NOVELSUncategorized

RUWAN JAKARA 7

*BRILLIANT WRITERS ASSOCIATION*                  
( _pens of freedom, home of exceptional and magnificent writers_)                 *RUWAN JAKARA*………….    
    { _idan baa sha abirni ba asha akauye_)} 
                *~LITTAFIN~*???????? 

*MARYAM HAMISU YUSUF (maman boy*) 

~TRUE LIFE STORY~
“`page“` *7*Adai² katafaren kofar gidan Alhaji mansoor  ne mai adai²tar ya  Ajiyemu nida ummah…
 Habar hijabinta  ummah ta warwaro ta fiddo naira dari data sha squeezing da tsufa  tabiya mai adai²tar  muka nufi gate din gidan…. 
Wata uwar harara umma taballomin yadda taga fuskata a hade duk  da ina yawaita yin yake wanda yafi kuka ciwo.. Amma hakan bai Hana  umma ta ganoni ba “kinsan zarah wlh idan muka shiga gidannan banga kinsaki fuskarki ba na rantse da Allah mai rabani dake sai Allah idan muka koma gida”… 


Dolena na saki Dan guntun murmishi ina kokarin mayar da kwllr da take gudanyowa a kurmin idanuna “kiyi hakuri umma Kai nane keyimin ciwo shiyasa”… 
Nafada hakan ina Dafe kaina tare da yamhtsa fuskana… Dan inaso ta yarda dani… 

Tabe baki naga tayi da aIamun zancen nawa bai shigetaba “kyaji dashi ni dai kinji abinda na fadamiki”…  Ta idar da maganr tana knocking din gidan….. 
Bamu jima atsaye ba mai gadin ya budemana kasancewar ya shaidamu… Ya saka kaitsaye ya barmu muka shigo harabar gidan… 
Umma idanu kawai take budewa tana karewa  tsaunin gidan da shikoki da suka kara kawata gidan da kallo  tare da jinjina kai… Abubuwa da dama a ranta da take kissimawa Har muka isa babban falon gidan …. 
Da sallama muka shigo falon nasu… 

Mommy muka tarar zaune akan daya daga cikin kayatttun kujerun falon suwaiba na zaune akan carpet na sanya mata lalle a fingers dinta…. Satan hannun kuwa ta rike remote control tana canja chennel 
Fuskanta babu yabo ba fallasa ta amsa saidai tunda ta amsa bata kuma kallon inda muke ba bare ta bamu Gu mu zauna… 
Ummah kam bata jira abinda zata fada ba ta zauna akan kujerar sai washer baki takeyi tare da kai gaisuwa wurin mommy… Itakam tana amsa mata cikin iko… 
Lallai mommy badai nuna sarauta ba. Musamman a inda take ganin ya kamata ta nuna ta din… 
Jikina a matukar sanyaye na zauna akan carpet din ina gaida momy… 
Shiru falon ya dauka idan banda sautin plasma din dake falon da dakeji… 
Umma kam kokarin jan momy da fira kawai takeyi duk da ta fahimci ita din miskila ce… 
Nan da nan momy ta hade face dinta.. Ranta ya soma baci… Idan akwai abinda ta tsana zama inuwa daya da talaka… Talaka ma marasa galihu irinnmu… 
Zame hannun ta momy tayi daga lallen da suwaiba ke saka mata ta have upstairs ranta a bace… 

Sai a, lokacin suwaiba yasamu ta kawomana abinci da lemuka masu sanyin gaske… Ta baje mana akan carpet…. 
Kadan na soma ci shima dan guduna sababin umma na tee hannuna… Umma kuwa ci takeyi tana zuba Santi… Suwaiba na biyemata dan suwaiba itama badai surutuba… 

Saida umma taji takai geji kafin ta ture abincin… Tare da gyatsewa tana fadin “garin dadi na nesa inji ungulu data leka Masai…. 

Momy na fita daga falo bata zame ko ina ba sai bangaren ya anwar domin tana cikakken yakinin tunda ya shigo bai fita ba… 

Ranta a bace take knocking din kofar sa…. Ta jima tana knocking kafin ya bude sanye cyake cikin farar singlet da gajeran wando… Zuba mata rinannun idanunsa wadanda suke alumshe  yayi da suka koma kalar gauta.. 
Jinginar da kansa yayi a kofar yana sauke numfashi.. 
Dasauri momy taja da Baya  tare da toshe hancinta sakamakon wani irin hamami da taji ya ziyarci Han cin ta… 

Rai abace tasoma magana “anwar bazaka daina yimana shaye² agida bane.. Duk can waje abinda kake yi bai ishekaba saima shigo har gidane… “

Dakyar ya saki wata ajiyar zuciya “momy me yakawoki pls”…. 
Amaimakon amsa mata tambayarta ya jefo mata wata tambayar…. 
Harara momy ta watsa masa cike da masifa take magana “wadancan sharar da kasa suka debo jiki suka zo su nake so kaje ka sallama… “… 
Tunda ta fada hakan yasanya ko suwaye take nufi…murmishi yayi tare da kokarin dai²ta nutsuwarsa “yes zarah  but mom sudin bashara bace… Kisan irin sunan da zaki kirasu “.. 
Harara takuma ballamasa.. 
Yana kokarin rufe kofar ta rike sakamakon yan mata da ta gani su biyu a dakin nasa daya na akwance akn bed ta lullube jikinta da blanket.. Daya kuwa daure da towel da alamu wanka zata shiga… Bakidayansu bazasu wuce shekaru 25 ba…. 
“Dakata meneke shirin gani ne anwar….? “. 
Dafe kansa yayi tare da tokare kofar da faffadan kirjinsa yassni sarai ta tsani kawo matan da yakeyi a gidan….. 
“Just go mom… I will come back soon “… 
Ya idar da maganr tare da rufe kofar baki daya… 
Haka ta baro bangarennasa sai sababi takeyi…. 
Anwar na shiga dakin… Ya shige toilet… Bakidaya yan matan suka koma rufo masa baya… Duk yadda sukaso ya biyemusu basu Samu ba… Saboda yafison.. Ya Fito da yar sauran nutsuwar dayake tunanin tayi saura a brain dinsa a yayinda dazai gana da kykkyawar fuskar zarahnsa… 

