Uncategorized

SAMEEHA N

*_????SÂMÊÊHÂ????_*

            (N)

Ruwan na ratsa su,ta jima tana zubawa idonta ruwa har taji yajin ya ragu amma zugin sa kamar yanzu ake ƙara zuba mata yajin a idon ta,ta fito daga bayin ta koma nata ɗakin ta tattare kukar da kuɓewar da momy ta zazzaga mata akai da tsintsiya tasa faka a hankali ta kwashe tayi fallo dan ta zubar,da zuwa ta zuba a mazibin sharan dayake cikin fallon ta sake komawo ɗakinta ta ɗauki gyaɗar soyayya ta buɗe cikin sauri tana ƙarewa gyaɗar data soyu ido wani zazzafan hawaye ya silalo daga kunci ta,ta furta””


     “”Ummaaaaaa……….


a hankali kuka yasake ƙwace mata ta kifa kanta akan fullo tashiga yinsa yanda ranta yakeso,ta ɗauki kusan minti (30),tana hawaye daga baya ta fara jefa ƙwayar gyaɗar cikin bakinta tana ci tana kuka haɗe da kiran Umma Mona har da Ya jummai da Abba kamar wace aka tsikara ta miƙe zumbur da gudu ta fito daga ɗakin tayo hanyar da zata kai ta ƙofar fita daga fallon ƙafarta har sassarfa take tana harɗewa waje guda har ta

ƙaraso dai dai ƙofar ta ɗaga ƙafarta ta dama zata jefa ta waje,wani abu kamar mashi ya ciki ɗaya ƙafar Sameeha ta zube atake a ƙofar ɗakin tana gunjin kukan da babu hawaye ko ɗigo ɗaya sai tashin sautin sa kaɗai kakeji a ɗakin.

      kasa ɗagowa tayi ta miƙe ƙafar wani abu takeji na shigarta kamar zai farke mata ƙafa da ƙyar ta iya riƙo ƙafar ta soma karanta””


   *”””La’illaha’ilallah’,anta subhanaka inni kuntuminal zalimin*



Sau uku ta na nanatawa cikin ikon Allah abin yafara saukowa daga ƙafarta yana fita kamar hayaƙi taji nauyin da ƙafar tayi ya sauka nan da nan ta mike tsaye tayi shiru tana tunanin chan kuma ta jefa ɗaya ƙafar waje ta furta”””


   *”””Bisimillahir’Rahmanir’Rahim,*



        ta fito daga ƙofar kai tsaye tayi bakin get tana sauri sauri gudu gudu kar a hango ta,ta ɗora hannunta kenan akan mariƙin ƙofar get ɗin aka maka mata wani abu a kanta ko juyowa Sameeha bata iya yi ba ta sulale ƙasa ta suma.






*********





Kai tsaye mona ta Shigo gidan ko sallama babu ta faɗo kan cinyar Umma dake gyara wake da sauri Umma ta ture mona daga kan cinyar ta,tana”””


“Maza tashi ki koma inda kika fito ki koyo sallama zaki zo ki karya mun ƙafa.


kai Umma ni da ba nauyi gareni ba taya zan ƙarya miki ƙafa wallahi nagaji ne dayawa shi yasa,kuma Allah nayi sallama kafin na shigo sai dai idan baki jiba ai ko redio nan Umma ta hana ki jin sallamar.


ni dai banji ba ki tashi kije kiyi mana ko bakya son mu sami ladan ni dake ne,ƙarar redio bazata hanani jin sallama ba badai kiyi ba kawai zaki ce.


Allah nayi Umma amma a hankula nayi saboda raina gaba ɗaya ba daɗi nakeji ga jikina duk yayi sanyi,gaban umma ne ya yanke ya faɗi amma sam bata nunawa mona ba ta dubi mona da ita ma dubanta take yi ta ce.


ashe kanki kika yiwa sallamar kenan yanzu sai ki tashi kiyi mana dan bamu kaɗai ne a gidan ba harda bayin Allah da bama ganin su.


babu yanda mona ta iya ta ajiye ledar da momy ta bata ta,miƙe ta dawo dai dai ƙofar shigowa da sallama a bakinta ta shigo gidan da karfi,Umma ta amsa tana hararar mon tace””



to fasa min kunnan kiji daɗi saboda na ce ki koma kiyi sallama,mona bata ce komai ba ta nemi waje ta zauna ta janyo ledar gaban ta Umma ta cigaba da gyaran waken ta bayan ta kashe redio.


