NOVELSSANADIN LABARINA HAUSA NOVEL

SANADIN LABARINA CHAPTER 4

***Da gudun su suka fito jin sallamar Yayan, tana tsaye a tsakar gida suna gaisawa da Anty da su Abu, Amira ce ta rungumeta, tayi kamar zata yar da ita, ta tureta tana dariya

“Ke baki san kin girma bane ba? Ko dan har yanzu baki fara kirgar dangi ba?”

Kunyace duk ta kamasu, Anty tayi kamar zatayi dariya sai kawai tayi gaba tana cewa

“Yaya muje ki huta karki biye musu.”

“Ai fa dan na kwaso gajiya, shima Alhaji ya rasa da wanda zai zo daukata sai da wanchan mahaukacin dan naki, ya dinga gudu dani duk yasa dan abincin da naci ya zazzage.”

“Wai Tariq?”

“Kina da wani mahaukacin dan bayan shine?”

“Yanayin sa ne haka Yaya.”

“Shi kansa wanda ya gado din haka muka sha fama dashi ya buga ya barni, idan zamu kwana be ce min ufffan ba, bana tanka masa haka akayi zaman nan.”

“Allah sarki, Allah yasa ya huta.”

Anty tace tana ajiye mata flask din ta da aka zuba mata kunu wanda ya zama kullum sai ta shashi, saboda sabo.

“Kunu ne? Kai Allah yayi miki albarka kinji? Allah ya baki kema masu yi miki.”

“Amin.” Tace tana murmushi, sai kuma ta fita ta bar Amira da Umaima da Yayan

“Welcome back granny, we missed you.!”

“Uwar granny din, na fada miki bana son sunan ko? Sai karyar turanci, toh turancin ma…”

“Ba kyau zagi fa Yaya.”

“Anyi, idan ban yi ba ai ban cika bakatsiniyar ba, kuma ko gobe kika sake min turanci sai na zagi turancin, a banza a wofi wayon a zagi mutum ne.”

“Bari kiga, amira sai kin taho, ni nayi gaba, Allah ya dawo da mu ai.”

Ta mike,

“Idan kin je karki dawo, yar nema kawai.”

“Almasifatu.”

Tace ta ruga da gudu, tashi Yayan tayi ta jefa mata pillow din kujera

“Yar nema, zaki dawo har in da nake ne.”

***Be shigo gidan ba sai wajen takwas na dare, lokacin Mama ta dawo, ya sameta a dakin ta, tana waya da kawarta, zama yayi akan bedside drawer ganin sa yasa ta katse wayar.

“Tariq!

Ta kira sunan sa, amsawa yayi yana kallon ta

“Ya akayi?”

Tace tana zama daga gefen gadon kusa dashi. Tun bayan da ya fara wayo halin sa ya fito sosai, babu wanda yake zama ya fadawa matsalar sa, ya sha yin ciwo a daki shi kadai babu wanda ya sani, baya taba cewa ayi masa abu sai dai ka fuskanta da kanka kayi masa amma ba wai dan ya tambaya ba, da farko halin sa ya fara tsorata ta, amma kuma kasancewar kakansa mahaifin Baban haka yake sak halin sa ya saka kawai ta hakura dan tasan biyu ce ta hadu ita kanta miskila ce. Ganin sa yanzu ya saka tasan akwai muhimmiyar magaanar da zai mata shiyasa ma ta katse wayar dan zai iya chanja shawara cikin kankanin lokaci.

“Ina jinka.”

Ta sake maimaita masa tana kallon fuskar sa

“Dama na gama hada kayan tafiyar ne, sakon da kika ce zaki taho dashi daga cikin gida.”

“Oh ai ban manta ba Tariq, gashi chan miko ledar chan, karfe nawa ne jirgin naka?”

“9am, amma da asubah zamu fita.”

“Ok, Allah ya kaimu, ya bada sa’ar abinda aka je nema.”

“Amin.” Yace yana rike da ledar, be koma ya zauna ba, hakan yasa ta gane dama abinda ya kawo shi kenan.

“Nagode.”

Yace ya juya ya bar dakin, tayi murmushi kawai tana bin bayan sa da kallo.

***Da asubah bayan sun idar da sallah ya shigo cikin gidan, ya wuce shashen Anty ya kwankwasa, suna zaune bayan sun idar da sallah ita da Jidda suna karatun al’qur’ani, ta dauka Baba ne dan shine yake shigowa da asubah ya duba duk wadda ba ita ce da girki ba, tashi tayi ta bude kofar ganin Tariq yasa ta tuna da magaanar tafiyar sa

“Ba dai har kun fito ba?” Tace tana matsa masa ya shigo ciki

Kamshin turaren sa na Versace ne ya gauraye falon, ya zauna a kujerar dake gefen kofar sannan yace

“Barka da Safiya Anty!”

“Barka dai, ka tashi lafiya?”

“Alhamdulillah, yanzu muke shirin fita, jirgin karfe tara ne.”

“Ayya, Allah ya kaiku lafiya ya tsare, ya bada sa’ar abinda aka je nema.”

“Amin ya Allah.”

Yace yana mikewa,

“Ina kwana?”

Ta gaishe shi cikin muryar ta da take kara sashi mamakin yanayin ta, hatta muryar ta kama take da yanayin jikin ta, yar firit muryarta kamar ana busa usur. Be amsa ba sarai kuma yaji sai da Anty tace ana gaishe ka sannan yace.

“Lafiya.”

A gajarce, maimakon ya tafin sa kawai ya tsaya yana nazari, wajen minti daya ya dauka yana tsaye yana juya magaanar da take masa yawo akai, kafin yace

“Anty ki kai yarinyar nan asibiti a duba ta, inaga bata da ishashiyar lafiya.”

“Jidda?”

Gyada kansa yayi

“Yes, baki ganta ba? Tayi rama da yawa kar ayi iska me karfi ta tafi da ita.”

Dariya sosai ya bawa Anty, ta dinga girgiza kanta cike da mamakin sa

“Toh shikenan Tariq, zan kaita.”

Ajiyar zuciya ya sauke kamar wanda yayi wani aiki babba yace

“Yawwa. Sai anjima.”

“Allah kaddara saduwar mu.”

Tace ya fice da sauri yana tuna lokacin da ya rage masa.

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button