NOVELSUncategorized

RUWAN JAKARA 2

*BRILLIANT WRITERS ASSOCIATION*                  
( _pens of freedom, home of exceptional and magnificent writers_)                 *RUWAN JAKARA*………….    

                *~LITTAFIN~*???????? 

 _MARYAM HAMISU YUSUF (Maman boy)_
~True life story~


“`page“` *2* Yau ta kasance ranar asabar,  da misalin karfe Tara na safe nagama shirina na tafiya makaranta…
 Katon hijab Dina na saka  nikab Dina yana hannuna na fito tsakr gidan…. 
Inajin farin ciki araina koba komai nasan yau mahaifiyata bazata fita gantalin da ta sababa saboda mijinta agidan ya kwana… Bawai kuma dan tana tsoronsa bane take kin fita idan yana dakinta saidai daya saka kafa yabar gidan itama Zata fita.. 

Duk da kasancewar shidin ba yawan fita yakeyiba dan shikansa baida rikakkiyar sanaar yi daga bin inuwa sai zaman majalissa da kuma bin Mata…

 Tun kafin na isa kofar dakin ummah nakeji yadda suke ta sa insa da malam kabiru akn dole sai tafita tunda ba abinda zai wadatar da ita yake barmata.. 
Shikuwa ya kafe akn babu inda zata tafi matukar shine yake aurenta…. 
Sallamr danayi ce abakin kofar dakin yasakasu yin shiru cike da haki ummah ta amsa min sallamr sannan na shigo…. 

Cirko² na Tarar dasu kamar masu shirin taka dambe.. Umma Kuwa sai huci takeyi… Durkusawa nayi muryata na rawa sakamakon kwallar da ta cikamin idanu nace “zan tafi makaranta “
“To zan hanaki ne ki tashi ki tafi mana ko kuma na huce takaicin wannan najadun aknki”…. 
Dasauri na dago da kaina… “Anya mahaifiyata kuwa tasan darajar aure… Duk da mijinta ba na kirki bane ba halayyar arziki bane tana muzantasa agabana ba “….. 

Washe baki kabiru yayi yana kallona tare da katsemin tunanin “zarah tashi ki tafi makaranta, wlh hajara barikinah tafi taki”.ya idar da maganr yana Nuna umma da yatsa”

Jiki amace natashi ina sharar kwallah Idan Kin tashi daga makarantar ki wuce gidan Alhaji mansoor… Dan wlh na fara gajiya shima ai ubankune ko bayaso dan haka dole ya kula daku”. …… 

Umma ta fada tare da tillo min wata tsohuwar Dari biyu wacce zanyi kudin napep dasu… 
Durkusawa nayi nadauki kudin Allah  Maya sani na tsani zuwa gidan Alhaji mansoor.. Dan banason wulakanci ko kallon banza … Saidai ayadda umma take yanxu kamar kububuwa nayi Mata musu wani sabon masifar ne hakan yasa na fice daga dakin…. 

Saida na tsaya a soron gidanmu na goge fuskana data gama baci da kwallah sannan na saki nikabi na nacigaba da tafiya ahnkali har na isa makarantar….. 
Bayan na gama koyamusu kamar yadda ya kamata zan fita maman abbah ta biyo bayana “malama zarah akwai maganr da nakeso muyi dake amma dan Allah idan antashi makaranta inaso ki biyo ta gidana dan akwai abinda ke dsmuwa… “(Dayake a unguwarmu take) 
Jinjina kai nayi kafin nace allah yasa mu tashi lfy…. Amma bayan sallar zuhr  zan shigo insha Allah.. Domin akwai inda zanje idan na tashi makaranta “… 
Cike da shaawar halayena tayi murmishi bakomai malama  zarah allah yasaka da alkhairi ya baki miji na gari… “
Kunya tasaka nayi saurin Sakin nikab Dina na ta fi ina murmishi….


Bayan da aka tashi makaranta ina dai² fita daga get din makarantar naji a namin horn da rashin kifar hyjo.. Duk da ban juya ba nasan arra isiI madrisa ne {shugaban makaranta)… Murmishi nayi tare da Sauke ajiyar zuciya na tsaya har ya karaso… Shima kallon nawa yake yana murmishi irin kallon dayake jifana dashi yasani saurin sunkuyar da kaina kasa.. Ajiyar zuciya yasauke tare da Lumshe idanunsa ya waresu akaina…. “Zarah guduna ma kikeyi ko?  Ko shigo makaranta bakya yadda muhade…. “Ya idar da magana yana kuma zubamin tsimammun idanunsa duk da shi kansa yasan inasonsa tsananin. Kunya ne yasaka nake gujemasa.. Barinma nidin yarinta ce….. 

