsa ciki, tana ganin ya mai da gate ɗin ya rufe ta ɗan saki wata ajiyar zuciya, mamaki da wani kokonto ne suka ɗarsu acikin zuciyarta,  don son sake tabbatarwa da kanta cewa shiɗinne ko ba shi bane, yasa ta ɗan buɗe ƙofarta ahankali fitowa tayi ta tsaya abakin ƙofar,  dai dai lokacin shi kuma ya buɗe ƙofar falon ya shigo,  key ya murza ajikin ƙofar sannan yabar key ɗin ajiki,  Yana maiƙoƙarin cire rigar dake jikinsa ya ƙarasa gaban fridge. Buɗewa yayi ya ɗauko goran Fearless.  Wuceta yayi tamkar baiganta ba, alhali kuma tunshigowarsa idanunsa suka gane masa ita, harya ɗaura hanunsa akan handle ɗin ƙofar ɗakin nasa, sai kuma ya dakata batare da ya juyo ba yace.

 “Me kikeyi anan?” 

Ziyada dake ƙoƙarin komawa ɗaki, taji sauƙar muryartasa tamkar rugugi acikin kunnuwanta,    da sauri ta juyo garesa saidai bata iya kallonsa ba, duk da cewa  ya bata baya. 
 “Babu”
Tace murya asanyaye.

“Wani abu ya faru ne?”  Yasake tambayarta still batare daya juyo ya kalleta ba.

“A’a”  Ta bashi amsa muryarta naɗan rawa,  hakanan idan yana gabanta sai taji wani irin tsoronsa ya kamata. 

Murɗa ƙofarsa yayi ya shige ciki
 tare da rufo ƙofar,  tana tsaye taji ya murzawa ƙofar key ta ciki,  ajiyar zuciya ta sauƙe haɗe da komawa nata ɗakin itama,  da ƙyar ta samu bacci yasake ɗaukanta.

Shikuwa bai iya samu bacci ya ɗaukesa ba,  har sai da yasha maganin da ke taimaka masa wajen sanyashi bacci, duk da haka dai baccin baiyishi cikin daɗin rai ba.    


7:00 
Daidai ta gama shiryawanta, tayi kyau acikin uniform ɗinta kamar kullum, tana kammala saka white socks ɗinta, tasoma jin ana knocking ƙofar falon, school bag ɗinta ta rataya bisa kafaɗanta sannan tafi ta zuwa falon,  dama bata saba ganinshiba don haka batasa aranta zata ganshi ba. Tana buɗe ƙofar wanda ke kawo mata abinci kullum yaɗan yi mata murmushi, itama murmushin tayi masa tana ƙoƙarin gaidashi ne ya miƙo mata wata kula mai kyau wacce take da ɗan mariƙi a samanta. 
 “Madam ga saƙonki inji Oga”  yace da ita.
Karɓa tayi, shikuma ya juya yayi tafiyarsa,  komawa cikin falon tayi tare da buɗe kulan. Kulan irin mai hawa ukunnanne wato (3pieces) hawan farko da ta buɗe soyayyen dankali ne aciki wato chips da kuma ƙwai, sai hawa na biyun dake ɗauke da gasashshen nama mai albasa, hawan ƙarshe shine ke ɗauke da shinkafa fried rice wacce taji liver,  ɗaukan kulan tayi ta riƙe ahanunta, tana fita waje ta samu Kamalu yana tsaye ajikin mota yana jiranta.    Tunda suka ɗauki hanyar makarantar yau Kamalu keta mata zuba, ita dai ba gadon magana bace hakan yasa take amsa masa kaɗan kaɗan, shikuwa sai labarai yaketa bata, ganin yanda take amsa masa ne, yasa aranshi yace “Duk yanda akayi itaɗin jinsin Oga ce, da’alama duka zuri’arsu haka suke basason magana” 

Yau kam Su Nasmah sun rigata zuwa, tana zama Nasmah ta ce “Ki koma kinyi late” 

Dariya ta yi tare da ɗan satan kallon Shukrah,  matsawa kusa da Nasmah tayi sosai cikin ƙasa da murya tace.
 “Yau maiyasamu Shukrah na sake ganin fuskarta babu walwala?” 

Baki Nasmah ta taɓe haɗe da cewa.  “Hmm barta kawai kekam wahalane bai ishetaba, wai fa soyayya take kullum kuma sai sunyi faɗa da saurayin” 
Idanu Ziyada taɗan zaro waje cike da mamaki tace.  “Soyayya!” 

“Eh Soyyayya” Nasmah ta faɗa tana ɗan kallonta.

Shiru Ziyada tayi tare da jin wani abu acikin ranta. “Kenan dama Soyayya gaskia ce?”  tambayar da tayiwa kanta kenan sannan ta kuma sake tambayar kanta “Menene alamomin soyayya?” 

“Yanaga kamar kina tunani” Cewar Nasmah da ta shiga mamakin yanayin da taga Ziyada ta shiga. 

