NOVELSUncategorized

YAR SADAKA 1&2

???????? *’YAR SADAKA..*????????


*STORY & WRITING BY…*
         *BY*
*MOMN SULTAN*


*DEDICATED TO…..*
*MMN AMATULLAH*


*SPECIAL GIFT TO…*
*MMN FAREESAH**Alhamdulillah Naga comments iya comments,hakan ya nuna kuna da buqatan cigaba da labarin,,Dan a gaskiya nayi mamakin jama’an dakemin magana akan nasasu a group duk da ban Bude ba,,sedai inanan Zan Bude sabo zanyi adding zafafa wadanann Nike karanta comments nasu inajin nishadi lolxx*


*BISMILLAHIR_RAHMAANIR_RAHIIM*

*Yadda nafara a sa’a Allah kabani ikon gamashi lafiya,,Allah Ka Bani ikon rubuta abinda al’umma zasu amfana dashi su nishadantu su kuma ilmantu,ya Allah kasa duk Wanda ya karanta yaji farin ciki koda Yana cikin baqin ciki*

*A koda yaushe ina alfahari daku masoyana masoya labarai nah,,iya wuya muna tare da yar dar Allah*????????????????1⃣&2⃣
Yanzu kawu bazaka bar tafiya Saida nono ba,,kaduba yadda Aisha ke fama da danyen jego Amma a haka kuke yawo kasuwa kasuwa,,Baka tsoran sanyi ya kama yarinyar nan..


Shiru kawu yayi kallan dattijuwar dake magana tana qara riqe yar qaramar yarinya a hannunta,,Wanda bazata wuci wata 3 ba..

Yakumbo kiyi hakuri ki cire soyayyan yarinyar nan a zuciyanki,,tinda kinsan dole sai mun fita Saida nono kafin mu Sami abinda zamu sa a bakinmu,,kinga Aisha dauko kwaryar nono can mu tafi kinga Rana nayi..

Dasauri Aisha ta dauko zani ta miqa hannu biyu,, yakumbo kawota mu zamu tafi,, murmushi yakumbo tayi tana cewa..

Badan nasan halin nijlah da kuka ba,Aida na riqe diyarnan harkuje Ku dawo,, murmushi Aisha tayi tana girgiza Kai,,nan yakumbo tabasu nijla suka kama hanya suna sauri kowannensu dauke da kwaryar nono suka tafi titi..

Ki daga qafa Aisha kinga Rana ya cinmana gashi yau kasuwan cika yake,, banaso muyi kwantai” kayya Mai gida,,yanzu duk saurinnan danake Baka gani,,ni wallahi bayana har ciwo yakemin..

Kiyi a hankali kinsan dai bamu da yadda zamuyi,,turo Baki Aisha tayi tana gyara goyon nijlah tace,,nifa yinwa nakeji,,ace tin safe Mai Rai besa komai a cikinsa ba,ga nono ana damuna dashi.

Shiru kawu yayi suna cigaba da tafiya Dan daga kauyensu zuwa titi ba qaramin nisa gareshi ba..

Sunyi sa’a suna zuwa titi suka samu mota,,dasauri suka Shiga kayansu a hannu ga nizlah dake faman kuka a Baya..

Da shigansu mota ya tashi ana harhada kudin mota..

Drive kayi hakuri na koki arziqi,wallahi kaga banida ko Sisi sai naira ashirin,,nasan Kai musulmine zaka temakeni” Kai kuturin uba,uban wa kike tinanin ze cikamiki kudin,,kufa matsalan tsofi irinku Kenan..

Dakyar dattijuwar ta Kada Baki tace,,kayi hakuri Ka kaini sadaka,,to bazan iyaba drive ya fada Yana masifa..

Sosai ya riqa zazzaga jaraba har Baya ganin abinda ke gabansa,,kawu ne ya Bude Baki da niyyan magana ai kafin ya qarasa jikake,,gara rann gammm..


Qatuwan Mota tabi ta kansu,,gaba daya Yan Motan suka sa salati,,ihu da kururuwa suka riqayi ba masu ceto sabida gurin bana wucewan jama’a bane,,dakyar aka samu Motan dauko Kaya suka kawo musu agaji,,

Sedai wannan hatsari yazo da tashin hankali domin kuwa duk cikin Motan,, driver ne kawai ya rage sai nijlah daketa faman kuka sabida matsan dataji a bayan Aisha Wanda tini Rai yayi halinsa..

