NOVELSUncategorized

TARAYYA 27-28

Page 27
Haske writers associated????
Aje basket din hannunta tayi tana sake qaqalo murmushi tace,
Ashe kece babu lafiya baby baifadaminba kawai yafadamin numbern dakin ne,
Sannu ya jiki?

‘Daga kai tayi ahankali tana cewa,
Alhmdllh.
Shiru dukkaninsu sukayi babu wacce numfashinta bai fita da sauri sbd ganin ‘yar uwarta.
Suhailat cikin jikin rumanah din take satar kallo dan kuwa batasan haka take kishin mijintaba saidataga cikin dan kuwa Allah ne kadai yasan irin ciwo da radadin datakeji axuciyarta saidai tana qoqarin fincikewa sbd batason zubarwa da kanta qima a gurin mijinta da ‘yayanta harma da rumanar datake kishiyarta.
Rumanah kuwa jitayi duk atakure take da wanzuwar suhailat din gashi nurse tagama abinda takeyi ta fice.
Hakanan takejin bata iya kallonta sosai sbd ganin take zuciyarta da shaidan zasu hasaso mata maheer atareda suhailat din Wanda hakan na matuqar girgiza zuciyarta.
Cikin kulawa suhailat ta miqe ta bude basket din ta hada mata black honey tea sai pancakes da toasted chicken datai laushi sosai ta zuba matasu a plate tareda aje matasu yanda zata iya ci.
Cikin sanyin murya rumanah tace,
Nagode amma inaso zanshiga toilet….
Wayar suhailat dince tayi ringing ta sauka da sauri sbd mum ‘dintace batareda taji mai rumanah din ke fadaba ta fita dan amsa wayar.
Ganin ta fita yasa rumanah sauke qafafunta qasa ahankali ta sauko ta nufi toilet din dake dakin ahankali sbd jiri.
Tana kaiwa tsakiyar dakin wani irin jiri ya dibeta daidai shigowarsa dakin.
Saida tajita jikinsa tayi saurin sakin ajiyar zuciya sbd ta sadaqarda cikinta yagama zubewa idan ta fadi.
Bude idanuwanta data rintse tayi takallesa cikin fargaba sbd ganin kallon dayake mata murya na rawa tace,
Toilet zanshiga.
Yanda ya dauke gira daya yasa tasan menene azuciyarsa tayi qasa dakai cikin tsananin sanyin murya tace,
Yi hakuri bansan zan…..
Just shut up”””yafada yana daukarta gaba ‘daya ya bude toilet din suka shige.
Sauketa yayi ahankali kamar kwai
Ta dago takalli fuskarsa taga ba wasa tasaki 6oyayyan murmushi cikin zuciyarta tana cewa,
Ko fushi kyau yake masa. 1
Brush ya miqa mata ta karba tayi tana kallonsa sbd kallonsa yanxu matuqar nishadi da nutsuwa yake bata tana gamawa ya miqa mata towel tareda jawota jikinsa yazare mata kayan jikinta itadai ido kawai take binsa dashi sbd yau ko ta6insa nutsuwa yake bata.
Da yake shower ce bai shigaba ita kadai tashiga tayi wankan shikuma yana tsaye gaban mirror yana goge inda rigarsa ta baci da ruwan allurar dayaje yiwa wani patient kafin yashigo dakin.
Tana gama wankan ta dauki towel ta daura tareda zare shower cap din kanta ta tsaya gaban madubin da yake dubawa tana fuskantarsa.
Wasu kayan yasanya mata saidai bada bra ba duk saiyaji ransa yabaci da yanda kayan patients din sukai mata kyau amma bai nunaba yasake gyara mata gashinta ya dauketa suka fito tana kallonsa gira ‘daya ya dauke yace,
Wannan kallon fa matata tana nan so be carefull bata hadani da komaiba.
Murmushi daya bayyana fararen haqoranta tasaki tareda sake qanqamesa tana fitarda sautin murmushinta ahankali
shima murmushin gefen baki yasaki suna kawowa tsakiyar dakin sukai ido hudu da suhailat dake zaune tayi musu kallo ‘daya ta dauke kai tana qoqarin danna kira awayarta.