Sunkuyar da kai  na nayi ina murmishi kafin nace “ba hka bane muallim”… 
To naji kome kenan gobe insha Allah  zan shigo dan nakosa nafada samun soyayyarki “.. 
Dago da fararen idanuna nayi ina dubanss tacikin nikab kafin nace “ai maman amira na kula dakai”…(kasancewar yanada aure) 
Dariya yadanyi tare da shafa gemunsa “aike ta dabance zarah maman amira ma tasan da labarinki kuma takan yawan fadamin tana gaisheki… Zarah kibani dama nagana da iyayenki wlh aurenki nake so nayi.. Zanyi alfahri idan na zabawa yarana uwa tagari mai add in malama hafiza kuma irinki… “
Yadda ya idar da maganr yana dubana kawai hakan ya tabbatar min da gaskiyar abinda yake fada…. 
Tabbas inason malam kamal sosai… To saidai gani nake nidin nawa nake.. Koba komai kasan mahaifiyata bazata taba yadda da malam kamal ba dan bashine irin mijin da takeso na auraba…. Duk da shidin ba laifi yanada rufin asiri matarsa daya hannatu da yayansa biyu amira da ammar.. Shekarunsa biyar da yin aure… Tun ina yarinta kwarai malam kamal ke rainin soyayyata azuciyarsa har zuwa lokacin dayaga yadace yasanar dani….
A sanyaye na dubesa nace “ya mu allim ka kara hakuri kasan komai akwai lokacinsa…. 
Ajiyar zuciya ya saki “a gaskiya na kosa na mallakeki please… Zarah”… 
Ya idar da maganr a kasalance kamr mai shirin samin kuka….. 
Shiru na sanyi kafin nace “ya mu allim rana nayi zan wuce “.. 

Yaso yakaini gida amma naki.. Hakan yasa mukayi sallama dashi…. 
Mai napep na Tara na hau muka dauki hanyar gidan Alhaji mansoor…. Adai² katafaren gidan mai napep din yatsaya tamkar yadda nabasa umurni na ciro kudinsa na mika masa na nufin bakin gate din gidan na fara knocking zuciyata na tsananta bugawa… Na jima ina bugs gidan kafin mai gadi ya budemin gidan…. Kallon sama da, kasan da yake min ya tabbatar min da bai shaidaniba hakan yasa na yaye nikab Dina ina gaidasa…. 
Washe baki yayi dan yanxu ya ganeni…tsohon yanada mutunci duk wanda yake da alaka da Alhaji mansoor yana mutuntasa….. 
“Aah malama zarah kece agidan da rana haka bismillah shigo”….. 
Ya fada tare da kara budemin gidan… Na shigo inayimasa Godiya….. 

A sanyaye na fara keta farfajiyar gidan zuciyata duk atsorace take dan banason abinda zai saka awulakantani………… 


Da sauri na dauke idanuna daga abinda nagani..  Anwar ne shida wasu Mata uku da wani matashin saurayi kamarsa suna buga was an suluka a inda aka yanada domin wasanni.. Dan gidane mai she gen girma… Daga shi sai farar singlet da 3quarter wanda ko gukwowinsa basu gama rufewa ba…. Hakan zaisa har gashinan dake kwance akirjinsa da kafafunsa zaka iya gani…. Dan mutum ne shi mai faffadan kirji.. Ga wani irin aski da yayiwa sumar kansa da kasumbarsa da ya ajiye.. Yan matan dake gefensu kuwa basuda banbanci da a kirasu da karuwai… Tun daga irin shigarsu har zuwa karan sigarin dake hannun su suna suka…. Har gara abokinnasa Mubarak… Duk da, shima cikin shigar kananun kayan yake… 
Rike sander dake hannunsa yayi yana jifata da wani irin kayataccen kallo tamkar yaune yafara ganina…. 
Saurin kawar da kaina nayi nacigaba da tafiya a hnkli…. 
Ajiye Sandar yayi yana shafa gemunsa “ku jirani zan fito “…. 
Dariya mubarak yayi lallai anwar ido da Mata…. Waccan karamr cikar me kuma ka gani a ajikinta…. 

