NOVELSUncategorized

RUWAN JAKARA 10

*BRILLIANT WRITERS ASSOCIATION*                  
( _pens of freedom, home of exceptional and magnificent writers_)                 *RUWAN JAKARA*………….    
    { _idan baa sha abirni ba asha akauye_)} 
                *~LITTAFIN~*???????? 

*MARYAM HAMISU YUSUF (maman boy*) 

~TRUE LIFE STORY~

“`page“` *10*
“Ki kyaleshi ya tafi zuciyarsa ce ta dau zafi a yanxu zai dawo ya samemu… “.. 
Alhaji mansoor ya fada tare da zama akan kujera yana dunkule hannunsa yana bugawa…a dayan hannunsa sai huci yakeyi kamar kumurcin maciji Yana tunanin yadda zai billowa lamarin anwar….zuciyarsa namasa,  zafi sosai 


Girgiza kai momy takeyi takasa nutsuwa da kalaman alhaji mansoor  da sauri ta fice ta nufi sashin anwar… Tasan waye dannata zai aikata fiye da abinda ya fada din….

Anwar na shiga bedroom dinsa ya sakawa kofar key Dan yasan dole mom ko dad su biyosa rarrashi… Matukar bazasu bari yayi abinda yake bukata ba… Shima bazai saurarawa duk wani Wanda zaizama shamaki da zarah ba… 
Fadawa yayi akan royal bed dinsa aringingine face dinsa na kallonsa sama ya lumshe idanunsa… Zuciyarsa nayi masa turiri. UCI Kawai yakyi.. Ahankali ya soma jin sauki sakamakon kulle idanunsa da yayi suna kuma tariyomasa diri na halittar Fatima.. Wata irin wutar shaawarta ce ke bijiromasa wacce bayajin zai iya ssuketa a yanxu a wurin wata ya mace ba itaba… Tsagwaron boyayyen kyanta daya yank ya makantar dashi daga kallon wace ya mace (na naucin gadi)
Bude jajayen idanunsa yayi tare da tashi ya nufi medium fridge din dake dakin ya buda ya dauko robar ruwa ya kfa abakinsa yana sha a hankali ykejin sanyin ruwan na ratsasa….  Zama yayi bakin gadonsa ya kunna sigari yana aha tare da sauke ajiyar zuciya…. 
Knocking din da momy keyi ya sakasa kallon kofar 
“Anwar ka Budemin kofar… Kada kafara tunanin aiwatar da abinda kake tunanin dai² ne agareka….
 Yanajin mommy knocking  yayi banza da ita ya kyale daga karshe toilet ya shige ya watsa ruwa ya saka wasu kananun kaya ya dauki key din motarsa ya fice ta baya…. 
Gidan Mubarak ya anwar ya… Afalo Tarar da shi yagama shiri zai fita.. Tafawa sukayi… “Ina zuwa haka…
Anwar ya fada yana zama kn kujerar ya na duban Mubarak yana balle bottles din rigarsa “guy ta samu ne wata zazzafa ce mukayi p. A da ita… Babyn akwai class “… 
Tsaki anwar yaja tare da kwantar da kansa akan kujerar da yake dune “robishnesss… Nifa zan dagawa bariki kafa.. Cos aure zanyi immediately “.. 
Anwar ya idar da maganr Yana murmishi 


Zaro idanu Mubarak yayi tare da zama akan kujera Yana facing anwar fiskarsa cike da mamaki yace”what aure fa kace…. Hhh wai ko ta karemaka ne ko barikin ta daina yayinka ne “.. 
Ya idar da maganr Yana dariya…. 
Daure fuska anwar yayi Yana magana “brain dinka karamace.. Kamar yadda kake karami acikin barikin ko ka manta nine na Raine ka “… 
Gimtse dariya Mubarak yayi Yana bubbuga kafadar anwar “sorry my am so shocked  danaji kace aure.. Maida wukar.. Wace yarinyace kake son aura “… 
Ya idar da maganr Yana tattara attention dinsa akan anwar…. 
“Sunanta zarah.. Tana da karancin shekaru…. Shekarunta 17yrs ne.. Raunin taulacinsu shine zai bani damr mallakarta.. She’s my sis ta ko Ina yarinyar zafi ne da ita “… 

Jinjina kai Mubarak yayi “amma baka ganin zubewar ajinka a cikin abokanmu… But Miye old man dinka ya fada “.. 
Lumshe idanu anwar yayi ya ware su akan Mubrak “banason wani azan da maganar nan Dan in secret nake son aurenta . Old man dina  kuma na firgatsu shida momy Dan nsaanr musu zan dauke yarinyar na gudu da ita… 

Dariya Mubarak yayi tare da fdan “amma ka iya iskanci wato barikinnaka har su bai bariba… 
Dariya Shima anwar yayi… A tare suka ficee suka bar gidan.. 