STORY CONTINUES BELOW
Saurin saukowa jikinsa rumanah tayi sbd taji nauyin suhailat din sosai koba komai ka girmama mai girmama kansa ta zauna bakin gado tana suuke kanta qasa.
Kallo ‘daya yayiwa suhailat yagano halinda take ciki yaji tabasa mugun tausayi sbd baisan lokacinda ta dauka azauneba gashi sun dade aciki gashi qila batasan yana cikiba.
Hannu yakai yakamo hannunta tareda miqar da ita ya matsota gabansa yana kallon cikin idonta datake qoqarin 6oye halinda take ciki cikin kulawa yace,
Are you ok?
Kai ta ‘daga masa batareda yakallesaba
Yayi kissing forehead dinta yace,
I will be in my office””yasa kai yafice yabarsu.
Jawo abincin rumanah tayi tafara ci hannunta na rawa sbd rawar da zuciyarta keyi.
Suhailat ma batareda takalli fuskar rumanah din ba tace,
Zantafi office am getting late Allah yasauwaqa.
Tana gama fada ta dauki handbag dinta ta fice hawayen datake riqewa suka gangaro mata ko office dinsa bata biyaba ta wucewarta saidata isa office dinta ta rufe siririn kuka ya balle mata amma dannesa tashigayi sbd bataga dalilin kukanba tunda dama tasan tanada kishiya meye abin jin zafi dan taganta da ciki bayan itama Allah yabata nata ‘yayan ba juya yayitaba.
Saidata samu nutsuwa tayi masa text tace ta wuce office and she’s very late so shiyasa bata biyo office dinsaba.
Tana ficewa rumanah ta aje breakfast din sbd dama turawa kawai takeyi.
Yana gama karanta text dinta ya aje wayar tareda lumshe fararen oily eyes dinsa.
Yinin ranar dukkaninsu a darare sukayisa sbd kowanne da abinda ya maqalewa zuciyarsa.
Baibar asibitin ba yau sai qarfe goma na dare lokacinda rumanah tayi bacci kenan.
Koda yakoma gida suhailat bata nuna damuwar komaiba a fuskarta itada ‘yayanta su maqalqalesa suna masa oyoyo
Yayo wanka bai sauko cin abinciba sbd yaci pizza tareda rumanah a asibiti.
Koda suhailat taji cewar yayi dinner murmushi kawai tayi tace,
Ok bari nacewa Carolina tasaka a fridge. 2
Kodata dawo dakin yana kwance wayarsa a kunnensa yana magana da antynsa wadda yake biwa tana qara basa haquri akan abinda yafaru shidai kunnuwane kawai nasa baya iya zuba dogon zance.
Kwantawa tayi ajikinsa tareda rungumesa ta rufe ido alamar bacci
Yayi mamaki sbd basu cika kwana daki dayaba koman dare wani lokacin dakinta take komawa ta kwana.
Koda yagama wayar tayi bacci yakalli fuskarta kafin ya lumshe idanuwa fuskar rumanah daya baro tana barci tafado masa yasake rungume suhailat ajikinsa yana kamar rumanah ce ajikin nasa. 9
Washe gari ma tare sukaje asibitin saidai ko zama batayiba gaisawa kawai sukayi ta wuce gurin aikinta sbd ganin irin kallon da maheer kewa rumanah sbd sai yanxu cikinta yafito dakyau sbd kayan da aka canxa mata sunso kamata saikuma basu kama ‘dinba.
Bayan wucewar suhailat nurse ‘din dake kula da ita ta fita sbd idan yashigo fita sukeyi.
Kallon ‘dan cikinta yayi batareda ya amsa gaisuwartaba ya dauki file dinta yafara dubawa.
Qamshinsa daya cika dakin ta shaqa tana lumshe ido cikeda qaunarsa mai zafi dake cin zuciyarta.
Yana gama dubawa ya kalleta a miskilance yace,
Did you bleed today?
Girgiza masa kai tayi kala kallonsa ya juya yafice baisake cewa komaiba.