Tsaki anwar yaja “ni naga abinda nagani… Kasan bakowace kucaka nake kulawaba…. Koda ajikinki Saida rabonki “…dariya Mubarak yayi… Yayinda anwar ya nufi cikin gidan…. 

Falon babu kowa sai suwaiba me yimusu aiki tana goge plasma din dake manne a bangon falon … Washe Baki tayi tare dayimin sannu da zuwa bayan ta amsamin sallama ta…. 

Zama nayi a dayadaga cikin Kayattun kujerun falon…. Ruwa da lemo mai sanyi suwaiba ta ajeyimin agabana tare da tsiyayamin lemo… Murmishi nayi na karba na fara kurba sanyinsa yafara ratsani musamman yaddacna shawo rana duk da har ynxu banji motsin yan gidan ba…. 

Shigowar Anwar ta katsemin tunanina…. Karasowa yayi ya zauna kujerar dake facing Dina yana min murmishi…. Saurin dauke idanuna nayi… Dan basaba ganin namiji da shiga tarashin kunya ba irin anwar….. 
“Daga ina muka samo bakuwa hka? “…. 
Yayi maganar yana duban suwaiba… 
Takasan ido na kallesa rainin wayo nidin ce anwar bai gane ba? 
“Zarah ce fa.. Yar uwarku”…. 

Fiddo da manyan idanunsa yayi yana dubana “wow looking so pretty… Zarah kinkara kyau da girma “… 
Ya idar da maganr yana jifana da kallon kurullah da kayattun idanunsa… Sunkuyar da kai na nakumayi duk na takura da kallon daya tsare ni dashi… Ga fira dayake kokarin jana da ita… Saidai ya lura nidin miskila ce magana bata cika damuna ba wannan nadaga cikin abinda ke kuma burgeshi….. 
Shigowar Alhaji mansoor da hajiya salmai yasaka anwar tashi ya nufi mahaifinsa.. Rungume juna sukayi alhaji mansoor na bubbuga bayansa “daddy da baka Nigeria komai na, lamurran office banajin dadinsa gaskiya daddy ka dade a dubai “… 

Shoulder dinsa alhaji mansoor yasan bubbuga “kayane suka dan samu tsaiko dole sai ina wurin kafin su samu karasowa that is why na jima… Ya office baka wasa ko? “.. 

Daddy inada hard work zaka iya tambayar mom…. 
Itadai mom dariya kawai takeyimusu…. 
“Dad haka zarah ta girma takara kyau… “

Sai alokacin Alhaji mansoor da hajiya salmai suka dubeni…. Nikam kunya duk ta gama rufeni yadda na gardi kamar anwar yana zuba shagwaba…. 
Zamewa nayi daga kan kujerar na gaidasu…. 
Adakile suka amsa min… Musamman hajiya salamatu… Alhaji mansoor kuwa wucewa yayi abunsa…. 
Raina yayi mummunan baci amma bakomai umma ta jamin..
Haka na sha zamana har lokacin da nazifa tafito sanye cikin wata doguwar rigar bacci bacci.. Iyakarta guiwa kanta kuwa ba kallabi tasha kitson attach… shigar ta kawai ya isa ya nuna maka yanxu ta tashi daga bacci, Yayinda ta fara kadawa suwaiba wulakantaccen Kira… Da sauri suwaiba ta karaso… 
Ki hadomin tea ki kawomin aside Dina….  Dasauri suwaiba ta tashi zata tafi…. 
Hu
Jimana!!!! Karkumayimin gidadancin sakamin madara a tea vourn vita kawai zaki zubamin.. Idan kuma aka samu akasi saina wanks wannan mummanr fuskar taki dashi”…. 
Jinjina kai suwaiba tayi “kiyi hkr zan kiyaye”… 
Ta fada tare da ficewa… Ko kallo ban ishi nazifa ba bare magana haka takoma side dinta…. Nikam idanu kawai nake bazawa wannan wane irin bahagon gidane… Babu sanin darajar dan adam bare sanin islama”…. 

Bayan fitar suwaiba da nazifa anwar yadinga jana da surutu…. A hakali na fuskanci yadda yake kuma matso wa kusa dani… Ban Ankara ba sai ji nayi numfashi mu na karo Dana juna har yafara kokarin kai hannunsa jikna… 
Zumbur nayi na mike tsaye tare da fadan “azubillahi Minasshaidanirrajim……….. “


Kuyi manage
_maman boy_

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button