Hankalin momy yayi masifar tashi.  Akan kalaman anwar kwana uku kenan Bata saka sa a ido ba… Duk da wannan ba bakon Abu bane a gareta sai tajj ta damu da hakan… 
Kallon alhaji mansoor tayi da yayanta hankalinsu kwance suke dinner akan dining table… Itakam juya cokali Kawai takeyi a cikin plate… 
Karaf suka hada idanu da daddy.. Ajiye cokalin dake hannunsa yayi cikin kulawa yake duban momy “hajiya salmai wai meke damunkine haka.. Kintasa abinci gaba kina tunani…. “

Bata rai ta kumayi cikin shagwaba tasoma magana “ta yaya daman zan kwantar da hankalina.. Ka ki daukar mataki akan lamarin anwar.. Har yau bai shigo gidanba.. Zuciya na na bani ba lafiya ba… “

Ta idar da maganar tana juyar da kanta gefe… Rarrashinta dad ya somayi “haba madam kamar bakisan halin Dan namu bane… Kinsan anwar taurin kai ne dashi.. Kuma lokacin da muke rarrashinsa a lokacin yake kuma turbeke mana.. At least  ya dauki  almost two months baya zuwa office.. Bazaiyi abinda zai cutar da kansa shiga taro bane… “.. 
Turo baki ta kumayi tare da juya masa keya… 
“Sorry yanxu me kike so ayi”.. 
Jiyo da fuskarta tayi “Kawai ka amince ya aureta kuma yadawo gida na gansa hankalina ya kwanta…. 
Dariya alhaji mansoor yayi “indai wannan ne madam na jima da, amincewa… Kinsan ko ban amince ba sai yayi “…. 
Yanxu kici abinci please hajiyata.. “
ya fada Yana turo mata plate din gabanta… 
Murmishi tayi ta soma cin abincin…. 
Sai alokacin nazifa tayi magana tare da tabe baki “wlh ya anwar ya dai zubar da ajinsa ya tsaya auren yar fuqarau… Look at manyan matan dake zuwa gidannan suna sansa… Ko kawata kariyya tana maifar son ya anwar.. Na dakatar da ita.. Dan nasan yafi qjinta… Nikam wlh ko bikin bazanyi attend ba bare nayi invite din frnds dina …


 Ta idar da maganar ranta abace…. 
Sumaiyya ta karbe znacen da cewa “look at uh kinbi kinwani daga hankalinki.. Kamar bakisan waye ya anwar ba… Wlh na fahimci auren nice shaawa zai yi da yarinyar kuma da bukstar sa tabiya zai fitar da ita..  And as I telling uh auren na naucin gadi ne “… 
Rike haba momy tayi “lalai yarannan.. Anwar dinne kuma sakawa idanu hka..”
Tashi nazifa tayi tabar wurin sai hurar hantina takeyi… 
Dariya dad yayi “gaskiya nazifa tana da zafi… Babu inda ta baroki fa “
Ya idar da maganr Yana kashewa momy idanu cikin sugar zolaya…. 

Murmishi Kawai tayi Dan batajin yan maganar ayau.. Shysa.. 

Hankalin momy bai kuma kwanciya ba saida alhaji mansoor da kansa yaje gidanu ya nemawa anwar aurena. Bai baro gidanba saitare da ansaka ranar aurena da anwar sari uku masu zuwa… 
Ummah ji takeyi tamkar t zuba ruwa kasa tasha Dan murnar wannan rana datake ciki a ranar  ta siyo kwalayen biscuits da chewing gum.. Ta kulla ta kai ko Ina a makwabta na na saka ranar aurena… 
Duk abinnan da akeyi bansani ba Dan Ina makarantarmu boko kasancewar gab muke da fara exam sai laasar muke dawowa… 
Agajiye na shigo gidan ga yunwar dake kwakulata.. 
Ina shigowa da sallama… Iya asiya yayar mahaifiyata ta rangada guda…. 
Da gudu hannatu yarta ta karaso inda nake tare da rungumeni “amarya mai goshi walh zarah kinada saa… “

Cike da mamaki na zame jikina daga nata Ina kallonta na kalli gwaggo kwazo dake gefen ummah tana murmishi… 
Wacece kuma amaryar… Na jefomusu tambayar baki dayansu… 
Murmishi iya asiya tayi karaso amaryar saa bakida labarin yaune saka ranarki Leda yayanki anwar… Aike amaryar sati ukuce…., 
Ji nayi kafafuna ba zasu iya dauka taba… Girgiza kaina nayi ko tunani na ne ke fadamin karya…. Nan da nan naji cikina ya juya tare da gilmawar wani bakin duhu daga idanuna… 
Bansan ya akayi ba  sai jinayi Ana shekamin ruwa… Na dawo hayyacinsa tare da sanin wata irin ajiyar zuciya da kuka mai karfin gaske “innalillahi wa inna ilahir rajiun.. Dan Allah karku hadani da anwar ba mutumin kirki bane ba mu dace ba.. Wlh karya yakeyi jikina yakeso bani ba… Ya Allah ka dafawa rayuwata…. “
Tun ummah ta harzuka ta dauko mucciya tayi gadan² kaina zata bugamin “barin in IdA kasheki  zarah kafin bakin cikinki ya kasheni…. 

Da sauri gwaggo kwazo ta rike ummah… Iya asiya ta, shigar da ni  daki.. Ta kwantar dani akan katifar tarufe dakin Dan tbbas tasan umma  masifar zafine da ita zata iya shigowa ta bugamin mucciyar.. Ba abinda ya dameta….. Maman boy

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button