Numfashi tasauke a sanyaye ta zame takwanta.
Kwananta biyar a asibitin akayi discharging dinta tunda suka kamo hanyar gida numfashinta ke fita da qarfi
Jin tayi tafison komawa Libya gurin ammy hankalinta zaifi kwanciya acan. 1
Suhailat ma tunda tasan zasu dawo gida anyi discharging dinta jikinta yake sanyaye.
Carolina tagyarawa rumanah dakinta tun na farko sosai.
Qarfe goma sha biyu suka iso tareda driver sbd shi theatre zaishiga.
Koda suka iso gidan tuni kayanta dayayi shopping online suka iso har ankai mata dakinta
Itadai suhailat tana bedroom dinta sbd ita bata iya munafurciba arayuwarta bazata iya tsayawa tana rawar jiki akan abinda tasan ba haka bane cikin zuciyarta,
Abinda tasani shine bazata qi rumanah ba bakuma zatai munafurcin nuna mata soyayyar qaryaba saidai zata mutumta ba sbd mijintane ya ajiyeta kuma as along as babu Wanda ya wulaqanta wani acikinsu to zasu zauna lafiya babu takura saidai batai alqawarin ringa zaunawa suna fira tareba gwaradai nesa nesa da juna saisunfi mutunta junansu. 4
Carolina ta tarbota daga mota suhailat na dakinta suka shigo kai tsaye daki rumanah ta nufa ta zauna bakin gado tareda sakin ajiyar zuciya ahankali.
Ta jima a zaune kafin tamiqe tashiga toilet tayo wanka tazo tasaka doguwar riga mara dogon hannu ta daure gashinta ta saka qaramar hula mara nauyi tayi sallar ishai da akai tana gurin wanka tana idarwa ta fito palo tana qoqarin sakin fuskarta ta nufi kicin inda tajiyo muryar suhailat tana waya taje daukar Abu a fridge.
Gama wayar suhailat tayi ta juyo tana Murmushi tace,
Patient ya jikin?
Barka da dawowa gida.
Jiki alhmdllh naji sauqi sosai
Ina su amah banji hayaniyarsuba gashi naga lokacin dawowarsu daga school haryayi nisa da wucewa.
Sundawo tun dazu suna study room sbd Anfara musu exams.
Jinjina kai tayi tareda ficewa tabar kicin din
Itama suhailat tana gama abinda takeyi ta fice.
Yini guda adaki tayi abinta ko abinci ma daki Carolina ke kai mata.
Ita kuwa suhailat abinda ke gabanta kawai takeyi ba damuwar komai.
Baidawo gidanba sai cikin dare lokacin kowa gidan yayi bacci sama ya nufa dakinsa kai tsaye yashiga yayi wanka harya gama shirin kwanciya ya kwanta babu suhailat bare rumanah da dama baisa ran zata iya zuwaba.
Washe gari koda yayi shirin office harya wuce rumanah na dakinta bata fitoba saida dukkaninsu ta tabbatarda suntafi gurin aiki ta fito.
A dining ta yi breakfast dinta ita kadai tana gamawa tadawo palo ta zauna tana kallo duk da hankalinta ba akan kallon yakeba duka.
Ahaka dai ta wuni ita kadai sai Carolina dake dan tayata fira sama sama sbd ba laifi Carolina din tafi sakewa da ita akan suhailat sbd tafi sake mata.
Suhailat ce tafara dawowa da yamma lokacin tana palon zaune tana gyaran farcenta sanyeda blue skinny jean da red loose top sai gashinta dake dunqule cikin hula red cikin sakewar fuska sosai tayi mata sannu da zuwa.
Cikin sakewa itama ta amsa tana cewa,
Duk kadaici ya dameki babu kowa sai Carolina kuma ita bawani sakewane da itaba.
Nikuma naji dadin kasancewa da ita sbd ba laifi muna sakewa da juna sosai.
Dakinta ta nufa tayi wanka ta sanyo white skinny jean da white chiffon shirt tareda black hula ta fito palon ta zauna kusada rumanah tana cin pancakes suna kallo.