Farar jallabiya yasaka ya feshi jikinsa da manyan manyan turarukan dake zube aga an mirror… 
Kowace ya cake mata 50k “oya out… Idan ban neme kuba kada tunkiyar da talaucinta yakara ciyota ta nemoni”….. 
Ya fada tare da watso musu kudin… 
Dariya daya da ya cikinsu tayi “no worry munsan dai mu ruwa ne abokan aiki dole sai damu… 


Baibi takansu ba ya fice.. Ya nufi general falo…. 
Ta kofa r baya suka  bi suka tfi…. 


Tun a matattakalr benen idanunki suka gauraya da juna… 
A matukar razane na dauke idanuna daga nan anwar dan bazan iya jurar kallon jajayen idanunsa ba… Kirjina ya tsananta bugawa tare da tsoron shi kansa anwar din…. 

Dasauri suwaiba ta tashi tashige kitchen… 
Dai² kujerar da zai dinga fuskantar fuskana ya zauna… Suka gaisa da umamh wacce bakinta yakk rufuwa,… Idanuna akasa na gaidasa… Duk da yaso saka idanunsa acikin nawa amma naki… 
“Ummah daman zarah bata sakewa ne acikin mutane? “…. 
Ya fada hakan ya na kallon fuskana still…. 
Murmishin takaici ummah tayi “kasan kanwar taka kamar tayi zama a kauye.. Haka Fatima take… “

Wata irin ajiyar zuciya ya saki.. Farincikina cika azuciyarsa.. A randa yanaji ya gama samun nasara akaina 
. dan ya fison yarinya sosai irina.. Kuma wacce idanunta basu budeba.. Bareni da yake da yakinin babu namijjn da ya taba rike hannuna bare kuma yasanni a matsayin ya mace…. 
Lumshe rinannun idanunsa yayi tare da lasar soft lips dinsa ya waresu akaina ya na murmishi..
“Ummah gaskiya Fatima kyakkyawace sosai ta ta da karancin shekaru… But… Anya cikin familynmu akwai wacce takai zarah kyau”… 
Yayi maganar cikin salon barinkinsa da  yaudara… 
Washe baki ummah Kala man anwar nayimata dadi… 
Nikam zuwa yanxu nakosa nabar gidan danakejinsa tamkar  a kurkuku nake….
Duk yadda yaso yajani da fira na kanne na zama tamkar wacce bata magana… 
Ummah kuwa tamkar takaimin duka saboda takai ina daya cika mata zuciya… 
Tashi mukayi zamu tafi hakan yayi dai dai da shigowar suwaiba dauke da mooper a hannunta..
Kiran da anwar yayi mata yasa tayi saurin gurfana a gabansa… 
“As from today awurin girki akara yawan abinci.. Daga gobe zarah zata dinga zuwa tana karbar abinci… “. 
Ya fadi hakan yana safar kallona… Ya mayar da kallonsa ya ummah dayake shirin fara godiya yace “ummah… Bazaki same girki ba.. Cinku da shanku yana a gidannan “… 
Zubewa ummah tayi tana dinga yiwa anwar godiya nikam kunyar abinda ummah keyi ya isheni.. Tamkar anwar din ba a matsayin danta yakeba irin wannan biyayya da take mishi haka…. 

Da kansa yayi driving dinmu zuwa gida duk da banaso hakanba kawata kwata.. Har amota umma godiya kawai takeyi tare da share hawayen dadi… 
Ta gefen ido yake kallona.. Ya lura nakasa sakin jiki dashi.. Wanda hakan Sam baya masa dadi… Saida ya biya damu katon super market ya mask mana kudi na ban mamaki akan kayan masarufi iri²
Nikuwa ya shakomin wata Leda makil da tsadaddun chocolates da nay ikan kayan zaki…. 
Muna Dira kofar gidanmu nayi saurin bude motar saidai yadda muffin Yaki budewa ya tabbatar min motar a rufe take…. Komawa nayi na zauna nayi shiru.. Jmaah kam harta shige gida… Izuwa wannan lokacin na fara gano manufar yaya anwar akaina  su ya faruq suna zaune a majalissar su 
.. Babu abinda sukeyi sai gardandamu akan siyasa.. Dan tuni su yaya faruq sun zama yan bangan siyasa…. 

Su shigar da jibgin siyayyar kayan abincin da anwar ya siyo mana.. Da  dari biyar² ya bisu sai godiya suke zuba masa… Ya faruq kuwa dubu biyarya basa… 
dawowa cikin motar anwar yayi ya zauna… Ta re da zuba min rikitattun idanunsa ya kafawa lips dina idanu yana imagining yadda zaiji sucking dinsu.. wata irin zazzafar sugar shaawata na kuma bijiromasa…. Atake idanunsa suka kara rikidewa…. 

“Ka budemin motar inaso zan fita… “


Yadda nake maganr zai tabbatar maka a atsorace nake musamman yadda voice dina ke rawa
…. 


Yawan comments yawan typing 

Maman boy

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button