   Turarukan biyu mona ta ciro daga ledar ta buɗe jakarta ta zaro bandir ɗin kuɗin ta matso daf da Umma ta ajiye a gaban ta,ta ce”””



gashi wai inji momy tace na kawo muku,da zafi Umma ta ɗago kai ta dubi turaren da kuɗin da mona ta ajiye a gabanta ta sake duban mona da gaba ɗaya tsoro ya kamata ta ce”””


Me na faɗa miki kafin ki bar gidan nan maimuna,ashe kunnuwanki basajin magana daga abinda na gargaɗeki shine kika amso kika taho zunge zunge gobe ma rana ce maga inda zaki koma.


dan Allah Umma kiyi haƙuri karki hanani komawa wallahi ko ganin yaya Sameeha ban yi ba,kuma Allah ba laifina bane laifin momy ne.


babu ruwan momy idan kin ƙi amsa zata takura miki ne ko dukanki zatayi?


A a,cewa tayi in faɗa miki ke da ita ai ɗaya ne kuma ba’a maida hannun kyauta baya.



shiru Umma tayi tana nazarin maganar da mona ta faɗa gaskiya ne,a fili ta ce.



kika ce bakiga Sameeha ba,to ina ta,tafi.



kin haƙura zaki barni na koma idan an kwana biyu idan ma ya Sameeha tazo ma shikenan ba sai najeba,Umma ta kuma cewa.



naji na amshi uzirinki,ki bani amsar dana tambaye ki,gyara zama mona tayi ta kwashe duk abinda yafaru a gabanta da wanda momy ta faɗa mata ta faɗawa umma har saƙon turaren su na Abba da na Umma da kuɗin da momy ta bawa mona ɗin, shiru umma tayi ta kasa gyara waken dayake gabanta tana tunanin maganganun mona data faɗa mata daga ƙarshe ta share maganar ta miƙe ta shige ɗaki tabar mona da gyaran waken a tsakar gidan,koda Abban su mona ya dawo Umma ta bashi saƙonsa da murna ya amsa yana jinjinawa momy dan turaren na da tsada na manyan mutane ne ya kai dubu (20),ina ma bai fi ba ya ya ƙarasa da tambayar ya Sameeha take,anan Umma take sanar masa rashin lafiyar Sameer ɗin,Abba ya ce”Allah yabashi lafiya Umma ta amsa haɗe da murmushin ƙarfin hali zuciyarta cike da damuwa ta fito daga ɗakin.






*******






A hankali Sameeha ta fara buɗe idon ta,har ta buɗeshi gaba ɗaya cikin hanzari ta yunƙura zata miƙe ganin ta a wani ɗakin ƙasa da tukwane da aka lilliɓesu da jan ƙyalle taji ta katamau an ɗaure ƙafafunta da hannayenta da wata igiya mai kaurin gaske ga wasu tarin fatoci na dabbobi kalla kalla a ɗakin da layu manya manya ta soma ƙoƙarin ƙwance igiyar da bakin ta, tana shirin yin kuka, wani guntun mutumi ne ya faɗo ɗakin baƙi mumuna da uban gashi a fuskarsa himm babu ƙyan gani ko annuri babu,shigowar mutumin tayi dai dai da shigowar wata mata da ganinta yasa Sameeha zabura ta saki kukan daya tsaya mata arai ta fara””


Momy dan Allah kisa a kwance ni,duk abinda kike so zanyi miki wallahi bazan kuma ketara maganar kiba ko gidan yanzu kika ce na bari,zan barshi har abada karki sa acutar dani akan abinda bani da hakki akansa, momy menayi miki,mena tsare miki a rayuwa dakike son hallakin momy???



    a hankali momy ta tako daf da inda Sameeha ke ɗaure taja wani ɗan murmushi ta ce”””



“ke kuwa kika tsare mun dukkan farin cikina,kika rusa burin dana ɗauki tsawon lokacin ina tana dinsa, kika lalata shirin dana ɗau shekara da shekaru ina shiryawa,shin kin san wahalar danasha kafin nasamu kan kowa a gidan har da naki,wai shin Sameeha ke wace ce,waye yake tsare ki ya taimake ki akan sharrina har kika samo damar danake da buƙata shekara da shekaru,to bari kiji wallahi yanzu kinzo inda babu wanda ya isa yazo bare ya taimake ki babu wani mahalukin mutum ko aljanin da ya isa ya lalata shirin da muka shirya akan ki da abinda ke tare dake har abada sannan nayi yanda nake so dake daga ƙarshe ki bar duniyar ma gaba ɗaya na huta.



Lah…………karki kuskura ki ambaci Allah anan ki san a inda kike,momy ta juya ta dubi Sarkin hatsabibai ta ce cikin kakkausar murya”””



“”Kana gani tana shirin lalata mana shiri.



Me kike sauri akai wanda zai gagare mu babu wata kalma ɗaya da zata iya furtawa anan face *WAYYO ALLAH* da kinyi haƙuri dakinji inda zata sauka ina fatan kin gamsu da bayanina,sannan cikin dake jikinta zuwa yau da yamma ko cikin dare zamu bawa ɗan aiken mu kyauta ya cinye daga baya mu ɗora abinda ya sauwaƙa akai.

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button