Sallar magrib tasa rumanah barin palon ta nufi dakinta.
Sallah tayi magrib tayi bata fitoba saida tayi sallar ishai ta shiga wanka tana fitowar Carolina tayi knocking ta sanarda ita ana jiranta suci dinner.
Straight skirt tasaka black da black d&g shirt hasken fatarta yafito sosai cikin black shigar ta dauro siririn black scarf tafito tana fidda siririn qamshi ga cikinta daya fito cikin kayan sosai.
Tana fitowa kallo daya suhailat tayi mata ta dauke kai tana murmushi tace,
Ok everybody time for dinner.
Suka miqe fammah na maqale da hannun rumanah suka nufi dining suka zauna.
Abinci sukeci cikin nutsuwa itadai dama tafadawa Carolina noodles With veg zataci saigashi bata wani ci sosaiba saima papaya drink datake ta sha.
Coat dinsa riqe ahannu yashigo palon yana waya.
Kallo daya yayiwa dining area ‘din yaji gajiyar daya ‘debo ta ninku.,
Da gudu suhailat ta taso ta rungumesa tareda basa peck tana cewa, 8
Welcome baby.
Rungumeta yayi shima yana kallon idon rumanah datai saurin ‘dauke ido akansu jikinta na rawa.
#mamuhge
TARAYYA
    wattpad@mamuhgee
    haske writers association????
28
Not edited.
Miqewa tayi tabar dining area din ta nufi dakinta tana dafe ‘dan qaramin cikinta dataji yana murdawa.
bayanta yabi da kallo yanajin jikinsa na qara saki sbd wata irin kewarta dake cinsa.
Zame suhailat yayi daga jikinsa ya nufi stairs ya haye dakinsa.
Yana shiga ko zama baiyiba yashiga wanka yafito yashirya ya kwanta tareda rufe idanuwansa sbd jin yanda zuciyarsa ke wani iri.
Koda  suhailat ta shigo tagansa tayi tunanin yayi bacci tayi kissing lips dinsa ahankali kafin tafice takoma dakinta.
Kwance take iduwanta arufe saidai Sam bacci yakasa daukarta data rufe idanuwanta shi take gani lokacinda ya rungume suhailat
Takasa yakice abin aranta
Ta jinjinawa suhailat ranar data gansu a asibiti amma bata nuna jin zafintaba bayan tasan saita fita jin zafinma.
Duk yanda taso dannewa ta yakice kasawa tayi saidata saki wani irin siririn kuka tana tura kanta cikin pillow taji ‘dan sauqi aranta.
Qanqame pillow dinta tayi.
Taji kewarsa na sake shigarsa saidai tasan yanacan da matarsa
Wasu siriran hawaye suka sake gangaro mata ta rufe ido tana sakejin nauyin da zuciyarta ke mata.
Acikin su uku suhailat ce kawai tasamu yin bacci cikin nutsuwa da kwanciyar hankali.
Washe gari bai fita aiki da wuriba dan kawai yasan time dinda take fitowa daki
Koda yayi wanka ya shirya cikin kayan shan iska na zaman gida palon qasan yazo ya zauna yana karanta news paper yana shan black tea.
Koda suhailat taga bazai fita aiki yau Ba itama fasa zuwa tayi sbd ganin bazata iya ficewa tabarsa ba sbd gaba daya kwanakin basu sakeba sbd baida time kullum sai dare yake dawowa.
Doguwar rigace mai shape sosai da budadden wuya ajikinta orange sai tayi mata kyau sosai ta qaraso inda yake zaune ta zauna kan jikinsa tana kallon fuskarsa daya ‘dago idanuwansa ya zuba mata.
Murmushi tasaki tareda shafo fuskarsa tana cewa,
Na canzane?
Maida kallonsa ga karatun dayakeyi yayi yana cewa,
You’re getting late for office.
Sake shafo fuskarsa tayi tana murmushi tareda matso da fuskarta ga tasa sosai tayi kissing lips dinsa tace,
I’m missing my husband so zan zauna tareda shi a gida yau””taqarasa fada tana hade bakinsu.
