SARAN BOYE COMPLETE

Baisan lokacin daya dauka ba Yana bud’ewa numfashinsa ya fara barazanar d’aukewa
“Kafin kaga wasikar Nan munyi nisa Naseer Kayi hakuri da matakin da na dauka Naseer nagaji da ace Umma iya Ni takewa Zan iya jurewa Amma yanzu ta fara tab’a min. Yaya daga ni har Kai munsan ita ta d’auke Nadeeya duk sabida kiyayyar da takemin na rasa Mai na Mata idan bamu rabu ba Naseer watarana zaka rasani ko ka rasa yayanka Wanda nasan hakan sai yafi maka ciwo akan dai rabuwar mu banida kowa sai Allah sai Kai Amma Umma ta dage sai mun rabu na dauka auren data saka kayi zai saka na samu sassauci daga wajenta Amma bansamu sassauci ba sai Karin azaba hakane yasa na yanke guduwa da yayana muje garin kaduna ko Allah zai kawo Mai taimaka Mana rabuwar mu sai yafiyemin alheri Naseer kayiwa Umma biyaya ngd da alherinka a gareni dafatn bazaka…..
Wani irin sallati Naseer ya doka cikin fitar hayyaci Bai ma iya karasa.karantawa ba ya fita aguje ya nufi d’akin Hajara takarda rik’e a hannunsa Yana “Umma shikenan kin kasheni Umma Naeema ta gudu ta barni ta tafi da yarana sabida azabar da kikee gana Mata Umma kalli takardar Nan kiga mai tace Umma Naeema ta shiga duniya da yayana innalillahi wa Inna ilaihi rajiun”
Hajara duk da batayi karatu ba karbar takarda tayi ta mik’e zaune Dan Dama a kwance take “Mai kace Kara maimaita min naji kace Naeema ta gudu da Yara”?
Umma Naeema ta gudu da Zahira da Nadeeya da Minal da Humaira Umma tace ta gaji da azabar da kike gana Mata Umma Mai na Miki kika tarwatsa.min rayuwa? Mai na Miki kika rabani da farincikina”?Umma Naeema fa Bata da kowa sai Ni Umma Mai yasa kikemin Haka idan wani Abu mahaifina ya Miki kike San ki dau fansar hakan akaina ki gayamin na nemi yafiyarki Umma uwa da tausayi aka santa umma uwa Bata cutar da dan data Haifa Umma ban miki komai ba kina ta cutar Dani Ina Miki biyayya daidai gwargwado Naeema tana Miki bansan Mai yasa Kika dage sai kin rabamu ba gashi dai ta tafi min da yara har su hud’u”
“Rufemin baki shasha lusari Kai yanzu akan mace kake kuka ka dagawa kanka hankali Haka?Kai yanzu Sabida Naeema ta rabu da Kai kake wanan surutan?anya Naseeru Haka yarinya Nan ta barka?Naeema kadai ce mace a Duniya ko sai akace ma Dan ta rabu da Kai rayuwarka tsayawa zatayi? Karka manta fa kana da kudi kana da damar da zaka auri duk kalar macen da kakeso ta kuma Haifa maka maza”
“Ni kuma Mai matsayina a wajensa kenan da kike cewa zai auri wacce Ransa keso”?
Hindatu tace tana jifan Hajara da harara
“Ga Hindatu Nan dame Naeema ta fita Naseeru”?
“Ya kake Abu kamar ba Ni na Haifeka ba”?
Naseer kallon Hajara kawai yake hawaye na zubo Masa shi kadai yasan halin da yake ciki shi kadai yasan Mai yakeji a zuciyarsa.
Juyawa yayi a hankali ya fice daga d’akin Yana dafa bango Dan sosai yake Jin jiri na neman kayar dashi
Yana fita Hajara ta hau rawar murna rabonta dataji ta a farinciki Haka har ta manta gaskiya tafiyar Naeema da yaran ya balain faranta mata take ta fara addua Allah yasa Naeema ta lula duniya Tama hadu da ajalinta ita da yaran Dan batasan Nasser ma ya kalli wani Abu da zai tuna Masa Naeema.
Palon ta fito tana washe baki ganin Bata ga Naseer a palon ba yasa ta zauna a kujera palon tana zai Gama koke kokensa ya gama ne.
Zamanta da Yan mintina Naseer ya fito daga d’akin Idonsa ya kad’a yayi jawur.hannunsa rik’e da mukullin mota yayi hanyar waje.
“Ina zakaje”?
Ko kallonta baiyi ba ya fice waje.