Tini aka kwashesu zuwa hospital,,taimakon gaggawa aka Basu,inda aka samu nasaran tsayarda kukan nijlah,,ta hanyar bata madara,,shiko drive karaya ya Samu hannu da qafa..

Tini aka dauki photunan gawawwaki aka Fara yadawa a media Dan neman ‘yan uwansu..

Tare da bazawa a gidajen radio,,Malam dake zaune yasa radio a gaba Yana sauraran labaran Rana yaci Karo da wannan mugun labari..

Dagudu ya fito a daki Yana kwala Kiran yakumbo,, yakumbo dake fitowa a bayi ta fito tana Kiran,,Malam maiya faru kakemin irin wannan Kira,,kaiko yinwa bakaji, Ka iya magana da karfi haka..

Malam be iya magana ba,,sai Dora hannu da yayi aka, shikenan mutuwa tayimana zuwan sauri,,katangar da muka dogara da ita ta rushe,, subhanallah Malam kukafa kake,,meya faru,wa kuma ya mutu,,kayi saurin gayamin kafin zuciyana ta Ida bugawa,, yakumbo ta fada cike da tashin hankali..

Kawu ne,kawune yakumbo ya mutu kawu ya rigamu gidan gaskiya daga Shi har matarsa Aisha,kafin yakumbo tayi magana Inna Babar Aisha ta shigo hannu a ka tana kuka..

Tare suka runtuma zuwa asibitin,,basu sha wahala ba,aka Basu gawan kawu da Aisha tare da nijlah da Allah yasa tana da sauran kwana a gaba..


Tinda suka dawo gida aka sallaci aisha da mijinta,, Abu yayiwa yakumbo zafi,,ta Shiga cikin tashin hankali mara musaltuwa.

Bayan sadakan bakwai,Inna ta buqaci da abata nijlah Dan ta riqe tana Debe Mata kewan aysha.

Kuka yakumbo tasa tana cewa,,Inna bawai naqi bane,,sedai bazan iya Baki nijlah ba,,sabida ita nake gani kama kawu,,Sanin kanki ne tinkafin rasuwan Aisha Nike Kula da dawainiyar nijlah,,Dan a dole nake Basu iya idan zasu fita yawan kasuwan sabida kukanta.

Itama Inna kuka tasa tana cewa shikenan yanzu na rasa aishi nijlah ma bazan samu Zama da itaba,,hakuri mijin ya riqa bata Dan yaga alaman yakumbo bata da niyyan bada nijlah..

Tin bayan rasuwar iyayen nijlah yakumbo ta tattara komai nata da Soyayya ta maidashi Kan nijlah,,itace sirfe,dakau,Kai Harma da wanki yi take sabida Kula da nijlah,da sai Mata madara,,sedai duk da haka watarana bata samun kudin sai Mata madara,,haka ta riqa bin shanu tana matso nono me dumi tana Bama nijlah..

Akwana a tashi har nijlah ta Fara girma tana qara wayo,,kowa ya kalla nijlah saiya tausaya Mata,,Dan kowa yakanzo dandali ya sai Abu Banda nijlah danko biyar bata samu,,haka zata dawo gida tasa yakumbo gaba tana kuka tana birginia,,wata Rana sai dai yakumbo itama tasa kuka suyi tare..

Malam bashida karfi balle ya riqa aiki Yana Nemo kudin Kula dasu,, gashi kawu Shi kadaine dansa kuma Allah yamasa rasuwa..

Sosai abubuwa suka rinchabemusu,Abu Daya ke taimakonsu shine wadatar zuci da godiyan Allah.

Al’adan wannan fulani shine auran da yara kanana,duk yarinyar data haura shekara sha 3 tayi da yawa,,shiyasa malam yake Allah Allah nijlah ta Kai shekara 13 ya auran da ita…       **************


Mummy Dan Allah ki janye wannan matakin da kika Dora,,wallahi bazan iya tafiya da Yasmeen wannan kauyen ba,,

Mashkur Kenan kana tinanin Zan Bari Ka tafi service ba aure,,gashi amsa bikinnan, na kuma tabbata idan akace saika dawo dole a daga biki,,ni kuma abinda banaso Kenan.