Kallonta yayi itama shi take kallo tana kissing ‘dinsa
Sanin tunda yadawo babu abinda yashiga tsakaninsu yasa ya sake shigar da ita jikinsa yana cigaba da kissing ‘dinta yana shafo wuyanta zuwa qirjinta.
Jin shiru ya tabbatar mata da duk sun fice ta tashi kanta ko dankwali babu dan dama tayi wankanta,sanye takeda palazzo trouser brown da cowl neck top mara nauyi ko kadan ta fito palon tana tunanin yanda zata samu damar waya da ammy itadai gida takeso sbd zuciyarta zata iya tarwatsewa anan.
Bata lura dasuba saida takusa isa daf dasu idanuwanta suka sauka kansu
Gabanta yayi wata irin mummunan faduwa jiri ya ‘dibeta saura kadan ta fadi yasaki suhailat dake jikinsa cikin zafin nama ya tareta ta fado jikinsa
Atake ya lumshe ido tareda sakin wani muguwar 6oyayyar ajiyar zuciya.
Kallonsa suhailat tayi idanuwanta nacikowa da hawaye kafin takalli rumanah din wadda tuni nata hawayen suka 6alle mata ta zame jikinta ta juya dakinta tana ‘danne kukan dake taso mata
Wlh batason nan tafison gurin ammy,
Nan zuciyarta bugawa zatayi gwara ta tafiyarta inda bazata riqa ganinsa da matarsaba.
Qofar dakinta ya qurawa ido yanaji kamar zuciyarsa zatabar qirjinsa ta shiga dakin
Ko juyowa baiyiba ya nufi stairs ya haye sama sbd idan ba itace ta kusantosaba ayanxu komai na iya faruwa na 6acin rai.
Zubewa suhailat tayi a gurin itama tareda sakin kukan datake riqewa ahankali,
Soyayya batai mata adalciba data yiwa mijinta mugun kamun da har abada bazata samu gurbi azuciyarsa ba dan tagani tun ba ayau ‘dinba soyayyarsa mai tsanani ce akan kishiyarta.
Miqewa tayi tabar palon tana shiga dakinta ta toshe baki tana sake sakin wani siririn kukan.
Rumanah ma kukan takeyi sosai tana dafe cikinta dake motsawa gabaki daya kewar ammy takeji.
Ganin zaman gida qara hargitsa masa lissafi zaiyi ya dauki keys din mota yasauko yafice gaba ‘daya.
Yini guda cur kowaccensu a dakinta tayisa
Carolina ce ta kaiwa rumanah abinci sbd dama tasaba kai mata kullum matuqar bata fito ci ba Wanda tsatsauran umarni ne daga maheer daya bata akan koyaushe ta tabbarda rumanah taci abinci.
Suhailat bata fitoba sai maraice sosai lokacinda taji hayaniyar su amah sundawo daga Islamic classes da ake kaisu daga school kullum shiyasa sai yamma suke dawowa.
Wanka tayi ta gyara fuskarta sbd idanuwanta dasuka kumbura ta sanyo dogon yellow skirt da red floral lace top ta fito tafara qoqarin sakewa cikin ‘yayanta tana tambayarsu school dakuma abinda yafaru a school ‘din sbd tasamu tasake daga damuwarta tun kafin yadawo yagano halinda take ciki.
Itama rumanah jin hayaniyarsu a palo yasa ta tashi tayi wanka ta sako purple doguwar riga mai guntun hannu kanta sanye da hula bata shafo komaiba a fuskarta sbd tata fuskar bata kumbura ba tadaiyi jajir kasancewar tafi suhailat zama fara sosai.
Idonta kawai ta sanyawa kwalli tafito.
Kallo daya sukaiwa juna kowacce ta qaqalo murmushin dole suhailat tafara cewa,
Hayaniyarmu ta tayar dake ko?
Murmushi tayi tareda girgiza kai tace,
Aa dama natashi kawai jin gidan tsit yasa nayi tunanin Baku dawoba yanxu ina jin hayaniyar nace bari nafito.