“Babu” Ziyada tafaɗi haka tana ɗan yin murmushi, Malamin English ne ya shigo cikin ajin hakan yasa suka bada gaba ɗaya hankalinsu gareshi. 

Yau a wajen da aka tanadar musamman dan cin abincin ɗalibai sukaci abincinsu,   ita dai Shukrah gaba ɗaya bata da wani walwala, Ziyada da Nasmah ne kawai suketa sha’aninsu.   Shaƙuwar da ke tsakanin Ziyada da Nasmah shine ke ƙarawa Ziyada jin daɗin rayuwar makarantar.   Yau ba atashesu ba har sai biyar da rabi kasancewar anshiga dasu meeting akan jarabawan da zasu fara next month.    Agajiye ta dawo gida ga ciwon cikin dake  sanɗanta, da ruwan zafi tayi wanka sannan ta kwanta.  
 11:00  ta farka daga ɗan baccin daya ɗauketa,  wani irin ciwon da cikinta keyi mata shine abun daya ɗaga mata hankali,  Kuka take hanunta dafe da saman mararta wanda takejinta kamar zata ɓalle. 

Yana zaune akan gado yana danna laptop ɗinsa, ahankali ƙaran kukanta ya shiga kawowa kunnensa ziyara.  Ɗauke hanunsa yayi daga kan laptop ɗin tare da yin shiru yana mai sauraran yanda kukan nata ke tashi. Kallon agogo yayi yaga ƙarfe 11:10 na dare,  wata ƴar ƙaramar tsuka yaja tare da sanya hanu ya dafe goshinsa.  “Me na ɗaukowa kaina ne?” tambayar da yayiwa kansa kenan.  

Jin kukannata na daɗa ƙaruwa ne yasan yashi miƙewa, ƙofar ɗakin ya buɗe ya fita, tsayawa yayi ajikin ƙofar ɗakin da take yana mai tunanin shiga cikin ɗakin.  Jin taƙi daina kukan ne yasashi murɗa handle ɗin kofar ya shiga.   Yashe ya ganta aƙasa tanata birgima gaba ɗaya gashinta ya watse akan tiles, kuka take irin na fitar hayyaci.  Ƙarasawa yayi inda take yashe aƙasan tana ta mutsu mutsu, hannayensa yasanya ya kama kafaɗunta, jin sauƙar hanun mutum akan kafaɗunta yasanya ta kama hunun nasa ta damƙe da ƙarfi,  da ɗayan hanunnasa da bata kama ba yayi amfani wajen ɗago haɓarta, gaba ɗaya fuskarta ta ɓaci da hawaye, zara zaran eye lashes ɗinta sun jiƙe da hawaye sun manne akan fatarta.  Hanunsa dake cikin hanunta ta ƙara matsewa tare da sakin wani ƙara,  ji take kamar taita buga kanta ajikin gini ko zata samu salama,  ganin yanda take shiɗewa ne yasanya shi ɗagata caɗak ya nufi kan gado da ita, kwantar da ita yayi, tare da ɗauko magungunanta ya bata.
***
After 30 minute har yanzu gunjin kukanta ne ke tashi acikin ɗakin, sama da mintuna talatin kenan da bata magani amma har yanzu ciwon bai lafa ba, tun tanayin kukan da duka jarumtarta har takai tanayin kukan acikin yanayi na galabaita, hankalinsa ne yasoma tashi,  wayarsa ya ɗauka ya ƙira Number’n Dr.Waleey, shaida masa abun dake faruwa Sooraj yayi, shiru yayi yana maijin amsar da Dr.Waleey ke bashi, cikin rashin ƙarfin guiwa ya aje wayartasa bayan sunyi sallama da Dr.Waleey’n,   shiru yayi haɗe da zuba mata mayun idanunsa,   sosai zuciyarshi ta karaya akanta, wani irin tausayinta yaji ya daki zuciyarsa, duk wanda yaganta acikin irin wannan halin sai ya tausaya mata, musamman yanda tayi buji buji da gashin kanta, ga numfashinta dake ƙoƙarin sarƙewa tsabar kukan da tayi,  maganganun Dr.Waleey ne suke dawowa cikin kunnensa.   Bayajin zai iya aikata abun da Dr.Waleey yace yayi, sannan kuma bayajin zai iya jure ganinta acikin halin wahala,  baisan maiyasa yake jin son taimakonta ba tun farko, ayanzu yanaji inama da ace tun farko bai taimaketa ba,  rumtse idanunsa yayi da ƙarfi sakamakon yanda yaga takeyi, baida wani zaɓi wanda ya wuce ya taimaketa, tashi yayi ya nufi gadon, sautin bugawar zuciyarshi ne ya tsananta yayinda ƙirjinsa ke tsalle kamar zai faɗo ƙasa, da ƙarfi bugun zuciyarsa ke harbawa…  


(Na yau dana gobe duka na haɗa muku???? kuji daɗinku ku more, idan ku naga kamar naso kaina, sai ku karanta rabi yau gobe ku ƙarisa karanta rabi????) 


          [12/April/2020]


      *Vote Me On Wattpad*
          @fatymasardauna

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button