To Amma mummy shikenan saina kama da tafiya da Yasmeen bayan kinsanta da kyankyami,,salan muje da ita ta kasa cin abinci,,Azo arasa mafita,,koma dai menene kaje kasan yadda zakayi,ko a daura aurenka Ku tafi ko kuma Ka fasa zuwa service..

Eyyah mummy nah, shikenan nayi karatu abanza,, mummy kiji tausayina,,

Turesa mummy tayi tana masa Wani irin duka,,kafin tafara Magana cikin fada,, mashkur narasa meyasa bakasan ayi maganan aure Sai anyi magana kace Baka shirya aure yanzu ba,, mashkur ka Duba arziqin da Allah ya bamu,ka Kalli gidannan Na tabbata munada kudinda zamu aura Maka Mata Dari Idan anayi,,toka gayamin menene Shirin Naka..

Shiru yayi Yana sauraranta sedai yakasa cewa Koma,,jiyake ajikinsa Baya buqatar auren yanzu sedai ya Rasa ta hanyar daze sanar da mahaifan nasa..

Kai dubani mashkur bafa kai daya ka Iya miskilanci ba,,da sainayi Magana kasani gaba kana kallo, Idan Yasmeen ce bakaso kaduba yara Yan Mata gasunan ‘ya’yan masu kudi irinka, saika aura Baka tsaya kana batamana lokaci ba,, Shiru mashkur yayi nan ma be Iya Magana ba..

Kai mashkur mummy ta daka masa duka a cinya”kaga Idan bakada lafiyane ka gayamana..

Wannan Karan haushi tambayan Mummy ta bashi Dan haka ya turo Baki kama mace Yana kallanta”” eh mana Naga da anyi maganan aure kake hade giran Sama Dana qasa,,ko wani ne yace kafara soyayya da Yasmeen..

Mummy Nima abinda nagani kenan,ni mace inasanta sedai banshirya aure yanzu ba,,to mummy ba sekumin hakuri ba zuwa lokacin Dana shirya,,Amma kunqi,,sai dagamin hankali kuke,,to wallahi akayi Wasa saina fasa aurenta kowama ya huta..

Riqe Baki mummy tayi tana sauraran Dan autan nata,,

Cigaba da magana yayi, ahankali Yana qara kwantar da kansa jikin mummy,, mummy Dan Allah ki amince nayi tafiyan nan,kinga Dana dawo sai ayi auren hankalinki ya kwanta…

To amma,,hannu yasa ya rufe bakin mummy cikin Wasa yace,,addu’a kawai zakimin kinji sweet mom..

Anya ko mashkur zaka girma yanzu ni kake dannewa haka Hadda rufemin Baki,,eyyah mummy duk wannan girman nawa..

To ai Naga zaka….kash mummy Naga dai barewama da danta take Wasa a dawa..


Nan dai yayita bata Baki harta hakuri da niyyan Daya dawo za’a daura auren..


Yau ya kama Monday kuma yaune mashkur ze tafi kauyen kankan Dan yin service,,tin asuba yake shiri har dai yaga..

Karfe 10 daidai ya fito get mummy riqe da yar akwatinsa tana ja,, drive ne ya amsa da sauri yasa a mota yayinda mashkur ya rungume mummy..

Mummy zanyi missing dinki,,nida zaki yadda tare zamu wuce,, murmushi Mummy tayi irin na manta tana shafa kansa tace,,Aida Yasmeen Ka dauka zaifi sauqi Dan gaskiya ni banasan Zama cikin Fulani,sabida kasan banison nono.

Shikenan mummy nizan wuce sabida mu 3 aka tura can,nasan sauran suna jirana,kafin ya rufe Baki wayanshi yafara ringing.    *Comment & share,na rasa meyasa bakusan sharing dakun karanta saiku barshi a watanku,,pls ku riqa turawa wasu group’s kodan jamaa su amfana*


*Comment ne kadai zesa nacigaba da typing,kunsani ina iya 3 page a Rana,kuma kuke sani hakan*

*Momn sultan ce*✍✍✍

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button