Shiru sukayi kowacce na ‘dan jansu amah da zance sama sama ahaka dai kuma suka maida hankalinsu ga kallon wani series da akeyi THE LEGACY a cwtv.
Lokacin sallah nayi suka miqe kowa yaje dakinsa yayi sallah babu wadda tasake fitowa sai bayan sallar ishai.
Kiransa suhailat tayi sbd jin kozai dawo da wuri su jirasa dinner yace su jirasa zai dawo sbd yasan dole itama rumanah zata jira.
zaune suke Suna fira sama sama rumanah takalli suhailat cikin jin nauyi tace,
Kozaki kiramin ammy tunda nazo ban gaishetaba.
Kallon mamaki suhailat tayi mata saidai ba hurumintaneba tambayar meyasa haryanxu batada waya sai kawai ta dauki wayarta dake gefenta tayi dialing numbern ammy tamiqa mata tabar gurin data bata damar magana.
Cikin kulawa ammy data daga wayar tace,
Suhailat ya kuke?
Cikin sanyin muryar dakeson yin kuka tace,
Ammy ina wuni?
Wani irin sanyi da farin ciki yasa ammy tashi zaune daga kishingiden datake tace,
Rumanah ya kike?
Ya jikinki?
Lafiya klau ammy naji sauqi sosai,
Yaya su ummee nayi kewarku ammy inason nadawo gida.
Cikin kulawa ammy tace,
Bakyajin dadin nan ne dakikeson kidawo bayan mijinki na tareda ke ga suhailat nasan itama batada matsala.
Ina jin dadin nan din amma nafison nadawo gurinki.
Shiru ammy tayi cikin nazarin zancenta sbd tasan yanayi na zaman kishi dole wata rana akwai jin zafi amma dole zatai hkr sbd shine auren.
Murmushi mai sauti ammy tasaki tace,
Qiyi hkr rumanah kibari idan kin kusa haihuwa saiki dawo amma idan kinji bazaki iyaba kifadawa maheer din yabari kidawo gida idan kin haihu saiki koma daga baya.
Shiru tayi sbd batasan yazata fada masaba bayan qilama ya manta da ita kwata kwata ta matarsa yakeyi dama ita sbd ciki aka aureta yanxu tunda tasamu shikenan aikinta ya qare.
Hawaye suka gangaro mata murya na rawa tace,
To ammy.
Tambayarta ammy tafarayi akan lafiyarta da lafiyar cikinta daqyar take iya amsawa sbd nauyi da damuwar datake ciki.
Tana gama wayar koda ta ‘dago yana tsaye bakin qofar palon yana jifanta da wani irin kallo dayasa jikinta rawa tana hango tahowar suhailat ta miqe ta nufeta ta miqa mata wayar cikin sanyin murya ta nufi dakinta suhailat data hangi irin kallonda yake biyo rumanah din dashi ta hadiye abinda takeji tace,
Kitsaya kiyi serving dinsa dinner zanyi making wani call ne.
Tana fada ta juya takoma dakinta tareda saurin dannawa qawarta siyah kira sbd ‘daukewa kanta damuwa.
Tana shigewa daki shima ko kallon inda rumanah din take baisake yiba ya nufi dakinsa ransa na 6aci da yanda rumanah kamar gudunsa take dakuma yanayin daya hango atareda suhailat.
Wanka yayi ya shirya cikin kayan bacci farare as usual kafin ya dauki wayarsa yakira suhailat amma number busy har kusan tsawon mintuna
Dior Slippers yazuro tareda saukowa qasa ya nufi bedroom dinta yana kawowa palo yaganta tsaye bakin qofar bedroom din rumanah tayi knocking.
Tsayawa yayi yana kallonta lokacinda rumanah ta bude mata fuskarta daukeda murmushi tace,
Kina neman wani abune?
Kishigo.
Aa basai nashigoba dama baby baici dinner bane shine nace kozaki diba kikai masa kaina yana ciwo banaso nayi kaida kawo da yawa gashi gobe dole naje office tunda banje yauba.