Gidan mmn Mannir ya Kara komawa da takardar a hannunsa Dan gani yake kila tana da masaniyar Inda Naeeema taje
Yana k’ok’arin Sallama mmn Mannir ta fito cikin tashin hankali ya Mik’a Mata takarda Yana
“Dan Allah Mmn Mannir idan kinsan wajen Wanda Naeema taje a kaduna ki gaya min nasan bazata ki Gaya miki ba sai dai kawia ki boyemin Dan darajar Allah ki gayamin idan kinsan Inda zata a kaduna ki taimakamin sabida kananan yaran data tafi dasu Naeema kanta Bata gama mallakar hankalinta ba ba kuma ta da kowa babu Kuma Wanda ta sani karki boyemin Dan Allah idan kin sani ki gayamin”?
Sosai ya kashewa mmn Mannir jiki bare data ga Yana ta hawaye
Tayi wa Naeema alkawarin bazata gayawa kowa ba Amma a yanzu Anya zata iya cika alkawarin data daukar Mata bayan taga halin da Naseer yake ciki
“Dan Allah kigayamin mmn Mannir Kar ta fada hannun mugayen mutane”?
“Naseer a gaskiya Mahaifiyarka ta takurawa Naeema Mahaifiyarka tana cin zalinta sabida tana ganin Bata da kowa mai Naeema ta Mata Haka data tsaneta nidai bansan Inda Naeema taje ba ta dai cemin zata gudu Amma bansan dgaske ta gudun ba sai yanzu da kazo kana tambayata Amma a gaskiya bansan Inda taje ba da nasani Zan Gaya maka”
Mmn Mannir tace tare da kau da kanta data tuna girman Alkawarin data daukarwa Naeema
Naseer cije lebb’ensa yayi batare da sake cewa komai ba ya tafi.
Motarsa ya bud’e ya Shiga ya zauna ya rufe Ido yana tunanin ta Inda zai fara neman Naeema wa ta sani a kaduna da zata tafi wajen wa zataje ?Mai yasa Naeema zata Masa haka ta gudar Masa da Yaya shi akaran kansa akwai abinda yake tsara musu Gaya Mata ne kawai baiyi ba Dan ya Kara shirya su gudu zuwa wani garin na Dan lokaci kafin suga ko Umma zata hakura ta kyallesu.
Amma sai gashi Naeema.ta gudu da yayansa tashin hankalinsa Bai wuce Ina zata je ba wajen wa Kuma zata sauka Bai San har Naeema tayi wayo yin wanan tunanin ba Naeema daya sani tana da tsoro Mai yasa zata Masa Haka yanzu idan sun Isa kaduna Ina xasu kwana ita da yaran tunani iri iri Haka ya ringa yi kirjinsa na Masa nauyi.
Take zazzabi Mai zafi ya rufeshi
Sai su lukman ne Suka Gane bashida lafiya Suka Kira likita a kasan layinsu yazo ya duba Naseer ya mishi allura ya Sha magani.
Dak’yar ya koma cikin gida Inda Yana Hawa sama.yaga Umma taci kwalliya ita da Hindatu fuskarsu kamar gonar auduga sai cin kaza suke Bai kallesu ba ya Shiga d’aki a ranar ko runtsawa baiyi ba washegari da sassafe ya dau hanyar kaduna.
A takaice sai daya kwana uku a kaduna Yana bulayi duk da Bai San takaimaimai Inda zai ga su Naeema ba a cikin kwana uku ya zama kamar mahaukaci Dan ko wanka baya yi balle ya samu cikakken bacci.
A ranar daya kwana biyar a kaduna Yana yawon nemansu Naeema Tasha tasha.unguwa unguwa ya yanke zuwa garin su Naeema Dan Haka kawai yaji kuma zuciyarsa ta karkata can.
Naeema
Duk da sauye sauyen da aka samu a garin na cigaba hakan Bai Hana ni Gane unguwarmu ba rabona da garin tun rasuwar mahaifina da Mahaifiyata kaina tsaye gidan Mai unguwa na nufa da su Zahira da har kuka suka ringa min da Sunan sun gaji.
Sosai na ringa adduoi a Raina Akan Allah yasa Kar Mai unguwa ya canjamin sabida Yana ganin iyayena sun rasu.
Ga mamakina muna Isa ya.gane Ni Suka Kuma Mana tarb’a Mai kyau Inda naji wani irin kwanciyar hankali da nutsuwa Wanda rabona ma danaji Haka Zan iya cewa tun kafin na auri Naseer.
Sai da muka huta daddare ya aika a kirani Inda ya hau tambayata mahaifinsu Zahira dafatan lafiya yagani da Yara.
Kuka na fashe dashi na tsinci kaina da karyar Naseer s’akina yayi
Sosai ya nunamin baiji dadin abinda ya faru ba ya min nasiha akan na rungumi kaddara zasu rik’eni tunda banida kowa sun Kuma Yi zaman mutunci da mahaifina Amma fa sai.na mayar dasu Zahira Dan bazai iya rikesu ba baima Kamata na taho da yaran gabadaya ba.