Sauke kai tayi tana ta6a yatsan hannunta cikin sanyi tace,
Dan Allah kiyi hakuri amma bazan iya zuwaba ni tamkar baquwace anan dan haka banajin zuwana yanada wani mahimmanci zan diba nabawa Carolina takai masa.
Da mamaki suhailat takalleta idan ta fahimta daidai saitakejin yanayin maganar rumanah din kamar batason zuwa gurinsane sbd wani dalilin bawai dan tana matsayin baquwaba kamar yanda tace.
Bazata iya tsayawa takurataba dama sbd fita haqqin su biyun ne yasa tace taje dan haka babu wata damuwa tace,
Shikenan kibawa Carolina din takai masa.
Ta juyawarta tabar gurin itama rumanah dakinta takoma ta kwanta.
Juyawa yayi dakinsa yana zuwa ya zauna ransa amasifar 6ace.
Kiran suhailat ne yashigo wayarsa da farko bai dagaba saidata sake kira ya daga
Cikin kulawa tace,
Sorry baby I……bata qarasaba yace,
I need a coffee.
Ajiyar zuciya tasaki kafin tace,
Ok.
Kitchen taje tasaka Carolina ta ‘dora mata tana gamawa ta zubo masa a coffee cup ta nufi dakinsa.
Tana shiga taqarasa jikinsa ta zauna tareda miqa masa yakarba yafara sha yana duba saqo a wayarsa koda yagama yamiqa mata cup din ta ajiye kan table yace,
Ruwa.
Tashi tayi taje ta dauko masa yasha ta karba ta ajiye tareda komawa jikinsa tana cewa,
Baby are you ok?I mean you……jawota jikinsa yayi ya rungume tareda sakin ajiyar zuciya sbd jin 6acin ransa ya ragu sbd ‘yar kulawar data nuna masa.
Murmushin jin dadi tasaki tana cewa,
Ok ok I got it,you’re missing me right?
Wani irin murmushi yasakar mata sbd girma da ko yaushe take qarawa a idanuwansa dan yasan tana fadane dan tabawa kanta matsayi dakanta idanma bai bataba sbd ta cirewa kanta damuwa bayan shi yana iya hango damuwar a idanuwanta.
‘Daga kai yayi tareda matso da fuskarta tasa yana goga hancinsu yace,
I always missed this sweet voice of mrs m.a shams idan bata kusa.
Dariyar jin dadi tayi soyayyarsa naqara shigarta ya hade bakinsu yana zura hannunsa cikin rigarta ta riqe hannun tana daria tace,
Heyy kana sakani waiwayi plsss.
Daka tawa yayi yana kallonta
Tayi dariya tareda maida bakinta kan nasa ba musu yasake matseta jikinsa yana shafata daganan ya dauketa suka koma kan gado.
Kasa bacci tayi sbd tunanin baici abincinba ta tashi zaune tareda saukowa gadon ta nufi qofa ta fita taje dining ta dauki abincin datasan dominsa akayi taje kitchen tayi warming dinsa kafin ta jero a tray tareda komawa daki ta canxa riga zuwa doguwar riga mara hannu da wani sahirtattan qamshi ta dauka ta nufi saman.
Kai tsaye ta bude qofar palon tashiga ta nufi qofar bedroom dinsa tayi knocking ahankali.
Shiru babu alamar za’a bude tasake knocking lokacin suhailat ta taso daqyar daureda towel dinsa sbd bazata iya mayarda kayanta batai wankaba.
Cikin muryar gajiya tace,
Carolina is that you?
Muguwar faduwa gaban rumanah yayi
Tray din hannunta yafara rawa tayi saurin ajewa kan table din palon ta juya salin alin tabaro saman tadawo dakinta
Tana zuwa ta kwanta tana adduar bacci sbd sotake yayi gaggawar daukarta batareda zuciyarta tasamu damar wani wahalallen tunani ba.
Ita kuwa suhailat najin shiru jikinta yabata rumanah ce takasa budewa ta juya sbd babu dadi tabude mata qofa a wannan yanayin datake ciki.
#mamuhgee

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button